Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Jabir Mustapha Sambo

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu na yau sai kuma gobe idan da rai da lafiya.

  2. An sallami shugaban dakarun juyin juya halin Iran daga aiki

    Mehr

    An sallami shugaban hukumar leƙen asiri na dakarun kare juyin juya halin na Iran daga aiki.

    Hossein Taeb ya jagoranci hukumar leƙen asirin tun lokacin da aka kafa ta a (2009).

    Zuwa yanzu ba a san dalilin sauya shi ba. Amma a baya bayan nan an samu jerin mutuwar wasu sojoji da masu bincike da ke da alaƙa da dakarun na Juyin Juya halin da ba a bayyana ba.

    Yanzu an nada Mista Taeb a matsayin mai ba da shawara ga babban kwamandan rundunar.

    Yanzu Birgediya Janar Mohammad Kazemi ne ya maye gurbinsa a matsayin shugaban hukumar leken asirin.

  3. An kama korarren shugaban 'yan sandan Malawi kan cin hanci

    .

    Hukumar da ke yaƙi da Rashawa a Malawi ta kama tsohon babban jami'in ƴan sandan ƙasar, kwana biyu bayan tuɓe shi.

    Ana tuhumar George Kainja da hannu a badaƙalar da ta shafi wasu kwangilolin gwamnati.

    A ranar Talata shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya kori Mr Kainja bayan hukumar yaki da rashawa ta ACB ta ambaci sunansa cikin jerin sunayen jami'an gwamnati sama da 50 da suka karɓi kudi daga attajirin Birtaniya ɗan asalin Malawi Zuneth Sattar - wanda ya musanta zargin.

    Hukumar ta ce an kama Mista Kianja kan karɓar cn hancin na wata kanglar da ta shafi samar da kayan abinci ga ƴan sandan Malawi.

    Mista Kainja ya gurfana gaban kotun Malawi inda ya musanta zarge-zargen. An kuma bayar da shi beli.

  4. Yan tawayen Tigray na rokon a bude bankuna da layukan waya

    BBC

    'Yan tawayen Tigray da ke arewacin Habasha sun yi kira ga tarayyar turai na ta matsa wa gwamnatin kasar wajen ganin harkoki sun dawo kamar yadda aka saba a yankin da ake fada.

    Daukacin yankin ya kasance ba tare da wutan lantarki da harkokin bankuna da kuma layukan sadarwa na tsawon watanni.

    Hakan kuma na faruwa ne kuma duk da yarjejeniyar da bangarorin da ke fada suka cimma a watan Maris na na ganin an kai kayan agaji yankin.

    Bayan yarjejeniyar, an samu karuwar kayan agaji da ke zuwa Tigray, inda fada tsakanin gwamnatin kasar da kuma 'yan tawayen yankin ya sanya miliyoyin mutane da ke bukatar agajin gaggawa.

    Wannan sanarwa daga 'yan tawayen Tigray din, na zuwa ne bayan ziyarar da kwamishinan tarayyar Turai kan kare afkuwar bala'i da bada agaji, Janez Lenarčič ya kai yankin a baya bayan-nan.

  5. Khaby Lame ya zama wanda ya fi kowa yawan mabiya a duniyar TikTok

    .

    Haifaffen Senagal kuma fitaccen dan TikTok Khaby Lame ya zama wanda ya fi kowa yawan mabiya a duniya cikin masu amfani da manhajar.

    Yana bidiyonsa ba tare cewa kala, yana kwatanta masu amfani da TikTok da na Charli D’Amelio.

    A yanzu Khaby na da masu bibiyarsa miliyan 142.8 a manhajar, idan aka kwatanta da D’Amelio's 142.3

    A watan Nuwambar 2020, D'Amelio ta zama ta fi kowa yawan mabiya inda ta haura miliyan 100.

    Khaby ya bude shafinsa na TikTok a watan Maris na 2020 yayin annobar korona bayan an kore shi daga aikin kamfani a Italiya.

    A shafinsa yana yin bidiyo masu abin dariya da ke nuna yadda ake yin abubuwa masu wuya babu gaira babu dalili.

  6. Halin da ake ciki a Afghanistan

    Getty Images

    Hukumomin Taliban a yankin Afganistan da ya fuskanci mummunar girgizar kasa da ake kyautata zaton ta kashe mutane fiye da dubu, sun ce an kawo ƙarshen aikin neman masu sauran kwana .

    An yi fargabar cewa mutane da dama ne suka makale a baraguzan gidajensu a ƙauyukan da girgizar kasar ta shafa da safiyar Laraba.

    Sai dai gwamnan lardin Paktika na riƙo ya shaida wa BBC cewa masu aikin ceto sun samu isa dukkan yankunan.

    Ruwan sama da aka tafka da ya lalata hanyoyi da hanyoyin sadarwa ya kawo cikas ga ayyukan agaji.

    Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce ta aika kayan agaji ga mutanen da girgizar ta shafa.

    EPA
  7. Mayaƙan ƙasashen waje da ke taya Ukraine yaƙar Rasha

    Ukraine ta shafe shekara 100 tana cikin yanayin yaƙi.

    Tun daga lokacin, sojoji fiye da 20,000 na ƙasashen waje daga ƙasashe fiye da 50 suka tafi Ukraine don taya ta yaƙi da Rasha.

    Su waye su, kuma me ya sa suke sa rayuwarsu a haɗari? Wakilin BBC Olga Malchevska ya samu damar shiga ɗaya daga cikin sansanonin sirri da ake bai wa waɗannan mayaƙa horo.

    Danna hoton da ke kasa don kallon bidiyon:

    Video content

    Video caption: Mayakan kasashen waje da ke taya Ukraine yakar Rasha
  8. Hedikwatar tsaron Najeriya ta umurci rundunonin soji su kori sojoji marasa da'a

    .

    Hedikwatar tsaro ta fitar da wani gargadi ga wasu jami’anta da ake zargi da nuna rashin da’a da nuna wasu munanan dabi'u.

    Har ila yau, ta umurci shugabannin sojojin Najeriya, na ruwa da na sama, da su ‘kori’ jami’an da basu da kwarin guiwa a kansu, wajen sauke nauyin da ke kansu na hidimtawa kasa.

    Umarnin na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Mayun da ya gabata, mai dauke da sa hannun daraktan harkokin gudanarwa na ma’aikatar tsaron Najiyar Rear Admiral Muhammed Nagenu, a madadin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor.

    Shima kakakin ma’aikatar Major Akpon ya tabbatar da wannan wasika, sai dai ya ce ba wai za a kori sojojin ban aa aiki, illa dai gargadi irin na gyara kayanka, domin a cewarsa dabiu irin wadannan na iya haifar a rashin kwarin guiwa a kansu, musamman ta fuskar tura su fagen fama don tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

    Ta ce a yayin da take ke iya bakin kokarinta wajn yaki da matsalolin taron da ake fuskanta, rashin maida hankalin wadannan dakaru na iya maida hannun agog baya, a don haka ko su gyara, ko kuma yi musu ritayar, tunda zai rage babu wani zabi da ya uce hakan.

    Birgedya Janar Sani Usman Kuka Sheka, mai sharhi ne kan lamuran tsaro a Najriya, ya kuma ce akwai abubuwan cikin gida da wasu bata gari suke fita suna yadawa ga mutanen waje, ana haka a aikin damara, amma ba a korar mutum haka kurum, sai an bi wasu hanyoyi masu yawa, kuma in da hakkokin mutum sai an biya shi hakkokinsa.

    Wannan dai na faruwa ne yayin da ake unkarar zabukan 2023, kuma a cewar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, dama akan yi gargadi irin wannan a lokaci irin wannan da aka shiga harkokin siyas.

    A Najeriya dai an jima ana kokakawa kan karancin jami’an tsaro, yayin da matsalolin taron ke karuwa a kasar.

    Kuma wasu na kallon gargadi irin wannan a matsayin wani mafari na korar irin wadannan jami’ai da ake magana a kansu, abun da ka iya rage yawanus, maimakon karawa, matakin da ake ganin dole sai an dauka kafin iya shawo kan matsalar.

  9. A karon farko an samu bullar kyandar biri a Afrika Ta Kudu

    BBC

    Hukumomin a Afrika Ta Kudu sun tabbatar da bullar kyandar biri a karon farko - hakan ya sa ta zama kasa ta biyu da annobar ta bulla bayan kasar Morocco.

    Cibiyar da ke lura cutuka masu yaduwa ta kasar ta tabbatar da samun butar a jikin wani mutum dan shekara 30 da ke zaune a lardin Gauteng.

    An fara bibiyar wadanda ya yi mu'amala da su - duk da cewa babu bayanin ya yi tafiya a kusa.

    Masana kimiyya na ta kokarin ganin yadda za su samu dalilan da suka sanya ake samun yaduwar kyandar biri a duniya, ko da yake an ce cutar ba ta da alaka da tafiye-tafiyen da mutane ke yi zuwa nahiyar Afrika da ta fi kamari.

  10. Kotun Ƙolin Amurka ta bai wa dukkan Amurkawa damar mallakar bindiga

    Bindiga

    Kotun Ƙolin Amurka ta soke wata dokar New York ta taƙaita mallakar bindiga.

    Dokar ta buƙaci ƴan ƙasar da ke son lasisin mallakar bindiga da su gabatar da gamsasshiyar hujjar su ta son ɗaukar makaman, da kuma tabbatar da cewa suna fuskantar hatsari.

    Dokar da ta sanya waɗancan matakan ta ci karo da damar mallakar makamai da kundin tsarin mulki ya tanada.

    Sannan hukuncin Kotun Ƙolin ya yi tasiri a kan takaita mallakar makaman da ke aiki a wasu jihohin tare da faɗaɗa damar mallakar bindigogin.

    Alkali Clarence Thomas, wanda ya yanke hukuncin a madadin alkalai shida mafi rinjaye masu ra'ayin mazan jiya, sun ce Amurkawa na da damar mallakar "bindiga" don kare kawunansu.

    Sai dai sauran alkalan uku masu sassaucin ra'ayi Elena Kagan da Sonia Sotomayor da Stephen Breyer ba su goyi bayan hukuncin ba.

  11. An sallami shugaban hukumar leken asirin Iran

    An sallami shugaban hukumar leƙen asiri na dakarun kare juyin juya halin na Iran.

    Hossein Taeb ya jagoranci hukumar leƙen asirin tun lokacin da aka kafa ta a (2009).

    Zuwa yanzu ba a san dalilin sauya shi ba. Amma a baya-bayan nan an samu jerin mutuwar wasu sojoji da masu bincike da ke da alaƙa da dakarun na juyin juya halin da ba a bayyana ba.

    Yanzu an nada Mista Taeb a matsayin mai ba da shawara ga babban kwamandan rundunar.

    Yanzu Birgediya Janar Mohammad Kazemi ne ya maye gurbinsa a matsayin shugaban hukumar leken asirin.

  12. An kama Ekweramadu da matarsa a London da yunkurin cire sassan jikin mutum

    Ekweremadu

    Jami'an tsaro a birnin London da ke Burtaniya sun kama Sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice Ekweramadu da zargin yunkurin cire sassan jikin mutum.

    Ekweremadu mai shekaru 60 da mai dakinsa za su gurfana a gaban kotun Uxbridge nan gaba a yau.

    Yanzu haka yaron da ake zargin anso a cire ma wani sassan jikin na karkashin kulawar hukumomi.

    Za a tuhume su a kotun da zargin hada baki don cire wa karamin yaro wani sashe na jikinsa.

    Ekweremadu wanda yanzu haka Sanata ne a majalisar dattawan Najeriya, ya taba zama mataimakin Shugaban majalisar a gwamnatin da ta wuce.

  13. Rasha na dab da kwace yankin Severodonesk na Ukraine

    SEVERODONESK

    Gwamnan yankin Luhansk a Gabashin Ukrane ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai tsanani, yayin da Rasha ke ƙoƙarin ƙwace dukkanin yankin Severodonesk.

    Serhiy Haidai ya ce dakarun Rasha na ci gaba da luguden wuta a Lysychansk da ke makwabta yayin da suka ƙwace wasu ƙauyuka biyu na kudanci.

    BBC ta fahimci cewa kwanakin da ake ciki na daga cikin mafi ƙalubale ga Ukraine, yayin da Rasha ke ci gaba da ruwan wuta ta sama.

    A ɗaya ɓangaren kuma ministan tsaron Ukraine ya karɓi makamani na zamani da Amurka ta sake ba ƙasar.

    Rasha na amfani da karfin makamanta a nasarorin da take samu a gabashi.

  14. An ceto jarirai da mata hannun yan bindiga a Zamfara

    GUSAU POLICE

    Jami'an tsaro a jihar Zamfara a Najeriya sun ceto mutum 14 daga hannun yan bindiga a garuruwan Nasarawar Wanke da Rijiya da ke karamar hukumar mulkin Gusau.

    A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na Rundunar Yan sanda a jihar SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce an kubutar da mutanen ne a dajin Kuncin Kalgo, kuma sun hada da mata 10, da maza biyu, da jarirai biyu.

    SP Muhammad Shehu ya ce sun samu bayanan sirri kan inda aka boye mutanen, kuma aikin ceton na hadaka ne da wasu yan kishin jiha da ke son ganin an samu zaman lafiya a Zamfara.

    Tuni an mika mutanen ga yan uwansu, bayan jawabin manema labarai a hedikwatar rundunar yan sandan da ke Gusau.

    Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewacin maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindiga da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

  15. An kama yan Najeriya biyu a London da zargin cire sassan jikin mutum

    LONDON MET POLICE

    'Yan sanda a Birtaniya sun kama mutane biyu daga Najeriya da zargin shiga kasar da karamin yaro da nufin cire wani sashe na jikinsa.

    'Yan sandan sun bayyana sunayensu a matsayin Ike Ekweremadu da Beatrice, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu yau Alhamis.

    Kazalika 'yan sandan sun ce yanzu haka yaron na hannun hukumomin da ke kula da kananan yara.

    Sun ce an kaddamar da bincike ne bayan jami'an tsaro sun ankara kan batun, a karkashin dokar bauta da aka samar a kasar watan da ya gabata.

  16. Aung San Suu Kyi: An garzaya da tsohuwar Shugabar Myanmar gidan yari mai tsanani

    Aung San Suu Kyi

    Gwamnatin soji a Myanmar ta kai tsohuwar Shugaba Aung San Suu Kyi gidan yari mai tsananin tsaro da ke birnin Nay Pyi Taw.

    Dama Aung San Suu Kyi na fuskantar daurin talala ne a wani boyayyen wuri, bayan da kotu ta yanke mata shekaru 11 bisa kamata da laifin cin hanci da rashawa.

    Sojoji sun kifar da gwamnatin tsohuwar Shugabar mai shekaru 77 a watan Fabrairun 2021.

    Sai dai kafin nan ta rasa martabarta a idon duniya, bayan da ta goyi bayan muzgunawar da sojojin ke yi wa musulmin kabilar Rohingya.

    Hakan yasa ta rasa lambar girmamawa ta 'Nobel Laureate Prize' kan zaman lafiya.

    Yanzu haka Aung San Suu Kyi na fuskantar karin wasu zarge-zargen, da zasu sa a iya yanke mata daurin sama da shekaru 190 a gidan yari.

  17. Ba mu da masaniyar zama da ministan kwadago kan yajin aiki- ASUU

    ASUU

    Shugaban kungiyar malaman Jami'o'i ta ASUU a Najeriya ya ce ba su samu wata sanarwa daga gwamnatin kasar ba kan zama da Ministan Kwadago, da nufin kawo karshen yajin aikin da suke yi.

    Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fada wa BBC cewa Ministan Kwadago, Chirs Ngige, ne ma ya yi watsi da tattaunawar, ya kuma dakatar musu da albashi da tunanin cewa hakan zai sa su sauya matsayarsu.

    A jiya Laraba ne Mista Ngige ya shaida wa manema labarai cewa za su yi wani zama da wakilan ASUU yau Alhamis da nufin kawo karshen tirka-tirkar da ke tsakaninsu, don ganin cewa dalibai sun koma azuzuwansu.

    An shafe watanni daliban na zaune a gida, bayan gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami'o'in da gwamnatin Najeriya.

  18. Boris Johnson ya isa Kigali don taron kasashen Commonwealth

    Rwanda

    Firanministan Burtaniya Boris Johnson ya isa birnin Kigali na Rwanda don halartar taron kasashen Commonwealth.

    Kafin ya bar Landan, Johnson ya kare shirin gwamnatinsa na tura masu neman mafaka zuwa Rwandar.

    Ya kuma ce halartar taron dama ce gare shi ta karfafa dangantakar da za ta yi kyakkyawan tasiri ga kasashen biyu.

    Ana sa ran taron na Commonwealth zai mayar da hankali ne kan cinakayya, da habaka hanyoyin samar da abinci, da sauyin yanayi, daa kuma karfafa wa mata da yan mata neman ilimi.

    Burtaniya na ci gaba da shan suka kan shirinta na tasa keyar masu neman mafaka kasar zuwa Rwanda.

    Ko a makon da ya gabata sai da wata kotu ta hana jirgin da ke dauke da sawun farko na masu neman mafakar tashi zuwa Kigali.

  19. Za a fara shari'ar likitocin Maradona saboda mutuwarsa

    Maradona

    Ma'aikatan lafiya takwas za su gurfana gaban kotu da laifin sakaci kan mutuwar tsohon dan kwallon duniya Diego Maradona.

    Maradona ya mutu a watan Nuwamban 2020 a gidansa dake Buenos Aires, sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60.

    Kafin mutuwarsa ya yi jinya bayan an yi masa tiyata a farkon watan da ya rasu.

    Sai dai yan kwanaki bayan mutuwarsa ne masu shigar da kara suka kaddamar da binciken likitoci da sauran ma'aikatan lafiyar da suka yi jinyarsa.

    Kuma a bara ne suka bada rahoton cewa akwai sakaci da rashin kwarewa ga wasu daga cikin ma'aikatan lafiyar da suka yi jinyar tasa.

    Idan aka kama su da laifi a mutuwar tsohon dan kwallon na Argentina, za su iya fuskantar daurin shekaru 25 a gidan yari, kamar yadda kundin sharia a kasar ya tana da.

  20. Covid-19: Za a binciki yadda aka kashe dala biliyan daya da rabi a Ghana

    Ghana covid

    'Yan majalisar dokoki a Ghana za su binciki yadda aka kashe dala biliyan daya da rabi wurin yakar annobar korona a kasar.

    Hakan ya biyo bayan samun bayanai mabambanta da ke kunshe a takardun da ministan kudi Ken Ofori-Atta ya gabatar.

    'Yan majalisar bangaren adawa sun ce ministan ya kasa ba da gamsasshen bayanin kan yadda aka kashe kudin, a lokacin da ya je gaban majalisar ranar Laraba.

    Sai dai ministan ya ce babu nuku-nuku kan yadda gwamnati ta kashe kudaden na covid-19.

    A yanzu Shugaban majalisa Alban Bagbin ya umurci kwamitocin kudi da na lafiya su binciki yadda aka kashe wannan kudi.