Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Shariff Bappa

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin daga nan sashin hausa na BBC. Sai kuma gobe da yardar Allah.

  2. Yan majalisa na son a yi zaman tattaunawa a Ethiopia

    Daruruwan ƴan majalisar Ethiopia daga yankin Oromo sun bukaci gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi zaman tattaunawa da ƴan tawaye da domin kawo karshen rikici a yankin.

    Gwamnati ta sha yin watsi da matakin tattaunawa da ƴan tawayen na Oromo wadanda ta bayyana a matsayin ƴan ta'adda.

    Rikici na baya bayan nan a yankin ya tursasawa dubban mutane ƙauracewa gidajensu.

    A wata wasika da suka rubutawa Firaminista Abiy Ahmed, ƴan majalisa takwas sun bukaci gwamnatinsa ta kawo karshen matsalar tsawon.

  3. An ɗaure wani babban ɗan siyasa a Turkiya

    An ɗaure wani ɗan siyasar Turkiya da ake ganin babban mai hamayya da shugaba Recep Tayyip Erdogan shekara biyu da rabi a gidan yari tare da haramta masa shiga harakokin siyasa a ƙasar.

    Hukuncin ya biyo bayan samun sa da laifin furta munanan kalamai ga jami'an gwamnati.

    Rahotanni na cewa laifinsa Ekrem Imamoglu shi ne yadda a jawabinsa na samun nasarar zama magajin garin Istanbul ya kira wasu jami'ai wawaye.

    Hukuncin daurin zai haramta masa rike wani muƙamin siyasa ko kuma damar tsayawa takarar shugaban kasa.

    Mr Imamoglu na jam'iyyar RPP ya ce hukuncin ɗaurin ya tabbatar da halin da Turkiya ke ciki. Ya ce zai ƙalubalanci hukuncin.

  4. An cire Iran daga hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya

    iran

    An cire Iran daga hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke tabbatar da daidaito da kuma karfafawa mata.

    Amurka ce ta gabatar da daftari da ya nemi a jefa ƙuri'a game da matsayin Iran a hukumar.

    Mambobi 29 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da matakin, takwas kuma suka kaɗa kuri'ar adawa da matakin, yayin da 16 suka ƙaurace.

    Amurka ta nace cewa murƙushe masu zanga-zanga - da mata ke jagoranta ya saɓa wa ƴancin mata da yara.

    Jekadiyar Amurka kenan, Linda Thomas ke cewa wakilcin Iran a wannan lokacin bacin suna ne ga hukumar.

    Mutuwar Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro ne ya haddasa zanga-zangar a Iran - an kama ta ne a Satumba saboda ta ƙi rufe kanta da mayafi da kyau.

  5. Yadda ake sayar da litar fetur sama da N300 a Kano

    Fetur

    Masu ababen hawa na ci gaba da kokawa game da karancin man fetur da kuma tsadarsa a jihar Kano.

    Wannan na zuwa ne bayan da jami'an tsaron farin kaya a jihar Kano suka yi wata ganawa da dillalan man fetur din game da karancinsa.

    Gidajen mai da dama na sayar da shi kan fiye Naira 300 kowace lita, kuma kuma a rufe babu man.

    Gidajen man da ake sayar da shi a farashin gwamnati kuwa sai mutum yaci kwakwa kafin ya samu saboda dan karan layi.

    Game da wannan matsalar mai ne, hukumar tsaro ta DSS ta yi wata ganawa da dillalan man fetur a Kano cikin wannan mako.

    Bayanai na cewa wasu dillalan man na boye shi ba tare da wani dalili ba.

    Sai dai Shugaban kungiyar dillalan man IPMAN, reshen arewacin Najeriya, Bashir Dan Mallam, ya ce sun tattauna sosai da jami'an tsaron.

    A farkon makon nan ne, majalisar dokokin Najeriya ta umarci kamfanin mai na NNPC da hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur da kuma dillalan man fetur da su yi duk mai yiwuwa cikin mako guda su kawo karshen matsalar man fetur, tare da tabbatar da sayar da man a farashi man rangwame.

  6. Burtaniya ta bada damar daukan malaman makarantu daga Najeriya

    g

    Najeriya na cikin kasashen Afirka da Burtaniya ta amince su nemi aikin koyarwa a kasarta.

    Sauran kasashen da aka bai wa wannan dama sun hada da Ghana da Hong Kong da Indiya da Jamaica da Singapore da Afirka Ta Kudu da Ukraine sai kuma Zimbabwe.

    Sanarwar da suka fitar na cewa baa bukatar mutum dole sai yana da ilimin koyarwa, domin akwai tanadi na musamman na horarwa kafin a soma aikin koyarwar.

    Kawai abin da ake bukata shi ne mutum ya kasance matakin karatunsa ya kai na ka'idoji ko dokokin da ake bukata a fanin Ingilishi da kuma lissafi.

  7. An gurfanar da mutanen da ake zargi da karbar rashawa a Tarayyar Turai

    Mutum hudu da ake zargi da laifin ƙarbar cin hanci a Majalisar Tarayyar Turai za su gurfana a gaban kotu a Brussels.

    Mutanen sun hada da ƴar Majalisar Girka, Eva Kaili, wacce ake zargi da karbar cin hanci na sama da dala dubu dari daga Qatar, domin ba kasar goyon bayan siyasa.

    Masu binciken sun ce sun gano kusan dala miliyan daya da rabi - a samamen da aka kai a wurarare da dama a babban birnin Belgium.

    Eva Kaili ta musanta zargin.

  8. Na yi iya kokari na a matsayin Shugaban kasa, in ji Buhari

    SHUGABA BUHARI

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce ya yi iya kokarinsa a matsayinsa na shugaban Najeriya.

    Shugaban ya shaida hakan ne a Amurka lokacin da yake tarban Sakatare Janar na kungiyar Abu Dhabi, Sheikh Al- Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa, Fasto Bob Roberts na Amurka, a wata ziyarar da suka kai masa.

    Buhari ya ce Najeriya kasa ce mai yawan al'umma da ke fuskantar kalubale daban-daban, sai dai a tsawon shekarun mulkinsa ya san cewa ya yi iya kokarinsa.

    Shugaban ya kuma kara da cewa shawo kan matsalolin matasa su ne kashin-bayan mulkinsa domin samawa kasar makoma mai kyau.

    Bin Bayyah ya ce ya ziyarci Buhari ne, domin gayyatarsa taron da gidauniyarsa Abu Dhabi ta shirya domin karrama shugaba saboda rawar da ya taka ta fuskar tsaro da zaman lafiya.

    Ya ce ayyukan Buhari kusan sun zo guda da fafutikar gidauniyar na yaki da kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi da tabbatar da zaman lafiya da hadin-kai tsakanin addinai.

  9. DR Congo na makoki kwana uku sakamakon mutuwar mutum 100 a ambaliya

    Gwamnatin Congo ta bada hutun kwana uku domin makokin mutuwar mutane fiye da 100 a ambaliyar da ruwan sama mai karfi ta haddasa a birnin Kinshasa.

    Wannan iftila'i ya lalata kayayyakin more rayuwa dayawa a birnin ma biyu mafi girma a Afrika.

    Yawancin mutanen da abun ya shafa sun shiga yanayi na kaduwa bayan ambaliyar ta lalata gidajen su a kan tudu.

    Wannan yanayi ya tilastawa shugaban kasar congo Felix Tshisekedi baro taron da yake halarta a birnin Washington domin jajantawa al'ummarsa.

    Gwamnati ta sanar da cewa zata sauyawa mazauna wasu yankunan matsugunai domin aukuwar makamanci wannan asara sakamakon ambaliya.

  10. Wannan shi ne wasan karshe da zan buga a gasar cin kofin duniya - Messi

    Messi

    Kyaftin din Argentina Lionel Messi ya ce wasan karshe ta ci kofin duniya da za a gudanar a ranar Lahadi shi ne wasansa na karshe na gasar cin kofin duniya da zai buga a rayuwarsa.

    Dan wasan mai shekaru 35 ya ci kwallonsa ta biyar a Qatar a 2022 kuma ya taimaka wajen zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Croatia da ci 3-0 a ranar Talata.

    Messi ya ce ya yi matukar farin ciki da kammala tafiyarsa a gasar cin kofin duniya a wasan karshe.

    Argentina za ta kara da Faransa ko kuma Morocco a wasan karshe.

  11. An karrama ɗan sandan da ya ƙi karbar rashawar dala 200,000 a Najeriya

    NPA

    Cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci CAJA, ta karrama jami'in dan sandan nan da ya ki karbar cin hancin dala dubu ɗari biyu.

    Yayin taron karramawar an gabatar da lakca game da mahimmancin girmamawa da kimanta wadanda suka cancanta don karfafa hanyoyin yaki da cin hanci da rashawa a cikin al'umma.

    Taron girmamawar da kuma lakca ya gayyaci masu ruwa da tsaki a fannin yaki da cin hanci da rashawa inda aka tattauna mahimmanci da nagarta a matsayin hanyar magance matsalar cin hanci.

    Wadanda suka shirya taron sun ce a Najeriya ana yaki da matsalar cin hanci da rashawa ta hanyar kama masu aikata laifin a hukunta su ko kuma yi musu terere.

    Malam Kabiru Sa'idu Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci CAJA ya ce ba kasafai wadanda suka nuna nagarta ake nemo su a nuna musu an yaba abin da suka yi ba shi yasa suka shirya irin wannan taro.

    Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ACP Daniel Amah shi ne mutumin da aka karrama saboda bajintar da yayi na mayar da makudan kudaden da aka bashi a matsayin cin hanci da rashawa.

    Babban sufetan 'yan sandan Najeriya IGP Alkali Baba Usman wanda DCP Abubakar Zubairu ya wakilta ya ce sun yi matukar farin ciki da cibiyar CAJA ta lura da cewa akwai nagartattun jami'ai a cikinsu, kasancewar akasarin jama'a na yi musu kallon gurbatattu a ko yaushe.

    Sannan ya ce yana da kwarin gwiwa yin irin wannan taro hanya ce ta murkushe matsalar rashawa.

    Sauran jami'an tsaron da suka halarci taron kamar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta roki al'umma da su taimaka musu wajen sanar da su wadanda ke aikata cin hanci da rashawa a cikin al'umma don yakar matsalar ta kowacce fuska.

  12. China ta yi watsi da tattara alkaluman masu cutar korona

    Gwajin korona

    China ta sanar da matakin yin watsi da shirinta na tattara alkaluman wadanda ke da cutar korona saboda a yanzu babu yadda za a iya kirga su.

    Jami'an kiwon lafiya sun ce shawarar kawo karshen yi wa mutane da dama gwaji lokaci guda na nufin mutane da dama da ba su nuna alamun cutar ba, ba za a yi masu gwaji a hukumance ba, don haka ƙidaya ba ta shafe su ba.

    Daga ranar Laraba ne, gwamnati ta yanke shawarar tattara alkaluman wadanda suka nuna alamomin cutar.

    Hakan na nufin adadin yawan masu korona a China a hukumance ba zai bayar da asalin yawan wadanda suka kamu da cutar ba.

  13. Masu bukata ta musamman sun bukaci gwamnatin Najeriya ta rinka kulawa da muradunsu

    Masu bukata ta musamman

    Kungiyar masu bukata ta musamman a Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki a kan a biya mata wasu muradunsu uku.

    Kungiyar ta yi kiran ne a wajen wani taron ranar tunawa da masu bukata ta musamman da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

    Kungiyar ta shaida wa BBC cewa abubuwan da ta ke so a biya mata bukatun a kansu sun hadar da shigar da mutanensu cikin tsare-tsaren bangaren bankuna da ma sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Kasar ya kawo a kwanan nan.

    Shugaban kungiyar Isiyaku Adamu Gombe, ya ce ko kadan Babban Bankin Najeriya ba ya la'akari da wasu daga cikinsu musamman marasa gani idan zai bullo da wasu tsare-tsare.

    Ya ce a don haka suke so gwamnatin tarayya ta sa a rinka tunawa da su a dukkan wani abu da za a fito da shi sabo.

    Abu na biyu da kungiyar ta bukaci gwamnati ta yi mata shi ne batun dokar hakkin mallakar da ke gaban majalisa a yanzu, suna bukatar shugaban kasa ya sanya hannu a kai saboda akwai abin da ya shafi mutane masu bukata ta musamman a ciki.

    Sai abu na uku da kungiyar ta ce tana so a yi mata shi ne, 'yan takara da jam'iyyun Najeriya su rinka sanya manufofi na masu bukata ta musamman a dukkanin manufofin da suke son yi wa kasa ko jiha.

    Isiyaku Adamu Gombe, ya ce suna da bukatu da suke so a cika musu a don haka suna so su ji manufofin 'yan takara don su san wadanda za su zaba.

    Kidididga ta nuna cewa mutane masu bukata ta mussamman a Najeriya sun kai kashi 15 cikin dari na al’ummar kasar, wato kimanin mutane sama da milyan 30 ke nan.

  14. An soke wasu daga cikin jiragen da za su yi jigilar 'yan Morocco zuwa Qatar

    Jirgi

    Magoya bayan tawagar Morocco da ke fatan zuwa kallon wasan kasar da Faransa a ranar Laraba, sun fuskanci ɓacin rana, yayin da aka soke wasu jiragen da ya kamata su yi jigilarsu da kuma matsalar ɓacewar tikitin jirgi.

    Kamfanin jirgin kasar - Royal Air Moroc, ya soke tashin jirage bakwai a yau, yana mai ɗora laifin ga hukumomin Qatar.

    Wasu ƴan ƙasar da suka riga suka isa Qatar sun ce babu tabbas kan dubban tikitin da hukumar ƙwallon Morocco ta yi alƙawari.

    Morocco dai ta kasance ƙasa ta farko daga Afrika, kuma ta farko daga ƙasar Larabawa da ta kai zagayen dab da ƙarshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

  15. Nijar za ta dawo da tsoffin sojoji da 'yan sanda aiki don murkushe masu ikirarin jihadi

    Sojoji

    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta bukaci tsofaffin sojoji da 'yan sandan kasar su dawo aiki don taimaka mata murkushe masu ikirarin jihadin da da ma sauran 'yan ta'addan da suka addabi kasar.

    Rahotanni sun ce mako daya gwamnatin kasar ta ware don aikin rijistar sunayen tsoffin sojojin kasar da suka karbi tayinta na sake dawowa aiki don taimaka wa sojojin kasar na yanzu wajen tabbatar da tsaro da gwagwarmaya da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

    Aikin da aka fara a ranar Litinin din data wuce, zai bada damar daukar tsoffin sojoji dubu guda daga cikin wadanda suka yi ritaya tsakanin shekara ta 2017 zuwa ta 2022.

    To amma wasu sharudda da aka gindaya wa tsoffin sojojin su na da wahalar gaske in ji wasu da suke je wajen tantancewar.

    Daga cikin sharudan akwai rashin dawo da tsoffin sojojin da aka kora daga aiki saboda aikata wani laifi.

    Akwai mata a cikin jami'an tsaron da za a dawo da su bakin aikin.

    Nijar na daga cikin kasashen Afirka da ke fama matsalar hare-haren masu ikirarin jihadi, inda sakamakon hare-haren mutane da dama suka rasa ransu wasu da dama kuma suka rasa muhallansu.

  16. Majalisar Dinkin Duniya ta kadu da mutuwar 'yanci rani 27 a Chadi

    Sahara

    Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi matukar kaduwa da kuma bacin rai bayan da aka gano gawarwakin 'yanci rani ciki har da yara a wani yankin sahara da ke Chadi.

    Hukumar ta ce, rahotanni sun ambato cewa 'yanci ranin sun bar Moussoro, wani gari da ke tsakiyar Chadi a cikin wata babbar mota.

    Mutanen da suka hada da yara hudu sun mutu ne saboda kishirwa, kuma ga dukkan alamu sun yi batan hanya ne a cikin tsakiyar sahara.

    Tuni shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijrar a Chadi, Anne Kathrin Schaefer, ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalan 'yanci ranin, inda ta yi kira da dauki kwararan matakai na kare afkuwar haka a gaba.

    Hukumar ta ce tun daga shekarar 2014, sun samu adadin mutuwa da batan mutane fiye da 5,600 da ke tsallaka sahara, inda a wannan shekarar kadai aka samu mutum 149 da suka mutu a irin wannan yanayi.

  17. Abubuwa sun fashe a tsakiyar birnin Kyiv na Ukraine

    Wuta

    Jami'ai a Ukraine sun ce sun harbo jirage marasa matuka da dama a yayin wani hari da Rasha ta kai babban birnin kasar Kyiv.

    Rahotanni sun ce an ji karar fashewar abubuwa jim kadan bayan wani hari ta sama da Rashan ta kai.

    Jami'an Ukraine sun ce da alama jirage marasa matukan irin wanda Iran ta aikawa Rasha ne.

    Tun a watan Oktoban da ya wuce Rasha ke ta kai hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka kan tashoshin makamashin Ukraine.

    Shugaban babbar tashar samar da makamashin Ukraine ya ce hare-haren na ranar Laraba da Rashan ta kai ba su lalata kayayyakin aikin tashar ba, kuma hakan na da nasaba da irin jajircewar dakarun kasar ta Ukraine in ji shi.

  18. 'Yan kasar Morocco sun shirya fuskantar wasan kusa da na karshe da kasarsu za ta buga

    'Yan wasan kwallon kafar Morocco

    Al'ummar kasar Morocco sun kagu da ganin an buga wasan kusa da na karshe da kasarsu za ta kara da Faransa idan anjima.

    Morocco, ta zamo kasar Larabawa kuma ta Afirka ta farko da ta kai zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.

    Morocco ta kai wannan matakin ne bayan ta doke Portugal a makon da ya wuce, nasarar da ta ba wa mutane da dama mamaki.

    A birnin Casablanca, masu shagunan shan gahawa sun shirya shagunansu tsaf bayan sun jera kujeru da tebura da kuma hada kayan shayi kala-kala don masu kallon wasan da za a buga.

    Ana ta sayar da tutoci da kuma rigunan 'yan kwallo a yawancin biranen kasar.

    Masoya kwallon kafa a kasar sun ce ba su taba tsammanin za su ga wannan rana ba, sannan kuma wannan nasara bata kasar bace ta illahirin nahiyar Afirka da ma kasashen Larabawa ce.

    Yawancin 'yan kasar na fatan kasar tasu ta samu nasara a kan Faransa.

  19. Shugaban Ghana ya bukaci kasashen Afirka su daina 'bara'

    Nana Akufo-Addo

    Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce dole kasashen Afirka su yaye kansu daga barace-baracen da suke a wajen kasashen turai domin dawo da martaba da kima da kuma mutuncinsu a idon duniya.

    Ya ce yakamata kasashen Afirka su sauya kallon da ake musu na matalauta.

    Ya ce." Idan har za mu daina bara, sannan mu rage kashe kudinmu a cikin nahiyar, to ko shakka babu Afirka ba za ta bukaci wani taimako a wajen kowa ba,kuma hakan zai matukar kara mana kima."

    Shugaban na Ghana ya yi wannan bayanin ne a yayin bude taron shugabannin Amurka da Afirka da ke gudana a Washington DC.

    Mr Akufo-Addo, ya kuma bukaci hadin kai a tsakanin shugabannin kasashen nahiyar don samun ci gaba mai dorewa.

    Ya ce, " 'Yan Afirka sun fi jajircewa idan sun fita waje maimakon a cikin gida.Yakamata mu sani babu inda ya fi mana gida, makomarmu a matsayin al'umma daya ta dogara ne a kanmu."

    Shugaban na Ghana ya ce nahiyar Afirka, ta na da kwararru da ma'aikata da kayan aikin da duk ake bukata wadanda za a iya amfani da su wajen ciyar da nahiyar gaba fiye da yadda ake tsammani.

    Kalaman mr Akufo-Addo, sun zo ne a ranar da Asusun Lamuni na duniya ya amince zai ba wa Ghana bashin dala biliyan uku don ta farfado da tattalin arzikinta da ya durkushe.

    Gwamman shugabannin Afirka ne suke a Washington don tattaunawa a kan hada kai da Amurka a yayin da China da Rasha ke kara samun karbuwa a nahiyar.

  20. 'Yan majalisar Dattawan Najeriya sun nemi Buhari ya dakatar da aikin wutar Zungeru

    Tashar wutar lantarki ta Zungeru

    'Yan majalisar dattawan Najeriya sun nemi shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya dakatar da aikin wutar Zungeru.

    Kwamitin Majalisar kan Makamashi ne ya yi kiran bayan nazari a kan yadda aikin ke gudana.

    Shugaban kwamitin, Sanata Gabriel Suswan, a yayin zaman kwamitin ya ce ba wai ba sa so a gudanar da aikin ba ne, tafiyar hawainiyar da aikin ke yi ne ta sa suka yanke wannan hukunci.

    Ya ce, baya ga tafiyar hawainiyar da aikin ke yi babu kuma kayan aikin da ake bukata.

    Sanata Suswan, ya ce a don haka suka bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aikin har sai samar da kayayyakin da ake bukata wajen gudanar da aikin samar da wutar lantarkin a Zungeru.

    Kididdiga ta nuna cewa a tsakanin shekarar 2015 da 2022, babban layin da ke ba wa Najeriya wuta sau 98 ya na samun matsala, abin da ke jefa mutane da dama cikin duhu da kuma durkusar da harkokin kasuwanci a wasu sassan kasar.