Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin, Umar Mikail da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Ma'abota BBC Hausa, karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kamfanin fina-finan Saudiyya na shirin haɗin gwiwa da takwaransa na Faransa

    Kamfanin shirya fina-finai na kasar Saudiyya, ya sanar da cewa yana haɗa gwiwa da wani fitaccen kamfanin shirya fina-finai na ƙasar Faransa Johnny Depp, game da rayuwar tsohon sarkin Faransa na biyar King Louis.

    Kamfanin fina-finan na Saudiyya, ya ce wannan shi ne karon farko da ya yi haɗin gwiwa da ƙasashen ketare, inda kamfanin na Faransa wanda shahararren mai shirya fina-fina na Faransa Maiwenn ya rubuta wasan kwaikwayon.

    A shekarar 2021, an gudanar da bikin baje kolin fina-finai a karon farko a birnin Jiddah naƙkasar Saudiyya.

    Daga wancan lokacin an shirya-shirya fina-finai akalla 170 a yankin Larabawa da Afrika.

  3. Shekaru takwas din da suka gabata su ne mafiya zafi a duniya - WMO

    WMO

    Alkaluman Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya ta tabbatar da cewa shekaru takwas din da suka gabata, su ne mafiya zafi da aka taɓa fuskanta a duniya.

    Hukumar ta ce yanayin zafi yana ci gaba da ƙaruwa sakamakon ƙaruwar sinadarai masu ƙara yawan ɗumamar yanayi a sararin samaniya.

    Ta ce babu tabbaci ko alkaluman adadin ƙaruwar ɗumamar yanayin duniya zai iya kasa da maki 1.5 a ma'aunin zafi na celsius.

    Hukumar hasashen yanayin ta kuma ce za a samu yanayin sanyi kaɗan sakamakon tasirin yanayin La Nina wanda yanayin sanyin tekun Facific ya haddasa.

  4. Shugaban Brazil ya zargi jami'an tsaro da buɗe kofa ga masu zanga-zanga

    Brazil protest

    Shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva, ya zargi jami'an tsaro da laifin buɗe kofofin shiga fadar shugaban kasar ga dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka lalata gine-ginen gwamnati a ranar Lahadi.

    Sai dai a taron 'yan jarida da ya gabatar, Lula ya ce, babu wasu shaidu da ke nuna cewa an shiga fadar shugaban kasar ne da ƙarfin tsiya.

    Wakilin BBC ya ce matakin ya janyo zargi na cewa akwai haɗin baki daga 'yan sanda da jami'an sojoji.

    Magoya bayan tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, sun kutsa cikin ginin majalisar dokokin kasar da helkwatar kotun kolin kasar, inda suke ta kiraye-kirayen sojoji su yi juyin mulki a kasar.

  5. An kori dogari a masarautar Zazzau kan zargin fyaɗe

    Masarautar Zazzau ta tabbatar da cewa jami'an tsaro na ci gaba da bincike kan wani dogarinta da ake zargin ya yaudari wata mata da ta je fada ganin sarki, inda ya aikata lalata da ita tare da wasu abokansa.

    Lamarin na zuwa ne makonni bayan samun wani hadimin yaron sarki da yi wa wani ƙaramin yaro fyaɗe.

    Abdullahi Aliyu Ƙwarbai shi ne mai magana da yawun masarautar Zazzau, ga ƙarin bayanin da ya yi wa Mukhtari Adamu Bawa ta wayar tarho. Amma ya fara ne da bayani a kan dogarin da ya yi lalata da wata.

    Danna hoton ƙasa ku saurari tattaunawar.

    Video content

    Video caption: An kori dogari a masarautar Zazzau kan zargin fyaɗe
  6. Malaman addini a Kano sun gargaɗi 'yan takarar gwamna kan girman shugabancin al'umma

    Malamai a jihar Kano sun gargadi 'yan takarar gwamna game da girman shugabancin al'umma.

    Cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci CAJA ce ta shirya wani taron nasihaa ranar Laraba inda aka gudanar da jerin lakcoci kan girman shugabanci da yi wa al’umma adalci.

    Sheikh Mansur Isa Yelwa na sashen harkokin addinin musulunci a jami'ar Bayero da ke Kano na daga cikin malaman da suka gabatar da nasihar ga ‘ƴan takarar gwamnan da suka halarci zaman, ga kuma karin bayanin da yiwa Zahraddeen Lawan kan maudu'in da ya gabatar.

    Ku danna hoton kasa don sauraron tattaunawa.

    Video content

    Video caption: Malaman addini a Kano sun gargaɗi 'yan takarar gwamna kan girman shugabancin al'umma
  7. Ɗalibai a Malawi sun koma makaranta bayan barkewar Kwalara

    Cholera

    Hukumomin Malawi sun ce daliban da aka hana su komawa makaranta a karshen bukukuwan Kirsimeti saboda fargabar barkewar cutar kwalara na iya komawa a yanzu.

    Ministan lafiya Khumbize Chiponda ya sanar a Lilongwe cewa yanzu haka yawancin makarantu sun shirya don kula da lamarin cutar ta kwalara.

    Kasar Malawi dai na fuskantar mummunar barkewar cutar wadda kawo yanzu ta kashe mutane sama da 750.

    Kwamitin Shugaban kasa kan cutar korona da Cholera ya ba da umarnin cewa kada a buɗe makarantu a babban birnin kasar, Lilongwe, da kuma birnin Blantyre domin kare dalibai da dalibai daga kamuwa da cutar.

    Matakin ya janyo suka daga masu fafutukar kare hakkin ilimi saboda ya shafi makarantu ne kawai a garuruwa biyu yayin da aka ba da damar buɗe wasu a wuraren da suka kamu da cutar.

    Mista Chiponda ya ce a cikin makonni biyu da suka gabata, kwamitin sa ido kan lamarin ta gamsu da samun ruwa da wuraren wanke hannu da tsaftataccen bayi a dukkan makarantun, inda suka yanke shawarar sake bude su.

  8. Jami'an tsaron Habasha na farautar fursunonin da suka tsere a hari kan gidan yari

    Prison Break

    Jami'an tsaron Habasha da ke yankin kudanicn ƙasar, na farautar ɗaruruwan fursunoni da suka tsere daga gidan yarin garin Bule Hora da ke da nisan kilomita 450 da babban birnin ƙasar bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari.

    Magajin garin Girja Urago, ya faɗawa BBC cewa dakarun gwamnati na ci gaba da nema don gano su.

    Gidan yarin ya kasance wajen tsare manyan fursunoni wanda ya haɗa da mambobin kungiyoyin 'yan tawaye da aka kama bayan samamen sojoji.

    Harin, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Lahadi, ya janyo rasuwar fursunoni biyar da wani ganduroba a cewar hukumomi. Hukumomi sun ce gidan yarin na dauke da fursunoni sama da 480.

    An ɗora laifin harin kan 'yan tawayen Oromo Liberation, sai dai babu wani martani daga kungiyar.

    A baya, kungiyoyi masu rike da maƙamai sun yi iƙirarin sake fursunonin siyasa daga gidajen yari a yankin Oromia - wacce kuma ta kasance garin mahaifar Firaiministan ƙasar Abiy Ahmed.

  9. Ukraine na shirin samar da cibiyoyin hatsi a Najeriya

    Grain Hub

    Gwamnatin Ukraine ta bayyana shirinta na samar da cibiyoyin hatsi a Najeriya da sauran kasashen Afirka yayin da ta ba Najeriya gudummawar kimanin tan 25,000 na hatsi domin bunkasa alakar kasashen biyu.

    Ministan harkokin noma da abinci na Ukraine, Mykola Solskyi ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja lokacin da ya jagoranci tawagar da ta gana da ministan harkokin wajen kasar, Geoffrey Onyeama.

    Solskyi ya ce hatsi daga Ukraine zai isa Najeriya a cikin watan Fabrairu a karkashin shirin da ta tsara.

    Ya ce duk da ƴakin da kasar ke yi da Rasha, masana'antar abinci ta ƙasar na son kulla alaka da Najeriya, inda ya kara da cewa "muna matukar godiya a gare ku cewa kasar ku a shirye take ta bunkasa dangantakar".

    Ministan ya ce haɓaka irin waɗannan wuraren zai ba da damar shigo da hatsi masu inganci a cikin Najeriya kuma hakan zai yi tasiri mai kyau kan farashin kayaki.

  10. Za a fuskanci yanayin hazo na kwana uku a Najeriya - NiMET

    Dust-Haze

    Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Najeriya NiMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo na tsawon kwana uku a faɗin ƙasar farawa daga ranar Alhamis zuwa Asabar.

    Ta ce za a fi samun hazon ne a yankin arewacin Najeriya musamman ma a jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba.

    ''Hakanan, ƙura za ta mamaye arewa ta tsakiya da biranen kudanci a tsawon wannan lokaci. Ana kuma sa ran hazo da sanyi a biranen bakin teku tsakanin ranakun,'' in ji NiMET.

    Hukumar ta shawarci mutane da ke fama da matsalar numfashi da su kare kansu saboda yanayin kura da ake samu a yanzu na da haɗari ga lafiyarsu.

  11. Man United ta amince da ɗaukar Weghorst

    Weghorst

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta amince ta ɗauki aron ɗan wasan gaba na ƙasar Netherlands Wout Weghorst har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.

    Ɗan wasan na ƙungiyar Burnley mai shekara 30 ya taka leda tsawon rabin kakar bana a ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya, yanzu haka yana kan hanyarsa ta zuwa gwajin lafiya a Man United.

    An cimma yarjejeniyar soke kwantaraginsa a Besiktas.

    Weghorst ya ci ƙwallo takwas kuma ya taimaka aka ci huɗu a wasa 16 da ya buga wa Besiktas ɗin.

    A bayyane take cewa United na neman lamba 9 don cike gurbin da Cristiano Ronaldo ya bari, kuma Weghorst zai iya zama nau'in ɗan ƙwallon da suke nema.

    A ranar Asabar ma ya ci ƙwallon da ta bai wa ƙungiyar nasara kan Kasimpasa, har ma ya yi wa magoya bayan ƙungiyar baibai.

  12. Buhari ya umarci a kamo 'yan fashin da suka kashe 'yan Civil Defense bakwai

    Muhammadu Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana "ɓacin ransa" game da kisan jami'an tsaron Civil Defense bakwai da 'yan fashin daji suka yi a Jihar Kaduna, yana mai ba da umarnin a kamo su.

    Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce shugaban wanda ya siffanta kisan da "tsautsayi", ya jinjina musu "saboda sadaukar da rayuwarsu ga ƙasa Najeriya".

    "Ina jimami tare da 'yan uwan waɗanda aka kashe da kuma abokan aikinsu. Allah ya ba su da kuma hukumar haƙurin rashinsu," in ji Buhari.

    Sanarwar da Garba Shehu ya fitar a yau Alhamis ta ƙara da cewa shugaban ƙasa ya umarci sojojin Najeriya su bi sawun 'yan fashin da suka kashe su "don bi musu haƙƙinsu".

  13. Mazauna Yawunde na Kamaru na fuskantar ƙarancin gas ɗin girki

    Bayan ƙarancin man fetur da ya shafi mazauna birnin Yawunde na Kamaru a 'yan kwanakin nan, yanzu kuma ƙarancin gas na girki ne ya dabaibaye su.

    Duk da cewa ba a dukkanin gidajen jama’a ba ne ake amfani da makamashin na gas, tarin jama’a sun fara shiga cikin halin ni-‘yasu sanadiyyar ƙarancin gas ɗin, musamman daga wasu kamfanonin da suke samar da shi.

    Cikin rahoton da Mahamman Babalala ya aiko mana daga Yawunden, ya ce lamarin ya sa mutane da dama na shan wahala sosai kafin su samu biyan bukata.

    Danna hoton ƙasa ku saurari rahoton:

    Video content

    Video caption: Mazauna Yawunde na Kamaru na fuskantar ƙarancin gas ɗin girki
  14. Mahara sun kashe 'yan banga huɗu a Jihar Anambra

    Ƙonannun gine-gine a Jihar Anambra

    'Yan bindiga sun kai hari tare da kashe dakarun 'yan banga huɗu a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya anar Alhamis.

    Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a Ƙaramar Hukumar Ihiala da misalin ƙarfe 2:55 na dare, kuma a daidai lokacin ne ta samu kiran gaggawa daga mazauna yankin.

    Sanarwar da kakakin rundunar, DSP Ikenga Tochukwu ya fitar, ta ce dakarunsu sun yi nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan bayan sun isa wurin.

    "Sai dai miyagun sun kashe 'yan banga uku, suka cire kan ɗaya sannan suka cinna wa gida biyar wuta ta hanyar amfani da bam na man fetur da kuma bama-bamai," in ji sanarwar.

    DSP Tochukwu ya ce sun yi nasarar hana maharan haddasa ƙarin fitina, inda suka fatattake su da kuma ji wa ƙarin wasu raunuka.

    Jami'an tsaro da mazauna yankin kudu maso gabashin Najeriya na fuskantar hare-hare sakamakon ayyukan 'yan ƙungiyar Ipob da ke son ɓallewa da kuma kafa ƙasar Biafra.

  15. An cire wa sojan Ukraine gurneti da ya maƙale a ƙirjinsa

    Likitan sojan Ukraine

    An cire wa wani sojan Ukraine makamin gurneti a ƙirjinsa wanda bai fashe ba.

    Cikin hotunan da rundunar sojan Ukraine ta wallafa a shafinta na Facebook, an ga yadda abin fashewar ya kwanta kusa da zuciyar sojan a ƙirjinsa, wani hoton kuma na nuna likitan riƙe da makamin.

    An yi tiyatar ba tare da amfani da salon lantarki ba na electrocoagulation - wanda aka fi amfani da shi don kare kwararar jini lokacin fiɗa - saboda "makamin zai iya fashewa a kowane lokaci".

    Sanarwar ta ce soja biyu ne suka taimaka wajen gudanar da aikin tiyatar cikin nasara.

    Yanzu haka sojan yana ci gaba da murmurewa, in ji rundunar.

  16. Ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen 2023 ba - Inec

    Farfesa Mahmood Yakubu

    Shugaban Hukumar Zaɓe a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓe na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa "ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba".

    Independent National Electoral Commission (Inec) ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya, daga baya kuma a zaɓi gwamnoni da 'yan majalisar jiha a watan Maris.

    Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami'in Inec ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ɗaga zaɓen a wasu yankunan Najeriya.

    "Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi. Irin tabbacin da jami'an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma'aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu," in ji farfesan a ranar Laraba.

    Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam'iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da yawansu ya kai miliyan 93.4.

    "Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce," kamar yadda ya jaddada.

  17. DSS ta kama Doyin Okupe a hanyarsa ta zuwa asibiti a Landan

    DOYIN OKUPE

    Hukumar tsaro ta DSS ta sanar da kama Doyin Okupe, tsohon shugaban kwamitin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam'iyyar Labour.

    A cewar lauyan Okupe, Tolu Babaleye, an kama ɗan siyasar ne a tashar jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, a hanyarsa ta zuwa Landan domin duba lafiyarsa.

    Okupe wanda ya taɓa riƙe mukamin mashawarci ga tsohon shugaba Goodluck Jonatha, wata Kotun Tarayya ta same shi da hannu a badakalar kuɗin makamai a Najeriya.

    Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta ci tarar Okupe naira miliyan 13 a wannan lokaci.

    A 2019, Hukumar EFCC ta same shi da laifin rashawa kan kuɗaɗen da yawunsu ya kai naira miliyan 240.

    Mai shari'ar ta samu Okupe da aikata laifuka 26 cikin tuhume-tuhume 59 da EFCC ta gabatar a kansa.

    Ojukwu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu ko kuma ya biya tarar naira 500,000.

    A cewar lauyansa, DSS sun bukaci Okupe ya gabatar da shaidar da ke nuna cewa ya biya wannan tara.

    Sai dai DSS ba ta ce uffan kan wannan batu ba kawo yanzu.

  18. An gano karin kunshin takardun bayanan sirri kan shugaba Biden

    Biden

    Kafofin watsa labarai na Amurka sun ce hadiman Shugaba Joe Biden, sun sake gano karin kunshin wasu takardun bayanan sirri na tun yana mataimakin shugaban kasa.

    Tarin takardun farko an gano su ne a wani ofishi da ba na gwamnati ba a Washington, wanda kuma Mista Biden ke amfani da shi.

    An ruwaito cewa an gano su ne a wani gini na daban, amma ba a san ainahin wurin ba ko kuma matsayin girman sirrin takardun.'

    A ranar Talata Mista Biden ya ce, bai san abin da takardun farkon suka kunsa ba, amma dai yana bayar da hadin kai ga binciken da Ma'aikatar Shari'a ke yi a kai.

    Kwamitocin majalisar dokokin kasar masu kula da bayanan sirri sun nemi a yi musu karin haske kan takardun na Biden da kuma, uwa-uba masu yawa wadanda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya rike, lokacin da ya bar mulki, wadanda ba a son ransa ba ya mika su.

  19. Za a shafe wata shida cikin karancin fetur a Najeriya, in ji IPMAN

    IPMAN

    Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a faɗin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar.

    Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaƙa da shirin gwamnati na janye tallafin mai baki daya a cikin watan Yuni.

    Tun a shekarar da ta gabata al'ummar kasar ke fama da karanci mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewaci.

    A ranar Litinin ministan albarkatun fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu.

    A makon da ya gabata, ministan kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ya ce gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

  20. Gwamnatin Najeriya na garƙame da 'yan zanga-zangar Endsars a cikin akuba, in ji Amnesty

    Endsars

    Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukaci a saki sauran mutane da ake rike da su cikin akuba sakamakon zanga-zangar Endsars.

    Kirayen Amnesty na zuwa ne bayan sakin mutum 9 daga cikin gwamman masu zanga-zangar da ake garkame da su a gidajen yari daban-daban na Najeriya.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Amnesty ta ce binciken ta na watan Oktoban 2022 ya nuna cewa ana rike da sama da masu zanga-zanga 40.

    Sanarwar ta kuma kara da cewa abin takaici shi ne ganin har yanzu anki yarda 'yan uwa da lauyoyin masu zanga-zangar su gana.

    Zanga-zangar ta EndSARS wadda aka fara a Legas da Abuja a watan Oktoban 2020, ta kuma fantsama zuwa wasu jihohin kasar, kafin daga bisani ta rikiɗe ta koma rikici, abun da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.

    Masu zanga-zangar sun zargi jami'an tsaro da buɗe masu wuta a Lekki da ke jihar Legas, wato cibiyar inda ake gudanar da zanga-zanar, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.

    Zanga-zangar ta ja hankalin duniya sosai inda har shahararrun mutane a fadin duniya suka dinga tsoma baki suna nuna goyon baya ga masu yin ta.