Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai-tsaye ƙarshen labarai da rahotannin kenan.

    Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kaimu.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Yaƙin Ukraine: 'Yan Birtaniya biyu sun ɓace a Ukraine

    'Yan sandan Ukraine sun ce wasu 'yan kasar Birtaniya biyu sun ɓace a yankin Donetsk da ke gabashin ƙasar

    Mutanen biyu waɗanda duka maza ne na aiki da ƙungiyoyin bayar da agaji, kuma 'yan sanda sun ce rabon da a gansu tun ranar Juma'a a lokacin da suka nufi garin Soledar, inda ake tsananin faɗa.

    A ranar Litinin Dakarun sojin Ukraine suka ce suna ƙara yawan dakarunsu a Soledar, wani ɗan ƙaramin gari a kusa da Bukhmut a gabashin yankin Donbas, a ƙoƙarin da suke yi na karya lagwan sojojin Rasha da ke yawan kai garmaki a yankin.

  3. Karnuka sun kashe tsohon ɗan ƙwallon Zambiya

    Zambiya

    Karnuka sun kashe tsohon ɗan wasan Zambiya Philemon Mulala a garin Lichtenburg na Afirka ta Kudu .

    Mista Mulala mai shekara 60 ya mutu ne sakamakon cizon da karnukansa suka yi masa.

    A wata sanarwa da jami';an 'yan sanda suka fitar ta ce matar mistan Mulala ce ta gano gawarsa a cikin lambun gidansu, inda kuma nan take ta kira jami'an bayar da agajin gaggawa, waɗanda suka tabbatar da mutuwarsa.

    'Yan sandan Afirka ta kudu sun ce suna kan gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

    Tuni ƙungiyar yaƙi da farmakin dabbobi ta ƙasar ta fitar da karnukan uku daga gidansa tare da killace su a wani wuri.

  4. Saudiyya ta cire matakan Korona a aikin hajjin bana

    Mahajjata

    Hukumomin Saudiyya sun ce za su cire duka matakan da suka saka kan korona a yayin aikin hajjin bana, wanda ake sa ran gudanarwa a cikin watan Yunin bana.

    Wannan ne karo na farko da Saudiyya za ta ɗauki irin wannan matakin tun bayan bullar annobar ta korona.

    Cikin matakan da aka sanya a baya har da na ƙayyade shekarun mahajjata.

    A bara an ƙayyade cewa sai wanda yake ƙasa da shekara 65 kaɗai ne zai yi aikin hajin tare da tabbatar da cewa an yi wa mahajjata riga-kafi.

    Kusan mutum miliyan biyu da rabi ne suka yi aikin hajji a 2019 kafin a rage adadin a shakarar 2020 saboda annobar.

  5. An kuɓutar da fasinjoji shida na jirgin ƙasan Edo

    Jirgin ƙasa

    Hukumomin jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun ce jami'an tsaro sun kuɓutar da mutum shida, ciki har da ƙananan yara waɗanda 'yan bindiga suka sace a tashar jirgin ƙasa ta Igueben a jihar.

    A ranar Asabar ne dai aka kai hari tashar tare da kama fasinjoji a daidai lokacin da suka shiga jirgi domin zuwa garin Warri na jihar Delta.

    Fiye da mutum 20 ne ba a gani ba kawo yanzu, a yayin da hukumomi suka rufe zirga-zirgar jiragen ƙasa a yankin.

    Tuni dai gwamnatin ƙasar ta yi Allah-wadai da harin tana mai bayyana shi da cewa 'hari ne na jahilci'.

    A cikin watan Maris ɗin shekarar da ta gabata wasu mahara suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna tare da kama fasinjoji masu yawa.

  6. Rashin tsaro ka iya haifar da soke zaɓe – INEC

    zabe

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta yi gargaɗin cewar babban zaɓen ƙasar da ke tafe ka iya gamuwa babban ƙalubalen sokewa a wasu mazaɓun ƙasar idan matsalar tsaro ta ci gaba da addabar wasu sassan ƙasar.

    Shugaban cibiyar bayar da horo ta hukumar zaɓen Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ne ya bayyana gargaɗin ranar Litinin a lokacin duba kayan aikin horaswa na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.

    Ya ce ''duka mun sani cewa tsaro a lokacin zaɓe abu ne mai muhimmanci ga dimokradiyya , domin tabbatar da samun sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasa''.

    “Dan haka a cikin shirye-shiryen da hukumarmu ke yi game da zaɓen 2023, dole mu yi iya bakin ƙoƙarinmu domin tabbatar da cikakken tsaro ga ma'aikatanmu da kayan aikin zaɓe da kuma hanyoyin da za mu bi wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara'', in ji Farfesa Zuru.

    “Amma idan ba a magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta ba, hakan zai haifar da soke zaɓen ko kuma ɗage shi a mazaɓu da dama, lamarin da kuma zai shafi bayyana cikakken sakamakon zaɓen, abin da kuma ka iya haifar da wasu matsaloli da suka shafi kundin tsarin mulki''.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar.

  7. Fasinjoji a yankin Tigray sun ce an hana su hawa jirgi don zuwa Addis Ababa

    Jirgi

    Fasinjoji a yankin Tigray na arewacin ƙasar Habasha sun faɗa wa BBC cewa an hana su hawa jirgin sama domin zuwa birnin Addis Ababa.

    Fasinjojin sun zargi 'yan sanda a filin jirgin saman Mekelle babban birnin yankin na Tigray da hana mutanen da ke tsakanin shekara 16 zuwa 64 hawa jirgi, ba tare da wani cikakken bayani ba, sai dai waɗanda kawai za su je domin neman lafiya.

    To sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar ya ce ba su da masaniya game da wannan iƙirari.

    A ƙarshen watan da ya gabata ne babban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasar 'Ethiopian Airlines' ya koma zirga-zirga zuwa yankin bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu da suka shafe shekara biyu suna yaƙin basasa.

    A yanzu dai an fara mayar wa da yankin abubuwan more rayuwa, kamar wutar lantarki da sabis ɗin waya.

  8. Buhari ya isa jihar Yobe don ƙaddamar da ayyuka

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Yobe domin ƙaddamar da wasu ayyukan a jihar.

    Rahotonni sun ce shugaban ya isa jihar ne bayan ya halarci taron ƙaddamar da 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar Adamawa.

    Shugaban na tare da manyan hafsohin tsaron ƙasar da babban sifeton 'yan sandan jihar da kuma shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmed Lawan.

    View more on twitter

    A jerin wasu saƙonni da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce shugaban ya ƙaddamar da asibitin 'yan sanda da kasuwar zamani da kuma sabon asibitin koyarwa a Damaturu babban birnin jihar

    View more on twitter
    View more on twitter

    A gobe ne kuma Buhari zai halarci taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a filin wasa na Damaturu.

  9. An kashe mutum guda tare da harbe 'yan sanda biyu a zanga-zangar masu kishin Yarabawa

    'yan sanda

    Zanga-zangar masu kishin Yarabawa a yankin Ojota na jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta yi sanadin kashe mutum guda tare da harbe jami'an 'yan sanda biyu.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ya fitar, ya ce an garzaya da jami'an 'yan sandan biyu da aka harba asibiti domin yi musu magani.

    Sanarwar ta ce tuni rundunar 'yan sandan jihar ta aike da tawagar jami'anta domin tarwatsa masu zanga-zangar.

    Masu zanga-zangar dai sun far wa jami'an 'yan sandan tare da ƙona motoci biyu a lokacin zanga-zangar.

    Jami'an 'yan sandan sun tabbatar da kama mutum hudu da ake zargi da hannu a rikicin.

    Sanarwar ta ce an maido da doka da oda a yankin, inda jami'an 'yan sanda suka yi kira ga mutane da su koma harkokinsu na yau-da-kullum, a yayin da rundunar ta ce tana kan ɗaukar matakai domin hana ƙara faruwar makamancin wannan rikici.

  10. Zaɓen 2023: Babu wasu sunayen ƙarshe na 'yan takara da muka fitar - INEC

    Mahmood

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta ƙaryata wasu labarai da ke yawo a wasu shafukan sada zumunta da cewa hukumar ta saki sabbin sunayen ƙarshe na 'yan takara gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    A wani sako da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu jefa ƙuri'a Festu Okoye, aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita, hukumar ta ce tana so ta bayyana wa al'umma ƙarara cewa babu wasu sabbin sunayen 'yan takara da ta fitar kamar yadda rahotonnin ke bayyanawa.

    Saboda haka hukumar ke kira ga jama'a da su yi watsi da labarin. Domin kuwa a cewar sanarwar hukumar zaɓen kan fitar da sunayen ƙarshe na 'yan takara kwanaki 150 kafin ranar zaɓen kamar yadda sashe na 32(1) na dokar zaɓe ta 2022 ta tanadar.

    Sanarwar ta kuma ce tuni hukumar ta fitar da sunayen ƙarshe na 'yan takarar shugaban ƙasa tun ranar 20 ga watan Satumba, yayin da ta fitar da na 'yan takarar gwamna ranar 4 ga watan Oktoba.

    Dan haka ne hukumar ta ce babu wasu sunaye da za ta sake fitar wa a halin yanzu da ake saura kwana 46 a gudanar da babban zaɓen, sai dai sunayen 'yan takarar da kotu ta bayar da umarnin maye gurbin sunayensu.

    View more on twitter
  11. MDD ta nuna takaici kan halin ko-in-kula da Pakistan ke ciki

    Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya bayyana cewa ya yi matukar nuna bacin ransa game da halin ko-in-kula da shugabannin duniya ke nunawa wajen tinkarar ayyukan gaggawa game da matsalolin sauyin yanayi, kamar batun matsananciyar ambaliyar ruwa da ta haifar da mummunar barna ga kasar Pakistan.

    Da ya ke gabatar da jawabi a wani taron neman tallafi ga kasar Pakistan a Geneva, Mista Guterres ya ce Pakistan ba ta haifar da wani matsalolin sauyin yanayi ba, amma tana dandana kudarta na mummunan tasirin sauyin yanayin.

    Ya bukaci al'ummar kasa da kasa su samar da gagarumin tallafi don tallafawa Islamabad a kokarinta na sake gina kasar.

    Washington ta ce zata bayar da karin dala miliyan dari ga Pakistan domin ta samu damar farfadowa.

  12. "Ban kashe matata ba saboda kudin burodi"

    Burodi

    Ndubuisi Wilson Uwadiegwu da ake zargi da kashe matarsa Ogochukwu Uwadiegwu ya musanta laifin da ake zarginsa.

    Uwadiegwu ya shaidawa BBC cewa babu shaka sun samu sabanni tsakaninsa da matarsa har ta kai ga sun yi rikici, amma kam ba kan burodi ba ne kuma ba shi da hannu a mutuwarta.

    A makon da ya gabata ne labarinsa ya rinka jan hankali a shafukan sada zumunta kan miji ya kashe matarsa saboda burodi.

    'Yan uwan matar da BBC ta tuntuba sun shaida cewa lamarin ya faru ne a Disamba 2022, a jihar Enugu da ke kundacin Najeriya.

    A cewar Chukwuebuka sun soma rikicin ne bayan matarsa ta bukaci ya siya mata burodi amma sai ya ce mata ba shi da kudi.

    Sai matar tayi amfani da kudinta ta saye burodi, sai kawai mijin ya cinye burodin.

    Daga nan ne aka soma rigima har ta kai ga ta fadi madubi ya yanketa. Sannan ya doke diyarsa yar shekara 14 ne saboda ta zageshi a lokacin da suke rigima da matarsa.

    Mutumin dai ya ce ajali ne kawai ya zo amma ba wai shi ne ya yi sanadin mutuwar matarsa ba.

  13. Shugaba Biden ya kai ziyarar farko iyakar kasarsa da Mexico

    biden

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya kai wata ƙwarya-ƙwaryar ziyara zuwa iyakar ƙasar da Mexico a wani yunƙuri na daƙile sukar da ake yi wa tsare-tsarensa kan baƙin da ke shiga ƙasar.

    Ita ce ziyararsa ta farko zuwa kan iyakar tun bayan da ya hau kan karaga shekaru biyu da suka gabata.

    Mista Biden ya leka wata mashiga mai cike da cunkoson jama'a a birnin El Paso da ke Texas inda ya yi tafiya ta jikin shingen ƙarfen da ya raba ƙasashen biyu.

    Ƴan jam'iyyar Republicans sun ce Mista Biden bai taka wata rawar a zo a gani ba wajen daƙile kwararar baƙi ta haramtacciyar hanya a Amurka.

    Gwamnan Texas, Greg Abbott ya zarge shi da haifar da hargitsi. Yanzu dai mista Biden ya tafi Mexico domin halartar wani taron shugabannin ƙasashen Amurka ta Arewa.

    Gwamnan Texas ke cewa ya kamata Biden yatashi haiƙanwajen ɗaukan mataki cikin gaggawa tare da mayar wa Texas kuɗaɗen da ta kashe amma samar da kayan aikin da suka kamata domin gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyanta.

  14. Iran ta sake zartar da hukunci kisa kan 'yan kasar uku

    An sake zartar da hukuncin kisa kan karin mutane uku a Iran, inda ake zarginsu da laifin kashe mambobin hukumar dakarun tsaron kasar uku a tsakiyar lardin Isfahan a lokacin barkewar zanga-zaga a duk fadin kasar.

    Mutanen su ne Saleh Mirhashemi, da Majid Kazemi Sheikh-Shabani da kuma Saeed Yaghoubi Kordsofla.

    An dai cigaba da gudanar da zanga-zanga a kasar tun bayan kisan wata matashiya mai suna Mahsa Amini mai shekara 22 wadda ta mutu a hannu 'yan sanda, da aka tsare ta bisa tuhumar ta da laifin karya dokar sanya tufafi ta kasar Iran.

    A ranar Asabar kuma, an rataye wasu matasa biyu 'yan shekaru 20, bisa zarginsu da laifin kashe jami'in tsaro a birnin Karaj kusa daTehran.

    An zartar da hukuncin kan matasan biyu ne a watan jiya bisa tuhumarsu da aikata laifuka iri daya.

  15. Bolsonaro ya nesanta kansa daga zanga-zangar Brazil

    Jair Bolsonaro wanda a yanzu yake Amurka, ya nesanta kansa daga zanga-zangar da aka ce magoya bayansa sun yi.

    Jair Bolsonaro ya yi magana a kafar sada zumunta inda ya ce gudanar da zanga-zangar lumana na cikin tsarin dimokraɗiyya amma abin da ya faru a jiya, ya saɓawa doka.

    Cikin wasu jerin saƙonnin Tuwita da ya wallafa, Mista Bolsonaro ya ce kutsen da aka yi kan gine-ginen gwamnatin, ya ci karo da yanayin zanga-zangar da dimokraɗiyya ta bada dama.

    Mista Bolsonaro ya yi watsi da zarge-zargen da Shugaba Lula da Silva ya yi cewa shi ne ya kitsa tashin hankalin.

    Ya dage cewa koda yaushe yana cikin mutunta kundin tsarin mulkin kasa da bin doka da oda.

    Amurka ta bi sahun ƙasashen duniya wajen yin tur da harin da aka kai kan majalisar dokokin ƙasar da ke Brasilia.

    Shugaba Biden ya bayyana harin a matsayin cin zarafi ga dimokradiyya.

  16. Dokar takaita cire kuɗi na CBN ta fara aiki a Najeriya

    Kudi

    A yau Litinin dokar takaita kudi ta ATM da babban bankin kasa wato CBN ya fitar ke soma aiki a fadin Najeriya.

    CBN ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.

    Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.

    Sannan bankin ya umarci bankuna su daina loda tsoffin takardun naira da aka sauya a nau'rorin ATM, inda suka bukaci kowanne banki ya ke fitar da sabbin kudade.

  17. Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen Kano

    ...

    Wutar rikici ta ƙara ruruwa a PDPn jihar Kano duk da hukuncin kotu na baya-bayan nan da kuma matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya banagaren.

    Lamarin ya faru ne bayan ɓangen Sadiq Wali wanda wata kotun tarayya ta ce ba shi ne ɗan takarar gwamnan ba, kuma ya ɗaukaka ƙara, daga baya ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a jihar.

    Sai dai ɓangaren da kotu ta ce shi halastacce na Muhammad Abacha ya fito ya yi Alla-wadai da wannan mataki yana cewa nuna raini ne ga kotu.

    Bayanan da BBC ta samu na cewa a wannan Litinin ɗin ne ake sa ran kwamitin yaƙin neman zaben da ɓangaren Sadiq Wali suka ƙaddamar zai fara zama domin tattauna yadda zai gudanar da aikinsa.

    A makon jiya ne aka kafa kwamitin, al’amarin da ya ƙara tayar da kura.

    Ɓangaren Muhammad Abacha sun ce ba su tare da wannan matakin kamar, yadda Barrister Ibrahim Isa Wangida, lauyan jam’iyyar PDP a Kano ya shaida wa BBC.

    To sai dai bangaren Sadiq Wali wanda ya ƙaddamar da kwamtin ya ce, waɗanda suke sukar wannan matakin ba su fahimci yadda tsarin yake ba, a ta-bakin kakinsu Dakta Yusuf Bello Danbatta.

    Masharhanta dai na ganin duk wannan rikici da taƙaddama, jam’iyyar ce ke yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, dai-dai lokacin da hankulan sauran jam'iyyu suka karkata ga yaƙin neman zaɓe.

    Jam'iyyar ta PDP da ke sahun manyan masu hamayya a Kano har yanzu kanta a rarrabe yake lamarin da ake ganin hakan ba zai yi mata kyau, kasa da wata biyu a gudanar da zabe.

  18. Yau ake fitar da sakamakon zaɓen 'yan majalisa a Benin

    Benin

    A yau Litinin ake sa ran fara samun sakamakon zaɓen ƴan majalisar dokoki a Jamhuriyar Benin, bayan kaɗa ƙuri'a jiya Lahadi.

    A zaɓen na jiya dai, ƴan adawa sun shiga an dama da su, bayan sun ƙaurace wa zaɓukan baya, sakamakon dirar mikiyar da jami'an tsaro suka riƙa yi musu.

    Masu zaɓe kimanin miliyan shida da dubu 600 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a don zaɓar ƴan majalisa 109, ciki har da aƙalla mata 24 –bisa tanadin wata sabuwar dokar zaɓe.

  19. Gwamnan Yobe ya bai wa ma'aikata hutun kwanaki biyu domin tarbar shugaba Buhari

    Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya bai wa ma'aikata hutun kwanaki biyu wato Litinin da Talata domin ziyarar da shugaba Buhari zai kai jihar.

    Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar dauke da sa hannun shugaban ma'aikata na jihar, Alhaji Garba Bilal a Damaturu a ranar Lahadi.

    Buhari zai ziyarci jihar domin kaddamar da wasu manyan ayyuka ciki har da tashar jirgin sama ta sauke kaya da wani katafaren kasuwar zamani da kuma cibiyar lafiya.

    Gwamnati ta ce ta bada hutu ne domin ma'aikata da sauran al'umma su samu damar tarbar shugaban wanda zai kai ziyarar kwana guda a jihar.

    Sai a ranar Laraba ake sa ran ma'aikata su koma bakin aikinsu.

  20. Senegal ta fara zaman makokin mutuwar 'yan kasar a hadarin mota

    Macky Sall

    A wannan Litinin din ne al'ummar Senegal ke fara zaman makokin kwanaki uku a faɗin ƙasar don juyayin waɗanda suka mutu a wani haɗarin mota mafi muni a tarihin ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Kaaffrine, bayan wasu motocin safa biyu sun yi taho mu gama da juna.

    Shugaba Macky Sall ya ce gwamnatin ƙasar za ta yi zaman gaggawa a wannan Litinin din domin ɗaukar matakan kariya da suka dace.

    Hatsarin ya kasance ɗaya daga cikin munanan hatsarin mota da ƙasar ta taɓa fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

    Haka kuma a wata mai kama da wannan aƙalla mutum 21 ne suka mutu a lokacin da wata motar bas da ke kan hanyarta ta zuwa birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta faɗi jim-kaɗan bayan da ta tsallaka kan iyakar Uganda da Kenya.

    Jami'an yan sanda su ce tsananin gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin.

    'Yan sandan Uganda sun ce an samu fiye da haɗura 100 a cikin kwanaki uku a ƙasar cikin sabuwar shekara, lamarin da a cewarsu ya yi sanadin mutuwar mutum 35.