Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Muhawara

    Masu bibiyarmu nan za mu rufe wannan shafi namu na kai-tseye wanda muka kawo muku yadda aka gudanar da muhawarar 'yanh takarar gwamna a jihar Kano da ke arewa maso yammacin najeriya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Kada kuma ku manta kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon yadda muhawarar ta gudana.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

    Diginza
  2. Zan tsaya wa Nnamdi Kanu idan gwamnati za ta sake shi - Soludo

    Soludo

    Gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Chukwuma Soludo, ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya saki shugaban ƙungiyar 'yan awaren Biafra ta IPOB Nnamdi Kanu.

    Gwamnan ya ce a shirye yake ya tsaya wa Nnamdi Kanu wanda ke hannun jam'ian tsaro na farin kaya a ƙasar, matuƙar gwamnati za ta sake shi.

    Mista Soludo ya yi kiran ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe a birnin Akwa na jihar, inda ya ce matsalar tsaron da yankin kudu maso gabashin ƙasar ke fuskanta na da alaƙa da manyan jagororin ƙungiyar IPOB.

    Dan haka a cewarsa dole ana buƙatar jagororin ƙungiyar a teburin tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da ƙungiyar.

    A 'yan kwanakin nan ne dai wata kafar yada labarai a ƙasar ruwaito mai tsawatarwa na majalisar dattawan ƙasar, wato tsohon gwamnan jihar Abia da ke kudu maso gabashin ƙasar Orji Kalu na cewa shi ma zai tsaya wa jagoran 'yan awaren domin a sake shi.

  3. United ta lallasa Man City a Old Trafford

    United

    Manchester United doke takwararta Manchester City da ci 2-1 a wasan hammayya da ƙungiyoyin biyu suka buya a filin wasa na Old Trafford.

    City ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Jack Grealish a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na rage yawan tazarar maki da ke tsakaninta da Arsenal wadda ke ta ɗaya a kan teburin Premier.

    To sai dai haƙar City ba ta cimma ruwa ba, bayan da Bruno Fernandes ya farke ƙwallon ana saura minti 12 a tashi wasan, duk da kasancewar Marcus Rashford a cikin da'irar satar gida.

    Minti huɗu bayan hakan ne kuma Marcus Rashford ɗin ya ƙara ta biyu bayan da ya zura ƙwallon da Alejandro Garnacho ya bugo masa.

    Da wannan sakamako United ta koma ta uku a kan taburin maki ɗaya tsakaninta da City wadda ke matsayi na biyu, maki biyar tsakaninta da Arsenal ta ɗaya.

  4. Gane Mini Hanya

    Hira da Sanata Ibrahim shekarau

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  5. Gwamnatin Zamfara ta gano likitocin bogi 199 da ke karɓar albashi

    matawalle

    Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatin jihar ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199 waɗanda ake biyan albashi a jihar.

    Gwamna matawalle na wannan jawabi ne ga taron manema labarai a shalkwatar ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar.

    A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.

    Gwamnan ya ƙara da cewa tuni ya zanta da ƙungiyar kwadago ta ƙasa domin gano waɗanan, likitoci 199 da suka ƙwashe tsawon lokaci suna karɓar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.

    Da kuma gano waɗanda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.

    Matawalle ya ce an gano waɗannan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma'aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa ƙarƙashin ofishin shugaban ma'aikata na jihar.

  6. Shirin Lafiya Zinariya

    Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya yi duba ne a kan ciwon 'Hangun'"

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  7. Ci gaba da kawo muku sauran labarai

    Yanzu kuma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu domin sanin halin da duniya ke ciki.

    BBC Hausa! Labaran duniya a duk inda kuke!

  8. Kammala muhawara

    Ibrahim Isa

    Masu bin mu a wannan shafi yadda ta kaya kenan a muhawar 'yan takarar gwamna na jihar Kano da BBC Hausa ta shirya.

    Amma kar ku manta za ku iya sake kallon wannan muhawa a shafukanmu na BBC Hausa Facebook, da YouTube.

    Haka kuma wannan muhawara ita ce farko daga cikin jerin muhawara da BBC Hausa ta shirya yi da 'yan takarar gwamna a wasu jihohin arewacin ƙasar biyar.

    Za mu kawo muku muhawararmu ta gaba a daga jihar Kaduna ranar 18/01/2023. Sai ku tara da mu a wannan rana domin kawo muku muhawar tare da 'yan takarar gwamnan jihar ta Kaduna.

    Bayan jihar Kaduna kuma sai jihar Katsina, da Bauchi da kuma jihar Sokoto, myna fata za ku kasance tare da mu domin kallon muhawar a duka waɗannan jihohi.

    Mun gode

    Muhawara
  9. Jawabin kammalawa: Sha'aban Sharada

    nn

    ''Ina kira ga magoya bayanmu da mu yi siyasa ba da gaba ba'', in ji shi

    Kuma ''za mu yi aiki da matasa ta hanyar zaƙulo ma'aidan da Kano ke da su''.

    daga ƙarshe ya yi alƙwarin yin aiki tare da kowa

  10. Jawabin kammalawa: Nasiru Yusuf Gawuna

    ''A duba mutumin da ya cancanta a zaɓa'', A yi siyasa cikin lumana, domin kuwa ''yanzu da muka zo nan BBC Hausa ta sauke mu a ɗaki ɗaya kuma duka muka gaisa tare da mutunta junanmu'', dan haka ina kira ga magoya bayanmu da su zauna lafiya''

    Gawuna
  11. Jawabin kammalawa: Mohammed sani Abacha

    ''Ina fatan za a mu yi wa juna da 'yan uwa adalci''

    hausa
  12. Jawabin kammalawa: Salihu Tanko Yakasai

    bbb
  13. Nasiru Yusuf Gawuna kan tambayoyin jama'a

    Kawar da maganar Rashawa

    Tsarkake zukata domin yin abin da ya dace

    Gyara tsarin bayar da kwangila

    Yin doka domin samar da hukumar masu bukata ta musamman

    Inganta ɗakunan gwaje-gwaje

    Gawuna
  14. Sha'aban Sharada

    Horar da matasa kan fasahar zamani da ICT

    Gwanati za ta riƙa wallafa abun da ta samu da abin da ta kashe a duka wata a shafin intanet

    Samar da makarantu da inganta waɗanda ake da su ga masu buƙatar lalura da musamman

  15. Salihu Tanko Yakasai kan tambayoyin mutane

    Babu maganar 10 fasen a gwamnatinsa

    Za a dama da masu buƙatar lalura ta musamman ta hanyar horas da su sana'o'i

    Dawisu
  16. Mohammen Abacha kan tambayoyin da aka yi

    Bayar da kwangila ga 'yan asalin jihar Kano maimakon 'yan wasu jihohin ko 'yan ƙasashen waje, sannan za mu tabbatar da aikin kwangila ya inganta da ayadda za a yi aiki mai inganci,

    Tabbatar da cewa 'yan kwangila sun cika ƙa'ida

  17. Yanzu an zo gabar tambayoyi daga masu sauraro

    Yanzu kuma lokacin masu tambayoyi ne waɗanda za su yi tambayoyinsu ga 'yan takarar

    masu kallo
  18. Haɓaka kasuwanci: Salihu Tanko Yakasai

    Samar da jari ga 'yan kasuwa

    'Yan kasuwar Kano su tsaya da kafafunsu, su daina zama dilallai

    Inganta wutar lantarki a jihar Kano

    Zamanatar da kasuwanci da kasuwannin Kano

    Gyara kasuwanni domin tsaftace su daga kwatami

    Zamanantar da kasuwar 'yan kaba

  19. Bunƙasa kasuwanci : Sha'aban Sharada

    Inganta harkokin samun kudin shiga

    bayar da cikakken yancin kudi ka ƙananan hukumomi

    Gyara masa'antun chalawa da na Bomfai

    Janyo 'yan kasuwa daga ƙasashen waje domin su zo su zuba jari

    Samar da ƙananan bankunan bayar da rance domin inganta jihar

    Inganta kudin shigar Kano zuwa biliyan 10

    Sha'aban sharada
  20. Noma da Kiwo: Mohammed Sani Abacha

    noma

    Samar da ingantaccen iri na zamani

    Inganta madatsun ruwan da Kano ke da su domin haɓaka harkar noma

    Wadata jihar da takin zamani da magungunan ƙwari