EFCC na neman A.A Zaura ruwa-a-jallo

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. A kwana lafiya

  2. Shugaban ANC na son a yi fatali da batun tsige Shugaba Cyril Ramaphosa

    Shugabancin Jam’iyyar ANC mai Mulki a Afirka ta Kudu ya ce zai ba da shawarar a yi fatali da duk wani yunƙuri na majalisar dokokin ƙasar na tsige Shugaba Cyril Ramaphosa.

    Babban sakataren ANC ke nan yake cewa Kwamitin zartarwa ya yanke shawarar yin watsi da rahoton kwamitin ganin cewa Shugaban ƙasar yana nazari a kai.

    Wani rahoto da ake sa ran ƴan majalisar za su kaɗa ƙuri’a a kansa gobe Talata, na zargin Shugaban da yiwuwar aikata ba dai-dai ba.

    Ana zargin Mista Ramaphosa ya ajiye miliyoyin daloli a gonarsa sannan kuma ya ƙi ba da rahoton kuɗaɗen sun ɓata a lokacin da aka sace su.

    Ya musanta saɓa doka inda kuma ya shigar da ƙara domin ƙalubalantar rahoton kotun tsarin mulkin ƙasar

  3. Fitacciyar mawaƙiya ta Nijar Hamsou Garba, mai waƙar Lagireto ta rasu

    Hamsou Garba

    Asalin hoton, IciNiger

    Ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa a jamhuriyar Nijar Hamsou Garba ta rasu ne a jiya da daddare a wani asibiti a babban birnin ƙasar Niamey.

    Hamsou ta rasu ne tana da shekara 64 bayan da ta sha fama da rashin lafiya.

    An haifi Hamsou ne a birnin Maraɗi, kuma ta shafe fiye da shekara 30 tana waƙa.

    Tawagarta ta waƙa ta haɗa da mata da maza, kuma da Hausa take waƙar sai dai takan sirka da Faransanci a wasu lokutan.

    Waƙoƙinta sun fi mayar da hankali ne a kan soyayya da addini da zamantakewa da gwagwarmayar siyasa da kuma kishin ƙasa.

    Ana matuƙar girmama Hamsou har ma ana mata laƙabi da "akwatin waƙa" saboda basirarta da yadda a take tana iya haɗa waƙa.

    Ƙungiyar mawaƙa ta ƙsar ta bayyana rasuwarta a matsayin asara ga fannin waƙa na ƙasar, inda har mawaƙi Amadou Yacouba ke cewa "babu mutane irin ta sosai" a masana'antar waƙe-waƙe ta ƙasar.

    An taɓa ɗaure mawaƙiyar a shekarar 2016 saboda sukar gwamnati da ta yi a wajen wani wasa da kuma kiran babban ɗan hamayya na ƙasar a lokacin Hama Amadou, a matsayin "Mandelan Nijar".

    Kazalika hamsou kan yi magana kan zamantakewa a wani shiri na gidan rediyonta na Turaki.

    Ta rasu ne mako biyu bayan rasuwar mijinta da kuma babbar ƴarta da it ma ta rasu wata ɗaya da ya wuce.

  4. An aiwatar da hukunci kisa sama da 500 a Iran a 2022

    Wata kungiyar kare haƙƙin bil adama ta ce Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan fiye da mutum ɗari biyar a wannan shekarar – ƙarin fiye da kashi talatin cikin ɗari na adadin bara.

    Ƙungiyar ta Iran Human Rights da ke da mazauni a Norway ta ce adadin ɗari biyar da huɗu shi ne mafi yawa da aka taɓa samu a wata ƙasa.

    Adadin ya haɗa da wasu mutum huɗu da ke jiran hukuncin kisa ranar Asabar bayan da aka same su da laifin yi wa Isra’ila aikin leƙen asiri.

    Yanzu kuma fargaba na ƙaruwa game da masu zanga-zangar da aka kama a Iran.

    Tuni aka yanke wa shida daga cikinsu hukuncin kisa sannan wasu ashirin da shida na fuskantar tuhume-tuhumen da ka iya sa wa a yanke musu hukuncin kisa.

  5. China ta soma sassauta dokar yaƙi korona

    China

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama China na neman janye manyan ƙa’idojinta na ƴaƙi da annobar korona wato yi wa jama’a gwajin cutar.

    Rashin gabatar da shaidar da ta nuna mutum ba ya ɗauke da cutar ya sa tafiye-tafiye ya zama jidali ga al’ummar ƙasar.

    Daga yau Litinin, babu buƙatar jama’ar da ke amfani da motocin haya a Beijing da Shanghai su nuna shaidar ba su da cutar.

    Birane da Larduna a sassan China sun sanar da ɗaukar irin wannan matakin.

    A Hangzhou kuwa, hukumomi sun sanar da dakatar da gwaje-gwaje a yankin baki ɗaya. Sai dai zuwa yanzu, gwamnatin ƙasar ba ta yi sanarwa a hukumance ba.

  6. Yadda Shugaba Buhari ya kaddamar da taron sojoji a Sokoto

    BASHIRAHMED

    Asalin hoton, BASHIRAHMED

    BASHIRAHMED

    Asalin hoton, BASHIRAHMED

    BASHIRAHMED

    Asalin hoton, BASHIRAHMED

    BASHIRAHMED

    Asalin hoton, BASHIRAHMED

  7. Yadda aka gudanar da taron wayar da kawunan 'yan siyasa a Kano

    Wani kwamitin wanzar da zaman lafiya a Kano ya gudanar da taro da shugabannin kafafen watsa labarai a jihar.

    Kwamitin yace ya hada kan masu ruwa da tsaki a fanni watsa labaran ne, don tattaunawa tare da samar da hanyoyin da za a ci gaba da wayar da kan ‘yan siyasa ta yadda za a gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.

    Kwamitin inganta zaman lafiyar wanda aka kafa domin samar da zaman lafiya, kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe ya gana da kafofin watsa labarai na jihar Kano, inda aka tattauna tare da bayar da shawarwarin yadda za a tunkari babban zaben 2023.

    Taron ya nemi hadin kan 'yan jarida wajen tsaftacce kalaman da ake yi a kafafen yada labaran jihar Kano musamman a wannan lokaci da ake ci gaba da yakin neman zabe, kamar yada Ambasada Ibrahim Wayya babban jami'I a kwamitin wanzaar da zaman lafiya na jihar Kano ya shaida

    Malam Abubakar Salihu wanda ya wakilci shugabannin kafafen watsa labarai na jihar Kano ya ce za su tabbatar 'yan jarida sun bi ka'idojin aikin jarida don tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe a jihar Kano.

    Hukumar da ke sanya ido kan kafafen watsa labaran Najeriya, NBC, sun gabatar da kasida kan kiyaye ka'idojin aikin jarida.

    Kwamitin samar da zaman lafiya a jihar Kano, ya ce nan gaba zai shirya gagarumin taro inda ake fatan dukkan 'yan takarar gwamna da shugabannin jam'iyya za su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben 2023.

  8. Sojoji sun sanya hannu kan kawo karshen rikicin siyasa a Sudan

    s

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin soji da farar hula a Sudan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin siyasa a ƙasar.

    A cewar wakiliyar BBC, ƙungiyar Tarayyar Afirka da ƙasashen Larabawa da ƙasashen Yamma sun goyi bayan tattaunawar tsakanin sojoji da farar hula a matsayin wata kafa ta samar da zaman lafiya da kawo ƙarshen zanga-zanga.

    Tun bayan da babban hafsan sojin ƙasar, Abdel Fattah al-Burhan ya ƙwace shugabanci a wani juyin mulki a ƙarshen shekarar da ta gabata ne, ake gudanar da zanga-zanga duk mako domin nuna adawa da matakin.

    Sabuwar yarjejeniyar na neman share fage ga dawowar mulkin dimokraɗiyya.

    Yarjejeniyar ta samu sa hannun ƙungiyoyin farar hula da dama amma wasu masu fafutukar tabbatar da dimokraɗiyya sun yi watsi da yarjejeniyar inda suka ce ya zama dole a hukunta sojojin da ke mulki saboda kashe-kashen da aka yi.

  9. Sojojin ruwan Najeriya sun musanta zargin yin rufa-rufa, Daga Ibrahim Isah

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin man kasar ya yi rufa-rufa tare da kambama alkaluman da suka shafi satar mai.

    Rundunar na mai da martani ne ga wasu rahotonni da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa rundunar ce ta ce kamfanin man kasar yana nuku-nuku ko rufa-rufa, wato yana boye gaskiya game da satar man da ake yi a Najeriya.

    Maganar ma ba ta tsaya nan ba, in ji rudundunar sojin ruwan, saboda rahotannin na cewa rundunar ta ce kamfanin man yana shirga karya ko kambama alkaluman da suka shafi satar man.

    Wata sanarwar da kakakin rundunar, Kwamanda Ayo Vaughan ya sanya wa hannu, ta ce wasu kafafen yada labarai sun jahilci bayanan da wakilin rundunar ya yi ne, a wajen wani zaman jin bahasi da kwamitin majalisar dattawan Najeriya a kan laifukan da suka shafi tattalin arziki ya yi

    Inda kwamitin ya yi ta bijiro da wasu tambayoyi a kan dalilan da suka sa har yanzu matsalar satar ma i ba ta kau ba, duk kuwa da ikirarin da rundunar sojin ruwan ke yi cewa an samar da tsaro a hanyoyin ruwa da kuma tekun kasar.

    Kakakin ya ce na fuskanci kalubale na miyagu da matatunsu, wadanda ke zukar man daga bututan da ake fitar da man zuwa kasashen ketare, amma wannan matsala ta kau tun a watan Fabrairu zuwa Maris din wannan shekarar.

    Kazalika, Kwamanda Ayo Vaughan ya ce tun daga watan Fabrairun zuwa Maris manyan tsasoshin man Najeriya ba sa iya sarrafawa da tura mai.

    kuma wannan ne ya sa wasu ke dauka satar man ake yi, amma abu ne mawuyaci a sace gangar mai 100,000 a cikin kurmi ko surkukin daji a kowace rana.

    Rundunar sojin ruwan Najeriyar ta ce akwai kyakyawar fahinta tsakanin jami`anta da kamfanin man Najeriya.

    Kuma suna aiki kafa da kafada da juna da nufin dakile matsalar satar mai, hasali ma dangantakar ta kara yauki tun a watan Afrilun wannan shekarar, lokacin da aka kaddamar da wani gangami na musamman a Onne da ke jihar Rivers, mai suna Operation Dakatar da Barawo!

  10. Ana cikin fargaba sakamakon kiran zanga-zanga a Iran

    An rufe kantina da dama a biranen da ke sassan Iran bayan da masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati suka kira yajin aikin kwana uku.

    Wasu hotunan bidiyo da ba a tantance su ba sun nuna shaguna a rufe a babbar kasuwar Tehran da wasu a manyan birane har da Isfahan da Shiraz da Karaj.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta ce birane 19 a yankunan da Ƙurdawa ke da rinjaye suma sun bi sahun yajin aikin.

    Rahotanni na cewa hukumar hisba ta ƙasar na ci gaba da tafiyar da harkokinta duk da iƙirarin hukumomi na rushe hukumar.

  11. Zulum ya ziyarci ƴan gudun hijira a jamhuriyar Nijar

    B

    Asalin hoton, BORNOGOVT

    Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ziyarci 'yan gudun hijrar da ambaliya ruwa ta raba da muhallansu waɗanda ke zaune a garin Bosso da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar.

    Mutanen 'yan asalin garin Malam-Fatori ne, shalkwatar ƙaramar hukumar Abadam da ke kusa da tafkin chadi a arewacin jihar.

    Al'umar Najeriya da Nijar dai sun kwashe shekaru masu yawa suna tsallaka kan iyakar ƙasashen biyu domin cin kasuwannin da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

    Gwamnan ya ce ya je wajensu ne domin ya jajanta musu game da ambaliyar da ta shafe su, tare da alkawarta cewa gwamnatin jihar za ta taimaka musu wajen mayar da su garuruwansu da zarar ruwan ya janye.

    Gwamna Zulum ya kuma gode wa jami'an ƙasar Nijar game da yadda suke tarbar mutanen jiharsa a lokutan da bala'o'i suka auku.

  12. An ji ƙarar fashe-fashe a wasu sansanonin sojin Rasha

    Kafafen yaɗa labaran Rasha sun ce wasu fashe-fashe da suka auku a sansanin sojoji da ke kudu maso yammacin ƙasar sun halaka kimanin mutum uku.

    Kamfanonin dillancin labaran Rasha sun rawaito cewa kimanin mutum uku sun mutu, wasu da dama kuma sun ji rauni lokacin da wata tankar mai ta fashe a wani sansanin soji da ke kusa da Ryzan a tsakiyar Rasha.

    A wani harin na daban kuma, rahotanni sun ce mutum biyu sun ji rauni. Babu tabbaci kan musabbabin fashewar. Yankunan da fashewar ta faru na da nisan ɗaruruwan kilomita daga iyakar Ukraine.

  13. EFCC na neman A.A Zaura ruwa-a-jallo

    ..

    Asalin hoton, others

    Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta bayyana neman ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura.

    Lauyan hukumar EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin bayan da aka dawo da batun shari’ar dala miliyan 1.3 da ake yi wa A.A Zaura a babbar kotun tarayya da ke Kano.

    Duk da cewa shari’ar da aka shirya yi wa ɗan siyasar ba ta samu ba, saboda rashin halartar alkalin da ke sauraron shari’ar, wanda aka ce yana halartar wani taron ƙasa a wajen birnin na Kano.

    Haka kuma lauyan na EFCC ya bayyana cewa ya kamata A.A Zaura ya kai kansa ga hukumar.

    “Muna neman Zaura kuma za mu kama shi da zarar mun same shi''.

    ''A ƙa’ida, ya kamata a ce yana hannunmu domin kuwa kotu ta tabbatar da haka, amma ina tabbatar da cewa za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba ranar 30 ga Janairun 2023''.

  14. An rufe kantuna a Iran saboda zanga-zangar ƙin jinin gwamnati

    An rufe kantina da dama a biranen da ke sassan Iran bayan da masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati suka kira yajin aikin kwana uku.

    Wasu hotunan bidiyo da ba a tantance su ba sun nuna shaguna a rufe a babbar kasuwar Tehran da wasu a manyan birane har da Isfahan da Shiraz da Karaj.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta ce birane 19 a yankunan da Ƙurdawa ke da rinjaye suma sun bi sahun yajin aikin.

    Rahotanni na cewa hukumar hisba ta ƙasar na ci gaba da tafiyar da harkokinta duk da iƙirarin hukumomi na rushe hukumar.

  15. Sojoji za su mayar da mulkin Sudan hannun farar hula cikin shekara biyu

    ...

    Ƙungiyar masu rajin tabbatar da demokuraɗiyya a Sudan da kuma gwamnatin sojin ƙasar sun sanya hannu kan yarjejeniyar mayar da mulkin ƙasar hannun farar hula.

    Yarjejeniyar ta samar da tsawon shekara biyu na shiryawa kafin miƙa mulkin.

    Sai dai tuni aka fara zanga-zangar adawa da yarjejeniyar a Khartoum, babban birnin ƙasar, yayin da ake fargabar za ta iya yaɗuwa zuwa wasu yankuna.

    Mutane dai na kira ne da a gurfanar da waɗanda suka jagoranci juyin mulkin ƙasar na 2021.

    An kwashe kimanin shekara huɗu ƙasar tana tangal-tangal bayan tuntsurar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.

  16. An kashe ƙasurguman ƴan fashin daji da ke addabar jihar Zamfara

    ...

    Asalin hoton, NIGERIAN AIR FORCE HQ

    Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu ƙasurguman ƴan fashin daji waɗanda ke addabar ƙauyukan jihar Zamfara.

    Rahoton ya ce an samu nasarar kashe ƴan fashin ne a wasu hare-hare da jiragen sojojin Najeriya suka kai a wasu ƙauyukan jihar Kaduna.

    Waɗanda aka kashen a cewar rahoton sun haɗa da Jibrin Gurgu, da Isah Jauro da kuma wani da ake kira Tambuwal.

    Sauran sun haɗa da Noti, da Bala, da Yunusa da kuma Burti.

    Bayanin da jaridar ta samo ya ce an kai farmakin ne a wasu sabbin sansanonin ƴan fashin a yankin ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

    Haka nan an kai wasu hare-haren a yankunan ƙananan hukumomin Igabi da Birnin Gwari.

    Wata majiyar tsaro ta ce an ga dacewar kai harin ne bayan rahotannin da ke cewa an samu ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a yankin.

  17. 'Ƴan bindiga ne ke iko da rabin babban birnin Haiti'

    Wata mata na kuka saboda tashin hankalin da al'umma ke ciki sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga a babban birnin Haiti

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama a Haiti sun ce matasa ɗauke da miyagun bindigogi ne ke iko da rabin babban birnin ƙasar Port au Prince.

    Ƙungiyoyin sun shaida wa BBC cewar ɗaruruwan mutane ne aka kashe cikin ƴan watannin da suka gabata sanadiyyar arangama tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindigan, yayin da mutane da dama suka tsere daga muhallansu.

    Ƙungiyoyin bayar da agaji sun ce ƴan bindigan su ne ke iko da hanyoyin shiga da fita birnin.

    Haka nan ma ƴan bindigan ne ke riƙe da unguwannin da ke zagaye da ginin majalisar dokokin ƙasar.

    Firaiministan ƙasar Ariel Henry ya roƙi ƙasashen duniya su kai wa ƙasar ɗauki.

    Zaman lafiya ya yi ƙaranci a ƙasar tun bayan kisan da aka yi wa shugaban ƙasar Jovenel Moize a watan Yulin 2021.

  18. Ƙasashen yammacin Afirka za su samar da rundunar tsaro ta bai-ɗaya

    ..

    Asalin hoton, AP

    Ƙasashen yammacin Afirka ta yamma sun amince su kafa runduna ta musamman wadda za ta rinƙa kai ɗauki a wuraren da aka samu rikici na masu iƙirarin jihadi da kuma ƙasashen da ake samun juyin mulki.

    Shugaban ƙungiyar habbaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, Omar Alieu ya tabbatar wa manema labaru cewar an ɗauki wannan mataki ne domin ganin yankin ya tunkari matsalar tsaron da ke addabarsa da kansa.

    Alieu ya ce wannan mataki zai sauya tsarin tsaro na ƙasashen.

    Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen ne za su tattauna kan yadda rundunar za ta kasance a tsakiyar shekara ta 2023.

    Ƙasashe da dama na yankin dai na fama da barazana ta tsaro.

  19. Za a sanya hannu kan mayar da mulki hannun farar hula a Sudan

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ana sa ran jami'an tsohuwar gwamnatin haɗin gwiwa ta Sudan da jagororin sojin ƙasar za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar mayar da mulki a hannun farar hula.

    Kafofin yaɗa labarun cikin gida da suka ruwaito labarin sun ce ana sa ran yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya mamaye ƙasar tun bayan juyin mulkin da aka samu a ƙasar a watan Oktoba na 2021.

    Shugabannin dakarun tabbatar da ƴanci da kawo sauyi sun ce yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen mulkin soji, da kuma samar da sabon kundin tsarin mulki wanda zai share hanyar tsayar da lokacin da ƙasar za ta koma kan tafarkin mulkin demokuraɗiyya.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, dakarun tabbatar da ƴancin sun ce abin da suka mayar da hankali a kai shi ne ƙoƙarin samar da adalci, da tarwatsa tsarin da aka samar na gwamnatin da aka kafa ranar 30 ga watan Yunin 1989, da ƙawato kuɗaɗen al'umma da sauran su.

  20. Likitoci sun roƙi Musaveni ya tsaya takarar shugaban Uganda a karo na bakwai

    ..

    Asalin hoton, Yoweri Museveni / Twitter

    Wasu gungun likitoci a Uganda sun haifar da cece-ku-ce bayan da suka durƙusa a gaban shugaban ƙasar Yoweri Musaveni suna roƙon sa ya tsaya takarar shugaban ƙasa a karo na bakwai.

    Musaveni mai shekara 78 ya kasance kan mulki tun shekarar 1986. Sannan za a gudanar da zaɓen ƙasar na gaba ne a shekarar 2026.

    Likitocin ƙarƙashin Ƙungiyar likitoci ta Uganda (UMA) suna halartar wani taro ne kan kishin ƙasa a Kampala, babban birnin ƙasar, lokacin da shugabansu ya jagorance su suka duka a gaban shugaban ƙasar domin roƙon sa.

    Shafin yaɗa labaru na Nile Post ya ruwaito shugaban ƙungiyar likitocin Dr Samuel Odongo Oledo na yaba wa shugaban ƙasar, wanda ya ce ya gyara harakar kiwon lafiya tare da inganta walwalar likitoci.