Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Jam'iyyar LP ta yi watsi da yadda ake tattara sakamakon zaben shugaban ƙasa

    LP

    Jami'iyyar Labour Party, ɗaya daga jam'iyyun hamayya a Najeriya a zaben 2023 ta yi watsi da yadda ake tatttara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ake yi a Abuja.

    Jam'iyyar ta ce ta yi watsi da sakamakon ne saboda INEC ta gaza wallafa sakamakon mazabu a shafinta na intanet a manhajar iREV kamar yadda ta yi alƙawari.

    LP ta sa ayar tambaya kan sahihancin yadda ake karɓar sakamakon zaɓen da cibiyar tattara sakamako ta ƙasa da ke Abuja ke yi.

    Ɗan takarar jam'iyyar LP Peter Obi na ɗaya daga ƴan takarar shugaban ƙasa huɗu da ke kan gaba a zaɓen na shugaban ƙasa, kuma tuni ya samu nasara a wasu jihohi, ciki har da Legas, jihar da ɗan takarar APC Bola Tinubu ya fito.

  2. Atiku Abubakar ya lashe zaɓe a Katsina

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu nasara a ƙuri'un da aka kaɗa a jihar Katsina.

    Katsina, ita ce jihar shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

    Sakamakon da aka gabatar a zauren tattara sakamakon shugaban ƙasar a Abuja ya nuna alƙaluman da kowace jam'iyya ta samu kamar haka.

    APC 482,283

    LP 6,376

    NNPP 69,386

    PDP 489,045

  3. Sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Adamawa

    Yawan kuri'un masu rijista 2,196 566

    Yawan wadanda aka kada 761, 621

    Kuri'u masu kyau 731, 140

    wadanda suka lalace 30, 481

    Abin da manyan jam'iyyu suka samu

    Bola Tinubu na APC 182, 881

    Atiku Abubakar PDP 417,611

    Peter Obi na LP 105,648

    Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP 8,006

  4. Tinubu ya ci zaɓe a Jigawa

    Bayan komawa daga hutun da aka dauka, hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta karɓi sakamakon zaɓen daga jihar Jigawa, abin da ya nuna Bola Tinubu na jam'iyyar APC ne ya lashe zaɓen.

    Ga dai yadda alƙaluman suke

    APC 421,390

    LP 10889

    NNPP 98234

    PDP 386,587

  5. Obasanjo ya bukaci a soke zaɓen shugaban ƙasa a yankunan da aka yi tashin hankali

    Obasanjo

    Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce babu nagarta a babban zaɓen ƙasar da aka yi ranar Asabar a don haka ya ce dole ne a soke shi a yankunan da aka yi tashin hankali.

    Ya buƙaci Shugaban Hukumar zaɓe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Najeriya daga faɗawa haɗarin rikici.

    Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya yi wa taken "Zaɓen Shugaban Najeriya na 2023: Rokon A yi taka tsan-tsan da kuma gyara.''

    Obasanjo ya ce ba wani abin sirri ne, cewa an zargi wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zaɓen da suka gudanar da aikin sun bayar da kai sakamakon aika alkaluman zaɓen ba ta hanyar na'ura ba, abin da ya sa ake zargin wani sakamkon an ƙirƙire shi ne.

  6. Gwamna Wike ya nesanta kansa daga zargin da ake masa na tayar da rikici

    Wike

    Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ƙaryata zargin da ake masa cewa ya yi ta yi wa mutane barazana tare da haifar da rikici a yayin babban zaɓen Najeriya da aa gudanar ranar Asabar.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Chris Finebone ya fitar, Wike ya ce zargin ya fito ne daga "maƙiya masu mugun nufi".

    Ta bayyana cewa Wike ba ya tare da sojoji a tawagarsa musamman a lokacin zaɓe.

    A cewar sanarwar, Wike da mai ɗakinsa sun wuce gida ne kai tsaye bayan jefa ƙuri'arsu a ranar zaɓen.

    A lokacin da ya isa rumfar zaɓensa, an samu tsaiko kafin ya jefa ƙuri'a saboda na'urar BVAS ba ta yi saurin tantance shi ba.

  7. Ƙananan jam'iyyu sun ce sun gamsu da yadda INEC ke karɓar sakamakon zaɓe

    Wasu ƙananan jam'iyyun siyasa a Najeriya sun ce sun gamsu da yadda hukumar INEC take gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ke gudana a zauren tattara sakamakon zaɓen.

    Tuni dai wasu jam'iyyu ciki har da manyan jam'iyyun Adawa PDP da LP, suka fice daga zauren bayan da suka yi ƙorafin cewa INEC ba ta ɗora sakamakon zaɓen a shafinta na intanet ba.

    Ƙananan jam'iyyun sun bayyana matsayarsu ne a matsayin martani kan ficewar da manyan jam'iyyun hamayya PDP da LP da wasu jam'iyyun suka yi daga zauren da ake kaɓar sakamakon zaɓen shugaba ƙasa a Abuja.

    Jam'iyyun da suka fice sun nuna rashin gamsuwa da yadda INEC ke karɓar sakamako daga jihohi.

    Sun nemi lallai INEC ta tabbatar an sanya sakamakon zaben a shafin intanet na hukumar zaɓen kamar yadda INEC ɗin ta alƙawarta yi tun da farko.

    Wakillan ƙananan jam'iyyun sun tashi ɗaya bayan ɗayan a zauren cibiyar tattara sakamakon inda suka nesanta kansu daga ficewar jam'iyyun na hamayya.

    Wasu daga cikin Jam'iyyun da suka ce suna tare da INEC sun haɗar da PRP da APP da BP da NRM da YPP da AAC da AA da AP da kuma jam'iyyar NNPP.

    Ita ma jam'iyyar APC mai mulki wacce kawo yanzu ita ce kan gaba a sakamakon da INEC ta karɓa ta ce ta gamsu da yadda hukumar zaɓen ke karɓar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

  8. Bello El-Rufa'i ya lashe zaɓe a Kaduna

    Bello El-Rufa'i, ɗan gidan gwwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya lashe zaɓen majalisar wakilai daga mazaɓar Kaduna ta arewa, inda ya ka da Sama'ila Sulaiman.

    Bello, wanda ya yi takara a jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 51,052, yayin da abokin hamayyarsa ya samu ƙuri'u 32,802.

    Sama'ila Sulaiman na jam'iyyar PDP shi ne yake wakiltar mazabar ta Kaduna ta arewa a majalisar wakilan Najeriya, a Abuja

    Zaɓen dai ya ɗauki hankali sosai, inda jama'a da dama suka ringa sanya ido don ganin wane ne zai samu nasara.

    Bello El-Rufa'i
  9. An ɗage bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zuwa takwas na dare

    INEC

    Hukumar zabe ta sanar da dage karba da sanar da sakamakon zaben shugaban ƙasa daga jihohi da take yi a babbar cibiyar sanarwar da ke Abuja, har zuwa karfe takwas na dare.

    Shugaban INEC Farfesa Mahood Yakubu ne ya sanar da tafiya hutun, bayan sanar da sakamakon jihohi tara a yau, amma goma jumulla har da Ekiti a jiya.

    Jihohin da aka kammala bayyana sakamakon nasu na zaben shugaban kasa daga cikin 36 zuwa yanzu su ne;

    1- Ekiti inda dan takarar APC Bola Tinubu ya samu nasara da kuri'u 201,494

    2- Osun inda dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da kuria'a 354,366

    3- Ogun inda dan takarar APC Bola Tinubu ya samu nasara da 341,554

    4- Ondo dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri'u 369,924

    5- Kwara dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri'u 263,572

    6- Yobe dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da 198,567

    7- Oyo dan takarar APC Bola Tinubu ya yi nasara da kuri'u 449,884

    8- Gombe dan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara da 319,123

    9- Lagos inda dan takarar LP Peter Obi ya yi nasara da kuri'u 582,454

    10- Enugu inda dan takarar LP Peter Obi ya yi nasara da kuri'u 428,640

  10. Atiku ya ci zaɓe a jihar Gombe

    Babbar jami'ar zaɓe da ta tattara sakamakon shugaban ƙasa a jihar Gombe ta gabatar da sakamakon zaɓen a zauren tattara sakamakon a Abuja.

    APC 146,977

    LP 26,160

    NNPP 10,520

    PDP 319,123

  11. Sakamakon zaben jihar Lagos

    APC 572,606

    LP 582,454

    NNPP 8842

    PDP 75750

    Babban jami'ar zaɓen ta bayyana cewa an soke zakamakon zaɓe a ƙanana hukumomi uku

  12. Zaben shugaban ƙasa na jihar Enugu

    Hukumar zaɓen Najeriya a jihar Enugu ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a zauren tattara sakamakon dake Abuja. Ga sakamakon kamar haka

    APC 4,772

    LP 428,640

    NNPP 1,808

    PDP 15,749

  13. Jama'a sun yi zanga-zanga saboda zargin maguɗin zaɓe a jihar Ebonyi

    Ebonyi

    Wani gungun matasa ya yi dafifi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi domin gudanar da zanga-zanga kan zargin an tafka maguɗi a zaben shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a jihar.

    Lamarin na zuwa ne yayin da hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakamakon zaɓen sanatoci da na ƴan majalisar wakilai.

    Waɗanda suka gudanar da gangamin sun haɗa da magoya bayan tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sam Egwu da sauran magoya bayan ƴan takara kamar Micheal Amannachi da Linus Okorie da Laz Nweru Ogbe da Eze Emmanuel.

    Sun yi zargin cewa an fara yin zaɓen cikin lumana amma daga bisani kuma labari ya sha banban inda maguɗi ya shigo ciki.

    Masu zanga-zangar sun yi kira ga INEC da ta gaggauta ɗaukan mataki tare da sanar da sahihin sakamakon zaɓen da aka gudanar a yankunan Ebonyi domin kare afkuwar tashin hankali.

    Mrs Paulin Onyekachi, Shugabar INEC a jihar ta Ebonyi, ta yi kira ga masu zanga-zangar da su rungumi zaman lafiya.

  14. An kama jami'an yan sanda da ke da hannu a maguɗin zaɓe a jihar Rivers

    Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta sanar da kama wasu jami'anta uku bayan da suka bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ya nuna suna da hannu a maguɗin zaɓe.

    Bidiyon ya nuna jami'an ƴan sandan da ke bakin aiki a lokacin zaɓen cikin wata mota mai lamba "RRT O50".

    Sanarwar da kakakin rundunar, SP Garce Iringe-Koko ta fitar ta ce an kama motar domin gudanar da bincike.

    Rundunar ta kuma bai wa al'ummar Rivers tabbacin ci gaba da aikinta na tabbatar da doka da oda da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda aka samu da aikata ba dai-dai ba.

    Rundunar ta kuma buƙaci al'umma su kwantar da hankalinsu su kuma dakaci sanarwar sakamakon zaɓe a hukumance.

    View more on twitter
  15. Sakamakon zaɓen jihar Yobe

    Fafesa Umaru Pate shi ne baturen zaben jihar, wanda ya gabatar da bayanai a zauren tattara sakamakon shugaban ƙasa dake Abuja.

    Abin da jam'iyyu suka samu

    APC 151,459

    LP 2,406

    NNPP 18,270

    PDP 198,567

    An soke zabe a wata rumfar zaɓe a Fika mai yawan jama'a da suka kai 781 saboda na'urar tantance masu kaɗa ta kasa tanatance su. Haka kuma an soke wata rumfa a Jakusko mai masu zaɓe 1,073 saboda an lalata kayan zabe.

  16. Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Ogun

    Jumullar kuri'un jihar su ne 2 688 305

    Yawan wadanda aka tantance su ne 612 341

    Yawan wadanda aka jefa su ne 611 448

    Yawan kuriun da aka jefa daidai 580 124

    Wadanda suka lalace su ne 31324

    Abin da jam'iyyu suka samu :

    APC 341, 554

    PDP 123,831

    LP 86 829

    NNPP 2,200

    APMA 6,012

    APGA 934

    ADP 1,734

    ADC 10, 529

    Party A 1,153

    An soke wasu daga cikin zaben saboda aringizo na kada kuri'a sama da daya da kuma neman rikici zaben.

  17. Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Oyo

    Hukumar zaɓen Najeriya a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa kamar haka:

    APC - 449,884

    PDP -182,977

    LP - 99,110

    NNPP - 4,095

    Farfesa Olusola Babatune Kayode shi ne babban jami'in da ya gabatar da sakamakon a wajen tattara sakamakon zaben shugaban ƙasa a Abuja.

  18. Labarai da dumi-dumiWakilan PDP da na LP sun fice daga wajen tattara sakamakon shugaban ƙasa a Abuja

    Wakilan PDP da Labour lokacin da suke ficewa daga ɗakin bayyana sakamakon zaɓe

    Wakilan jam'iyyun PDP da na Labour Party sun fice daga wajen ɗakin da ake tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa dake gudana a babban birnin ƙasar Abuja.

    Kimanin wakilan jam'iyyu 10 ne suka fice daga ɗakin bayan shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da wakilan suka yi, kan yadda ake tattara sakamakon.

    Sun nemi shugaban na INEC ya ba da umarnin sanya duka sakamakon jihohi a shafin intanet na hukumar ta zaɓe, kamar yadda aka tsara.

    Shugaban na INEC ya bayyana musu cewa, za a duba duk wasu ƙorafe-ƙorafe da jam'iyyu suka gabatar, amma kamar yadda yake bisa doka, za a yi hakan ne bayan tattara sakamako.

    Ficewar ta su alama ce ta nuna cewa ba su gamsu da bayanin da Farfesa Mahmud Yakubu ya yi musu ba.

  19. Kura ta lafa a Legas bayan hargitsin da aka samu bayan zaɓe

    Legas

    Rundunar ƴan sanda a jihar Legas ta tabbatar da samun hatsaniya a jihar Legas inda wasu ɓatagari suka kutsa cikin kasuwanni dai-dai lokacin da al'umma ke ci gaba da dakon sakamakon babban zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar Asabar.

    Rundunar ta ce tuni komai ya lafa har ma ɗan takarar APC na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu suka fitar da sanarwa inda suke neman jama'a su kwantar da hankalinsu.

    Sun bayyana haka ne bayan da sakamakon wucen gadi da hukumar zaɓe a jihar ta fitar ya nuna cewa Jam'iyyar Labour ce ta samu nasara a jihar.

    Legas

    Tinubu dai ya ce nasarar da Labour ɗin ta samu ba dalili bane na tada rikici saboda dimokraɗiyya ta bai wa kowa damar jefawa zaɓinsa ƙuri'a.

    Gwamna Sanwo Olu ya ba da rahoton samun hargitsi da wasu sassan jihar amma ya ce ya bai wa hukumomi umarnin tabbatar da doka da oda.

    Jami'an rundunar sojin ƙasar ma suna ci gaba da rangadi a wasu Lagos Island domin kare al'umma da dukiyoyinsu.

    Legas
  20. APC ta lashe kujerun sanata uku a Katsina amma Atiku ya doke Tinubu

    ...

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Katsina ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan samun ƙuri'u mafi rinjaye.

    Sai dai a ɓangare guda jam'iyyar APC mai mulki ce ta lashe dukkanin kujerun majalisar dattijai, wato na yankin Daura, da Katsina ta tsakiya da kuma shiyyar Funtua.

    A ɓangaren majalisar wakilan tarayya kuwa jam'iyyar PDP ce ta lashe kujeru tara daga cikin 15.