Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  2. Gwamnatin Guinea Bissau za ta karrama Shugaba Buhari

    Guinea Bissau

    Gwamnatin Guinea Bissau za ta karrama shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da lambar girmama mafi a kasar.

    Za ta karrama shugaba Buharin ne bisa la'akari da gudummuwar da yake bayarwa wajen daidaitawa da bunkasa demokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma.

    Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoko Embalo shi ne zai lika wa shugaba Buharin lambar yabon, a wani gagarumin biki da aka shirya a kasar.

    Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin Guinea Bissau din ta yanke shawarar karrama shugaba Buharin da lambar yabo ko girmamawa mafi daukaka ne sakamakon gagarumar gudummuwar da yake bayarwa wajen raya dimokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma.

    Kuma wannan ne ya sa shugaban kasar, Umaru Sissoko Embalo da kan sa ya gayyaci shugaban Najeriyar zuwa Guinea Bissau domin a yi bikin karramar a fadar gwamnati.

    Bayan lambar yabon, a cewar sanarwar, yayin bikin akwai wani titi da za a raɗa masa sunan shugaba Muhammadu Buharin duka a cikin Bissau, babban birnin kasar.

    Bikin dai kamar yadda sanarwar ta fayyace zai mai da hankali ne wajen yin bayani a kan rawar da shugaba Buharin ya ke takawa wajen yin jagorancin da ya kasance abin koyi a shiyyar Afirka ta yamma musamman ma kasar Guinea Bissau.

    Akwai kuma batun kwaɗaita wa shugabanni kyawawan dabi'u na son zaman lafiya da siyasa irin wadda ake damawa da kowa da kowa da nuna halin gima ko mutunci, tare da karfafa tsare-tsaren tattalin arziki don cigaban al'ummomin shiyya baki daya.

    Wata ribar-kafa atttare da bulaguron, kamar yadda Mallam Garba Shehu ya ce da shugaba Buhari da takwaransa na kasar Guinea Bissau za su yi amfani da wannan dama wajen tattaunawa a kan hanyoyin ciyar da kasashen nasu gaba.

  3. Kungiyar M23 za su soma janyewa daga yankunan da suka kwace a DR Congo

    Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƴan tawaye a Gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, M23 ta ce a shirye take ta fara janyewa daga yankunan da ke ƙarƙashin ikonta.

    Tuni dai ƙungiyar ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan da ya gabata sai dai hukumomin Congo sun zargi ƙungiyar da ci gaba da kai farmaki.

    Hukumomi a Kinshasa sun zargi Rwanda da goyon bayan M23, wani abu da gwamnatin Rwandan ta musanta.

    Ƙungiyoyin ƴan tawaye da dama a Congo sun shiga tattaunawar sulhun da aka yi a Kenya wadda tsohon shugaban ƙasar, Uhuru Kenyatta ya shiga tsakani.

    Sai dai rahotanni na cewa ƙungiyar M23 ba ta samu goron gayyata ba.

  4. Hungary ta datse wani kunshin tallafin bilyoyi daloli ga Ukraine

    Hungary ta toshe wani shirin kunshin tallafi na biliyoyin daloli ga Ukraine saboda takun saƙar da ke tsakaninta da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

    Ministocin kuɗi na EU sun gana a Brussels domin kammala aikin miƙa kuɗin amma wakilin Hungary ya hau kujerar naƙi domin hana aiwatar da lamarin.

    Firaministan Hungary na baya-baya da yin hulɗa da EU saboda ita ma an hana mata damar karɓar kunshin tallafi.

    EU ta hana Hungary karɓar kuɗaɗen har sai ta inganta manufofinta na yaƙi da rashawa sannan ta sauya tsarin da take bi wajen naɗa alƙalai.

  5. Sojoji sun fatataki Al Shabab daga wani muhimmin yanki a Somalia

    Sojojin Somalia na haɗin gwiwa da jami’an tsaron sa kai sun fatattaki mayaƙan Al Shabab daga wani muhimmin gari da ke tsakiyar ƙasar wanda masu iƙirarin Jihadi suka ƙwace tsawon shekara shida.

    Bayan zaɓen Hassan Sheikh Mahamud a matsayin shugaban ƙasa a watan Mayu ne, ya ayyana yaƙi kan Al Shabab.

    Magajin garin Adan Yabal ya ce mayaƙan sun ƙwace garin ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba.

    A watannin baya-bayan nan ne, dakarun AU suka taimaka wa gwamnati wajen ƙwace iko da ƙauyuka da garuruwa da dama.

  6. Morocco ta fitar da Sifaniya daga Gasar Kofin Duniya a Qatar

    m

    A karon farko Morocco ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan da ta yi nasara a kan Sifaniya a bugun fenariti a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.

    Tawagogin biyu sun buga minti 90 ba ci daga nan aka yi karin minti 30, sannan aka kai minti 120 ba ci aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.

    Abdelhamid Sabiri ya fara ci wa Morocco kwallo, sai Sifaniya ta barar da daya ta hannun Pablo Sarabia.

    Hakim Ziyech na Morocco ya kara na biyu, sai Carlos Sole daga Sifaniya ya kasa cin wadda ya buga.

    Sai dai kuma Badr Benoun ya kasa ci wa Morocco ta uku, kenan tawagar Afirka ta ci biyu kenan.

    Sifaniya ta buga ta uku ta hannun kyaftin, Sergio Busquet, amma Bono ya tare, wanda ya hana ta Sole shiga raga.

    Achrat Hakimi ne ya buga na uku ya kuma zura a raga, inda Morocco ta kai zagayen gaba da ci 3-0.

    Morocco za ta kara da duk wadda ta yi nasara tsakanin Portugal da Switzerland ranar Asabar a fafatawar Quarter finals.

  7. An samar da maganin zazzabin Lassa a Najeriya

    o

    Hukumar da ke inganta tsirrai da dabbobi ta Najeriya ta ce ta yi nasarar samar da maganin zazzabi Lassa, wanda ke halaka al`umma a wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya.

    Zazzabin Lassa dai ba shi da wani magani sadidan.

    Amma yanzu hukumar ta ce jami`anta sun gano maganin, bayan shafe shekara shida suna gudanar da bincike, kuma a halin da ake ciki yana matakin gwaji.

  8. Najeriya za ta cimma burinta kan fitar da adadin danye man fetur, in ji gwamnati

    Ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva ya sanar da cewa zuwa mayun shekara mai zuwa, Najeriya za ta cimma burin Kungiyar Kasashen Duniya masu azrikin man fetur OPEC domin fitar da gangar mai miliyan daya da dubu dari takwas.

    Wata sanarwa da mai ba ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai Horatius Egua ya fitar, ministan ya ce Najeriya za ta yi iya kokarinta domin ƙara tsaurara tsaro kan manyan hanyoyin da bututun mai na ƙasar suke da kuma toshe duk wani wuri da yake yoyo a bututan.

    Karamin ministan man fetur ɗin Timipre Sylva ya bayyana cewa tun asali dalilin da ya sa Najeriya ta kasa cimma muradun kungiyar OPEC ba wai saboda ta kasa haƙo ɗanyen man fetur ɗin bane, amma saboda kamfanonin da ke haƙo man ba su son tura ɗanyen man ta bututan ƙasar saboda kada su rinka tafka asara.

    Ya bayyana cewa da zarar an ƙara tsaurara tsaro an tabbatar bututan suna lafiya ba su huje ba, za a ci gaba da tura man fetur ɗin domin cimma muradin OPEC din na samar da ganga miliyan daya da dubu dari takwas a kullum.

    Mista Bala Zaka wanda mai shari ne kan makamashi ya ce akwai yiwuwar kalaman da karamin ministan ya yi za su iya zama gaskiya

    Haka kuma ya ƙara jaddada cewa kamfanonin da ke haƙar mai su ma za su samu tagomashi idan aka magance matsalar fasa bututan mai aka tsaurara tsaro.

    Ministan ya ƙara jaddada cewa man da ƙasar ke samarwa ya ƙaru fiye da a baya inda ya ce a halin yanzu ana samar da sama da ganga miliyan ɗaya.

    Ministan ya bayyana cewa gyaran da ake yi a halin yanzu na matatun man Fatakwal da Warri da kuma shirin da ake yi na gyaran matatar Kaduna da bude matatar dangote da ke shirin fara aiki duk wani tabbaci ne da Najeriya ke da shi na samar da wadataccen mai

  9. Xi Jinping na jimamin mutuwar Jiang Zemin

    Shugaban China, Xi Jinping ya yaba wa marigayi Jiang Zemin wanda ya mutu a makon da ya gabata, saboda jajircewarsa wajen yanke shawarwari masu tsauri a lokuta masu muhimmanci.

    A wajen taron addu’oi, Shugaba Xi ya ce Mista Jinag ya tsaya kai da fata a lokacin da ƙasar take fama da matsalolin siyasa a gida da kuma waje.

    An watsa zaman addu’oin ta Talabijin.

    A wasu lokutan, mutanen China suna amfani da mutuwar tsaffin ƴan siyasa wajen sukar shugabanni masu ci.

  10. Ana zargin wasu maza uku da yi wa agola fyaɗe

    'Yan sanda a Ribas ta kama wasu mutum biyar ciki har da mijin matar da ake zargi da yiwa diyarta 'yar shekara 11 fyade.

    An aikata wannan ta'asa ne a karamar hukumar Taru na Ribas.

    Bayan mijin matar da aka yiwa diyarta fyade mai shekara 53, wanda fasto ne kuma malamain makaranta, sauran matasa ne su hudu.

    Uwar yarinyar ta ce tun yarta na da shekara shida mazan ke cin zarafinta.

    Alkalin da ke sauraron karar, Menenen Poromon, ya dage sauraron shari'ar tare da hana belin mutanen da ake zargi.

  11. Rasha ta tsananta hare-hare kan wuraren adana man fetur na Ukraine

    ...

    Kafafen yaɗa labaran Rasha sun rawaito kai ƙarin hare-haren jirage maras matuƙa kan wuraren adana man fetur da ke da nisa daga iyakar Ukraine.

    Hotunan bidiyo daga yankin Kursk a Rasha sun nuna baƙin hayaƙi na tashi daga wata tankar mai a wani sansanin sojoji.

    Gwamnan yankin ya ce an gudanar da taron hukumar yaƙi da ayyukan ta’addanci a yau.

    Game da wutar da ta tashi a sansanin Kursk, an ɗauki matakin soke ajujuwa a makarantu biyu.

    Wata wutar kuma ta tashi a yankin Bryansk. Ba a bayar da rahoton asarar rai ko dukiya sanadiyyar lamarin ba.

    A ranar Litinin ne, ma’aikatar tsaro a Rasha ta zargi jiragen Ukraine maras matuƙa da kai hare-hare kan wasu sansanonin sojoji biyu kan yankin Rasha.

    Shugaba Vladmir Putin ya jagoranci wani taron kwamitin tsaronsa sai dai babu cikakken bayani kan abin da ya wakana.

  12. Hisbah ta kama kwalaben giya 18,000

    ...
    Image caption: ...

    Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama wata mota maƙare da kwalaben giya sama da 18,000 a ƙaramar hukumar Gwarzo da ke jihar.

    Kwamandan rundunar, Sheikh Harun Sina ne ya tabbatar wa manema labaru hakan a yau Talata.

    Ya bayyana cewa an kama motar ne yayin da take ƙoƙarin shiga babban birnin jihar.

    Kwamnadan na Hisbah ya ce dokar da ta kafa rundunar ta haramta sha ko sayar da kayan maye a jihar.

  13. Gidan talabijin na Al Jazeera ya maka Isra'ila kotu kan kisan ƴarjarida

    Shireen Abu Aqla
    Image caption: Shireen Abu Aqla

    Kafar yaɗa labarun Al Jazeera ta maka sojojin Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC game da kisan ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Shireen Abu Akleh.

    Lauyan Al Jazeera ya ce wannan muhimmiyar rana ce saboda sun gabatar da cikakkun shaidu a madadin kafar yaɗa labaran kuma abin da Al Jazeera ke nema shi ne a gaggauta sauraron ƙarar ba tare da ɓata lokaci ba.

    An harbe ƴarjaridar ne tana tsaka da aiki yayin wani samamen sojojin Isra’ila a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan cikin watan Mayu.

    Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar cewa akwai yiwuwar sojojinta ne suka halaka Ms Abu Akleh amma a cewarsu bisa kuskure.

    Firaminista Yair Lapid ya yi watsi da batun gudanar da bincike daga waje.

    Al Jazeera ta ce shaidun da za ta gabatar ga kotun ta ICC za su haɗa da bidiyon da ke nuna lokacin da sojojin Isra’ila suka harbi ƴar jaridar.

  14. Hazo zai lulluɓe wasu jihohin Arewa - NiMet

    ...

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen cewar nan da kwana ɗaya hazo zai lulluɓe wasu jihohin arewacin ƙasar sanadiyyar iska da za ta kwaso ƙura daga ƙasashe maƙwaftaka.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a, Muntari Yusuf, ta ce yanayin zai yi ƙamari na tsawon kwana uku.

    Ta ƙara da cewa bayanan da aka samu bayan lura da yanayi a jamhuriyar Nijar, da Chadi sun nuna yadda iska mai ƙarfi za ta kwaso ƙura har zuwa yankin arewa-maso-tsakiyar Najeriya.

    Jihohin da lamarin zai fi ƙamari a cewar sanarwar su ne Katsina, da Zamfara, da Kano, da Kaduna, da Yobe da kuma Jigawa.

    Ana kuma sa ran cewar yanayin zafi zai sassauto.

    Hukumar ta buƙaci al’ummar jihohin da lamarin zai shafa su ɗauki matakan kariya domin ƙurar da za ta iya cutar da lafiya.

    Ta kuma akwai buƙatar a tanadi kayan sanyi musamman ga yara saboda yanayin sanyi da za a fuskanta.

  15. INEC ta roƙi ƴan Najeriya su kare ofisoshinta

    Mahmood Yakubu

    Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya roƙi al’ummar ƙasar su taimaka wurin kare kadadrorin hukumar gabanin babban zaɓen ƙasar mai zuwa.

    Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshin hukumar a baya-bayan nan.

    Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ƙungiyar dattijan yammacin Afirka, a ofishinsa da ke Abuja, a ranar Litinin.

    Shugaban na INEC ya ce babban abin da ake fargaba gabanin zaɓen mai zuwa shi ne matsalar tsaro.

    Ya ce “an kai hari a ofisoshinmu a ƙananan hukumomi uku, a cikin ƙasa da mako uku, irin waɗannan hare-hare guda bakwai ke nan aka kai a cikin wata huɗu.”

    Ya ƙara da cewa “nauyi ne a kanmu baki ɗaya mu haɗa hannu domin kare su. Dole ne a daina kai hare-haren kuma wajibi ne a kamo tare da gurfanar da masu alhakin kai harin.”

    Sai dai ya tabbatar wa al'umma cewa za a gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara, duk da barazanar tsaro da ake fuskanta.

  16. Wasu sun yanka mai ciki domin sace ɗan-tayi

    ...

    Hukumomi a Mexico sun ce wata mai juna biyu ta rasa ranta bayan da wasu ɓata-gari suka farke cikinta suka sace ɗan-tayi.

    Wata sanarwa daga ofishin mai shari'a na jihar Veracruz ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ɗauke da jariri.

    A ranar Litinin ne aka gurfanar da waɗanda ake zargin, mace da namiji bisa zargin su da laifin garkuwa da mutune da kuma kisan mace.

    Wani daga cikin masu gudanar da binciken ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa ana zargin mutanen biyu sun aikata laifin ne saboda daya daga cikin maharan ta gaza samun ciki..

    'Yan uwan wadda aka kashen sun ce an yaudare ta ne ta shafin sada zumunta inda aka yi alkawarin yi mata kyautar kayan jarirai.

    Wannan ne karo na uku da aka samu irin wannan kisa a cikin shekarun da suka gabata.

    An kiyasata cewa an kashe mata 1,000, bisa dalilai masu nasaba da jinsi, a kasar ta Mexico cikin shekara ta 2021.

  17. Rashin aikin yi ne ke rura wutar rikici a arewa-maso-gabas Peter Obi

    Peter Obi
    Image caption: Peter Obi

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya ce tarin matasa marasa aikin yi da ake da su a arewa-maso-gabashin Najeriya na daga cikin abubuwan da ke ƙara iza wutar rikici a yankin.

    Obi, wanda ya bayyana haka a Abuja, sa'ilin da ya gana da masu ruwa da tsaki daga yankin, ya ce dubban matasa ne suke wayar gari a yankin babu abinci kuma babu muhalli.

    Sai dai ya ce Allah ya huwace wa yankin makeken filin noma wanda za a iya amfani da shi wajen noma abinci da kuma kayan gona da za a fitar zuwa ƙasashen ketare.

    Arewa maso gabashin Najeriya dai na fama da matsalar tsaro ta ƙungiyar Boko Haram, sai dai rikicin ya yi sauki a baya-bayan nan inda yawan hare-haren da mayakan ke kai wa suka ragu.

    Amma har yanzu akwai ɗinbin ƴan gudun hijira da rikicin ya tarwatsa waɗanda ke rayuwa ko dai a sansanonin da gwamnati ta tanada ko kuma wasu garuruwan na daban.

    Ya bayyana cewar matsalar tsaro za ta zama tarihi idan ya zama shugaban ƙasa.

  18. An kama wani ɗan ci-rani da zargin kai hari da wuƙa a Jamus

    ...

    Ƴan sanda a Jamus sun kama wani mai neman mafaka ɗan asalin ƙasar Eritrea bisa zargin shi da hannu a harin da aka kai wa wasu ɗalibai mata su biyu, inda ɗaya ta mutu, ɗayar kuma ta samu munanan raunuka.

    Jami'ai sun ce ɗaliban masu shekara 13 da 14 na kan hanyarsu ce ta zuwa makaranta a ranar Litinin a wani ƙauye a daidai lokacin da wani ya fito daga gidan da ake ajiye masu neman mafaka ya kai masu hari da wuƙa.

    Daliba mai shekara 14 ta rasu sanadiyyar raunukan da ta samu.

    Ƴan sandan da suka bincike gidan sun zaƙulo wani mutum ɗauke da wuƙa, wanda suke tunanin shi ne ya kai farmakin.

    Yanzu haka yana tare da jami'an tsaro a wani asibitin da ake yi masa magani bisa wani ciwo da ba a bayyana ba.

  19. Majalisar dokokin Afirka ta kudu ta ɗage zaman tantance makomar shugaban ƙasar

    Daga Nobuhle Simelane

    ...

    An ɗage zaman da ya kamata majalisar dokokin Afirka ta kudu ta gudanar a yau domin yin nazari kan rahoton da ya samu shugaban ƙasar da laifin yin karan-tsaye ga kundin tsarin mulki, zuwa nan da mako guda.

    Rahoton dai ya ce Ramaphosa ya rufe wata sata da aka gudanar, inda ya ɓoye kuɗin a gonarsa.

    Tuni shugaban ya musanta zargin, kuma mai magana da yawunsa ya ce an jirkita rahoton.

    Kwamitin tsara ayyukan majalisar ya yi zama a ranar Litinin inda ya amince a mayar da zaman da za a yi kan batun zuwa ranar 13 ga watan Disamba domin bai wa ƴan majalisa damar halartar zauren majalisar da ke Cape Town.

    Za a tattauna ne kan ko akwai buƙatar tsige shugaba Ramaphosa, sai dai jam'iyya mai mulki ta ANC ta ce za ta yi adawa da duk wani mataki na tsige shi.

    A ranar Litinin shugaban ƙasar ya garzaya kotu inda ya buƙaci kotu ta hana majalisar ɗaukan kowane irin mataki a kansa.

  20. Zaɓen 2023: Atiku ya ce zai sayar da matatun man fetur

    Atiku Abubakar
    Image caption: Atiku Abubakar

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen Najeriya na 2023, Atiku Abubakar ya ce zai sayar da matatun man fetur domin samar da kuɗin tallafa wa ƙananan sana’o’i.

    A lokacin yaƙin neman zaɓe a Lagos, Atiku ya ce zai samar da kuɗi dala biliyan goma domin tallafa wa matasa su samu aikin yi.

    A cewarsa “idan na sayar da matatar mai ta Fatakwal, da ta Warri da kuma matatar mai ta Kaduna.”

    Bugu da ƙari a lokacin yaƙin neman zaɓen nasa, Atiku ya ce gwamnatin tarayya ce ta gina birnin Legas ba gwamnatin jiha ba.