Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

.

Asalin hoton, Ado Doguwa/Facebbok

Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ba wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu na kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano.

A yau Laraba ne jami'in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar da haka, tare da cewa za a sake zaɓen a wasu runfuna 13.

Tun da farko an bayyana Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilan ta Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Sai dai kuma bayan da hukumar zaɓen ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓukan majalisun tarayya da aka yi ranar, ba ta sanya sunansa ba a don haka ba ta ba shi takardar shedar cin zaɓen ba.

INEC ta ce an bayyana sunanasa ne a matsayin wanda ya yi nasara a bisa tilastawa.

Wannan ya biyo bayan kama Ado Doguwan bisa zargin hannu a tashin hankalin da aka yi a mazaɓar a lokacin tattara sakamkon zaɓen.

Rahotanni sun ce an kashe aƙalla mutum biyu lokacin da aka kunna wuta a hedikwatar jam'iyyar hamayya ta NNPP a yankin.

'Yan sanda sun gurfanar da dan majalisar a gaban kotun majistare, wadda ta tura shi gidan waƙafi.

Amma kuma wata kotun tarayya ta bayar da belinsa bisa dalilin cewa laifukan da ake zarginsa da su sun haɗa da kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba saboda haka kotun majisatre ba ta da damar da za ta tura shi zaman waƙafi.

A ranar 6 ga watan nan na Maris ne Mai shari'a Muhammad Nasir Yunusa ya bayar da belinsa a kan kuɗi naira mliyan 500.