Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba da Mukhtar Adamu Bawa

time_stated_uk

  1. Obasanjo ya nemi Kotun Birtaniya ta yi wa Ekweremadu sassauci

    Hoton Obasanjo

    Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya aika wasiƙa ga Kotun Birtaniya da ta samu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da mai ɗakinsa Beatrice da laifin safarar ɗan'adam don cirar sashen jikinsa.

    A wasiƙar da ya aike wa babban akawun kotun da ke London, tsohon shugaban ƙasar ya nemi akawun ya sa baki, kuma ya tabbatar cewa gwamnatin Birtaniya ta yi sassauci a hukuncin da za ta yanke.

    Manyan jaridun Najeriya sun ruwaito cewa Obasanjo ya aika wasiƙar Birtaniya, inda Ekweremadu ke iya fuskantar ɗaurin shekara 10 bisa tanadin dokokin ƙasar, bayan an same shi da laifi.

    Tun bayan samun Ekweremadu da mai ɗakinsa da laifin ne, ake tsare da su har zuwa 5 ga watan Mayu - ranar da za a yanke hukunci.

    An kama Ekweremadu da matarsa bayan wani matashi ya yi ƙorafi kan yadda mutanen biyu ke ƙoƙarin cire masa ƙodarsa.

    Sai dai, Obasanjo a cikin wasiƙar mai kwanan watan 3 ga Afrilun bana, ya ce Ekweremadu da mai ɗakinsa sun koyi darasi daga abin da ya faru.

  2. Gwamnatin Kaduna ta mayar da malaman da ta kora bakin aiki

    NASIR EL-RUFAI

    Gwamnatin Kaduna ta amince a mayar da malaman makarantar firamare fiye da duɓu ɗaya da ta sallama a Yunin 2022 bayan yi musu wata jarrabawar tabbatar da ƙwarewarsu.

    Kakakin ma'aikatar ilimi ta jihar Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da aka fitar yau Laraba.

    Hajiya Hauwa ta ce malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a Yunin 2022 ne ma'aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.

    Ita ma jaridar Punch ta ruwaito ma'aikatar ta yi bayanin cewa an sallami malamai 2,192 saboda ƙin rubuta jarabawar yayin da malamai 165 kuma aka kore su saboda rashin tabuka abin a zo a gani.

    Wasu daga cikin malaman da matakin ya shafa sun yi ƙorafin cewa sun rubuta jarrabawar kuma sun ci kuma duk da haka aka kore su yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa ba su da lafiya a lokacin da aka yi jarabawar kuma sun gabatar da takardar shaida.

    Su kuwa wasu malaman cewa suka yi an yi garkuwa da su ne a lokacin, yayin da wasu suka ce a lokacin an dakatar da su ne saboda aikin tantance takardunsu.

  3. An yi wa ƴan tawaye afuwa kan kisan tsohon shugaban Chadi

    Chad

    Gwamnatin Chadi ta ce ta yi afuwa tare da sakin ƴn tawaye 380 da suke zaman ɗaurin rai da rai a gidan yari saboda mutuwar tsohon shugaban ƙasar, Idriss Deby.

    An kashe tsohon shugaban ƙasar shekara biyu da suka wuce a filin daga a ƙoƙarin yaƙar ƴan bindiga da ake kira Front for Change and Concord.

    A watan Maris ne aka yanke wa ƴan tawaye sama da 400 hukunci saboda aikata laifukan ta'addanci da ɗaukan yara aikin soja da kuma cin zarafin shugaban ƙasa.

    Ɗan tsohon shugaban ƙasar - Mahamat Idriss Déby - ya yi wa akasarinsu afuwa.

    Mahamat Deby ya karɓi ragamar ƙsar bayan mutuwar mahaifinsa.

    Sai dai afuwar ba ta shafi jagoran ƴan tawaye Mahamat Mahdi Ali ba wanda ake nema ruwa a jallo.

  4. 'Tun yaƙin basasa rabon da Najeriya ta samu rarrabuwar kai kamar yanzu'

    Hoton Sanusi

    Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II ya yi gargaɗi cewa Najeriya ta fi fama da rarrabuwar kai saboda ƙabilanci da bambancin addini tun bayan yaƙin Biafra fiye da shekara 50 da ta wuce.

    Da yake jawabi a wani taro a Legas, Muhammadu Sanusi wanda ya ce "ba na tunanin Najeriya ta taɓa kasancewa a mawuyacin yanayi kamar yanzu tun bayan yaƙin basasa. Muna da ƙalubale game da aikin gina ƙasar nan.

    Ya ce Najeriya tana fama da bambance-bambancen addini da na ƙabilanci.

    "Muna da tattalin arzikin da ke fuskantar taɓarɓarewa kuma abin takaici, da alama muna fama da ƙarancin shugabanci na gari."

    Kalaman tsohon gwamnan CBN ɗin na zuwa ne yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke shirye-shiryen miƙa mulki ga Bola Tinubu.

    Tinubu ne ya yi nasara a kan manyan abokan takararsa - Atiku Abubakar da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasar mai zafi da aka yi a watan Fabrairu.

    Atiku da Obi sun yi fatali da sakamakon zaɓen, kuma tuni suka shigar da ƙara a kotu.

  5. An samu ƴar siyasar Zimbabwe da laifin yaɗa labaran ƙarya

    Fadzayi Mahere
    Image caption: Fadzayi Mahere fitacciyar lauya ce kuma ƴar hamayya a siyasar Zimbabwe

    An samu wata babbar ƴar hamayyar siyasa a Zimbabwe Fadzayi Mahere da laifin yaɗa wani bidiyon ƙarya a shafin Tuwita cikin 2021 inda a ciki ake zargin wani jami'in ɗan sanda mai bayar da hannu da kashe wani jariri.

    Daga bisani kuma an gano cewa jaririn yana da rai kuma bai ji wani rauni ba.

    Mai shari'a Tuarai Manwere ta ce wallafa bidiyon ganganci ne wanda aka yi shi domin cire wa mutane ƙwarin gwiwar da suke da shi kan jami'an ƴan sandan ƙasar.

    Mai shari'ar ta ce ya kamata a ce Mahere ta tantance bidiyon kafin yaɗa shi.

    Jam'iyyar Ms Mahere ta Citzens' Coalition for Change (CCC) ta yi tur da matakin kotun.

    A ganin jam'iyyar, an yi wa Mahere haka ne saboda ra'ayinta na siyasa.

  6. Korona ta kashe mutum 30 a Iran cikin sa'a 24

    Korona

    Ma'aikatar lafiya a ƙasar Iran ta sanar da cewa cutar korona ta kashe mutum 30 cikin sa'a 24 da ya gabata.

    Rahotanni sun kuma bayyana cewa sabbin mutum 1,103 sun kamu da cutar .

    Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce waɗanda suka kamu da cutar 778 na sashin kulawa ta musamman a asibiti ana duba lafiyarsu.

    Ya zuwa yanzu, ana fargabar cewa biranen ƙasar da dama na cikin barazana kan mutanen da ke ci gaba da kamuwa da cutar.

  7. Abin da ya sa aka ga tankokin yaƙin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya

    ...

    Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta yi karin haske kan wasu motocin yaki na Majalisar Dinkin Duniya da aka gani a ƙasar da cewa Kudancin Sudan ne suka nufa.

    Bayanin hakan ya zo ne sakamakon wani hoton bidyon da ke wadari a shafukan asada zumunta, wanda ke nuna motocin yaki na majalisar da wasu kayayyaki a wasu jihohin da ke kudancin kasar.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hedkwatar tsaron Tukur Gusau ya fitar, ya ce an tanadi motocin ne don aikin wanzar da zaman lafiya a wajen Najeriya.

    Ya ce a halin yanzu Najeriya na tura dakarunta zuwa aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a ƙasashe da dama; na baya-bayan nan shi ne na wanda aka yi a Kudancin Sudan.

    “Hedkwatar tsaron Najeriya na son tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ƙasarmu ba ta cikin wata barazana da za ta sa a aiko da dakarun Majalisar Dinkin Duniya...motocin da aka gani ana fitar da su ne daga tashar ruwa ta Warri don zuwa aikin wanzar da zaman lafiya a Kudancin Sudan," in ji Gusau.

    Ganin motocin da aka yi ya sanya fargaba a zuƙatan mutane bayan zaman ɗar-ɗar na tsawon makonni da ake ciki bayan zaɓukan da aka gudanar a ƙasar.

    Najeriya dai ta fuskantar jerin hare-hare da ƴan bindiga ke kai wa ƙauyuka, wanda ke ƙara janyo taɓarɓarewar tsaro.

  8. Mahari ya kashe ƙananan yara a makarantar reno a Brazil

    Makarantar reno

    Jami'ai a Brazil sun ce wani mahari ya kashe aƙalla yara huɗu a makarantar renon yara da ke birnin Blumenau a Kudancin ƙasar.

    Ƙarin wasu yara huɗu kuma sun ji rauni sakamakon harin da mutumin mai shekara 25 ya kai da ƙarfe tara agogon ƙasar.

    Likitoci sun ce dukkan waɗanda suka ji rauni ƴan ƙasa da shekara uku ne.

    Ƴan sanda sun faɗa wa kafafen yaɗa labarai cewa maharin ya miƙa kansa kuma tuni aka tsare shi.

    Jami'an kashe gobara sun ce kusan ƙananan yara 40 ne ke cikin makarantar a lokacin harin.

    Sun ƙara da cewa maharin ya haura katanga domin samun shiga makarantar inda kuma ya afka wa yaran.

    Iyaye dai sun garzaya makarantar bayan da suka samu labarin abin da ya faru.

    Hukumomi kuma sun dakatar da azuzuwa a Blumenau har zuwa gobe.

    Gwamnan jihar Santa Catarina inda birnin Blumenau yake, ya ayyana makokin kwanaki uku domin jimamin mutuwar ƙananan yaran.

  9. Ƙasashen Larabawa sun yi Alla-wadai da harin dakarun Isra'ila kan Masallacin Kudus

    Ƙasashen Larabawa

    Ƙasashen Larabawa sun yi Alla-wadai da harin da sojojin Isra'ila suka kai Masallacin Kudus da kuma artabu tsakanin masallata da jami'an tsaro.

    Babban Sakatare-janar na kungiyar ƙasashen larabawan, Ahmed Abdoul Ghiet, ya bayyana cewa, dabi'ar masu tsattsauran ra'ayi da ke kula da manufofin gwamnatin Isra'ila, za su haifar da rikice-rikice da Falasɗinawa matukar ba a kawo karshen su ba.

    A yau, kungiyar za ta gudanar da wani taron gaggawa domin tattauna abubuwan da suka faru a birnin Kudus.

  10. Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Easter

    Rauf Aregbesola

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranakun Juma'a 7 ga watan Afrilu da kuma Litinin 10 ga wata a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan bikin Easter na wannan shakarar.

    Ministan al'amuran cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma'aikatar Shuaib Belgore ya fitar ranar Laraba.

    Sanarwar ta buƙaci kiristocin ƙasar da su yi koyi da halayen sadaukarwa, da haɗin kai, da yafiya, da mutunta juna, da soyayya da zaman lafiya da haƙuri na Yesu Almasihu.

    Ministan ya kuma yi kira al'ummar Kiristocin ƙasar da su su yi amfani da lokutan bukukuwan na Easter domin yi wa ƙasar addu'o'in samun zaman lafiya da kawo ƙarshen matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

  11. 'Shari'ar Trump za ta iya kwashe tsawon shekaru'

    Donald Trump

    Wani tsohon mai gabatar da ƙara ya faɗa wa BBC cewa shari'ar da ake yi wa Donald Trump, za ta iya ɗaukar tsawon shekaru.

    "Ba za a iya gama sauraron shari'ar ba, watakila sai a 2025 ko ma fiye da haka," in ji Mariotti.

    "Game da yadda sakamakon shari'ar zai kasance, ina ganin ko da an gama ta, Trump zai fuskanci ƙarin wasu tuhume-tuhume."

    Da yake magana kan sauran tuhume-tuhume da Trump ke fuskanta, Manotti ya ce "Ina ganin sauran tuhume-tuhumen da za a yi wa Trump za su ƙara janyo hankalin mutane fiye da ta farko, saboda za su kasance masu wahala a gare shi.

    Trump zai iya fuskantar tuhume-tuhume aƙalla a wasu shari'o'i biyu, ciki har da binciken lauya na musamman kan kokarin tsohon shugaban wajen kawo cikas a zaɓen 2020, da kuma yadda ya tafiyar da bayanan sirri bayan barin ofis.

  12. Uwargidan gwamnan Kano na farko, Ladi Baƙo ta rasu

    ...

    Da tsakar ranar yau Laraba ne, ake jana'izar uwargidan tsohon gwamnan Kano, Hajiya Ladi Baƙo, bayan ta rasu a wani asibiti da ke cikin jihar.

    A fadar Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu za a yi wa marigayigar mai shekara 93 salla, kafin a binne ta daga bisani.

    'Yar marigayiyar, kuma tsohuwar kwamishiniya a jihar Kano, Hajiya Zainab Audu Baƙo ce ta tabbatar da mutuwar cikin alhani lokacin zantawa da BBC Hausa ta wayar tarho.

    Mijin marigayiyar, Kwamishinan 'Yan sanda, Audu Baƙo ya jagoranci Kano a matsayin gwamna daga 1967 zuwa 1975.

    Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin Kano da suka fi aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a jihar.

  13. Yadda direban jirgin sama ya yi artabu da maciji a sararin samaniya.

    gamsheka

    An yaba wa wani matuƙin jirgin ɗan Afirka ta Kudu kan nasarar saukar gaggawa da ya yi, bayan da ya lura da wani maciji nau'in gamsheƙa a ƙarƙashin kujerar zamansa.

    Rudolph Erasmus ya ɗauko fasinjoji huɗu daga birnin Cape Town zuwa arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin amma saboda artabun da ya yi da gamsheƙar ya sa shi saukar gaggawa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito

    Direban ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Time Live cewa “ina duba ƙarƙashin kujerata, kawai sai na ga macijin na ƙoƙarin mayar da kansa ƙarƙashin kujerar”.

    Sarar gamsheka zai iya kashe mutum cikin mintuna 30 idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

    Minista harkokin sufurin jiragen sama ta Afirka ta kudu ya yaba da jarumtar Mr Eramus, kamar yadda shafin yanar gizo na news24 ya ruwaito.

    Direban jirgin yace ya shiga yanayi mai rikitarwa wajen fada wa fasinjojin ainihin abin da ya sa ya yi saukar gaggawar.

    Na fada musu cewa akwai matsala., akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yaƙinin cewa yana ƙarƙashin kujera ta don haka za mu yi saukar gaggawa”.

    Ya yi ƙoƙarin ganin ya yi saukar gaggawa a birnin Welkom dake Afirka da Kudu.

    Injiniyoyin da suka caje jirgin ba su ga gamsheƙar ba, inji Mr Eramus.

    Ya ce yana sa ran komawa bakin aikinsa a ranar Laraba.

  14. Fursunoni uku sun mutu a artabu da kungiyoyin ƴan daba a Ecuador

    Gidan yarin Ecuador

    Akalla fursunoni uku sun rasa ransu a yayin wata taho mu gama da aka yi tsakanin kungiyoyin 'yan daba a wani gidan yari da ke Ecuador.

    Ministan cikin gidan ƙasar ya ce kawo yanzu jami'an tsaro sun shawo kan rikicin da ya barke a gidan yarin da ke birnin Guayaquil.

    Ana yawan samun tashin hankali a yankin da gidan yarin yake a shekarun baya-bayan nan,tun bayan da kungiyoyin da ke hada-hadar miyagun ƙwayoyi na Mexico suka yi hayar 'yan dabar da ke yankin domin su rinka yi musu safarar hodar-iblis ɗin da aka samar a yankin.

    A ranar Asabar ɗin da ta wuce, shugaban ƙasar Guillermo Lasso ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankunan da ake yawan samun rikici.

  15. Kotu ta samu likitoci uku da laifin mutuwar matar da aka yi wa fyaɗe a asibiti

    Fyaɗe

    Wata kotu a ƙasar Guinea ta samu wasu likitoci uku da laifin mutuwar wata budurwa da aka yi wa fyaɗe a asibiti.

    Gwamnati ta ce a shekarar 2021, M'Mah Sylla, ta mutu a Tunisia inda aka kai ta don neman magani, bayan an yi mata fyaɗe.

    Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Guinea.

    Yanzu haka, wata kotu a Conakry babban birnin ƙasar ta yanke wa Daniel da Patrice Lamah hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

    Sannan an yanke wa likita na uku, Celestin Millimouna - wanda ke gudun hijira - hukuncin ɗaurin shekara 20.

    An same su da laifin far wa matar, da yi mata duka, da kuma zubar da ciki.

    Haka zalika, kotu ta samu Patrice Lamah da Millimouna da laifin aikata fyaɗe.

  16. Mene ne hukuncin fita sallar dare ga mace a lokacin Ramadan?

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  17. Hotunan yadda ƴan sandan Isra'ila suka kai samame kan masallata a Masallacin Kudus

    Ƴan sandan Isra'ilan sun kai samame Masallacin Kudus ɗin ne lokacin da musulmi ke ibada.

    Ƴan sandan sun ce sun kai harin ne a matsayin martani ga masu zanga-zanga.

    Masallacin Kudus
    Image caption: Nan, ƴan sanda ne ke jan wata mace a ƙasa a cikin Masallacin
    Masallacin Kudus
    Image caption: Nan, wani ɓangare ne na Masallacin Ƙudus, mutane na karatun Al-Qur'ani
    Masallacin Kudus
    Masallacin Kudus

    Kakakin shugaban Falasɗinawa ya yi Allah-wadai da harin na Isra'ila, yana cewa da ma sun gargaɗi masu mamayen kada su keta haddin wurin, ta hanyar shiga wuraren ibada masu tsarki na Masallacin, abin da zai iya haddasa mummunan rikici.

  18. Ƴan sanda sun rufe majalisar dokokin jihar Filato kan rikicin shugabanci

    Majalisar dokokin Filato

    Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta rufe zauren majalisar dokokin jihar kan rikicin shugabanci da ake ci gaba da yi.

    'Yan sandan kwantar da tarzoma sun isa harabar majalisar ne da misalin karfe 5 na safiya, inda suka toshe hanyar shiga.

    Duk da cewa, babu wata sanarwa a hukumance daga 'yan sandan kawo yanzu, amma rahotanni sun ce hakan ba ya rasa nasaba da rikici tsakanin mambobin majalisar a kan wanda zai shugabance ta.

    Kawunan ƴan majalisar ya rabu biyu, inda wasu ke ɓangaren kakakin majalisar na yanzu Rt. Hon Yakubu Sanda, yayin da wasu kuma ke goyon bayan kakakin majalisar da kotu ta mayar kan kujerar, Rt. Hon Ayuba Abok wanda aka tuɓe a watan Oktoban 2021.

    Wata kotu ce ta sake mayar da Ayuba Abon kan kujerarsa ta shugaban majalisar a ranar Litinin, inda washegari yai bayyana a majalisar a matsayin shugaba.