Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma yanzu a madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Buhari ya nemi a kawo ƙarshen tashin hankalin Binuwai

    gg

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen baya-bayan nan da aka samu a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

    Rahotonni sun ce an kashe gwamman mutane a ƙauyen Umogidi da ke ƙaramar hukumar Otukpo

    A wata sanarawa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce za a yi duk mai yiyuwa wajen kawo ƙarhen tashe-tashen hankula a ƙasar.

    Shugaban ƙasar ya yi Allah-wadai kan amfani da abin da ya kira ta'addanci wajen rura wutar faɗan ƙabilanci a ƙasar,.

    Ya kuma bayar da umarnin zaƙulo maharan domin fuskantar hukunci kan laifin da suka aikata.

    Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon harin.

    “Muna miƙa sakon ta'aziyyarmu ga iyalan waɗanda aka kashe. Kuma ƙasarmu za ta tsaya tsayin-daka domin yaƙar ayyukan ɓata-gari da na 'yan ta'adda'', in ji Buhari.

    Daga ƙarshe shugaban ya umarci jami'an tsaron ƙasar da su ƙara sanya idanu tare da sake nazarin fannin tsaro musamman a yankunan da lamarin ya faru.

  3. Rasha na tuhumar Evan Gershkovich da leƙen asiri

    BBC

    Kafar yada labaran Rasha ta ce ana tuhumar wakilin mujallar Wall Street Jounal Evan Gershkovich - wanda aka tsare kwanaki 10 da suka wuce - da leƙen asiri

    Rahotanni sun ce ya musanta zarge zargen da ake masa.

    Babu wasu cikakkun bayanai game da tuhume tuhumen sannan kuma babu wata shaida da kawo yanzu aka gabatar.

    Mujallar ta Wall Street Jounal, ta buƙaci a gaggauta sakin Mr Gershkovich, tana mai bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya da kuma jajircewa a aiki.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ce ta ba shi damar yin aiki a matsayin ɗan jarida a kasar.

    A cikin wata sanarwar haɗaka, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka da ma na marassa rinjaye a majalisar sun ce an tsare shi bisa kuskure, kuma ya kamata a gaggauta sakinsa.

  4. Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa danderu da kazar gida

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon
  5. Hajjin bana: Kano ta sa ranar rufe karɓar kuɗin maniyyata

    haji

    Hukumar kula da alhazai ta jihar Kano ta yi kira ga maniyyata da suka kai kuɗin ajiya a wani ɓangare na zuwa hajjin bana, su kammala biyan kuɗinsu daga nan zuwa ranar 21 ga wannan wata.

    Tun da farko, hukumar alhazan ta buƙaci maniyyatan su cika kuɗin tafiyarsu zuwa naira miliyan biyu da rabi kafin Hukumar kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da haƙiƙanin farashi.

    A ranar Juma'a ne, Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta sanar da kuɗin tafiya aikin hajjin bana, inda Kano ta faɗa cikin jihohin da za su biya N2,919,000.00.

    Da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar, Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Kano, Alhaji Mohammad Abba Dambatta, ya ce nan ba da jimawa ba za a rufe karɓar kuɗin tafiya aikin hajjin.

    Ya ce maniyyatan Kano za su biya sama da naira miliyan biyu da dubu ɗari tara ne saboda tashin farashin dalar Amurka da ƙarin haraji daga Saudiyya da kuma kamfanonin sufurin jiragen sama.

  6. An sake kama fursunan da ya yi ƙaryar mutuwa don kuɓuta daga gidan yari

    An sake kama fursunan nan da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yaudarar mutanen domin yi musu fyade a Tanzaniya.

    Bayan da ya yi ƙaryar mutuwa domin ficewa daga gidan yarin da yake zaune a Afirka ta Kudu.

    Fitar Thabo Bester - wanda ka fi sani da 'Mai fyaɗen Facebook'' - daga gidan yari ta tayar da hankali a shekarar da ta gabata.

    An yi ta samun rahotonnin da ke cewa ana ganin Thabo Bester, ciki har da wani rahoto da ya ce an gan shi a lokacin da yake sayayya a wani shago da ke wajen birnin Johannesburg.

    To sai dai a wannan karon 'yan sandan ƙasar Afirka ta Kudu sun ce an sake kama shi a Tanzaniya.

    A wani taron manema labarai da suka gabatar, sun ce an kama mista Bester ranar Juma'a a lokacin da yake tare da budurwarsa da kuma wani abokinsa.

    A yanzu za a mayar da shi Afirka ta Kudu domin ci gaba da tsare shi.

    An dai yi ta sukar hukumomin kula da gidan yarin bayan tserewar mista Bester a shekarar da ta gabata.

    An zargi kamfanin tsaro na G4S na Birtaniya - wanda shi ke da alhakin lura da gidan yarin - da taimaka wa mista Bester wajen tserewa.

    Thabo Bester dai na fuskantar ɗaurin rai-da-rai ne sakamakon aikata laifin kisan kai.

    A baya an taɓa kama shi da laifin fyaɗe da fashin da ya yi wa wasu mutum biyu bayan da ya yaudare su a shafin Facebook.

    Ƙasar Afirka ta Kudu na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da matsalar fyade a duniya.

  7. Ra'ayi Riga

    Shirin na wannan makon ya yi duba kan yadda mata ke rarraba lokacinsu tsakanin aiki da ibada a watan Ramadan

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  8. Sabon Babban Hafsan Sojojin Nijar ya karɓi ragamar aiki

    Sojin Nijar

    An gudanar da bikin miƙa ragamar jagorancin rundunar sojin Nijar ga sabon babban hafsan sojojin ƙasar Janar Abdou Sidikou Issa.

    Nijar

    A ranar 1 ga wannan wata na Afrilu ne, Shugaba Mohammed Bazoum ya naɗa sabon babban hafsan dakarun sojin Nijar, daidai lokacin da ƙasar ke fafutukar murƙushe ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

    Nijar

    Kawo yanzu, gwamnati ba ta yi cikakken bayani a kan dalilan maye gurbin Janar Salifou Mody, da sabon babban hafsan sojojin, Janar Abdou Sidikou Issa ba.

    A baya dai ya riƙe manyan muƙamai a ɓangaren harkokin sojojin ƙasar.

    Nijar

    Akwai ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Nijar ciki har da Boko Haram wadda ta samo asali daga Najeriya mai maƙwabtaka.

    Nijar

    Mali da Nijar sun amince a farkon watan nan, su yi aiki tare domin murƙushe ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS.

  9. Lafiya Zinariya

    Shirin namu na wannan makon ya duba matsalar gwagwiyewar gashi a goshi da tsakiyar kai, da kuma sanƙo a tsakanin mata.

    Habiba Adamu ce ta gabatar da shirin wanda ya tatauna da wata mace mai fama da wannan lularar, kuma ta bayyana halin da take ciki saboda matsalar.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  10. 'Yan matan Iran ne suka fi fama da cutar kansar mama a duniya

    BBC

    Shugaban cibiyar binciken kansa a Iran Mohammad Esmail Akbari ya ce matan Iran za su riƙa kamuwa da kansar mama shekaru 10 gabanin yadda sauran mata ke kamuwa da cutar a duniya.

    A cewar cibiyar ana yawan samun rahoton kamuwa da kansar mama tsakanin maza da matan Iran, yayin da aka fi samun ta huhu a ƙasashen yamma.

    Mista Esmail ya ce matan Iran na fara kamuwa da cutar kansar mama ne lokacin da suke tsakanin shekara 45 zuwa 55, yayin da sauran matan duniya ke kamuwa da cutar tsakanin shekara 50 zuwa 60, kuma babban dalilin shi ne matasan Iran.

    Ya ce adadin yadda ake kamuwa da kansar maman a kasashen yamma baya ƙaruwa, amma a Iran yana ƙaruwa saboda shekaru da kuma matsalar abubuwan da suke ta'azzara cutar.

  11. Gane Mini Hanya

    Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar da cewa maniyyata aikin hajjin bana za su biya kuɗi da ya kai naira miliyan biyu da dubu 890 a matsayin kuɗin kujera.

    Hira da Nura Hassan Yakasai kwamishina mai kula da ma'aikata da harkokin kudi na hukumar alhazan Najeriya kan karuwar farashin kujerar aikin hajjin bana.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  12. An yanke wa mutanen da suka kashe jakadan Italiya ɗaurin ra-da-rai

    BBC

    Wata kotun soji a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta yanke wa mutum shida ɗaurin rai-da-rai bayan ta same su da laifi a kan kashe jakadan Italiya na ƙasar a watan Fabrairun 2021.

    Luca Attanasio na cikin mutum uku da aka harbe lokacin da aka yi wa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya kwanton ɓauna.

    Sai da aka fara kashe direbansa, kafin a yi awon gaba da shi, tare da mai tsaron lafiyarsa.

    Daga bisani an kashe shi, bayan wasu dakarun ƙundumbala sun yi ƙoƙarin ƙwato shi daga hannun mutanen, aikin bai tafi cikin nasara kamar yadda aka tsara ba.

    Lamarin ya faru ne a gabashin ƙasar, inda kungiyoyi 'yan bindiga da yawa ke harkokinsu.

    Suna tafiya ne a kan titi cikin yankin gandun dajin Virunga, wurin da UNESCO ke da iko da shi a Goma lokacin da lamarin ya faru.

  13. 'Yan bindiga sun kashe mutum 34 a sansanin 'yan gudun hijira da ke Benue

    g

    'Yan bindiga sun kashe mutum 34 a wani hari da suka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke wata makarantar firaimari a ƙauyen Mgaban da ke Ƙaramar Hukumar Benue ta Arewa a ranar Juma'a da daddare.

    Wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun isa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 9 na daren Juma'a.

    Ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai wata mata mai ciki da ɗanta sannan kuma da dama sun jikkata.

    Ka zalika mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na Ƙaramar Hukumar Guma Christopher Waku, ya shaida wa jaridar cewa an kashe mutum 34 yayin da aka jikkata wasu 40 na daban.

    Kakakin 'yan sanda ta jihar SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar sakon waya da ta turawa wakilin jiridar, sai dai ba ta yi wani cikakken ƙarin bayani ba.

  14. Gomman mutane sun jikkata a zanga-zangar Sudan

    BBC

    Gomman mutane ne suka ji raunuka a Sudan yayin wata gagarumar zanga-zanga da aka shirya ranar Alhamis don nuna adawa da mulkin soja

    Masu zanga-zangar sun fusata ne da yawan jinkirin da ake samu wajen sa hannu kan yarjejeniyar ƙarshe don sake dawo da gwamnatin farar hula Sudan.

    Haka kuma, zanga-zangar ta zo daidai lokacin da ake cika shekara huɗu shahararren boren da ya kai ga kifar da tsohon shugaban Sudan mafi daɗewa a kan mulki Omar al-Bashir.

    Ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka toshe manyan titunan babban birnin ƙasar, Khartoum da ma sauran biranen ƙasar.

    BBC

    Da yawansu na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce, wasu kuma suna rera taken yin Allah-wadai da shigar sojoji cikin siyasa.

    Dakarun tsaro sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa cincirindon mutane da ke shirin dannawa zuwa fadar shugaban ƙasa a Khartoum.

  15. ‘Ban ji daɗin yadda zakara ya haɗa ni faɗa da makwabcina ba’

    g

    Mutumin da ya mallaki zakaran da aka zartar wa hukuncin kisa a jihar Kano, ya ce bai ji daɗin yadda marigayin ya haɗa shi faɗa da maƙwabcinsa ba.

    A ranar Talatar da ta gabata ne, Mai shari’a Halima Wali a wata kotu da ke Kano ta yanke wa zakaran hukuncin kisa

    Matakin ya zo ne bayan wasu maƙwabtan mai zakaran biyu suka shigar da ƙara, inda suka zargi zakaran da hana su sakat saboda yawan cara, da zarar sanyin asuba ya kaɗa.

    Isyaku Shu’aibu
    Image caption: Naman zakaran kenan bayan an yanka shi ranar Juma'a

    A tattaunawarsa da BBC, mai zakaran, Isiyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin Kano, ya ce bai taɓa samun saɓani da makwabcinsa ba a tsawon shekara 20 sai a dalilin zakaran.

    Ya kuma ce ba zai yi kewar zakaran ba, kasancewar ba wata shaƙuwar ƙut-da-ƙut suka yi ba.

    Isyaku ya shaida wa BBC cewa yara ne ma suka yanka rigimammen zakaran kafin ma ya dawo gida a ranar Juma’a.

    Tun farko, ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙarar, Yusuf Muhammad, ya ce carar da zakaran ke yi, tana shiga haƙƙinsa don kuwa ba ya samun barci cikin lumana.

    Isyaku Shu’aibu ya faɗa wa kotun cewa da ma ya sayi zakaran ne don bikin Easter, inda ya buƙaci kotun ta yi masa rangwame zuwa ranar Juma’a kafin zartas masa da hukunci don amfani da naman a ranar Good Friday, abin da kotun ta amince da shi.

  16. Mace-macen mata masu haihuwa a arewacin Najeriya bai ragu ba – WHO

    .

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce matsalar mutuwar mata lokacin haihuwa a jihohin arewa ta tsakiya ciki har da Neja, ba ta raguwa saboda matsalar tsaro, duk da ƙoƙarin da jami'ai ke yi.

    Hukumar ta ce da yawan yaran da aka haifa a yankin ba a yi masu riga-kafi ba, saboda yawan rikicin da ake samu masu alaƙa da rashin tsaro.

    Shugabar da ke kula da shiyyar, Dr Asma'i Zeenat Kabir ce ta bayyana hakan a taron WHO na 75 da ya gudana a Minna babban birnin Neja.

    Ta ƙara da cewa har yanzu akwai gagarumin ƙalubale a ɓangaren haihuwa da mutuwa, da kuma a lokacin haihuwa da wasu matsaloli masu alaƙa da yara a mafi yawan jihohin yankin.

    Don haka akwai buƙatar sake zage damtse don bunƙasa harkokin lafiya a yankin.

  17. FUK ba za ta amince da harkokin tsafi da cin zarafin lalata ba - Farfesa Pate

    UPate

    Jami'ar Tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe, ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibai 3,849 na shekarar karatu ta 2022 da 2023.

    Shugaban jami'ar, Farfesa Umaru Pate ne ya ja ragamar bikin karo na 13 tun bayan buɗe ta, inda ya ce ɗalibai 3,849 da suka samu shiga jami'ar ba su kai rabin waɗanda suka nemi karatu a makarantar ba, a matsayin zaɓin farko yayin rubuta JAMB.

    Ya kuma gargaɗi duk sabbin shiga jami'ar su nisanci laifukan da ba za a amice da su ba, ciki har da satar jarrabawa da shaye-shaye da cin zarafin lalata da yaɗa labaran ƙarya da sauransu.

    "Kada kusa kanku cikin harkokin Yahoo-Yahoo. Jami'a ba za ta amince da wannan ba," in ji Pate.

  18. China ta fara atisayen soja a kusa da tekun Taiwan

    BBC

    Rundunar sojin China ta fara wani atisayen dakarunta na kwana uku a kusa da gabar tekun Taiwan.

    Ta ce atisayen gargaɗi ne a kan abin da ta kira 'yan a-waren Taiwan da haɗin gwiwar sojojin ƙetare.

    Jim kaɗan bayan China ta sanar da atisayen sojin nata, Taiwan ta ce ta hango jiragen sama na yaƙi 13, da kuma jiragen ruwa uku a iyakar tekunta.

    An fara atisayen ne sa'o'i bayan shugaban Taiwan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Amurka, inda ya gana da shugaban majalisar wakilai, Kevin McCarthy.

    Ziyarar shugaban Taiwan ɗin ta fusata China, wadda ke iƙirarin cewa Taiwan ɗin yankinta ne.

  19. Gwamnatin Chadi ta kori jakadan Jamus daga ƙasar

    .

    Gwamnatin Chadi ta bukaci jakadan Jamus a ƙasar ya tattara nasa ya nasa, ya bar Chadi cikin sa'a 48.

    Cikin wata sanarwa, an zargi jakadan na Jamus Jan Christian Gordon Kricher, da saba dokokin diplomasiyya da kuma rashin martaba hukumomin Chadi.

    Sai dai, ba a yi cikakken bayani a sanarwar ba.

    Jamus da sauran ƙasashen Turai sun bayyana damuwa a kan jan ƙafar da ake yi wajen mayar da mulki hannun zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula a Chadi.

    Janar Mahamat Idris Deby Itno, na mulkin ƙasar tun bayan mutuwar mahaifinsa shekara biyu da ta wuce.

  20. Firaministan Isra'ila ya ƙara yawan jami'an tsaro a faɗin ƙasar

    BBC

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ba da umarnin a tattaro 'yan sanda da ke gadin iyaka da sojoji masu jiran ta-kwana bayan wani harin mota da aka kai birnin Tel Aviv.

    Mutum guda ya rasu, sannan wasu 7 sun jikkata kafin daga bisani a harbe maharin.

    Wasu hotunan bidiyo daga wajen da lamarin ya faru a Tel Aviv, sun nuna yadda wata mota ta kife a wajen ajiye motocin da ke kusa da wajen shakatawa na bakin teku, yayin da 'yan sandan Isra'ila kuma suka buɗe wuta.

    A jiya ne dai aka kashe wasu matan Burtaniya 'yan asalin Isra'ila biyu a GaƁar Yamma da Kogin Jordan.

    Rikicin baya-bayan nan ya samo asali ne saboda tunzurin da ya ɓarke tsakanin isra'ila da Falasdinawa masu gwagwarmaya da makamai.

    Hakan kuma ya faru ne bayan auka wa Masallacin Ƙudus da 'yan sandan Isra'ila suka yi.

    A ranar Alhamis, an riƙa harba makamin roka daga Lebanon zuwa arewacin Isra'ila, ita kuma Isra'la ta mayar da martani da hare-hare ta sama kan Zirin Gaza da kuma kudancin Lebanon.