Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. An samu ɓarkewar amai da gudawa a Gabashi da Kudancin Afirka – UNICEF

    Cutar amai da gudawa

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya damu matuƙa game da ɓarkewar cutar amai da gudawa a sassan gabashi da kudancin Afirka.

    Lamarin kuma ya shafi fiye da mutane dubu sittin tare da halaka mutum dubu ɗaya da ɗari bakwai.

    Malawi da Mozambique ne ƙasashen da lamarin ya fi yin muni.

    Wani babban jami'in UNICEF ya faɗa wa BBC cewa cibiyoyin kula da lafiya da ke farfadowa daga mummunan tasirin anobar korona a yanzu suna fafutukar daƙile yaɗuwar cutar.

    Ya faɗa wa BBC cewa sauyin yanayi na haifar da ƙaruwar cutar saboda yawan fari da ambaliyar ruwa da ke shafar muhalli da ruwa.

    Ministoci daga ƙasashe 11 suna ganawa a Malawi domin samar da dabarun tunkarar cutar da ke yaɗuwa.

  2. Belgium ta haramta wa ma'aikatanta amfani da shafin Tiktok

    .

    Hukumomi a Belgium sun haramta wa ma'aikatan gwamnatin tarayya amfani da shafin Tiktok a wayoyinsu na aiki.

    Ita ce ƙasa ta baya-bayan nan da ta ɗauki mataki na hana amfani da manhajar na ƙasar China.

    Hukumomin gwamnati da dama a Turai sun hana amfani da Tiktok saboda fargabar hukumomi a China na iya amfani da shafin domin tattara wasu muhimman bayanai.

    Matakin na Belgium ya zo ne bayan nazarin da aka yi game da yiwuwar leƙen asiri da jami'an tsaron farin kaya suka yi.

    Ƙasashen Turai da Amurka na ci gaba da ɗaukan tsauraran matakai kan manhajar mallakin wani kamfanin China mai suna ByteDance.

  3. Yadda aka tsinci gawar wata mahaifiya da ƴaƴanta biyu a London

    .

    An ga gawar wata mata da ƴaƴanta maza biyu yashe a wani gida da ke kudu maso gabashin birnin London.

    Ƴan sandan London sun ce an ga gawar Nadja De Jager, mai shekara 47 da Alexander mai shekara tara da Maximus mai shekara bakwai a titin Mayfield da safiyar ranar Alhamis.

    Jami'an sun ce ba sa neman wani da ke da hannu a lamarin a binciken da suke gudanarwa.

    Jami'in ɗan sanda, Ollie Stride ya ce "Abin takaici ne lamarin kuma muna ci gaba da nazari kan abin da ya kai ga afkuwar mummunan lamarin.

    Jami''an agaji sun isa wajen bayan wani rahoto da aka yi da ke bayana damuwa kan halin da mazauna gidan ke ciki.

    Bayanai na cewa za a gudanar da bincike kan gawarwakin domin gano ainahin abin da ya faru kuma tuni aka sanar da ƴan uwansu.

  4. Sojojin da ke mulki a Mali za su ɗage zaɓen raba gardama

    .
    Image caption: Colonel Assimi Goita said elections would be held next year

    Sojojin da ke mulki a Mali za su ɗage zaɓen raba gardama kan kundin tsarin mulki wanda aka tsara yi gaba a wannan watan.

    A watan Yulin bara ne, Kungiyar ECOWAS ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Mali bayan da shugaban soji, Kanar Assimi Goita ya ce za a gudanar da zaɓe a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

    Manema labarai sun ce matakin ɗage zaɓen raba gardamar bai zo da mamaki ba kuma zai ƙara haifar da shakku cewa Kanar Goita yana son tsawaita zamansa a kan mulki.

    A halin da ake ciki dai Mali na fuskantar ƙaruwar matsalolin tsaro inda ƙungiyoyin da ke iƙirarin Jihadi ke kai hare-hare.

  5. BBC ta dakatar da Gary Linekar, wanda ya fi kowa albashi daga gabatar da shirinta na ƙwallo

    Hoton Gary Lineker

    BBC ta dakatar da mai gabatarwar shirye-siryenta da ya fi kowa daukar albashi, wato Gary Linekar, daga jagorantar fitaccen shirinta na harkokin wasan kwallon kafa, bayan da ya soki shirin gwamnatin Birtaniya kan ƴan ci-rani.

    Kafar ta ce Linekar, tsohon ɗan ƙwallon Ingila ba zai ci gaba da gabatar da shirin Match of the Day ba har sai ta cimma yarjejeniya da shi game da yadda zai rika amfani da shafukansa na sada zumunta.

    Cikin wani saƙon Tuwita, ya kwatanta kalaman da gwamnati ta yi amfani da su wajen bijiro da tsarin kan baƙin haure da wanda Jamus ta yi amfani da su a shekarun 1930.

    BBC ta ƙara da cewa ya kamata Linekar ya kauce wa nuna ɓangaranci kan sha'anin siyasa kamar yadda yake a ƙa'idojinta na aiki.

  6. Gwamnatin Kogi ta yi barazanar rufe bankin da ya ƙi karɓar tsofaffin takardun naira

    .

    Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar rufe duk wani banki tare da kamawa da kuma gurfanar da duk wani da ya ki karbar tsofaffin takardun naira a jihar.

    Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga kwamishinan yada labarai na jihar Kingley Femi Fanwo a yau Juma’a wadda kuma aka wallafa a shafin gwamnatin da ke Facebook.

    A sanarwar, gwamnatin ta bukaci jama’a da su gabatar da rahoton duk wanda ya ki karbar takardun kudin ga jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnati domin daukar mataki a kansa kai tsaye

    Dangane da bankuna, gwamnatin ta ce ba za ta amince da zaman duk wata cibiyar hada-hadar kudi da ta ki bin umarnin kotu ba musamman ma umarnin kotun koli ta Najeriya.

    A sanarwar gwa,mnatin ta ce, ‘’Ba za mu ci gaba da durkusar da tattalin arzikinmu ba bayan da Kotun Koli ta ba mu ‘yanci.’’

    Yanzu dai gwamnatin jihar ta Kogi ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai tabbatar da bin umarnin Kotun Kolin.

    Jihar Kogi da Kaduna da kuma Zamfara ne suka shigar da kara a gaban kotun a kan matakin Babban Bankin Kasar na sanya wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

    Amma daga baya wasu jihohin suka mara musu baya, inda kuma Kotun Kolin kasar a baya-bayan nan ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin kudin har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

  7. Rikici ya ɓarke a Congo bayan tsagaita wuta

    .

    Kashin farko na jirgin agaji ya isa birnin Goma da ke Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo a wani ɓangare na sabbin ayyukan Turai na taimaka wa dubban mutanen da rikici ya ɗaiɗaita a can.

    Hakan ya zo ne bayan tashin hankalin da aka yi a yankin tsakanin dakaru da ƴan tawayen M23 - kwanaki uku bayan da ya kamata a soma aiwatar da shirn tsagaita wuta.

    Rikicin ya faru ne a wani ƙauye da ke Murambi wanda bai kai nisan kilomita 30 daga Goma, babban birnin Lardin North Kivu.

    Ana bayyana cewa ƴan tawayen M23 suna samun goyon bayan Rwanda wadda ta daɗe tana zargin hukumomin Congo da gazawa wajen mrƙushe ƴan tawayen Hutu - wasu dagacikinsu na da alaƙa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda.

    Rwanda dai ta musanta goyon bayan ƙungiyar.

  8. Turkiyya na shirin gudanar da babban zaɓen ƙasar a watan Mayu

    Shugaban ƙasar Turkiyya Racep Tayib Erdogan ya tabbatar cewa a ranar 14 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaɓen yan majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa, abin da ya kawo karshen raɗe-raɗen da ake yi a kan cewa watakila a ɗage zaɓen samakon girgizar ƙasar da ta faru a watan da ya gabata.

    Ana kallon zaɓen a matsayin babban ƙalubalen da ke gaban Mr Erdowan a shekaru ashrin da ya yi yana mulki a matsayin firamninista ko shugaban ƙasa.

    Kawancen jamiyyun hamayya shida sun zaɓi Kamal Kilicdaroglu, wanda shi ne shugaban jamiyyar Republicans people Party mai ra'ayin kawo sauyi a matsayin ɗan takararsu na shugaban ƙasa.

  9. Iran da Saudiyya sun amince su sake kulla hulɗar diflomasiya

    Iran-Saudiyya

    Kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ta ce Iran da Saudiyya sun amince su sake kulla hulɗar diflomasiya tsakaninsu tare da sake buɗe ofishoshin jakadancinsu nan da watani biyu.

    Sai dai Saudiyyar ba ta tabbatar da sanarwar ta Iran ba wadda ta yi bayan wata tattaunawa a ƙasar China.

    An ambato jami'an gwamnatin Iran suna jinjina ga China game da rawar da ta taka wajan sasanta ƙasashen biyu.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa ƙasashen biyu basu da wata alaƙa a hukumance tun bayan shekara ta 2016 bayan da aka kai wa ofishin jakadancin Saudiyya hari a Teheran bayan kisan da Saudiyyar ta yi wa wani malamin shia.

    Haka kuma ƙasashen biyu sun ci gaba da yi wa juna kallon hadarin kaji, inda kowanensu ya goyi bayan bangarorin da ke faɗa da juna a ƙasar Yemen.

  10. Majalisar dokokin China ta kaɗa kuri'ar da ya bai wa shugaba Xi damar zarcewa karo na uku

    Xi Jinping

    An nada Xi Jiping a matsayin shugaban kasar China a waadi na uku, inda ya tabbatar da matsayinsa na shugaban kasar da bai taba fuskantar wani da ya kalubalance sa ba.

    Sai dai duk da cewa nadi ne da ba shi da tasiri amma ya nuna cewa kawo yanzu Mi Xi na tasiri sosai a harkar siyasar kasar.

    An gudanar da bikin ne kamar yadda aka tsara, inda wakilai kusan dubu uku suka amince da naɗin mista Xi a majalisar dokokin ƙasar kuma babu wani da ya nuna adawa da naɗin nasa

    Sai dai ƙasar na fuskantar matsaloli ba kamar lokacin da mista Xi ya fara hawa kan karagar mulki a shekaru goma da suka gabata ba.

    Tattalin arzikin ƙasar na fuskantar koma baya sakamakon dokokin yaki da cutar korona da kuma dangantaka tsakanin ƙasar da Amurka ta yi tsami.

    Xi Jinping
  11. Ɗan bindiga ya buɗewa kiristoci wuta a birnin Hamburg

    Hamburg shooting

    Jami'an tsaro a birnin Hamburg na Jamus, sun ce ba a san dalilin da ya sanya dan bindigar nan da ya budewa kiristoci mabiya darikar Jehovah, wuta ba a lokacin da suke ibada.

    Mutane da dama ne sun mutu, kuma jami'an tsaro sun yi amanna maharin shi ne mutumin da aka gani a saman ginin kwance jina-jina.

    Wakilin BBC a wurin ya ruwaito cewa masu gwajin kwayar halitta sun shafe daren jiya su na gwaje-gwaje a wurin cikin tsananin sanyi tare da dusar kankara.

    Magajin birnin Hamburg Peter Tschentscher, ya bayyana kaɗuwa kan wannan hari.

  12. Kotu ta umarci INEC ta maye gurbin Shekarau da Rufa'i Hanga

    Hoton Hanga

    Kotun Ƙolin Najeriya ta umarci hukumar zaɓen ƙasar ta maye gurbin sunan Mallam Ibrahim Shekarau da na Rufa’i Hanga na jamiyyar NNPP, a matsayin sanatan mazabar Kano ta tsakiya.

    A hukuncin da mai shari’a Justice Uwani Abba-Aji ta yanke yau Juma’a, kotun ta amince da hukuncin da kotun ɗaukaka kara ta yi a baya, inda ta umarci INEC ta amince da Rufa’i Hanga a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP na mazaɓar a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu, 2023.

    Ita dai INEC ta ayyana shekarau a matsayin wanda ya ci zaben, kasancewar ta ki yarda da janye sunansa da ya yi a matsayin dantakarar NNPP tun da farko bayan da hukumar ta ce lokacin sauya dan takara ya wuce.

    Jam’iyyar NNPP ta maye gurbin Shekarau a matsayin dan takara bayan da tsohon gwamnan Kanon ya fice daga jam’iyyar ya koma PDP.

  13. Kotu ta ɗaure waɗanda suka yi wa ƴan Birtaniya fyaɗe a Ghana

    ...

    Wata babbar Kotu a Ghana ta yanke wa wasu mutum uku ɗaurin shekara 73 a gidan yari saboda yi wa wasu yan mata guda huɗu ‘yan asalin Birtaniya fyaɗe.

    An kuma samu mutanen uku da laifin yi wa yaran fashi, a lokacin da suke wata ziyara a Ghana.

    Mutanen da suka haɗa da ‘yan Najeriya biyu da wani ɗan Ghana sun amsa laifin zargin da aka yi musu wanda ciki har da mallakar bindiga ba bisa ka’aida ba.

    Alkalin Babbar Kotun da ke Accra, ya yanke musu hukuncin daurin shekara 24 saboda laifin fashi da makami, da kuma shekara 24 saboda aikata fyaɗe, sai kuma ƙarin wasu shekaru 25 a kurkuku saboda mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

    Mutanen za su yi zaman hukucin ne a lokaci ɗaya, wanda ke nufin zaman shekara 25.

    Shari'ar dai an gudanar da ita ne a cikin sirri domin gudun bayyana yaran da aka yi wa fyaɗen.

  14. Mutum 150,000 na cikin haɗarin fuskantar mahaukaciyar guguwa a Mozambique

    Cyclone Freddy

    Hukumomin Mozambique sun ce mutane 158,000 ne mahaukaciyar guguwar za ta iya shafa a lardin Zambezia da ke tsakiyar ƙasar.

    Ana sa ran guguwar za ta afka wa gaɓar tekun tsakiyar Mozambique da yammacin yau Juma'a.

    Mahaukaciyar guguwar ta nufi Mozambique a karo na biyu bayan ɓarna da ta yi a karshen watan Fabrairu.

    Ana yanzu danganta ta da guguwa ma fi daɗewa a tarihi.

    Hukumar kula da bala’o’i ta ƙasar ta ce mutum 8,000 cikin waɗanda abin ya shafa za su iya bukatar agajin gaggawa.

    Gwamnatin lardin ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantu daga yau Juma’a.

  15. Masu iƙirarin jihadi sun kashe sojojin Burkina Faso 11

    Burkina Faso attack

    Wasu da ake kyautata zaton masu iƙirarin jihadi sun kashe sojojin Burkina Faso 11 a wani samame na yunkurin sake ƙwace iko da wani yanki d ake gabashi da kuma arewacin ƙasar.

    A cewar sojoji, an kuma raunata wasu jami'an tsaro guda huɗu lokacin da lamarin ya faru.

    Ƙasar da ke yankin sahel ta sha fama da ayyukan 'yan-ta-da-ƙayar ba na tsawon shekara takwas wanda kuma ya yi sanadiyyar rayukan dubban fararen hula da ɗaiɗaita kusan miliyan biyu.

    Tun 2018, Burkina Faso na faɗa da 'yan-ta-da-ƙayar baya da ke alaƙa da al-Qaeda da kuma ISIS, waɗanda suka ƙwace iko da yankuna masu yawa na ƙasar.

    Kungiyoyin na ci gaba da kai hare-hare a mawaɓtan ƙasar a Nijer da Mali duk da kasancewar dakarun ƙasar da sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da kuma sojojin haya na Rasha.

  16. Kotu na tuhumar tsohon Firaiministan Malaysia da laifin halasta kuɗin haram

    Muhyiddin Yassin

    Kotu a Malaysia na tuhumar tsohon Firaiministan ƙasar, Muhyiddin Yassin, da laifin amfani da karfin mukaminsa fiye da kima da halasta kuɗin haram.

    Mista Muhyiddin ya musanta aikata ba daidai ba, kuma a baya ya ce zarge-zargen makarkashiyar sisaya ce.

    Idan aka same shi da laifi zai shafe akalla shekaru 35 a gidan kaso da tarar miliyoyin daloli.

    Gwamnati mai ci ta jima ta na tuhumar Muhyiddin Yassin da gwamnatinsa tun bayan karbe iko da ƙasar a shekarar 2021.

    Hukumar yaki da yi wa kasa ta'annati ta Malaysia ta ɗauki sa'o'i ta na masa tambayoyi kan wata dambarwa mai alaƙa da kuɗaɗen da aka kashe na yaki da annobar cutar korona.

  17. MDD ta yi tir da kisan masunta a Borno

    ...

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi Alla-wadai da kisan fararen hula akalla 37 a wani harin kwantan ɓauna a ƙauyen Mukdolo a karamar hukumar Ngala na jihar Borno.

    Rahotanni sun ce gwamman mutane ne waɗanda akasari manoma da masunta aka harbe a harin da ake zargin mayaƙan ISWAP da kai wa.

    Harin ya faru ne a garin Dikwa wanda ke kusa da garuruwan da 'yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram ke da karfi.

    Mutane da dama ne suka jikkata a harin yayin da wasu da yawa kuma suka ɓata. An kashe manoman ne a ranar Laraba lokacin da suka je daji neman itace.

    Majiyoyin tsaro sun ce gwamman mayaƙan na ISWAP sun yi wa garin dirar miƙiya a kan babura, inda bayan isarsu suka fara harbi kan mai uwa da wabi. Mutum tara ne kuma suka samu damar tserewa.

    A cikin wata sanarwar da ofishin kodinetan ba da agaji na MDD Mista Mathias Schmale ya fitar, ya mika ta'aziyya ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu.

    Ya ce akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su masunta ne da manoma waɗanda ke neman samun abin da dogaro da rayuwarsu.

    “Wannan harin abin tayar da hankali ne kuma hakan ya sake nuna barazana da halin rashin tsaro da 'yan gudun hijira da sauran mutanen da ayyukan 'yan ta-da-ƙayar-baya na shekara sama da 13 ay shafa ke ciki a yankin. Mutane sun tserewa ƙauyen Mukdolo kafin kawo wannan hari sanadiyyar ayyukan kungiyoyi masu ikirarin jihadi,'' in ji sanarwar.

    Mista Schmale ya yi kira ga hukumomin jihar da suka gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da nufin hukunta waɗanda aka samu da laifi.

  18. Najeriya na binciken jirgin Lufthansa kan zargin cin zarafi

    Lufthansa

    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ta fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin fasinjoji sama da 200 da suka nufi Najeriya a jiragen sama na Lufthansa na ƙasar Jamus.

    Kafofin yaɗa labaran sun ce jirgin ya yi barazanar kiran ‘yan sanda a ranar Juma’ar da ta gabata bayan fasinjojin da jirgin ya ɗauka suka bukaci a samar musu da wurin zama bayan jinkirta tashinsu.

    Rahotanni sun bayyana cewa jirgin da ya fito daga Frankfurt zuwa Legas, da aka tsara zai sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, amma sai da ya yada zangon a Cotonou a ƙasar Benin da Malabo na ƙasar Equatorial Guinea.

    Kamfanin Lufthansa ya nemi afuwar jinkirin da jirgin ya samu a wata wasika da ya aike wa fasinjojinsa a ranar Juma'ar da ta gabata.

    Fasinjojin sun yi zargin cewa ba a rufe filin jirgin sama na Legas ba, saɓanin iƙirarin da matukin jirgin na Lufthansa ya yi.

    Sam Adurogboye, jami’in hulɗa da jama’a na NCAA, a ranar Alhamis ya ce hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin bayan samun koke-koke daga fasinjojin. BBC ta tuntubi kamfanin jirgin domin jin karin bayani.