Manchester United ta lashe kofin Caraboa

united

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta lashe kofinta na farko tun a shekara ta 2017 bayan ta samu nasara a kan Newcastle United a wasan karshe na kofin Carabao da aka buga a filin wasa na Wembley.

An tashi wasa United na da ci biyu sai kuma Newcastle na nema.

Casemiro ne ya shigar da United gaba inda ya ci kwallo a minti na 33 kafin Sven Botman na Newcastle ya taimaki United da kwallo ta biyu.

Hakan na nufin cewa Newcastle za ta ci gaba da jira domin lashe kofinta na farko tun bayan shekarar 1969.

Wannan ne kofin farko na United ta lashe gasa a karkashin jagorancin Erik ten Hag.

Shekaru shida da suka wuce ne Manchester United ta lashe kofin Europa karkashin jagorancin Jose Mourinho kuma tun daga lokacin kungiyar ba ta kara lashe kofi ba.