Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Asuba ta gari

    Karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumiINEC na ganawar sirri kan zaɓen gwamnoni

    Zaɓen gwamnoni

    Hukumar Zaɓe a Najeriya na can tana gudanar da taro a shelkwatar ta da ke Abuja.

    Taron na zuwa ne jim kaɗan bayan hukuncin kotun da ya ba ta damar sake saita na'urorin tantanace masu kaɗa kuri'a na BVAS bayan an yi zaɓen shugaban ƙasa da su a ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Majiyar da ta tabbatar wa BBC zaman taron ba ta bayyana takamaime a kan abin da shugabannin hukumar ke tattaunawa ba.

    Sai dai ana kyautata zaton taron zai shafi makomar zaɓen gwamnonin da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

  3. An zargi ministan cikin gida a Tunisiya da tunzura jama'a

    Babbar kungiyar kwadago a ƙasar Tunisiya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da yan jarida sun zargi ministan cikin gida da tunzura jama'a bayan ya zargi yan hammaya da cin amana.

    Tawfik Charfeddine ya ce 'yan kasuwa da kungiyoyin kwadago da kuma jamiyyun siyasa sun sayar da kasar kuma sun hada kai da alummar kasar.

    Sai dai a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa kungiyoyin farar hula sun yi alla wadai da kalaman nasa suna cewa kalaman sun yi kama da barazanar da gwamnatin mulki kama karya ta yi a baya wadda aka kifar a shekarar 2011.

  4. Bisa kuskure ne cutar korona ta fita daga ɗakin gwaji a China - Dr Robert

    CDC Amurka

    Tsohon darektan hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Amurka, ya faɗa wa kwamitin bincike na majalisar dokokin kasar cewa ya yi ammanar cewa bisa kuskure ne kwayar cutar korona ta fita daga dakin gwaji a kasar China.

    Dakta Robert Redfield, wanda ya jagoranci hukumar ta CDC daga 2018 zuwa 2021 ya bayyana haka ne a rana ta farko ta sauraran bahasin jama'a na kwamitin majalisar wakilai da aka dorawa alhakin gudanar da bincike a kan asalin cutar ta korona.

    Ya ce a nazarin farko da na yi, na yi amanar cewa kuma har yanzu ra’ayi na bai sauya ba, a kan cewa bisa kuskure ne kwayar cutar korona ta fita daga dakin kimiya , ba haka ne kawai ta bulla ba.

    Ra’ayinsa ya zo ɗaya da na shugaban hukumar bincike na FBI, Christopher Wray wanda a hirar da ya yi a baya bayanan ya bayyana cewa hukumarsa ita ma tayi irin wannan nazari na dan lokaci.

    Sai dai China ta musanta zargin.

  5. Masu fafutuka sun yi gargadin cewa za a shiga ruɗani a zaben Zimbabwe

    Masu fafutuka a Zimbabwe sun yi gargaɗin cewa za a shiga cikin wani yanayi na ruɗani a babban zaɓen ƙasar da za a yi a bana bayan da suka gano cewa an saka wasu gundumomi a yankin Antartica a iyakokin zaɓe da aka shata a baya bayan.

    Kungiyar da ake kira Team Pachedu ta kuma gano cewa hukumar zaben kasar ta saka wasu mazabu a wasu wurare da suka hada da tsakiyar tekun Indiya da Zambia da Eswatini da kuma Afrika ta Kudu.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyar ta Pachedu wadda ita ce ta bankado kura kuran ta ce wannan ya nuna cewa za a tafka magudi a lokacin zaben.

    Masu fafutukar sun kuma ce kura kuran da aka yi wajan shata mazabun zai sa yan takara su yi yakin neman zabe a wuraren da ba su dace ba, kuma masu kada kuria ba za su san mazabar da gidansu yake ba.

    Ya zuwa yanzu dai hukumar zaɓen ba ta ce komai ba kan wannan alamari.

  6. An shiga rana ta biyu ta zanga-zanga a Georgia

    Georgian protesters

    Dandazon jama'a sun taru a wajan Majalisar dokokin ƙasar Georgia a dare na biyu, domin nuna rashin amincewa da dokar da suka ce ta saɓawa hakkin ɗan adam.

    Masu zanga-zangar sun yi maci suna rike da kwalaye da tutoci, wasu kuma sun rika busa usur ko buga ganguna.

    Masu zanga-zangar sun nanata cewa sabuwar dokar da ake kira Foreign Agents wato wakilan ƙasashen ketare, iri ɗaya ce da ta Rasha wadda aka yi amfani da ita wajan hana yancin tofa albarkacin baki.

    Suna kuma fargabar cewa hakan zai iya kawo cikas ga fatan kasar na zama mamba a Tarayyar Turai.

  7. Gobara ta lalata shaguna a kasuwar Rimi da ke Kano

    Gobara

    Wata gobara ta lalata shaguna 19 ciki har da masallaci a kasuwar Rimi da ke jihar Kano.

    Hakan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da wata gobara da ta ɓarke ta ƙona shaguna 80 a kasuwar Kurmi da ke jihar.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya, ta ruwaito shugaban kasuwar Alhaji Musa Tijjani na cewa ana danganta tashin gobarar ne sakamakon matsala da layin wutar lantarki ya samu, inda wutar ta tashi da misalin karfe 2 na dare.

    Ya ce cikin kayayyakin da suka ƙone a kasuwar sun haɗa da kayan amfanin gona da kayan gida da sauransu.

    Ya ƙara da cewa sun gode wa Allah ganin cewa babu asarar rai da aka samu sakamakon tashin gobarar.

    Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar, Saminu Abdullahi, ya ce bayan samun kirar waya da suka yi, nan da nan aka aike da jami'an hukumar, inda kuma suka samu nasarar kashe gobarar wanda ya dakatar da ita yaɗuwa zuwa wasu wurare.

  8. Buhari ya koma Najeriya bayan halartar taron ƙasashe masu tasowa a Qatar

    Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan halartar taron ƙasashe masu tasowa a birnin Doha na ƙasar Qatar.

    Taron na kwanaki huɗu da Buhari ya halarta shi ne irinsa karo na biyar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kan ƙasashen da basu ci gaba ba.

    Shugaban ya sauka a filin tashi da saukar jiragen ƙasa na jihar Katsina, inda zai zauna a Daura har sai bayan gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki a ranar Asabar da ke tafe.

  9. Buhari ya jajanta wa waɗanda gobara ta ƙona wa shaguna a kasuwar kayan mota a Legas

    Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa waɗanda gobara ta kona wa shaguna a wata kasuwa ta sayar da kayan mota da ke jihar Legas.

    A wani sako da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaban ya nuna alhini kan abin da ya faru da 'yan kasuwar da kuma iyalansu.

    Ya nuna takaici kan irin asarar dukiya ta miliyoyin naira da aka yi a kasuwar.

    Ya yi kira ga hukumomi a jihar da su tabbatar sun ɗauki matakin kare afkuwar hakan nan gaba, inda ya godewa hukumar kashe gobara ta jihar saboda kai agajin gaggawa lokacin da lamarin ya faru.

    Buhari ya kuma miƙa ta'aziyya ga iyalan wani mai gadi mai shekara 65 da ya rasu a sanadiyyar gobarar.

  10. An zartas da hukuncin kisa kan masu iƙirarin jihadi 13 a Somaliya

    An zartas da hukuncin kisa kan mutum 13 a yankin Puntland na Somaliya wanda ya ayyana cin gashin kai.

    An zargi tara daga cikin mutanen da alaƙa da kungiyar al-Shabab da kuma ta IS.

    Shida daga ciki sun kasance tsofaffin sojoji da aka samu da laifin aikata kisa.

    Jami'an harbi ne suka yi aikin a biranen Garowe da Bosasso da kuma Galkayo da ke arewacin ƙasar.

    Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun ce zartas da hukuncin kisa kan mutane na ƙaruwa a Somaliya.

    Yawancin waɗanda aka kashe ana zarginsu ne da alaƙa da kungiyoyin masu iƙirarin jihadi da masu aikata fyaɗe da kuma wasu jami'an tsaro.

  11. An girke jami'an tsaro kusa da fadar shugaban ƙasar Kenya kan fargabar zanga-zangar 'yan adawa

    Kenya

    Yan sanda sun saka shingayen bincike kan titunan da za su kai fadar shugaban Kenya a Nairbo babban birnin ƙasar, kan fargabar zanga-zangar da 'yan adawa suka shirya gudanarwa.

    Ana dai tsayar da motoci domin yin bincike.

    Wannan ya biyo bayan karewar wa'adin kwanaki 14 da 'yan adawar suka bai wa gwamnati na ganin ta shawo matsalar tsadar rayuwa da 'yan ƙasar ke fuskanta.

    Jagoran 'yan adawa Raila Odinga, shi ne ke jagorantar zanga-zangar mutane da ke adawa da gwamnati a faɗin ƙasar.

  12. Afghanistan ce ƙasar da ta fi cin zalin mata a duniya - MDD

    Hoton mata na zanga-zanga
    Image caption: Taliban ta hana mata zuwa manyan makarantu

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Aghanistan ta zama ƙasar da ta fi cin zalin mata a duniya ƙarƙashin mulkin Taliban, inda a cikin wata 18 aka tilasta wa mata zama a cikin gida.

    A jawabin da ta yi a ranar mata ta duniya shugabar shirin kare 'yancin mata ta majalisar a Afghanistan, Roza Otunbayeva ta nuna takaici a kan yadda ta ce ana take haƙƙin mata a ƙasar

    Sai dai wasu mata sun yi zanga-zanga a Kabul babban birnin ƙasar inda suka yi kira ga ƙasashen duniya da su kare ƴan ƙasar.

    Duk da cewa ƙanan yara mata suna zuwa makarantar boko to amma a 2021 Taliban ta hana 'yan mata zuwa manyan makarantun, inda a watan Disamba na 2022 kuma suna hana mata zuwa jami'a.

  13. Ƙungiyoyin kare haƙƙi na sukar dokar ƴancin aure ta mata a Saudiyya

    Hoton mata da abaya
    Image caption: Dokar ta bai wa mace ƴancin auren duk wanda take so ba sai waliyyi ko magabacinta ya amince ba

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'Adama sun ce dokar farko da aka kafa a Saudiyya kan batun waliyyin mace na aure wadda aka sanar a ranar mata ta duniya a bara ta sa ana nuna wa mata wariya a maimakon magance matsalar.

    Dokar wadda wani ɓangare ce na jerin sauye-sauyen da aka ɓullo da su a Saudiyyar a cikin shekarun da suka gabata ta bai wa mace ƴancin auren duk wanda take so ba tare da ikon wani magabacinta ko waliyyinta ba.

    Sai dai ƙungiyar kare haƙƙin bil'Adama ta Amnesty International ta ce dokar ta kawo wasu sauye-sauye kamar ƙayyade mafi ƙarancin shekarun aure.

    Amma kuma ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa dokar ta kafa tsarin nuna banbancin jinsi a duk fanin rayuwar iyali.

    Ita kuwa ƙungiyar Human Rights Watch ta ce har yanzu dokar tana ƙunshe da tanade-tanaden nuna wariya ga mata kan batutuwan da suka shafi aure da saki da kuma yanke shawara a kan yara.

  14. Gobara ta tashi a kasuwar kayan mota a Lagos

    Hoton gobara
    Image caption: An tsinci gawar wani mai gadi a kasuwar wanda aka harba

    An yi asarar kaya na miliyoyin naira a sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar sayar da kayan mota ta Akere da ke Ajegunle a Apapa, da ke jihar Lagos.

    Haka kuma an samu gawar wani mai gadi mai shekara 65, a kusa da inda gobarar ta tashi kamar yadda bayanai suka nuna.

    A wata sanarwa da darektar hukumar kashe gobara ta jihar Legas Adeseye Margaret, ta fitar a yau Laraba ta ce, gobarar ta tashi ne da wajen ƙarfe 3:30 na dare.

    Shugabanr ta kara da cewa sai an gudanar da cikakken bincike za a san dailin tashin gobarar da yawan shaguna da dukiyar da ta ɓannata.

    Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Benjamin Hundeyin ya tabbatar mata cewa mai gadin da aka tsinci gawarsa a kasuwar harbinsa aka yi.

    Kakakin ya ce an gane gawar ta wani mai gadi ce a kasuwar kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

  15. An fara raba kayan zaɓen gwamna da 'yan majalisa a Kaduna

    kayan zaɓe

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC, ta fara raba kaya da ma'aikatan da za su gudanar da zaɓen gwamna da 'yan majalisar dokoki a jihar Kaduna.

    Hukumar ta ce tana ganin hakan ya zama wajibi ne da ɗauki wannan matakin na shirya wa zaɓukan da wuri, inda ta fara aika muhimman kayan daga Babban Bankin Ƙasar inda aka ajiye su zuwa ƙananan hukumomin jihar 23.

    Kayan zaɓe
  16. Atiku ya haɗa tawagar manyan lauyoyi 19 domin ƙalubalantar nasarar Tinubu

    Hoton Atiku Abubakar

    Ɗan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya haɗa tawagar manyan lauyoyi 19 domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka yi na ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Atiku ya yi wa lauyoyin bayani a yau Laraba a hedikwatar yaƙin neman zaɓensa a Abuja, inad ya buƙace su da su tabbatar wa da kotu dokokin da aka keta a zaɓen tare da sake ƙwato abin da ya kira ikon 'yan Najeriya.

    Tawagar na ƙarƙashin jagorancin ƙwararren lauya mai zaman kansa JK Gadzama.

    Ɗantakarar ya sheda musu cewa abu ne mai muhimmancin gaske su tabbatar sun tsaya tsayin daka domin tabbatar da nasara a shari'ar ba saboda shi ba kawai da PDP, domin ma sake tabbatar da dumukuraɗiyya domin ƴan gaba.

    Tarin manyan lauyoyin sun haɗa da Chief Chris Uche da Paul Usoro da Tayo Jegede da Ken Mozia da Chief Mike Ozekhome da Mahmood Magaji da Joe Abraham da Chukwuma Umeh da Garba Tetengi da kuma Chief Emeka Etiaba.

    Akwai kuma Chief Goddy Uche da Farfesa Maxwell Gidado da mai bayar da shawara kan shari'a na na ƙasa na PDP A.K. Ajibade da O.M. Atoyebi da Nella Rabana da Paul Ogbole da Nuremi Jimoh da kuma Abdul Ibrahim.

  17. Peter Obi ya katse kamfe domin ya jagoranci lauyoyinsa zuwa kotu

    Hoton Peter Obi

    Ɗantakarar shugaban Najeriya na jam'iyyar Labour (LP) Peter Obi, ya ce shi da kansa zai jagoranci lauyoyin jam'iyyarsu yau Laraba, zuwa kotu saboda hukumar zaɓe, INEC, ta ƙi ba su kayan da aka yi amfani da su a zaɓen da aka yi su duba, kamar yadda kotu ta umarta.

    A saƙon da ya sa a shafinsa na Twitter Mista Obi ya ce ba zai samu damar zuwa yaƙin neman zaɓe na gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jihohin da aka tsara zai yi ba saboda zuwa kotun.

    Ya ce a da an tsara zai je jihohin da suka haɗa da Nasarawa da Lagos da Enugu da Abia da Delta da Edo da Rivers da Plateau da Borno, to amma ya fasa hakan domin ya jagoranci tawagar lauyoyin da kansa zuwa kotun a Abuja.

    Mista Obi, wanda ya ce za su ci gaba da wannan fafutuka ta fuskar shari'a domin ƙwato nasarar da ya ce an sace musu, ya buƙaci magoya bayansa da za su je kotun da kada su mayar da harabar wajen zanga-zangar siyasa.

    Sannan ya buƙaci magoya bayan nasa da ake musu laƙabi da Obidients da su mara wa 'yan takararsu a jihohin da za a yi zaɓen gwamnonin da 'yan majalisar jiha baya, su kuma kasance masu bin doka.

    View more on twitter