Idriss Deby: 'Yan tawaye sun kashe shugaban kasar Chadi

Idris Deby

Asalin hoton, Reuters

Rundunar sojin Chadi ta ce Shugaban kasar Idriss Deby ya mutu sakamakon raunukan da ya ji a fagen daga.

A halin yanzu dai Chadi tana fafatawa da mayakan da ke tawaye wadanda suka kaddamar da hari kan babban birnin kasar N'Djamena.

Ana sa ran Shugaba Idriss Deby zai lashe zaben shugaban kasar karo na shida bayan zaben da aka gudanar a watan Afrilu.

A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi "ya ja numfashinsa na ƙarshe a yayin da yake kare martabar ƙasar a fagen daga".

Tuni dai an rusa gwamnati da majalisar dokoki. Majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18.

An sanya dokar hana fita sannan aka rufe dukkan iyakokin kasar.

Mista Déby ya ɗare mulkin ƙasar ne tuna shekarar 1990.

A ƙarshen mako ne ya je fagen daga don kai wa dakarun da ke yaƙi da ƴan tawaye ziyara a kusa da kan iyakar Libiya.

A ranar zaɓe ne wata ƙungiyar ƴan tawaye ta kai hari Chadi daga sansaninta da ke Libiya.

Ƴan tawayen sun tunkari Ndjamena fadar gwamnatin ƙasar sannan ta ce ta ƙwace wani babban yanki.

Shugaban ƙasar, wanda ya sha tunkarar ƴan tawaye a cikin shekaru takatin ɗin da ya shafe yana mulki, ya tafi har arewaci don yaƙarsu, amma sai ya gamu da ajalinsa.

Wannan layi ne

Idris Deby ba shi da lafiya?

A watan Fabrairun 2021 ne wata kotu a ƙasar Chadi ta ɗaure wani ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin dan adam na ƙasar a gidan yari na tsawon shekaru uku da zummar gyaran hali.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta samu mutumin da laifin rubuta cewa shugaban ƙasar ba shi da lafiya ƙwarai da gaske, kuma yana jinya a ƙasar Faransa.

An dai kama Baradine Berdei Targuio, shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasar a cikin watan Janairun shekarar 2020, bayan da ya wallafa labarin rashin lafiyar shugaba Idriss Déby a shafinsa na Facebook.

Kotun hukunta miyagun laifuka ta garin N'Djamena babban birnin ƙasar na Chadi ta bayyana laifin da aka same shi da aka aikatawa a matsayin 'keta doka tsarin mulki'

Wani ɗan adawar Mista Déby a siyasance, Saleh Kebzabo, ya ƙalubalanci hukuncin da ya kira da rashin adalci mai kuma bita da ƙullin siyasa, tare da yin kira da a saki Baradine Berdei Targuio.

Ɗansa zai gaje shi

Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi

Sojojin Chadi sun ce Janar Mahamat Idriss Deby Itno ɗan marigayi Idriss Deby zai jagoranci majalisar sojin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito

Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi.