Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Aisha Buhari ta ziyarci iyalan Babban hafsan sojan Najeriya

    Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Babban hafsan sojan Najeriya Janar Ibrahim Attahiru.

    Aisha Buhari ta wallafa hotunan ziyarar ta'aziyar a shafinta na Twitter tare da saƙon ta'aziyya.

    A ranar Asabar aka binne Babban Hafsan sojan tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

    Aisha Buhari ta ce rasuwar babban hafsan sojin babban rashi ne ga iyalansa da kuma Najeriya baki ɗaya.

    View more on twitter
  2. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye a wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Kuna iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya a ranar Lahadi.

  3. Faransa ta ce tabbatar da ƴancin Falasdinawa ne kawai zai kawo ƙarshen wariyar Isra’ila

    Jean-Yves Le Drian

    Ministan Harkokin wajen Faransa ya yi gargaɗi kan abin da ya kira "haɗarin wariya mai ɗorewa" muddin ba a ba Falasɗinawan ƴancin gashin kansu ba.

    Jean-Yves Le Drian ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi game da rikicin da ya ɓarke a biranen Isra’ila tsakanin Yahudawa da Falasdinawa.

    Har yanzu Isra'ila ba ta mayar da martani kai tsaye ga kalaman na Mr Le Drian ba, amma a baya ta musanta cewa ba ta da wata manufa ta nuna wariya ga Falasdinawa.

  4. Bazoum ya yi wa Buhari jajen mutuwar Babban Hafsan sojin Najeriya

    Shugaba Bazoum

    Shugaban Nijar mohamed Bazoum ya jajanta wa Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari hatsarin jirgin da ya yi sanadin mutuwar Babban Hafsan Sojan ƙasar Janar Ibrahim Attahiru tare da wasu manyan sojojin ƙasar.

    Sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce, Bazoum ya yi wa Buhari jajen ne ta wayar tarho inda ya bayyana hatsarin jirgin a matsayin mummunan al’amari.

    Ya ce yana taya gwamnati da ƴan Najeriya jimami.

  5. Yadda Manchester City ta yi bikin lashe kofin Premier

    Manchester City ta bikin lashe kofin Premier bayan ta doke Everton a ranar Lahadi
    Image caption: Manchester City ta yi bikin lashe kofin Premier bayan ta doke Everton a ranar Lahadi
    City ta lashe kofin ne tun makwanni uku da suka gabata
    Image caption: City ta lashe kofin ne tun makwanni uku da suka gabata
    Manchester City
    Manchester City
  6. Chelsea da Liverpool za su buga gasar zakarun Turai bayan sun sha da ƙyar

    Liverpool ta kuɓutar da kanta inda ta tsallake zuwa gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa bayan ta doke Crystal Palace a Anfield.

    Chelsea ma ta samu hurumin gasar Zakarun Turai duk da ta sha kashi a hannun Aston Villa.

    Leicester City kuma ta ci wuya ne hannun Tottenham wadda ta fitar da ita daga huɗun farko a teburin Premier da za su buga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.

    An tantance makomar ƙungiyoyin na Premier ne a wasannin mako ƙarshe da aka fafata a ranar Lahadi.

    Ga yadda sakamakon wasannin ya kasance:

    Wasannin Premier
  7. OIC ta yaba wa Saudiyya kan yayyafa ruwa a rikicin Isra’ila da Falasdinawa

    Sarki Salman

    Ƙungiyar ƙasashen Musulmi OIC ta yaba wa gwamnatin Saudiyya kan ƙoƙarinta na tursasa Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare a Zirin Gaza, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito.

    Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hamas ta ci gaba da aiki kwana uku a jere wanda ya kawo ƙarshen rikicin kwanaki 11 da ɓangarorin biyu suka shafe suna yi.

    Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ce Ƙungiyar OIC ta yaba wa Sarki Salman kan kalaman da ya yi a zantawarsa da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas cewa Saudiyya za ta ci gaba da bin dukkanin matakan da suka dace domin matsin lamba ga Isra’ila ta dakatar da matakan da ta ke ɗauka da kuma hare-hare a birnin Kudus.

    OIC kuma ta yaba da ƙoƙarin mambobinta, musamman Masar da Jordan da kuma Qatar da suka taimaka wajen kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa.

  8. Saudiyya ta hana yawan amfani da lasifika a Masallatai

    Yariman Saudiyya mai jiran gado

    Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sabbin matakai da ke taƙaita yawan amfani da lasifika a Masallatan ƙasar.

    Ma’aikatar harakokin addini ta ƙasar ta ce Masallatai za su yi amfani da lasifika ne kawai yayin kiran Sallah kuma ba tare da ƙure ƙarar lasifikar ba.

    An ambato ministan harakokin addini na ƙasar Abdul Latif Al Sheikh na cewa duk wanda ya saɓa sabbin sharuɗɗan za a hukunta shi.

    Ma’aikatar ta ce manyan malaman ƙasarSaleh bin Fawzan al-Fawzan da marigayi Sheikh bin Salih al-Uthaymin sun bayar da fatawa da ke hani da amfani da lasifika yayin gudanar da Sallah. Sun ce za a yi amfani da lasifika ne kawai lokacin kiran Sallah.

    Tun bayan da Sarki Salman ya hau karagar mulki a shekarar 2015, Saudiyya ta fara wani yunƙuri wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ke jagoranta don sauya al’amurran ƙasar da ke da tsauri ga addini da kuma ƙoƙarin zamanantar da tattalin arzikinta.

    Sai dai kuma Yariman mai jiran gado ya sha suka kan manufofinsa da kuma yadda yake murƙushe ƴan adawa.

  9. Wani yaro ya rasu garin murnar cin kofin da Atletico Madrid ta yi

    B

    Wani yaro mai shekara 14 ya mutu a cikin wani cunkoso lokacin da ake murnar cin kofin Atletico Madrid, bayan nasarar lashe La Liga da suka yi a ranar Asabar.

    Yaron ya mutu duk da cewa masu aikin ba da agaji sun yi yunkurin ceto rayuwarsa, bayan share kimanin sa'a guda ba tare da samun agaji ba.

    Ya mutu ne bayan kanshi ya hadu da wata katanga ta hanyar da ake bi a shiga wata hanyar kasa a Madrid babban birnin Sifaniya, yayin da abokansa suke cikin mota shi kuma ya leko da jikinsa ta tagar mota.

    Magoya bayan kungiyar sun ci gaba da shagalin murnar daukar kofinsu na 11 a tarihi, kuma na farko tun 2014, duk kuwa da hukumomin kasar sun haramta tarukan mutane saboda annobar korona.

  10. Yadda Janar Kuliya ya yi amfani da tubabbu wajen tarwatsa Boko Haram

    PR

    Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya wanda shi ne ke jagorantar ayyukan leken asiri ya yi matukar taka rawa wajen tarwatsa sansanonin Boko Haram da kuma ISWAP.

    Cikin wani rahoto da jaridar PR Nigeria ta wallafa wadda ke da kusanci da sojojin kasar ta ce, shi ne ke jagorantar tawagar Lafiya Dole lokacin da Attahiru ke matsayin babban kwamanda a yankin arewa maso gabashin kasar.

    Ta ruwaito cewa lokacin da wasu mayakan Boko Haram su ka yi kokarin mika wuya domin tuba, shi ne ya gayawa Attahiru cewa a barsu cikin sansanin Boko Haram domin su zama masu yi masu leken asiri.

    Kuma hakan ya bayar da dama wajen gwara kan kungiyoyin biyu na ISWAP da Boko Haram wanda ya kai ga babbar rashin jituwa tsakaninsu.

    Kuliya na cikin wadanda suka jagoranci sauya wa rundunar Operation Lafiya suna zuwa 'Operation Hadin Kai’ da nufin samar da hadin kai tsakanin tubabbun mayakan Boko Haram da sojoji.

    An yi hakan ne da nufin samun bayanan sirri da za su bayar da damar murkushe kungiyoyin biyu na Boko Haram da ISWAP.

  11. Yadda aka yi wa Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya salla a Kano bayan an binne shi a Abuja

    H

    Al'umar Kano da dama sun halarci sallar da aka yi wa gawar Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya a Kano bayan an binne shi a Abuja.

    Wannan sallar dai da daruruwan mutane suka halarta ana kiranta da (Salatul Ga'ib) a koyarwar addinin Musulunci.

    Farfaesa Shehu Sa'id Galadanci ne ya jagoranci sallah a bayansa akwai Dr Bashi Aliyu Umar da kuma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

    A ranar Juma'a ne Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya da babban Hafsan Sojin Najeriya Attahiru Ibrahim da wasu sauran soji suka hadu da ajalinsu, bayan hadarin jirgin sama da ya rutsa da su a Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

    Dr Abdullahi Umar Ganduje Facebook
    Dr Abdullahi Umar Ganduje Facebook
  12. Ba dole ba ne mu nuna wa duniya cibiyoyinmu na nukiliya - Iran

    j

    Iran tace yarjejeniyar da suka cimma da hukumar da ke sanya ido kan shirin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta zo karshe.

    Ta ce tunda wannan yarjejeniya ta kare, to yanzu babu wanda zai matsa mata cewa sai ta nuna shirinta na nukiliya.

    Kakakin majalisar Kasar Baqar Qaleb ya ce Iran ta yi amannar wa'adin da aka dibarwa yarjejeniyar na matsagaicin lokaci ya zo karshe a ranar Asabar.

    Mohammad Baqar ya ce "Yarjejeniyar wata ukun da aka diba ta zao karshe ranar Asabar 22 ga watan Mayu, Bayan wannan hukumar da ke sanya ido kan makamashi ta MDD ba ta da hurumin ganin hotuna ko kuma bidiyon yadda suke shirye-shiryensu a cibiyoyin nulikyarsu."

    Wadannan masu sa idanun na cikin shirin kasashen duniya na hana Iran samar da makamin nukiliya.

    Sai dai Iran ta sha jaddada cewa shirin nukiliyar na ta tana yi ne saboda zaman lafiya.

  13. Kimanin mutum 70 ne suka jikkata a gobarar da ta ta shi a Kano

    BBC

    Hukumomi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbar da jikkatar gwamman mutane a wata gobara da ta faru a wani gidan mai da ke Unguwar Sharada a Jihar.

    Cikin wata tattaunawa da manema labarai kwamishin ayyuka na Jihar Alhaji Garba Idriss Unguwar Rimi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya na cewalaifun na mahukuntan gidan man ne.

    "Kowa ya sani doka ta haramta sauke mai da tsakar rana musamman a irin wannan yanayi da Kano ke ciki na matsanancin zafi, wanda kuma hakan ne ya yi sanadiyyar tashin wannan gobara.

    "Wannan gobara ta rutsa da mutum 43 na gari, sai kuma jami'anmu 8 da suke je aikin kashe gobarar, wadanda bayan an kashe ta farko wani ma'aikacin gidan man ya bude wani tanki gobara ta biyu ta kara ta shi ta rutsa da su," in ji Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

    Sai dai rahotanni na cewa adadin wadanda suka jikkatan ya zarce wanda hukumomin suka zayyana.

    Da yake kan babbar hanya gidan man yake, lamarin ya rutsa da gwamman mutane da ke kan hanyarsu ta zuwa inda suka nufa, sai kuma 'yan kallo da suka ciki inda gobarar ta faru.

    b
  14. Afganistan za ta fara dauko malaman makaranta haya a fadin kasar

    B

    Ma'aikatar Ilimi ta Afghanistan ta sanar da cewa za ta fara daukar hayar dubban malamai a matsayin 'yan kwantaragi a fadin kasar kasar.

    Wannan mataki na zuwa ne bayan da fadar shugabancin kasar ta amince da wannan ta yi da ma'aikatar ilimi ta yi mata na dauko malaman haya a makarantun kasar.

    Jami'ai a ma'aikatar sun ce a bara ma'aikatar ta gaza dauko malaman ne saboda annobar korona ga kuma koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi.

    Sai dai a wannan shekarar za a kai ga dauko su bayan da ma'aikatar ilimi da ta kudi suka sahhale hakan.

    Ana samun rahotannin karancin malamai da kuma littatafan karatu a kusan gaba daya lardunan Afghanistan.

  15. 'Yan bingida sun kashe mutum biyu a harin da suka kai wani ofishin 'yan sanda a Ebonyi

    b

    'Yan sanda sun harbe daya daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari ofishin 'yan sanda na Ugbuodu da ke jihar Ebonyi a arewacin Najeriya.

    An harbe matar ne lokacin da 'yan sanda ke musayar wuta da 'yan bindigar sama da su 20.

    Mai magana da yawun rundunar 'yansandan Loveth Odah, ta ce an ga bindiga kirar AK47 da wayar salula da wuka a jikin matar, yayin da sauran suka tsere da muggan raunika a jikinsu.

    Odah ta kara da cewa a yayin rikicin an kashe wani dan sanda guda.

    Kwamishinan 'yan sanda na jihar Aliyu Garba ya yi umarnin a gudan da bincike kan lamarin.

  16. Rashin yanayin mai kyau ya yi sanadiyyar mutuwar masu tsere a China

    b

    Mummunar rashin kyawun yanayi, ya hallaka masu tsere 20 a China.

    Mutanen na cikin wadanda ke gasar tseren yada kanin wani a kasar, a lokacin da ruwan sama hade da iska maikarfi ya afka musu a tsaunin da ke gundumar Gansu.

    Jami'ai a birnin Baiyin sun ce masu tseren su shiga mawuyacin hali sakamakon yadda yanayin ya sauya cikin gaggawa.

    Akwai karin wasu takwas da suka ji mummunann rauni, ya yin da ake ci gaba da neman mutum guda.

    Tuni aka dakatar da gasar tseren da ake yi a wajen yawon bude ido da ke dajin Yellow River.

    b
  17. Shugaban Brazil ya yi kira ga magoya bayansa su yi watsi da dokar korona

    k

    Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya yi kira ga daruruwan masu tuka babura su yi jerin gwano a titunan birnin Rio de Janeiro a yau Lahadi, domin take dokokin da aka gindaya don yaki da cutar Korona.

    Kiran Bolsonaro na zuwa ne, kwana guda bayan gwamnan arewa maso gabashin jihar Maranhao wato Flavio Dino ya ci shugaban tara, saboda take dokar taron jama'a da ya yi, da mutane sama da 400 suka halarta ba kuma tare da sun sanya takunkumin rufe fuska ba.

    Kawo yanzu cutar korona ta kashe 'yan Brazil dubu 400, wanda kasar na daga cikin wadanda korona ta fi yi wa illa a duniya.

  18. Muna kara kiran a mutunta yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza - MDD

    Reuters

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Isra'ila da Falasdinu su mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da ta fara aiki a ranar Juma'a.

    A sanarwar farko da kwamitin ya fitar tun bayan barkewar rikicin, ya kuma nuna damuwa da muhimmancin kai kayan agaji ga Falasdinawa fararen hula.

    Wakilin BBC ya ce an shiga rana ta 3 da fara aikin yarjejeniyar, baya ga kiran bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar, kwamitin tsaro na MDD ya yi makokin farar hular da suka rasa rayukansu a kwanaki 11 da aka dauka ana fada tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

    Wata babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan jin kai, Lynn Hastings wadda ta kai ziyara Gaza, ta ce mutanen yankin sun sare sun zubawa sarautar Allah ido, hare-haren makamai masiu linzaami da Isra'ila ta dinga kai wa ya hallaka yawancin iyalai a Gaza.

  19. Barka da safiya

    Masu bibiyarmu a wannan shafi da fatan an tashi lafiya.

    Buhari Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya.

    Ku kasance tare da mu.