Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu

..

Asalin hoton, CAMPER PHOTOGRAPHY

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa.

Ya rasu ranar Lahadi.

Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84, bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Tuni Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya wallafa saƙon ta'aziyyarsa a shafinsa na Twitter, inda gwamnan ya ce za a yi jana'izar Sarkin a Fadar Zazzau a yau Lahadi da misalin ƙarfe biyar na yamma.

Kauce wa Twitter
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter

Wannan layi ne