Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu sakamakon bugun zuciya

Pierre Nkurunziza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nkurunziza ya shafe shekara 15 a kan mulki

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu yana da shekara 55 a duniya.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Talata ta ce Nkurunziza ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

Sanarwar ta kara da cewa ranar Asabar da daddare aka kwantar da Mr Nkurunziza a wani asibiti mai suna Karusi bayan ya dawo daga wasan kwallon kafa a kusa da gidansa.

Gwamnatin kasar ta sanar da zaman makokin kwana bakwai daga ranar Talata.

Mista Nkurunziza ya jagoranci Burundi tun daga 2005 kuma yana shirin mika mulki ga zababben shugaban kasar, Evariste NDayishimiye a ranar 20 ga watan Agusta.

A shekarar 2015, sanarwar da ya bayar cewa zai tsaya takara a karo na uku ta jefa kasar cikin tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Nkurnziza

Asalin hoton, AFP

Bayan sauya kundin tsarin mulki, ya samu damar yin takara a karo na huɗu a zaɓen da aka gudanar na watan da ya gabata amma sai ya zaɓi ya yi ritaya a matsayin "wani aikin kishin ƙasa".

Yana gab da karɓar dala dubu 540 a matsayin kuɗin sallama daga aiki da kuma wata fada ta ƙasaita.

Mista Nkurunziza ya hau mulki a shekarar 2005 bayan yaƙin basasa da ya yi ajalin mutum 300,000 a ƙasar.