Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Ban kwana

    A nan ne muka kawo karshen labarai da rahotanin da muke kawo muku daga sassan duniya.

    Sai mu tara a gobe idan Allah ya kaimu Buhari Muhammad Fagge ne ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An samu raguwan masu zaman kashe wando a Amurka

    Reuters

    Shugaba Biden na Amurka ya yi farin ciki da wata kididdig da hukumomin kasar suka fitar wadda ta nuna cewa adadin al'ummar kasar masu aikin yi ta karu da dubu 916 a watan Maris.

    A cikin wani jawabi da ya yi a kafar talbijin din kasar, Mr Biden ya ce har yanzu akwai abubuwan da ya kamata ayi wajen rage marassa aikin yi a kasar, amma duk da haka an samu ci gaba bisa la'akari da yawan masu aikin yin da aka samu a yanzu haka.

    Wayar da kan mutanen da aka rinka yi akan muhimmancin rigakafin cutar korona da kuma kudaden tallafin da gwamnati ta ware sun taimaka matuka gaya wajen nasarar da aka samu a yanzu haka ta rage marassa aikin yi a kasar.

  3. Kamfanin Mai na Total ya janye daukacin ma'aikatansa daga Mozambique

    Total

    Rahotanni daga Mozambique na cewa kamfanin Mai na Total mallakar Faransa ya yanje dukkan ma’aikatansa daga inda suke aiki a arewacin kasar.

    A makon da ya wuce ne mayakan jihadi sun karbe iko da yankin Palma inda kamfanin Total ke gudanar da aiki, ana kuma ci gaba da gwabza fada a wajen.

    Tadakayar bayan mayakan jihadin ta haddasa mutuwar gwamman mutane ya yin da wasu dubbunnai suka tsere cikin daji, wasu kuma sun yi amfani da kwale-kwalen zuwa kasashe makofta.

    A makon da ya wuce kamfanin Total ya dakatar da batun komawa bakin aiki a yankin Cabo Delgado wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arzikin Mozambique idan an kamala.

  4. CAF ta saki sunayen kasashen da za su gasar cin kofin Afrika na 2021

    BBC

    A maraicen ranar Juma'a ne hukumar CAF ta saki jerin sunayen kasashen da za su halarci gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2021.

    Gasar da za a buga a kasar Kamaru, an kammala wasannin samun gurbinta ne a tsakiyar wannan makon da muke ciki.

    A 2021 ya kamata a buga gasar amma aka daga ta zuwa 2021 sakamakon annobar korona.

    Yanzu dai za a buga gasar ne tsakanin ranar 9 ga watan Janairun 2022 zuwa shiga ga watan Fabrairun shekarar.

    Mataki na gaba shi ne raba jadawalin gasar wanda ake sa ran za a yi a ranar 25 ga watan Yuni mai zuwa.

    View more on twitter
  5. An kama wani mutum da ya kutsa kai masallacin Makka da makami

    Google

    Dakarun da ke lura da masallacin Makka sun kama wani mutum da ke dauke da wuka a harabar mmasallacin a yammacin ranar Talata.

    Maimagana da yawun 'yan sandan da ke lura da masallacin ya ce mutumin ya fado masallacin ne yana ihu yana nuna goyon bayansa ga kungiyoyin 'yan ta'adda, bayan an idar da sallar La'asar a hawa na farko na masallacin mai tsarki.

    "Nan da nan aka kama mutumin kuma za a dauki matakan shari'a da suka dace a kan shi," in ji kakakin 'yan sandan.

    Shugaban limaman masalacin Sheikh Sudais ya ce, "Mutumin bai girmama muhimmancin wurin ba. Allah ya sanya masallacin ya zama wurin bauta, a yi sallah da ɗawafi da kuma aikin Hajji."

    View more on twitter
  6. An yi bajakolin kambun da Ronaldo ya jefar a filin wasa

    Google

    An yi bajakolin kambun kyaftin din Portugal mai taka leda a Juventus Cristiano Ronaldo, kan kudi dala dubu 75.

    A ranar Asabar din da ta gabata ne dan wasan ya yar da kambun, yayin wasan share fagen samun gurbi a gasar cin kofin duniya da suka buga da Serbia.

    Awasan da aka tashi 2-2 Ronaldo ya jefa wata kwallo da ta ci a karshen lokaci, sai dai alkalin wasan bai ba da ci ba.

    Wasni jami'in kashe gobara ne ya tsinci kambun ya kuma bayar da shi ga wani gidan ba da agaji.

    Duk abin da aka samu na bajakolin za a yi amfani da shi ne a yi wa wata yarinya 'yar wata shida maganin ciwon da ke damunta a kwakwalwa

    Reuters
  7. 'Yan sanda sun ceto gadaci da aka yi garkuwa da shi

    Nigerian Police

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta ceto wasu mutane hudu da ake zargin an yi garkuwa da su a yankin Oshiagu Amia-Ngbo, da ke karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya.

    Kakakin rundunar reshen jihar ta Ebonyi ce ta bayyana hakan, tana cewa an samu nasarar ceto mutanen ne da hadin gwiwar tawagar 'yan sintiri na karamar hukumar.

    "Wasu mutane da ba a sansu ba ne suka sace mutanen a ranar Alhamis, amma kuma an samu nasarar ceto su.

    "Ina amfani da wannan dama ina shaidawa mutane cewa ya kamata su rungumi dabi'ar kwarmata wa 'yan sanda duk wasu ayyukan laifi da ke faruwa a yankunansu.

    "An sace dagacin wannan kauye tare da mutum uku da misalin karfe 2 na yamma a rabar Alhamis, babu kuma wanda ya kawo wa 'yan sanda koken hakan."

  8. Sai an fara maganar mazaunan Falasdinu kafin mu daidaita da Isra'ila - Saudiyya

    Reuters

    Ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan ya ce bai sani ba ko an kusa sabunta alaka tsakanin Masarautar Saudiyya da Isra'ila," yana cewa hakan ya dogara ne kan irin ci gaban da ake samu game da maganar zaman lafiya.

    Bin Farhan ya bayyana hakan ne a watan tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CNN inda ya ce sabunta alakar zai samar da wani gagarumin alfanu a yankin, "kuma sai an fi samun shi ta fuskar tattalin arziki, da zamantakewa da kuma bangaren tsaro.

    A 2002, yace kasarsa ta mika bukatar neman sabunta alaka da karkashin wani shiri na "Samar da zaman lafiya a kasashen larabawa". An fara gabatar da shirin ne a shekarar 1982, wanda a ciki aka yi maganar yadda za a sabunta alakar da kuma maganar sauya wa Falasdinawa mazaunai.

    Bin Farhan ya bayyana cewa ba za a taba daidaita wa har sai an fara cimma matsaya kan mazaunan Falasdinu.

  9. Bankin Raya Najeriya 'ya raba N191.7bn ga masu kananan masana'antu'

    BBC

    Bankin Raya Najeriya ya ce ya raba wa masu kananan da matsagaitan masana'antu bashin naira biliyan 191.7 a 2020.

    Cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Alhamis, alkaluma sun nuna karuwar da aka samu da kusan kashi 89 na duka adadin bashin da aka bayar na naira biliyan 101.5 a 2019.

    Da yake gabatar da bayanin rahotansa na 2020 daki-daki, ya ce an samu cu gaba a kadadrorinsa daga naira biliyan 474.7 a 2019 zuwa 493.5 a 2020, yayin da kuma bashin da ba a kai ga biya ba ya karu da kaso 110 cikin dari daga 101.9bn a 2019 zuwa naira 214,0bn a 2020.

    "Kudaden shigar da aka samu sun karu da kashi 60 kusan ko wacce shekara daga ₦6.6bn a 2019 zuwa ₦10.5bn a 2020."

    Bankin dai ya gano cewa ya samu riba mai yawa karshen 2020 inda takai N34.6 bn, duk da cewa an samu koma bayan tattalin arziki wanda korona ta haifar a shekarar.

  10. Iran ta yi watsi da tattaunawa da Amurka a Vienna

    Reuters

    Iran ta yi watsi da duk wani shirin tattaunawa da Amurka a Vienna, a wani taro da za ta halarta a makon gobe tare da sauran kasashen da aka cimma yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da su, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Iran ta wallafa a shafinta.

    "Amurka ba za ta halarci duk wano taro da Iran za ta je ba, ciki kuma har da taron hadin gwiwar kasashen da aka yi yarjejeniyar nukiliya da su, kuma hakan tabbas ne," In ji mataimakin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi.

    Ya kara da cewa, "Abu da ya dame su ne, in sauran kasashen da ke cikin wannan yarjejeniya suka ce za su tattauna da Amurka.... ko a Vienna ko a wani wuri na daban, Wakilan Iran ba za su yi wata tattaunawa da na Amurka ba a ko wanne irin mataki."

  11. An kashe 'yan sa kai 6 a wani harin kwantan bauna a Burkina Faso

    AFP

    Wani harin kwantan Bauna da 'yan ta da kayar baya suka kai a ranar Alhamis a yankin arewacin Burkina Faso, ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sa kai shida, wadanda suke taimakawa a yakin da ake da masu tsatssauran ra'ayi a yankin.

    Daya daga cikin shugabannin 'yan sa kan ya ce an yi wa mutanen nasu gadar zare ne a yankin "Dablo", wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum shida daga cikin mutanensu, wasu da dama kuma suka jikkata.

    Burkina Faso dai na iyaka da kasashen Mali da Nijar, kuma tana fama da matsalar hare-hare 'yan bindiga tun daga 2015.

    Rahotanni sun ce dalilin wannan rikici akalla mutum 1,200 ne suka rasa rayukansu, miliyoyin mutane kuma sun tsere sun bar muhallansu.

    Masu sharhi na tsokaci kan cewa jami'an tsaro ba su da kayan aiki ba kuma sa samun horon da ya kamata, duk da cewa akwai taimakon dakarun kasashen waje, musamman Faransa da ta ce akwai sojinta kimanin 5,100 a yankin Sahel da ke aikin taimakon yaki da masu ikirarin jihadi, "Barkhane".

  12. An kama mutum huɗu bisa hannu a kai hari kan taron siyasar Charles Soludo

    Soludo

    Rundunar 'yan sandan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta ce ta kama mutum hudu da take zargi da hannu wajen kai hari a taron siyasar tsohon gwamnan babban bankin kasar kuma dan takarar gwamnan jihar Farfesa Charles Soludo.

    Mai magana da yawun rundunar Ikenga Tochukwu ya ce sun kama Mbah Victor, John Olisakwe, Chigozie Omeh da kuma Emmanuel Nnobi bisa hannu a kai hari kan taron na Farfesa Soludo.

    Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kashe jami’an ƴan sanda da ke ba shi tsaro guda uku.

    Farfesa Soludo yana ɗaya daga cikin masu neman kujerar gwamna a zaɓen Anambra da za a yi 6 ga Nuwamban bana a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA)

    Lamarin ya faru ne a kauyen Isuofia da ke karamar hukumar Aguata.

  13. Gobara ta tashi a babbar kasuwar Funtua

    Gobara

    Gobara ta tashi a babbar kasuwar Funtua da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne tun da misalin karfe biyu na daren ranar Juma'a.

    Ganau sun ce gobarar, wadda kawo yanzu ba a san dalilin tashinta ba, ta faro ne daga bangaren da ake sayar da gwanjo na kasuwar.

    Wasu da suka ga yadda wutar take ci, sun ce an yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.

    Hotunan da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wutar take yin rimi.

    Ya zuwa yanzu hukumomi ba su yi karin bayani game da tashin gobarar ba.

    Sai dai wannan lamari na faruwa ne makonni kadan bayan tashin wata gobara a birnin Katsina, wadda ta lashe kayayyakin miliyoyin naira.

    Gobara
    Gobara
  14. Ana bincike kan matar da ta yi zargin yin aman jini bayan riga-kafin korona a Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan ikirarin da wata mata ta yi cewa ta rika aman jini bayan an yi mata allurar riga-kafin korona a jihar.

    Kwamishinyar Lafiyar ta jihar Kaduna Amina Mohammad Baloni ce ta bayyana hakan a sakon da ta wallafa a shafinta na Tuwita.

    Ta kara da cewa an yi wa mutum fiye da 72,000 allurar riga-kafin ta korona a jihar.

    "Mun gudanar da bincike kan mutum uku da suka fuskanci matsala bayan allurar. Kazalika muna gudanar da bincike kan matar da ta yi bidiyon da ya watsu tamkar wutar daji kuma za mu sanar da jama'a sakamakon bincike," in ji ta.

    Da ma dai masana harkokin lafiya sun ce wasu kan fuskanci 'yar matsala sakamakon riga-kafin korona irin su ciwon kai, da amai, suna masu cewa hakan ba ya nufin allurar tana da illa.

    View more on twitter
  15. Ana shirye-shiryen rantsar da Mohamed Bazoum

    Dimbin jama'a ne suke ci gaba da isa wurin da ake shirin rantsar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum kan karagar mulki a yau Juma'a.

    Za a rantsar da shi ne a Niamey babban birnin kasar bayan ya lashe zaben da Kotun Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa.

    Rantsar da Bazoum
    Rantsar da Bazoum

    Shugabannin kasashe da na gwamnati sama da 60 ne ake sa ran za su halarci bikin kuma tuni wasun su suka isa Niamey. Sai dai za a yi bikin cike da tsauraran matakan tsaro.

    Rantsar

    A watan da ya gabata ne Kotun Tsarin Mulkin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Nijar da aka yi zagaye na biyu.

    Mohamed Bazoum na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ya ci zaben da kashi 55.66 cikin 100 na kuri'un da aka jefa abin da ke nufin ya zarce tsohon shugaban kasar kuma dan takarar jam'iyyar Tchanji Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 44.34.

    Rantsar da Bazoum
    Rantsar da Bazoum

    Cikin manyan bakin da ke halartar bikin rantsuwar har da Alhaji Aliko Dangote da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.

  16. Mutum 48 sun mutu sakamakon hatsarin jirgin kasa a Taiwan

    Hatsarin jirgi

    Akalla mutum 48 sun mutu yayin da fiye da mutum 200 suke can a makale bayan wani jirgin kasa da ke dauke da kusan mutum 500 ya yi hatsari sannan ya kauce daga layin dogo a Taiwan.

    Mutane da dama ne suka jikkata, kuma yanzu haka masu aikin ceto suna kokarin shiga taragwan jirgin da suka lalace sosai.

    Rahotanni sun ce jirgin mai taragwai takwas ya tunkuyi wata motar da ke daukar kayan gini wacce ta hau kan layin dogo.

    Jirgin, wanda ya taso daga babban birnin kasar Taipei yana kan hanyarsa ta zuwa Taitung, yana dauke da mutanen da ke hanyar tafiya hutun karshen mako.

    Jirgin ya cika makil da fasinjoji inda sai da wasu suke rasa wurin zama.

  17. Mutum 106 ne suka kamu da korona a Najeriya ranar Alhamis

    Wata yarinya sanye da takunkumi

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 106 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Alhamis, yayin da mutum guda ya mutu.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 33.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 20 a Abuja, babban birnin kasar da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    A jihar Cross River an samu mutum 11 yayin da a Rivesr ma aka samu 11, a jihar Kaduna da ke arewa masu yammacin kasar mutane 7 aka tabbatar sun kamu da korona, sai kuma jihar Edo da aka samu mutane 6.

    Ga yawan waɗanda suka kamu a wasu jihohi • Ondo-6 • Nasarawa-3 • Ogun-3 • Kano-2 • Bauchi-2 • Osun-2 Zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya jimlatan ya kai 162,997, kodayake daga cikinsu an sallami 151,708, sai kuma wasu 2,058 da su kuma suka mutu.

  18. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan lokaci. Muna fatan za ku kasance tare da mu a tsawon wannan rana inda za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta sannan ku tafka muhawara a BBC Hausa.