Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da suka faru a zaɓen Amurka da Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta labarai da rahotannin abubuwan da suka faru.

    Da fatan za ku kasance da mu a gobe Laraba inda za mu shafe yinin ranar domin kawo maku labarai da rahotannin abubuwan da ke faru a sassan duniya.

  2. Biden: Ƙin amincewar Trump na shan kaye "abin kunya ne"

    Biden

    An tambayi Joe Biden bayan kammala jawabinsa kan wane sako Trump ke aikawa duniya kan ƙin amincewa da shan kaye a zaɓen shugaban kasa.

    "Ina ganin wannan abin kunya ne," in ji Biden.

    Ya ƙara da cewa hakan ba zai taimaka wa abin da za a tuna shugaban ba.

    "Na san daga tattaunawar da na yi da shugabannin kasashen waje har zuwa yanzu suna fatan cewa ana sake kallon dimokuradiyyar Amurka a matsayin mai karfi."

    "Nasan daga ƙarshe komi zai daidaita kafin 20 ga Janairu," a cewarsa, inda kuma ya ƙara da cewa sanatocin Republican za su amince da nasararsa.

  3. Trump za mu miƙa wa mulki wa'adi na biyu - Pompeo

    Mike Pompeo

    Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ki amsa tambayoyi kan batun miƙa mulki a lokacin da yake taron manema labarai.

    "Za a samu sauyin gwamnati mai sauki zuwa ga wa'adin mulkin Trump na biyu, "in ji shi, lokacin da aka tambaye shi game da yadda suka tsara miƙa mulki.

    Ya jaddada cewa shugaban zai yi nasara kafin cikar wa'adinsa na farko.

    Masu suka na ganin cewa kalmomin babban jami'in diflomasiyyar na Amurka sun sha bamban da irin maganganun da ya saba yi game da zaben wasu ƙasashe - inda yake kira ga shugabannin da su amince da sakamakon zaben kuma su mutunta tsarin dimokiradiyya.

    Ko jiya mista Pompeo ya faɗi haka kan zaɓen Myamar: "Amurka za ta ci gaba da sa ido kan tsarin zaɓen. Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da an tattara ƙuri'u tare da magance ƙorafe-ƙorafen cikin gaskiya da amana."

  4. An harbe mai gwagwarmayar kare haƙƙin mata a Libya

    An harbe wata fitacciyar yar gwagwarmaya kuma lauya yar kasar Libya a Benghazi yayin da ake ci gaba da tattaunawa game da makomar siyasar kasar a Tunisia.

    An harbe Hanan al-Barassi a cikin motarta a birnin na Benghazi da ke gabashin Libya.

    Ta sha fitowa ta yi magana kan zarge-zargen cin zarafin mata a birnin inda take zargin mayakan da ke da alaka da janar Khalifa Haftar, kwamandan daya daga cikin bangarorin da ke rikici a kasar.

    Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce Hanan da yarta sun sha fuskantar barazanar kisa. Mutuwarta dai ta janyo cece-kuce a Libya inda wasu da dama ke kiran a tabbatar da adalci.

  5. Buhari ya taya Mamman Daura murnar cika shekara 81

    Buhari da Mamman Daura

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura murnar cika shekara 81 da haihuwa tare da yaba masa.

    Sanarwar da fadar shugaban ta fitar, shugaba Buhari ya bayyana Mamman Daura a matsayin ma’aikaci mai ƙwazo kuma ɗaya daga cikin nagartattun mutane “waɗanda wasu ke yi wa mummunar fahimta.”

    Shugaban ya kuma ce Mamman Daura ƙwararre ne a aikin gwamnati da kuma ƙwarewa ta rayuwa da tafiyar da gwamnati.

    "Ba zai yiyu ba a zauna tare da Daura ba tare da an amfana da iliminsa da kuma hikimarsa ba," in ji shugaba Buhari.

    Shugaban ya kuma yi wa Mamman Daura addu’ar ƙarin lafiya da yawancin rai tare da bayyana shi a matsayin kogin ilimi kuma abin koyi.

    Mamman Daura ɗan uwa ne kuma makusancin Shugaba Muhammadu Buhari da ake ganin yana da ƙarfin faɗa a ji a gwamnati, ko da yake ya musanta cewa yana yi wa sha'anin gwamnati katsalandan a wata tattaunawa da ya yi da BBC.

  6. Tsoffin Kansilolin Sokoto sun ce wata 30 ba a biya su hakkinsu ba

    Tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli na jihar Sokoto sun ce sun shafe wata 30 ba a biya su hakkinsu ba.

    Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi 23 da mataimakansu da kuma kansiloli 240 na jihar Sokoto ne suka koka kan irin mawuyacin hali da suka ce sunaciki sanadiyar rashin biyansu hakkokinsu.

    Sun ce sun rubuta kokensu ga gwamnati amma har yanzu ba abin da gwamnati ta yi.

    A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana diba buƙatun kuma za ta biya.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar Muhammadu Bello ya ce gwamnatin gwamna Tambuwal na cikin gwamnatocin jihohin da suka tarar da dimbin basuka da yawa musamman na fansho.

    Ya ce gwamnati tana dibawa kuma a hankali za ta biya bukatun tsoffin shugabannin na ƙananan hukumomi.

    Ku saurari rahoton Abdou Halilou

    Video content

    Video caption: Rahoton Abdou Halilou
  7. Shugaban FA Greg Clarke ya yi murabus

    Greg Clarke

    Shugaban hukumar kwallon Ingila Greg Clarke ya yi murabus kan wasu kalamai da ya yi na nuna wariya ga ƴan wasa baƙaƙen fata.

    Clarke ya bayyana takaici kan kalaman da ya furta inda ya ce "launin ƴan wasa"

    Ya yi kalaman ne yayin da yake magana game da matsalar wariyar launin fata da ya ja hankali a kafofin sada zumunta.

    A cikin sanarwar da ta fitar hukumar FA ta ce Greg Clarke ya sauka daga muƙaminsa.

    Sanarwar ta kuma ce Peter McCormick ne zai jagoranci hukumar a matsayin shugaban riƙo kafin hukumar ta zaɓi sabon shugaba.

  8. Boris Johnson ya taya Biden murnar lashe zaɓe

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya taya zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden murnar lashe zaɓe ta wayar tarho a ranar Talata.

    Editar BBC kan harakokin siyasa Laura Kuenssberg, ta ce shugabannin sun yi minti 20 zuwa 25 suna maganata ta wayar tarho.

    An fahimci cewa Biden ne ya kira Johnson kafin kiran da yake jira daga sauran shugabannin ƙasashen Turai.

    Daga baya Johnson ya fadi a Twitter cewa ya taya Joe Biden murna.

    View more on twitter
  9. Fafaroma John Paul da Benedict sun rufe zargin lalata a fadar Vatican - Rahoto

    Fafaroma Benedict XVI

    Wani rahoto na fadar Vatican ya gano cewa manyan jami’an cocin katolika da Fafaroma biyu sun yi biris da zarge-zargen cin lalata da ake yi wa wani limamin cocin Cardinal Theodore McCarrick wanda ya tozarta a Amurka.

    Bayan sauraron shaidu 90, rahoton ya gano cewa Fafaroma John Paul II da Benedict XVI an shaida masu batun cin zarafin McCarrick amma suka zabi yin watsi da zarge-zargen da ake yi wa limaman cocin na katolika a Amurka.

    Kuma babu wani mataki na hukunci da aka yi yunkuri har sai da Fafaroma Francis ya karɓi abin da aka bayyana tabbatattun hujjoji a 2017.

    An tilasta wa McCarrick yin murabus kuma aka kore shi a bara – Kadinal na farko da aka taɓa tuɓewa kan zargin lalata.

    Sakataren harkokin wajen Vatican, Kadinal Pietro Parolin, ya bayyana takaici kan abin da hakan ya haifar tare da bayyana damuwa kan yadda hakan ya rusa amanar Cocin.

  10. An samu ƙaruwar yawan masu kashe kansu

    Japan ta sanar da adadi mafi girma cikin shekara biyar na mutanen da suka kashe kansu lamarin da masu fafutuka ke dangantawa da tasirin annobar korona musamman tsakanin mata.

    Ƴan sanda sun bayyana cewa mutum dubu biyu da dari da hamsin da uku ne suka kashe kansu cikin watan Oktoba abin da ke nuna an samu karin sama da kashi tamanin na matan da suka halaka kansu cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata.

    Rashin aikin yi na matukar shafar mata a Japan sannan samun kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa matsala ce da suka daɗe suna fama da ita.

  11. Isra'ila ta ce ta harbo jirgin Hezbollah

    Jirgi marar matuki

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta harbo wani jirgin ƙungiyar Hezbollah marar matuƙi bayan ya ratsa ta ƙasarta daga Lebanon.

    Rundunar sojin ta ce babu wata barazana ko hatsari da lamarin ya haifar ga al'umma ko kuma dakarunta.

    Tashin hankali ya sake ɓarkewa tsakanin ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran da Isra’ila a watannin Yuli da Agusta inda suka gwabza faɗa kan iyaka.

  12. Shugaba Erdoğan ya taya Joe Biden murna

    Joe Biden da Kamala Harris

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya aike wa zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden sakon taya murnar nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.

    A cikin saƙon, shugaba Erdogan ya ce yana fatan nasarar za ta amfani abokai da kuma aminnan Amurka

    "Ina taya ku murnar nasarar zabenku, jama'ar Amurka na nuna matukar fatan alheri ga zaman lafiya da ci gaba," in ji Erdogan.

    Shugaban na Turkiya nanata kudirinsa na yin aiki tare da gwamnatin Amurkakan ƙalubalen da ake fuskanta a duniya da kuma na yanki wanda ya ce wannan ya zama wajibi a ƙarfafa hulɗa da ƙawance bisa la'akari da buƙatu da manufofin kowa ta hanyar haɗin gwiwa mai karfi da kawance don bayar da gudummawa ga zaman lafiyar duniya.

  13. Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da haƙar zinari

    Masu hakar zinari a Najeriya

    Gwamnatin jihar Neja a arewacin Najeriya ta bayar da umurnin dakatar da aikin hakar ma’adinai a ƙananan hukumomin Paikoro da Shiroro.

    Gwamnatin ta sanar da ɗaukar matakin ne a cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya fitar.

    Sanarwar ta ce an dakatar da dukkanin ayyukan haƙo ma’adinan ne a ƙananan hukumomin saboda matsaloli na tsaro da kuma muhalli.

    Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta ɗauki mataki kasancewar lalacewar muhalli da rashin tsaro sakamakon ayyukan masu hakar ma'adanai a yankunan ya kai wani mataki na ban tsoro, wanda kuma ke buƙatar matakin gaggawa don magance matsalolin a ƙanana hukumomin da abin ya shafa.

    Sanarwar ta yi kira ga ƙungiyar masu haƙo ma’adinai da kuma shugabannin gargajiya na yankin da su ba gwamnati haɗin kai da kuma hukumomin tsaro.

  14. An ja hankalin ƴan siyasar Nijar kan furta kalamai marasa daɗi

    Kwamitin dattijan Jamhuriyyar Nijar ya ja hankalin 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a ƙasar a kan su guji furta kalamai marasa daɗi da za su iya haifar da tashin-tashina a tsakanin jama'a yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓe.

    A wata sanarwa da 'yan kwamitin suka fitar ɗazun nan a Yama, sun yi kira ga dukkan ɓangarorin siyasar Nijar ɗin da su sanya wa zuƙatansu ruwan sanyi don ganin an yi zaɓe lami lafiya an kuma ƙare lafiya.

    Kwamitin ya ce ya gana da dukkan ɓangarorin siyasar ƙasar daban-daban inda ya ja hankalinsu game da hakan.

    Video content

    Video caption: Rahoton Tchima kan Kwamitin dattijan Jamhuriyyar Nijar
  15. Rasha za ta aika dakarun wanzar da zaman lafiya Nagorno Karabakh

    Putin

    Rasha za ta aike ɗaruruwan dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa yankin Nagorno Karabakh da yankunan da ke kewaye da shi bayan da Armenia da Azerbaijan suka amince su kawo karshen yaƙin da suke gwabzawa na tsawon mako shida.

    Za a girke sojoji dubu biyu a yankin.

    Yarjejeniyar zaman lafiyar ta sa farin ciki a zuƙatan al'ummar Azerbaijan.

    Shugaban Azerbaijan, Ilham Aliyev ke cewa na sanya hannu kan wannan yarjejeniyar cike da farin ciki da kuma alfahari kuma ina son taya dukkan mutanen Azerbaijan murna da wannan abin tarihi.

    Sai dai akwai wasu da labarin bai yi musu daɗi ba a Armenia inda masu zanga-zanga suka lalata gine-ginen gwamnati tare da neman Firaminista Nikol Pashinyan ya yi murabus.

    Ƙarkashin yarjejeniyar, Azerbaijan za ta ci gaba da riƙe yankin da ta ƙwace a lokacin da ake rikicin.

    Sojojin Armeniya kuma za su janye daga manyan yankuna da ke kusa da yankin da ake taƙaddama a kansa wanda ya shafe kusan shekara 30 yana ƙarƙashin ikonsu.

  16. An jefar da gawar wata yarinya a maƙabarta bayan yi mata 'fyaɗe' a Kaduna

    Hukumomi a jihar Kaduna sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike don gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwar yarinyar nan da aka ga gawarta yashe a wata maƙabarta a ranar Lahadin da ta gabata.

    Lamarin dai ya auku ne a unguwar Kurmin Mashi da ke yankin ƙaramar hukumar Kaduna Ta Kudu, yarinyar dai ana fargabar an yi mata fyaɗe ne lamarin da ya kai ga mutuwar.

    Ku latsa alamar lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahoton Zahraddeen Lawan:

    Video content

    Video caption: Rahoton Zahraddin Lawan kan kisan yarinya a Kaduna
  17. Dole ne a raba rigakafin korona ga kowace ƙasa – Buhari

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya "wajabta" wa shugabannin duniya da su rarraba rigakafin annobar cutar korona ga dukkanin ƙasashe.

    "Dole ne duniya ta tabbata an raba maganin cutar ba tare da bambanci ba ga dukkanin ƙasashe domin kare rayukan jama'a," in ji Buhari, cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa a yau Talata.

    Buhari ya ce ya yi murna da samun labarin cewa rigakafin korona - wadda kamfanin Pfizer ya samar - "tana aiki kashi 90 cikin 100".

    A watan Mayun da ya gabata Shugaba Buhari ya amince a karɓo maganin gargajiya da ƙasar Madagascar ta samar a matsayin rigakafin korona. Sai dai ba a yi amfani da shi ba bayan rahotanni sun ce hukumomi a ƙasar sun gano ba zai iya maganin cutar ba.

    Cutar korona ce ta yi ajalin Abba Kyari, makusancin Buhari kuma tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ranar 17 ga watan Afrilun 2020.

    Ya zuwa yanzu, cutar ta kama mutum 64,184 a Najeriya, 60,069 daga cikinsu sun warke, sannan 1,158 sun rasa rayukansu.

    View more on twitter
  18. Baƙuwar cuta ta kwantar da mutum 11 a asibiti a Jihar Oyo

    Seyi Makinde

    An kwantar da mutum 11 a asibiti biyo bayan wata cuta da ta kama su a Ƙaramar Hukumar Lagelu ta Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.

    Kwamishinan Lafiya Bashiru Bello ne ya tabbatar wa da kafar Channels TV, yana mai musanta rahotannin cewa wasu sun mutu sakamakon cutar da ba a san haƙiƙaninta ba zuwa lokacin haɗa rahoton.

    Duk da cewa alamun cutar sun yi kama da na kwalara, Kwamishina Bello ya ce an ɗauki samfurin mutane daga asibitin domin yin gwaji kuma ana jiran sakamako.

    Ya ce ba za su iya danganta ta da kwalara ba a yanzu ganin cewa suna jiran sakamako, duk da cewa ma'aikatan lafiyar da aka tura yankin sun tabbatar da ƙarancin tsafta da kuma rashin ruwan sha mai tsafta.

    Wannan lamari na zuwa ne yayin da wata cutar da hukumomi suka ce shawara ce ta kashe mutum 35 a Jihar Delta da kuma wasu fiye da 50 a Enugu a watan Oktoba.

    Hukumar lafiya a matakin farko ta Najeriya ta ce za ta fara aikin rigakafin cutar cikin gaggawa a yankunan da abin ya faru.

  19. Biden zai kare tsarin kiwon lafiya na Obamacare

    Joe Biden

    Nan gaba kaɗan ake sa ran Joe Biden zai yi jawabi a jiharsa ta Delaware game da dokar tsarin kiwon lafiya mai sauƙi ta Affordable Care Act, wadda aka fi sani da Obamacare.

    Shugaba Trump ya nemi ya soke dokar bayan ya hau mulki, wadda miliyoyin 'yan ƙasa suka dogara da ita. Sai dai batun na gaban kotu.

    Zai yi maganar ne sa'o'i kafin fara shari'a a Kotun Ƙoli game da dokar, abin da ka iya kaiwa ga soke ta.

    Shekara takwas da ta gabata kotun ta yi hukuncin cigaba da amfani da mafi yawan ɓangarorinta, amma tun da Trump ya naɗa Coney Barrett a cikin alƙalin kotun, yanzu shida daga cikin alƙalan guda tara 'yan ra'ayin riƙau ne.

  20. Cutar korona ta kashe fitaccen ɗan siyasar Falaɗinu Saeb Erekat

    Saeb Erekat

    Ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasar Falasɗinawa, Saeb Erekat, ya rasu sakamakon cutar korona, a cewar gwamnati.

    Ɗan shekara 65 ɗin ya mutu ne a cibiyar Hadassah Medical Center da ke birnin Ƙudus.

    Erekat, shi ne babban sakatare na Palestine Liberation Organisation (PLO) kuma mai bayar da shawara ga Shugaba Mahmoud Abbas na Palestinian Authority (PA).

    Ya shafe shekara 25 yana jagorantar Falasɗinawa a teburin tattaunawa tsakaninsu da Isra'ila.

    Saeb Erekat ya taimaka wurin ƙulla Yarjejeniyar Oslo a 1993, wadda ta kai ga ƙirƙirar PA da bai wa Falasɗinawa ƙayyadajjen 'yancin kai a Zirin Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a karon farko tun bayan Isra'ila ta mamaye yankin a 1967.

    Shugaba Abbas ya ce mutuwar "ɗan uwammu kuma aboki, jajirtaccen nan, Dr Saeb Erekat, ta jawo wa Falasɗinawa babbar asara".

    Ranar 8 ga watan Oktoba Erekat ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona.