Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na bbchausa.com a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku kai tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya.

    A madadin Buhari Fagge da NAsidi Adamu Yahaya, ni Halima Umar Saleh nake cewa sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Kuna iya zuwa kasan wannan shafi don karanta wadanda aka wallafa tun safe.

    Mu kwana lafiya.

  2. Birtaniya za ta kakaba takunkumi kan mutane da kungiyoyin da suka taka rawa wajen cin zarafin bil'adama

    Birtaniya za ta kakaba takunkumi kan mutane 49 da kungiyoyin da suka taka rawa wajen mummunan cin zarafin bil'adama shekarun da suka gabata.

    Za a karbe kadarorin mutanen da ke Birtaniya, kan taka rawa a mutuwar lauyan nan dan Rasha Sergei Magnitsky a shekarar 2009e, a kuma haramta musu shiga kasar.

    Haka kuma lamarin zai shafi 'yan Saudiyya masu hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 20018.

    Wannan shi ne takunkumin da Birtaniya ta dauka na kashin kai ba tare da Tarayyar Turai ko Majalisar Dinkin Duniya ba.

    Sakataren harkokin waje Domonic Raab ya ce matakin kakkausan sako ne aka aike.

  3. 'Yan bindiga 200 sun kashe mutum 15 a Katsina

    Rahotanni daga kauyen 'yar Gamji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga kusan 200 dauke da makamai sun kai hari inda suka kashe mutane fiye da 15.

    'Yan bindigar wanda suka je a babura sun kashe manoman da suka tarar a gona ne.

    Video content

    Video caption: Rahoton Aisha Shariff kan harin Katsina
  4. Isra'ila za ta rufe wuraren shaye-shaye da gidajen rawa don rage bazuwar korona

    Benjamin Netanyahu

    Isra'ila ta ba da damar rufe wuraren shaye-shaye da gidajen rawa har ma da na motsa jiki, bayan da aka samu bazuwar annobar korona sosai.

    Firaminista Benyamin Netanyahu ya ce suna dab da daukar matakin kulle kasar baki daya.

    An fara samun masu kamuwa da cutar korona mutum dubu daya a duk rana a Isra'ila.

    Wani masanin cutuka masu yaduwa da ke Jami'ar Hebrew Hagai Levine ya ce sauran kasashe sai su dauki darasi daga Isra'ila, wurin ganin ba su cire dokar kulle ba a daidai lokacin da cutar koronar ke tsaka da bazuwa.

    Annobar korona ta harbi sama da mutum 30,000 a Isra'ila, ta kuma yi ajalin mutum 330.

  5. 'Yan majalisa sun kai ziyarar aiki filin jirgin saman Abuja

    Wasu 'yan majalisar tarayyar Najeriya sun kai ziyarar aiki filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin kasar.

    'Yan majalisar, wadanda suka hada da shugaban kwamitin zirga-zirgar jiragen sama, sun je filin jirgin saman ne ranar Litinin don duba yadda abubuwa ke gudana gabanin fara tashin jirage a kasar.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito 'yan majalisar na rokon hukumomi da su tabbatar da bin dokokin kariya a yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar.

    Lawmakers
    Lawmakers
    Lawmakers
    Lawmakers
  6. An kori manyan 'yan sanda 10 daga aiki a Najeriya

    Shugaban 'yan sandan Najeriya

    Hukumar kula da Aikin 'Yan sanda ta Najeriya ta kori wasu manyan jami'anta 10 tare da rage wa wasu takwas din girma sakamakon wasu laifuka da suka sabawa dokokin aiki.

    Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani, ya fitar a ranar Litinin.

    Ani ya ce an dauki matakin ne a wajen wani taro na hukumar, wanda aka shafe mako uku ana gudanarwa aka kuma kammala shi a ranar Laraba daya ga watan Yulin 2020.

    Duk da cewa dai sanarwar ba ta bayyana sunayen mutanen da abin ya shafa ba, ta bayyana cewa jami'an da aka sallama din sun hada da mutum daya mai mukamin sufuritanda SP da biyar masu mukamin DSP da hudu masu mukamin ASP.

    "Wani mataimakin kwamishina (DCP) da cif sufuritanda (CSP) na daga cikin wadanda aka rage wa mukami, wani mataki da ya shafi wasu masu mukamin sufuritanda hudu SP da DSP da kuma ASP,'' a cewar sanarwar.

    Ta ci gaba da cewa: ''Hukumar ta amince da yin hukunci mai tsanani ga jami'ai 16 da gargadi ga wasu hudun.''

  7. Labarai da dumi-dumiGwamnatin Najeriya ta sa ranar jarrabawar kammala sakandare ta WAEC

    waec

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya ranar fara jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC ta shekarar 2020.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewar karamin Ministan Ilimi na Najeriya Emeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen taron kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 a Abuja, babban birnin kasar.

    Ya ce za a yi jarrabawar ne daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumban 2020.

    Nwajiuba ya ce, “Za a fara jarrabawar daga 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba. Don haka iyaye ku aje hakan a ranku.

    ''Mun yi iyakar yin mu kuma mun tattauna da wakilanmu a WAEC yau da rana, muyn tabbatar da ranakun cewa za a yi jarrabawar ne daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba.

    “Daga gobe, za mu daddale da masu ruwa da tsaki a harkar, duk za su halarci taron na gobe.

  8. Ƙa'idojin kariya daga cutar korona a Hajjin bana

    Getty

    Hukumomi a Saudiyya sun wallafa wasu ƙa'idojin kariya daga cutar korona ga mahajjatan da aka yarjewa sauke farali a bana.

    Sabbin ƙa'idojin sun haɗa da haramta wa mahajjata taba Ka'aba yayin aikin Hajjin wanda ake ganin ya shafi hana taɓa Hajraul Aswad da ake taɓawa lokacin ɗawafi.

    Ga dai sharuddan a jere kamar yadda ma'aikatar ta fitar:

    • Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.
    • Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.
    • Ba za a bar mutanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba.
    • Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.
    • Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna.
    • Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.
    • Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen.
    • Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.
  9. Ana ci gaba da alhinin mutuwar wanda ya kirkiri taken The Good The Bad

    BBC

    Ana ci gaba da nuna alhinin mutuwar shahararren mai busannan a fina finan Hollywoood Ennio Morricone dan kasar Italiya.

    Firanministan Italiya Guissepe Conte ya bayyana Marigayi Morricone a matsayin mutumin da ya karfafa wa 'yan kasarsa wurin cimma burin da suke da shi a rayuwa.

    Sunan Mista Morricone ya fito a duniya a lokacin da ya yi busar shahararren fim dinnan na Hollywood wato 'The Good The Bad and The Ugly'.

    Morricone ya lashe kyautar fina finai ta Oscar har sau biyu, kuma ya mutu yana da shekaru 91.

  10. China ta cire wasu littattafai daga manhajar karatun sakandire

    AFP

    Hukumomi a China sun sha alwashin kwashe duk wani littafi da ke dauke da bayanan da ke tababa kan 'yancin da ta ke dashi a dakunan karatun makarantun sakandare da kuma jami'o'i.

    Haka kuma za su ci gaba da sa ido kan litattafan da dalibai ke karantawa don su tabbatar cewa dokar tsaro da China ta kakaba a Hong Kong ba ta samu cikas ba.

    Tuni aka fara cire littattafan da masu rajin kare demokradiyya suka rubuta a dakunan karatu da ke Hong Kong.

    A wata sabuwa Kanfanin sada zumunta na Facebook da Whatsapp sun yi watsi da bukatar gwamnati a Hong Kong na ba ta wasu bayanai da suka shafi wasu al'ummar yankin.

  11. China ta gargadi Burtaniya kan shiga harkokinta

    AFP/GETTY IMAGE

    Jakadan China a Burtaniya ya gargadi gwamnatin Burtaniyar da cewa za ta dandana kudarta matsawar ta fara yi wa kasarsa kallon abokiyar gaba.

    A wani taron manema labarai da ya maida hankali kan sabanin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu, Liu Shiyoming ya ce babu abin da zai hana fasahar intanet ta 5G mallakar kanfanin Huwaei na China samun karbuwa ko da hannun Burtaniya ko babu.

    Mista Shiyoming ya kuma soki shirin gwamnatin Firanminista Boris Johnson na bai wa yan Hong Kong kusan miliyan uku takardar zama yan kasa, biyo bayan sabuwar dokar tsaro da China ta bullo da ita a Hong Kong.

    Ya ce yin haka shiga sharo ba shanu ne.

    Mista Shiyoming kenan ya ke cewa Hong Kong wani bangare ne na Chana, kuma abunda Burtaniya ke kokarin yi katsalandan ne kan abinda bai shafe ta ba.''

    Tun farko mai fafutukar Demokradiyya a Hong Kong Joshua Wong, ya yi kira ga kasashen duniya da su saka baki kan abinda ya kira karfakarfar da Chana ke kokarin yiwa Demokradiyya a Hong Kong.

  12. An sassauta dokar kulle a Kenya

    Kenya

    Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da sassauta dokar kulle da aka saka da nufin dakile bazuwar annobar korona.

    Ya ce daga ranar Talata an bayar da damar shige da fice a manyan biranen Nairobi da kuma Mombasa.

    Duk da bayar da damar zirga zirga, Mr Kenyatta ya tsawaita dokar hana fita da dare na tsawon wata daya.Kuma babu batun bude wuraren shakatawa ko kuma hada tarukan siyasa.

    Bugu da kari jiragen da ke zirga zirga cikin gida za su dawo bakin aiki mako mai zuwa.

    Za kuma a bude tashoshin jirgin kasa da kasa a watan Agusta.

    Cutar korona ta kama mutum dubu takwas a Kenya, ta kuma yi ajalin mutum dari da sittin.

  13. Tanzania ta rufe kusan duka cibiyoyin killace masu korona a kasar

    Getty

    Tanzaniya ta rufe kusan duka cibiyoyin da aka ware domin lura masu annobar korona.

    Gwamnati ta ce raguwar masu cutar da ake samu a fadin kasar shi ne ya janyo rufe cibiyoyin a fadin kasar.

    A ranar Juma'a, Ministar Lafiya Ummy Mwalima ta ce yanzu cibiyoyi 11 ne suka yi ragowa, ciki har da masu zaman kansu da aka bude.

    Wadannan na cikin cibiyoyin 85 da aka kirkiro domin shawo kan annobar Covid-19.

    Misistar Lafiyar ta ce:

    "Muna godiya ga Allah kan cewa korona na kokarin barin kasar mu Tanzania.”

    Ta kuma ja kunnan mutane kan cewa kar su sakankance, akwai yiwuwar cutar za ta dawo a karo na biyu.

    Ministar ta ce mutane za su iya ci gaba da zuwa cibiyoyin domin duba lafiyarsu, tun da sun tashi daga cibiyoyim killace marasa lafiya.

  14. Ana kamen mata sakamakon sanya bidiyo a TikTok a Masar

    AFP

    Jami'an tsaro a Masar sun ce suna tsare da wata matashiya da ke da mabiya sosai a manhajar TikTok a wani kamen matan da ke da karfin fada aji a kafafen sada zumunta da suke yi a kasar.

    Ana zargin Hadeer al-Hady da wallafa bidiyon da bai kamata a intanet.

    A TikTok, Hadeer al-Hady na sanya bidiyon wata fitacciyar waka a Masar ta na wasa da lebenta.

    An kama mata da dama a Masar - tare da wasu maza kalilan, a yan makonnin bayan nan saboda yanzu bidiyoyin da basu kamata ba.

    Mai gabatar da kara na Masar ya ce za su ci gaba da sanya idanu kan intanet kamar yadda suke sanya idanu kan iyakar kasar.

  15. Messi na iya komawa Man City, PSG za ta karbo Bellerin

    Messi

    Manchester City za ta iya sayen dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, idan kwangilar shi ta kawo karshe a Barcelona a badi idan kuma Pep Guardiola ya bar kulub din.(Talksport)

    Chelsea na diba yiyuwar sayar da 'yan wasanta shida domin samun kudin da za ta karbo dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, wanda darajarsa ta kai fam miliyan £90m a kungiyarsa taBayer Leverkusen.(Express)

    Arsenal da Napoli na hamayya kan dan wasan gaba na Newcastle da Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekara 23.(Le10 Sport in French).

    Latsa nan don karanta cikakken labarin:

  16. India ta sha gaban Russia a yawan masu dauke da Covid-19

    India

    An samu karin mutum 24,000 da suka kamu da cutar korona a India cikin sa'a ashirin da hudu, don haka yanzu kasar ta fi Rasha yawan masu dauke da cutar.

    Yanzu India ita ce kasa ta uku da ta fi fama da cutar korona inda mutum 697,413 suka harbu da ita.Cutar ta yi ajalin mutum 19,693.

    An samu karuwar masu dauke da cutar ne sakamakon karuwar da aka samu ta wadanda suka kamu da ita a jihohin Telangana, Tamil Nadu da kuma Karnataka.

    India ta sake bude wuraren kasuwaci, da na ibada da kuma ofisoshi wata daya da ya wuce.

  17. Tsohon mataimakin shugaban APC Inuwa Abdulƙadir ya rasu

    Inuwa

    Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya (Arewa maso Yammacin kasar), Alhaji Inuwa Abdulkadir, ya rasu.

    Iyalan marigayin sun tabbatar wa BBC Hausa cewa fitaccen dan siyarar na jihar Sokoto a rasu ne ranar Litinin da safe.

    Sai dai ba a san sanadin rasuwarsa ba kawo yanzu.

    Inuwa Abdulkadir, wanda ya taba rike mukamin Ministan Matasa na Najeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyar APC .

    Sai dai jam'iyyar, lokacin shugabancin Mr Adams Oshiomhole, ta taba dakatar da shi da Lawal Shu'aibu, mataimakin shugaban daga cikinta.

    Amma a watan Maris, Mr Adams Oshiomhole, ya sanar da yafe musu laifukan da ya ce sun yi na zagon-kasa ga jam'iyyar.

  18. An soke bikin samun 'yancin Malawi saboda COVID-19

    Lazarus

    Sabon shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya soke bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar sannan ya rage shagulgulan da za a yi na bikin rantsar da shi ranar Litinin.

    An sa ran gudanar da gagarumin biki a dukkan tarukan biyu da za a yi a babban filin wasa na Lilongwe, babban birnin kasar.

    Ranar Asabar, shugaban kasar ya sanar cewa za a bar rabin mutanen da filin wasan zai dauka, wato mutum 20,000, su halarci bikin domin hana yaduwar cutar korona.

    Sai dai kuma yanzu an soke gudanar da dukkan tarukan a wurin, inda za a yi bikin shan rsantsuwa a barikin soji wanda mutum bai fi 100 za su halarta.

    Soke wadannan bukukuwa zai rage kaifin murnar da magoya bayansa suke yi tun lokacin da Lazarus Chakwera ya lashe zabe.

  19. Barkanmu da ranar Litinin

    Lale marhabin da sake zuwa wannan shafin namu mai dauke da labarai da rahotanni.

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Kuna iya bibiyarmu a ko da yaushe, sanna ku tafka muhawara a BBC Hausa.