Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge, Halima Umar Saleh da Badariyya Tijjani Kalarawi

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Muna godiya da kasancewa da mu a wannan yini na Juma'a baki ɗayansa.

    Ƙarshen rahotannin kenan na yau a wannan shafi. Sai kuma gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za mu zo muku da sabbin rahotanni kan wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    A madadin Buhari Muhammad Fagge da Badriyya Tijjani Kalarawi, Halima Umar Salehke muku mu kwana lafiya.

  2. Majalisar Dinkin Duniya ta ce hukumomi ba su kubutar da jirgin 'yan cirani ba

    Hukumar ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi hukumomin kasashe da dama da ƙin yin kataɓus wajen ceto ‘yan cirani 130 da suka mutu a tekun Libya.

    Hukumar IOM ta ce hukumomin kasashen da ke kusa, sun ƙi daukar matakin gaggawa bayan samun rahoton hadarin da ‘yan ciranin suke ciki duk da cewa hakkin hakan yana wuyansu.

    Masu fafutuka da suka yi ƙoƙarin taimaka wa ‘yan ciranin da ke tsaka mai wuya a tekun, sun shaida wa hukumomin Italiya da Malta da Libya halin da ake ciki.

    Kamar yadda suka sanar, jami’an Italiya sun ce hakkin kuɓutar da sun a wuyan masu gadin tekun Libya.

    Wadanda suka ce babu kyawun yanayin da za su shiga teku domin nemansu.

    Daga bisani kungiyar agaji ta SOS Mediterranée ta tsinto wani bangare na kwale-kwalen.

  3. Labarai da dumi-dumiMayaƙan ISWAP sun kai hari garin Geidam na jihar Yobe

    Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari garin Geidam a yau Juma'a.

    Mai magnaa da yawun ƴan sandan na Geidam ya tabbatar wa da BBC labarin sai dai ya ce zuwa yanzu hukumomi ba sa san yawan ɓaranar da mayaƙan suka yi ba.

    "Sai mun gama tattara bayanai sannan za mu yi ƙarin bayani.

    Amma ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6.30 zuwa 7 na yamma daidia lokacin buɗa baki.

    "Sun shigo ne ta ƙauyukan da ke kan iyakar Najeriya da Nijar, amma tuni sojojin sama suka fara shawagi da jiragen yaƙi, al'amarin da ya sa mayaƙan suka lafa.

    "Sai dai muna da tabbacin suna nan laɓe a garin ba su fita ba, don kuwa suna ta watsar da wata wasiƙa a ƙasa ta ko ina inda suke neman mutane su ba su haɗin kai don su ƙwace garin su kafa daularsu," a cewar kakakin ƴan sandan.

    Wasu rahotannin sun ce mayaƙan da ƙarfinsu da kuma yawansu suka shiga garin.

    Wani ganau ya cewa BBC mayaƙan sun yi ta harbe-harbe a garin inda mutane suka runtuma neman wuraren ɓuya.

    "Yanzu haka duk muna cikin gidajenmu a ɓoɓɓoye muna cikin tashin hankali don ba mu san me zai faru ba," in ji shi.

    wasikar iswap
    Image caption: Wasikar da ISWAP ke jefarwa a garin Geidam wadda BBC ta samu daga wajen ƴan sanda
  4. Gwamnatin jihar Kaduna za ta rushe kasuwar Panteka

    Gwamnatin jihar Kaduna ta bai wa 'yan kasuwar Panteka wa'adin kwanaki bakwai su kwashe dukkan kayayyakinsu, su bar kasuwar.

    A wata sanarwa da shugaban hukumar tsara birane da ƙauyuka ta jihar Kaduna ya rattaba wa hannu aka kuma aike wa manema labarai, ta ce idan 'yan kasuwar ba su yi biyayya ga wannan kira ba, har kuma wa'adin ya cika, to gwamnati ba ta da wani zabi face ta ƙwace kayansu tare da rushe shagunan da ke kasuwar kamar yadda sashe na 60(S) ya tanada.

    Kasuwar tana kusa da Kwalejin Kimiyya ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, sannan mazauna garin na cewa za ta kai kimanin shekara 50 da kafuwa.

  5. Jirgin sojin ruwan Najeriya ya kusa isa gida

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta sanar da cewa jirgin ruwa da ta saya ya baro Lisbon ranar Juma’a 23 ga watan Afrilu, inda ake sa ran zai bi ta kasar Sifaniya kafin ya iso Najeriya.

    Rundunar ta ce tawagar sojin Najeriya karkashin jagorancin Rear Admiral Monday Unurhiere da jami’an ofishin jakadancin kasar a Sifaniya ne za su tari jirgin idan ya isa kasar a ranar 27 ga watan nan, kafin ya wuce Banjul din kasar Gambia.

    Idan ba a manta ba a baya-bayan nan rundunar ta karbi jirgin ruwa samfurin NNS LANA a kasar Faransa.

    Jirgin irinsa na farko a Najeriya wanda zai dinga duba tsaron teku, zai maye gurbin wanda ake da shi a halin yanzu, wanda aka samar shekaru 10 da suka gabata.

    Yana kuma daukar fasinja da ma’aikata 50, sannan yana da tsananin gudu.

  6. Indiya na tsaka mai wuya saboda karuwar masu korona

    Asibitoci sun cika makil da masu cutar korona, ta kai wasu daga ciki sun dakatar da daukar marasa lafiya

    Iyalai ashirin da biyar a birnin Delhi na kasar Indiya sun wayi garin Juma’a da labarin mace-macen ɗaya daga cikin dangin kowannensu da ke jinyar cutar Korona a asibitin Sir Ganga Ram da ke birnin.

    Daraktan asibitin ya shaida wa manema labarai cewa suna fama da matsanancin karancin iskar shaka ta Oxygen, inda 25 daga cikin majinyatan da suke tsananin bukatar iskar suka mutu.

    Wannan na zuwa ne a karshen mako bayan yawancin asibitoci a Delhi sun bada rahoton karancin iskar shaka, wadda ke taimakawa masu fama da cutar korona yin numfashi.

    Ko a ranar Talata ministan lafiya ya roki kotun gwamnati ta sanya baki wajen umartar masu tankar gas kai iskar da zarar an bukata komai dare.

    Tankar Gas ta kai iskar shaka asibtin na Sir Ganga Ram, jim kadan bayan an sanar da cewa wasu Karin marasa lafiya 60 na cikin halin rai-kwa-kwai, mutu-kwa-kwai.

    Karuwar masu kamuwa da cutar korona ta janyowa fannin kiwon lafiyar Indiya neman durkushewa, bag a asibitocin da ke birane ba har zuwa na karkara.

  7. Amurka ta bai wa Najeriya maganin malaria miliyan 7, da gidan sauro miliyan 14 a 2020

    A rahoton da majalisar dokokin Amurka take fitarwa duk shekara, shugaban shirin yaƙi da cutar Malaria ya ce a shekarar da ta gabata duk da cewa ana fama da bala’in ɓarkewar annobar cutar korona, ta taimaka wa Najeriya da maganin cutar zazzabin cizon saura milyan14.7, da kuma miliyan 8.2 na mata masu juna biyu da ƙananan yara.

    Shirin magance zazzabin cizon sauron ya ba da tallafin gidan sauro sama da miliyan 7, da abin gwajin cutar miliyan sama da miliyan 7, an kuma bai wa jami’an lafiya sama da 9,000 da za su din ga kula da ma su cutar kamar yadda ya dace.

    Shirin na hadin gwiwa da hukumar USAID, da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Amurka CDC, jami’an sun yi aikin hadin gwiwa da abokan huldarsu da kungiyoyi masu zaman kan su, kuma ‘yan Najeriya miliyan 41 a sassa daban-daban na kasar ne suka ci gajiyarsa.

    Amfani da ITN na da matukar tasirin ba da kariya daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.

    Tun a shekarar 2010 shirin ya ke taimaka wa Najeriya wajen rarraba kayayyakin asibiti da suka hada da gidan sauro miliyan 61, wadanda ake amfani da su a jihohi 43.

    Daraktar USAID Anne Patterson da ke sa ido kan ayyukan ta ce; ‘’Cutar zazzabin cizon sauro, ita ce sahun gaba a cututtukan da ke saurin hallaka yara a Najeriya.

    "Muna farin cikin ganin aikin da muke yi tare da abokan huldarmu da gwamnatin Najeriya sun kawo sauyi da ci gaba, za kuma mu ci gaba da ba da tallafin kamar yadda ya dace domin ganin an kakkaɓe zazzabin cizon sauro a kasar.’’

  8. An kai mata jami'an tsaro 99 Masallacin Madina

    @Saudi_Gazette

    Rukunin farko na mata jami'an tsaro da za su yi aiki a Masallacin Annabi Muhammad sun isa harabar masallacin, domin taimaka wa mata masu ibada a yayin Azumin watan Ramadan.

    Manjo Janar Abdul Rahman Al-Mashhan wanda shi ne daraktan 'yan sandan Madina ya ce, rukunin farko na dauke da mata jami'ai 99 ne wadanda aka dauka aiki tun daga ranar 18 ga watan Oktoban 2020 (Rabi Al-Awwal 1).

    "Samar da matan zai taimaka wajen nuna wa baƙi mata yadda za su yi aiki a Rawdah Sharif yadda ya kamata.

    Matan suna kuma taimaka wa wajen tabbatar da an bi dokar kariyar korona da nuna yadda ya kamata a bi sahun sallah a bangaren mata yadda ya kama."

    Daraktan ya ce an ba su horon da ya kamata na harkar tsaro, domin dai su gudanar da ayyukansu cikin kwarewa yadda ya kamata.

  9. Yan bindiga sun kashe dalibai uku na Jami'ar Greenfield da aka sace a Kaduna

    Ma'aikatar tsaro ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce yan bindiga sun kashe dalibai uku na na Jami'ar Greenfield da aka sace a Jihar.

    Cikin wani sakon Twitter da Ma'aikatar ta fitar ta ruwaito Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa'i ya yi Allah-wadai da wannan mummunan rashin imani ga rayuwar dan adam.

    Ya kara da cewa dole a yaki wadannan 'yan bindiga ta ko wanne hali.

    Ya kuma ce sharri ba zai taba yin nasara ba kan alheri. Ya kuma aika ta'aziyyarsa ga mutanen jihar da iyayen yaran da suka rasa yarukansu.

    Kuma gwamnati za ta gaba da shaida wa mutanen jihar halin da ake ciki game da lamarin.

    View more on twitter
  10. Ghana ta haramta hakar zinare a fadin kasar

    Getty Images

    Hukumomin Ghana sun haramta hakar zinare a fadin kasar a wani mataki na hana hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

    Kasar ce dai ta fi ko wacce samar da zinare a Afrikasai dai harkokin da masu hakar ma'adanan ke yi ba bisa ka'ida ba sun matukar lalata wurrare a yankuna daban-daban.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar albarkatun kasa ta Ghana ta fitar, ta bai wa duka kamfanonin da ke da izinin hakar ma'adanai wa'adin kwana bakwai domin domin su dakatar da ayyukansu.

    Ma'aikatar ta zayyana wasu kamfanoni da kuma daidaikun mutane da ke da takardun izinin hakar zinare amma da dama sun kare a hakar ba bisa ka'ida ba.

    Harkokin hakar ma'adanai ta lalata ruwan sha a Ghana ta kuma jefa wasu al'umma cikin halin damu sakamakon hakan.

    A 2017, Gwamnatin Ghana ta so ta magance wannan matsala ta hanyar samar da wata tawaga ta hadin gwiwa tsakanin sojoji da 'yan sanda a wani atisaye da aka kira da Vanguard sai dai yunkurin bai yi nasara ba.

  11. An rufe kasuwanni hudu a Zamfara saboda 'yan fashin daji

    Getty Images

    Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe wasu kasuwanni hudu daga ranar 22 ga watan Afrilun da muke ciki sai sai baba ta gani.

    Cikin wata sanarwa da gwamantin ta fitar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara.

    Kasuwannan sun hada da Kasuwar Magami da ke karamar hukjumar Gusau, da ta Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru da Wanke ita ma a Gusau da Dauran da ke karamar Hukumar Zurmi.

    Sanarwar ta ce an bai wa jami'an tsaro umarnin su tabbatar da ana bin doka kamar yadda ya kamata.

    An kuma ba su umarnin su yi aiki babu sani babu sabo ga duk wanda suka kama ya karya doka a yankin da kasuwannin suke.

    "Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin shugabancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a ranar Laraba," in ji sanarwar.

  12. Labaran duniya cikin minti daya

    Video content

    Video caption: Minti Daya Da BBC Na Rana 23/04/2021
    • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa "Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba".

    Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da 'yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.

    • Ingancin wani sabon rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria da masu bincike suka samar a Burtaniya ya kai kashi 77 cikin 100 wajen dakatar da kamuwa da cutar.

    Sakamakon gwajin farko da aka yi wa rigakafin ya nuna yana da tasiri sosai fiye da allurar rigakafi daya tilo da ake da ita a yanzu.

    • Ministan harkokin tsaron Najeriya Bashir Magashi ya ce kasar ta kara tsaurara tsaro a kan iyakarta da Chadi biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban kasar Idriss Deby a farkon makonnan.

    Shugaban kamfanin kera motoci kirar Honda Toshihiro Mibe ya ce kamfanin zai mayar da hankali wajen kera motoci masu amfani da lantarki 100 bisa 100 nan da shekarar 2040

  13. Dan tsohon Shugaban Najeriya Murtala Muhammed ya ce ya hakura da siyasa

    AMG

    Babban dan gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Murtala Muhammed, Abba Risqua Murtala Mohammed ya bayyana aniyarsa a jiya a Kano kan cewa zai bar siyasa ya mayar da hankalinsa kan kasuwancinsa.

    Riqua a 2015 ya yi takarar a matsayin mataimakin gwamna a jam'iyyar PDP a Kano tare da Alhaji Sagir Salihu Takai.

    Da yake magana da magoya bayansa a Kano, Abba Risqua ya ce babu wanda ya matsa masa lamba ya dauki matakin, a radin kansa ya dauki wannan mataki domin gina rayuwarsa.

    A cewarsa "na bar siyasa ne domin na mayar da hankali kan harkokin kasuwanci na.

    Lokacin da na yi takara a Kano, na yi ta amfani da kuadden aljihu na ne, lokacin da na koma kan harkokin kasuwanci na sai na tarar ya yi matukar rauni, shi yasa nake son mayar da hankali yanzu kan kasuwanci in huta daga siyasa. Daga baya wani abu ya tabbatar mani da cewa gwara na koma kan kasuwanci."

  14. 'Yar gidan Sardauna ta mutu

    solacebase

    Yar Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta biyu Aishatu Ahmadu Bello ta mutu tana da shekara 75.

    Marigayiyar tsohuwar matar Marafan Sokoto ce Alhaji Ahmad Danbaba.

    Jaridar DailyNagerian ta ruwaito cewa Hassan Dan baba ne ya tabbatar da mutuwar mahaifiyar ta sa a ranar Juma'a, yana cewa ta mutu a wani asibiti ne a Dubai bayan fama da wata matsagaiciyar rashin lafiya.

    Hassan ya ce ana shirye-shiryen yadda za a dawo da ita Najeriya ne daga Dubai domin a binneta a Sokoto.

    Mahaifinta Sir Ahmadu Bello shi ne Premier arewa na farko kuma na karshe wanda ya rike mukamin daga shekarar 1954 zuwa 1966 lokacin da aka kashe shi a wani juyin mulkin soji.

  15. Kamfanin Honda zai koma kera motoci masu amfani da lantarki

    Fuelcellworks

    Shugaban kamfanin kera motoci kirar Honda Toshihiro Mibe ya ce kamfanin zai mayar da hankali wajen kera motoci masu amfani da lantarki 100 bisa 100 nan da shekarar 2040.

    Toshihiro ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a wata tattaunawar farko da manema labarai a karon farko tun da kamfanin ya koma matsayi na biyu na masu kera motoci a Japan a farkon watan Afrilu, yace wannan matakin zai taimaka wa gwamnati wajen cimma burinta na samar da tsaftataccen muhalli.

    "Na yi amannar cewa wannan wata rawa ce da kamfanonin kera motoci masu za su taka domin tabbatar da samun koren muhalli baki daya," in ji Toshihiro Mibe.

    Wannan sanarwa ta kamfanin na zuwa ne bayan da Firaiministan kasar Yoshihide Suga ya ce nan da 2030 Jafan za ta rage amfani da abubuwa masu gurbata muhalli domin tsaftace duniya.

  16. Buhari ya ce 'yan bindiga na son kure hakurin da yake yi da su

    Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa "Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba".

    Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da 'yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.

    Shugaban wanda ya yi gargadin cewa "Za a kawo karshen Irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da 'yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba", ya kara da cewa, "Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba",

    Shugaba Buhari ya tabbatarwa da al'ummar jihar Zamfara cewa "duk da gazawar da muka yi a kokarinmu na kare 'yan kasarmu, ba za mu taba bayar da kai bori ya hau ba wajen murkushe wadannan marassa tausayin."

    Buhari ya yi alkawarin kaddamar da wani shirin soji na musamman a Zamfara domin "dakile hare-haren 'yan bingidar" da kullum ke kamari.

    "Gwamnatinmu ba za ta yarda da kai kashe 'yan kauyen da ke talakawa ba suke fama da talauci da sauran matsalolin rayuwa," in ji Buhari a wata sanarwa da kakainsa ya fitar Garba Shehu.

  17. An samu rigakafin da zai hana kamuwa da Malaria

    SCIENCE PHOTO LIBRARY

    Ingancin wani sabon rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria da masu bincike suka samar a Burtaniya ya kai kashi 77 cikin 100 wajen dakatar da kamuwa da cutar.

    Sakamakon gwajin farko da aka yi wa rigakafin ya nuna yana da tasiri sosai fiye da allurar rigakafi daya tilo da ake da ita a yanzu.

    An gwada sabon rigakafin ne a kan jarirai dari hudu da hamsin a Burkina Faso.

    Yanzu dai za a yi gwaji mafi girma wanda ya shafi yara kanana kusan dubu biyar a duk fadin Afirka.

    Wakiliyar BBC tace cutar zazzabin cizon sauron na kashe sama da mutane dubu ɗari huɗu a kowacce shekara, yawancinsu yara ne a yankin kudu da hamadar sahara.

  18. Najeriya ta ƙara tsaurara tsaro a kan iyakarta da Chadi

    AFP

    Ministan harkokin tsaron Najeriya Bashir Magashi ya ce kasar ta kara tsaurara tsaro a kan iyakarta da Chadi biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban kasar Idriss Deby a farkon makonnan.

    Yace kasar da cewa Najeriya na fama da matsalar tsaro a kan iyakokinta dan haka dole ta zama ta mayar da hankali kan yiwuar tururuwar 'yan gudun hijira zuwa kasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Ministan ya ce 'yan Najeriya da ke zaune a Chadi kawai za a bari su shiga kasar.

    Iyakar Najeriya da CHadi ta bangaren arewa maso gabas na fuskantar karuwar hare-haren 'yan Boko Haram a baya-bayan nan.

    Ina yi wa Chadi kallon wata kasa mai mahimmanci a yakin da ake yi da matsalar tsaro a yankin Yammacin Afrika.

  19. Gobara ta kashe majinyatan korona 13 a Indiya

    Reuters

    Gobara ta kashe masu fama da cutar korona 13, a wani asibiti mai zaman kansa da ke jihar Maharashtra dake Indiya.

    Wutar ta yi kaca-kaca da sashin kula da marasa lafiya a hawa na biyu na asibitin mai suna Vijay Vallah.

    Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na yankin ya ce gobarar - wacce ta fara kafin wayewar gari, ta samo asali ne sakamakon fashewar abubuwa a wani sashin kula da na’urorin sanyaya daki.

    Indiya na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da annobar korona, kana jihar Maharashtra na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da cutar a kasar.

  20. Ana jana'izar Shugaba Idriss Deby na Chadi

    Reuters

    Za a gudanar da jana'izar Shugaba Idriss Deby Itno a yau Juma'a a N'Djamena babban birnin kasar kafin daga bisani a binne shi a ainihin garin da aka haife shi.

    An kashe shi ne a ranar Litinin lokacin da yake kan gaba wajen yakar 'yan tawaye, wata kungiya da wasu jami'an soji suka kafa a 2016.

    Shugabannin kasashen Mali da Guinea da kuma na Nijar sun isa kasar domin halartar jana'izar, ana sa ran shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai je N'Djamena duk da jan kunnen da 'yan tawaye suka yi kan cewa shugabannin kasashen waje kar su halarci jana'izar saboda dalilin tsaro.

    Bayan an kwashe awanni sojoji na bayani, limamin babban masallacin N'Djamena zai gabatar da addu'a ga marigayin.

    Da kuma yamma ne za a dauki gawar marigayin zuwa Amdjarass, wani karamin kauye kusa da mahaifarsa da ke kusa da iyakar kasar da ta Sudan.

    Shugaba Deby wani babban ƙusa ne a wajen tsare-tsaren da suka shafi matsalar tsaro a yakin Sahel.

    Dan gidan Idriss Deby Janar Mahamat Idriss Déby ne ya karbi jagorancin kasar karkashin kulawar majalisar sojoji ta kasar bayan mutuwar mahaifinsa, kuma a jiya Faransa ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin sojin.

    Janar Deby mai shekara 37 ya ce za a shirya zabe karkashin tsarin dimokradiyya a kasar nan da watanni 18, sai dai yan adawa sun yi Allah-wadai da wannan shugabanci na shi, yayin da wani janar din soja ya ce da yawan sojoji ba sa murna da shirin mika mulkin.