Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Imam Saleh da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. A nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. Wata mata ta nemi diyya kan kuskuren musayarta da aka yi wajen haihuwa

    Jariri
    Image caption: An haifi jaririan ne a asibiti ɗaya a arewacin Spain a 2002

    Wata mata ta nemi hukumomin lafiya a arewacin Spain su biya ta diyya bayan ta gano cewa an sauya ta da wata jaririya lokacin da aka haife ta shekaru 19 da suka gabata.

    Matar yanzu mai shekara 19 ta shigar da ƙara kotu.

    Hukumomin lafiya a Spain sun yarda cewa matar an yi kuskure ne aka yi musayartta a asibiti lokacin da aka haife ta a 2002.

    Lauyan matar wadda ba ta bayyana sunanta ba ya shaida wa wata tashar talabijin ta kasar Spain cewa tsakanin haihuwar jariran biyu sa'a biyar, kuma dukkansu an haife su a asibiti guda ne a garin Logroño, kudancin Bilbao.

    Ya kuma ce saboda an haife su da rashin cikakkiyar lafiya, sai aka ajiye su a ɗakin kulawa da jarirai na musamman, kuma daga bisani aka mika su ga iyayen da ba nasu ne ba.

    Bayanai sun ce kuskuren bai bayyana ba sai shekara hudu da suka gabata, bayan da ɗaya daga cikin iyayen ya buƙaci a yi gwajin kwayoyin halittar ƴar da ya zata tasu ce bayan da aurensa da matarsa ya mutu.

    A ranar Talata ministar lafiya ta gwamnatin La Rioja, Sara Alba, ta ce ba zai yiwu yanzu a ce ga wanda ya yi kuskuren ba.

    Ta ce "ba zai yiwu wani abu makamancin wannan ya sake faruwa ba" saboda hanyoyin tantance jarirai "amintattu ne kuma abin dogaro".

    Jaridar La Rioja wadda ta fara buga labarin ta ce matar na neman a biya ta dala miliyan uku da rabi, kuma rahotannin sun ce ma’aikatar lafiya ta amince ta biya €215,000.

    An sanar da ɗaya matar game da batun, amma ba ta nemi a biya ta diyya ba.

    Yanzu matar na jiran sakamakon binciken likita domin tabbatar da iyayenta na asali.

  3. Buhari ya ce Saudiyya alheri ce ga Najeriya

    Ministan harakokin wajen Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud lokacin da ya kawo wa Shugaban Najeriya ziyara a Abuja
    Image caption: Ministan harakokin wajen Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud lokacin da ya kawo wa Shugaban Najeriya ziyara a Abuja

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ƙasar Saudiyya ta kasance mai kyautatawa Najeriya.

    Shugaban ya faɗi haka ne lokacin da yake ganawa da ministan harakokin wajen Saudiyya a ranar Talata a Abuja, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a cikin wata sanarwa.

    Shugaba Buhari a cewar sanarwar ya shaida wa Yariman Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud cewa Najeriya mai dimbin jama'a kuma rauni ga abubuwan more rayuwa, kasar na dogaro ne da arzikin fetur domin samun kuɗaɗen shiga.

    "Kuma Saudiyya ta kyautata muna, ta hanyar sadaukarwar rage man da ke samarwa saboda mu a lokuta da dama," in ji shugaban.

    Shugaba Buhari ya kuma ce dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu mai ƙarfi ce."

    A nasa ɓangaren a cewar sanarwar, Yarima Al-Saud ya miƙa saƙon gaisuwar Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud ga Buhari, yana mai cewa "Saudiyya ta yaba da alaƙarta da Najeriya ta tsawon shekara 61 kuma tana fatan ƙarfafa ta."

  4. Wane ne babban kwamandan Taliban Hibatullah Akhundzada?

    Babban kwamandan Taliban Hibatullah Akhundzada
    Image caption: Babban kwamandan Taliban Hibatullah Akhundzada

    Babban kwamandan Taliban Hibatullah Akhundzada ya aiko da saƙon farko tun lokacin da ƙungiyar ta ƙwace ikon Afghanistan - inda ya faɗa wa sabuwar gwamnatinsu ta jaddada Shari'a.

    Akhundzada, wanda ke shugabantar kungiyar Taliban tun 2016, a ɓoye yake kuma har yanzu ba a gan shi a bainar jama'a ba tun lokacin da Afghanistan ta faɗa hannun kungiyar.

    Ana tunanin shekarunsa ba su wuce 60 ba kuma ya kasance a Afghanistan tsawon rayuwarsa.

    Duk da yana cikin mayaƙan da suka yaƙi sojojin tsohuwar Daular Soviet a Afghsnitan a shekarun 1980, amma an fi kallonsa a matsayin shugaban addini fiye da matsayin kwamandan soji.

    Akhundzada shi ne shugaban kotunan Shari'a a shekarun 1990, lokacin mulkin Taliban na farko - inda ake zartarwa mutane hukuncin kisa waɗanda suka yi zina da kuma yanke hannayen waɗanda suka yi sata.

    Za ku samu ƙarin bayani kan tsarin shugabancin Taliban a nan

  5. Babban kwamandan Taliban ya gaya wa gwamnati ta jaddada Shari'a

    Daliban Jami'a

    Babban kwamandan Taliban Hibatullah Akhundzada ya faɗawa gwamnati ta jaddada shari'ar musulunci a Afghanistan.

    A cikin wata sanarwa da harshen Ingilishi, ya buƙaci waɗanda ke riƙe da madafan iko da su tabbatar da kare babban muradin ƙasar da kuma tabbatar da "zaman lafiya mai ɗorewa" da kuma ci gaba.

    Wannan ne saƙon farko da ya fito daga babban kwamandan na Taliban tun lokacin da ƙungiyar ta ƙwaci mulki.

    Da yake magana kan ilimi, ya ce gwamnati "hakkinta ne ta samar da yanayi mai kyau ga ilimin addini da na kimiyar zamani ga duk ƴan ƙasa ƙarƙashin tsarin shari'a."

    Akwai dai fargaba kan makomar ilimin ƴaƴa mata da kuma tunanin mata za su sha wahala ƙarƙashin tsarin mulkin Taliban kan ƴancinsu.

    A zamanin mulkin Taliban na farko, mata ba su iya fita waje ba tare da muharrami ba kuma an haramta wa mata karatun boko.

    Wasu hotuna a ranar litinin sun nuna yadda aka sa shinge na labule wanda ya raba ɗaliban jami'a mata da maza.

  6. Sojojin Najeriya na shan yabo kan fatattakar ƴan bindiga a Zamfara

    Ƴan Najeriya na ci gaba da yaba wa sojojin Najeriya kan luguden wuta da suke yi wa ƴan bindiga da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya.

    Ƴan Najeriya na yaba wa sojojin ƙasar ne kan labarai da bayanai da ke nuna yadda sojojin ke kashewa da kama ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto.

    Wata sanarwa da gwamnatin Zamfara ta fitar a ƙarshen mako ta yi ikirarin cewa jiragen yaƙin rundunar sojin saman kasar sun yi luguden wuta kan fitattun sansanonin 'yan fashin daji a jihar da ma kewaye.

    Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa bidiyo a shafinta na Facebook da ke cewa babban hafsan sojin ƙasar Janar Faruk Yahaya ya kai ziyara a Zamfara.

    Ƴan ƙasar sun ta yaɗa hotunan sojojn a kafofin sadarwa na intanet, tare da yaba masu.

    Kuma duk da halin takura da matakin toshe layukan sadarwa ya jefa al'ummar Zamfara, ƴan Najeriya da dama sun bayyana cewa kwalliya na biyan kuɗin sabulu tare da nuna matuƙar goyon baya ga sabbin matakan da hukumomin ƙasar suka ɗauka don fatattakar 'yan fashin daji.

    Sanata Shehu Sani ɗan gwagwarmaya wanda ya yi suna wajen caccakar gwamnati, a shafinsa na Twitter ya ce:

    "Toshe layuka da aka yi a Zamfara na cikin jerin matakan da aka ɗauka na ƙoƙarin murƙushe ƴan ta'adda da suka haɗa da hana haƙo ma'adinai da haramta hawan babura da rufe makaranttu da kasuwanni. Don haka duk wani mataki na kawo ƙarshen ta'addanci abin maraba ne."

    Shehu Sani

    Haka ma tsohon minista sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode wanda ya yi ƙaurin suna wajen adawa da caccakar gwamnatin Buhari ya yaba wa sojojin Najeriya inda ya faɗi a Twitter cewa:

    "A Zamfara da sassan arewaci, dakarunmu na fatattakar ƴan fashin daji masu kisa. wannan kamar wani kiɗa ne a kunnuwana" ina alfahari da sake zama ɗan Najeriya."

    Femi

    Haka ma shafin @epiphanyfarmltd ya rubuta cewa "toshe layukan sadarwa a Zamfara mataki ne mai kyau, Babu wanda zai kwarmatawa ƴan ta'adda!

    Twitter

    @rifelex ya ce : "sojoji na kashe ƴan ta'adda a Zamfara. Muna jinjina masu.

    Twitter

    @Godsonolu shi ma ya ce: "Gwamnatin Najeriya na fatattakar ƴan fashi a Zamfara. Muna yaba wa shugaban ƙasa da gwamna.

    Twitter

    @AbdullahiJalin1 shi kuma ya bayar da labari ne cewa: "Sojojin Najeriya sun kama ƴan fashi sama da 50 da masu kwarmata masu bayanai tare da cinnawa sansanoninsu wuta tare da taimakon ƴan banga da suke aiki tare a jihar."

    Twitter
    Twitter
  7. An kama wani shugaban Islamic State a Libya

    Alan Johnston

    Middle East editor, BBC World Service

    Taswirar Libya

    Gwamnatin Libya ta ce dakarunta sun kama wani shugaban kungiyar Islamic State.

    An kama Embarak al-Khazimi a Bani Walid da ke kudu maso gabashin Tripoli.

    Firaiminista Abdul Hamid Dbeibah ya kamun nasa babbar nasara ce da za ta sa a samu bayanai kan kungiyar ta IS.

    Shekaru uku da suka gabata, an kori kungyar da sansaninta na karshe da ke Libya.

    Yanzu haka mambobinta na ci gaba da buya a wasu tsaunuka, kodayake har yanzu suna barazana ga kasar da ma lardin.

  8. An zargi 'yan majalisa da hannu a wasu kashe-kashe

    Taswirar

    Rudunar 'yan sandan Uganda ta zargi wasu 'yan majalisar dokokin kasar su biyu bisa hannu a jerin kashe-kashen da suka faru a lardin Masaka da ke tsakiyar kasar.

    An tuhumi Allan Ssewanyana da Muhammad Ssegirinya na jam'iyyar National Unity Platform (NUP) da laifukan kisan kai da kuma yunkurin kisa.

    Sai dai mataimakin shugaban jam'iyyarsu, Mathias Mpuuga, ya shaida wa BBC cewa ana tuhumar 'yan majalisar ne da zummar rage karfin jam'iyyar a yankunan karkara.

    Wasu 'yan daba ne dauke da adduna suka kashe mutum 26 a yankin a makonnin baya bayan nan, wasu ma an makure su suka mutu a gidajensu.

    Kakakin rundunar 'yan sandan Fred Enanga ya shaida wa manemab labarai ranar Litinin cewa 'yan majalisar biyu su ne suka kitsa kashe-kashen kuma sai da suka yi taro a kan hakan a kusa Kampala, babban birnin kasar.

  9. Ƴan Afghanistan sun fito sun yi gaba da gaba da mayaƙan Taliban

    Masu zanga zanga a Afghanistan

    Mayakan Taliban sun tarwatsa wata zanga-zanga a Kabul babban birnin kasar Afghanistan ta hanyar harba bindigoginsu a sama.

    Wasu bidiyo da aka wallafa a intanet sun nuna yadda mutane ke gudu domin tsira da rayukansu.

    Wannan ne bore mafi girma da 'yan kasar su ka yi wa 'yan Taliban, kuma daruruwan maza da mata sun rika yin Allah-wadai da abin da su ka kira katsalandan din da kasar Pakistan ke yi a harkokin cikin gida na Afghanistan.

    Sarah Fahim, wata mata da ta halarci zanga-zangar ta ce ''Mun gaji. Mun gaji da yadda Pakistan ke jefa bama-bamai a Panjshir. Mun gaji da zaman jiran da muke yi a filin jirgin sama domin kowa na da mutunci. Pakistan ta musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake ma ta na taimaka wa kungiyar Taliban''

  10. An ba da umarnin kama sama da mutane 200 saboda zargin juyin mulki a Turkiyya

    Erdogan

    Shekaru biyar bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya, masu gabatar da kara a yammacin Izmir sun bayar da umarnin tsare wasu sojoji dari biyu da goma sha hudu.

    Tuni aka kame fiye da rabin.su.

    Wasu daga cikinsu da dama na kan aiki a yanzu haka.

    Masu gabatar da karar sun ce an samu wasu bayanan bankunan mutanen da ke nuna suna da alaka da Fethullah Gulen, malamin da aka kora wanda gwamnati ke zargi da yunkurin juyin mulkin

    Kusan sojoji da ma'aikatan gwamnati dubu dari biyu aka wanke daga yunƙurin juyin mulkin.

  11. An sace mutane 18 a Kaduna

    'Yan bindiga

    Rahotanni daga jihar Kaduna ta tabbatar da sace wasu mutane 18 a karamar hukumar Chikun.

    An ce maharan sun kutsa garin ne da misalin karfe 12 na tsakar dare.

    Wasu shaidu sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun shiga garin ne ayari guda, tare da bude wuta, kafin daga bisani suka yi awon gaba da mutane 10.

    Yan sanda sun yi wa yankin tsinke a halin da ake ciki.

    Jihar Kadua dai na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a arewacin Najeriya.

  12. An ja kunne malaman Musulunci da na Kirista kan tunzura mabiyansu

    Majalisar tabbatar da haɗin kai tsakanin addinai a Najeriya ta ja kunnen malaman addinin Musulunci da na Kirista su daina kalaman tunzura mabiyansu yayin wa’azi.

    A jiya ne aka gudanar da wani babban taron ƙoli na zaman lafiya wanda majalisar ta shirya sakamakon tashe-tashen hankulan da ke faruwa a baya-bayan nan cikin jihar Filato.

    A baya-bayan nan ma tankiya ta ɓarke tsakanin ƙabilun Fulani da Iregwe musamman a yankin ƙaramar hukumar Bassa sakamakon kashe-kashen da ya ritsa da ɓangarorin biyu a ƙarshen makon jiya.

    To game da taron zaman lafiyar ne, Zahradden Lawan ya tuntuɓi kwamishinan yada labaran jihar, Mista Dan Manjang, ga kuma ƙarin bayanin da ya yi masa.

    Video content

    Video caption: Hirar Zahradden Lawan da kwamishinan yada labaran jihar Filato Mista Dan Manjang
  13. El-Rufa'i ya roƙi JAMB ta fasa rage wa ɗalibai maki

    '

    Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce rage makin da hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami'a ta Najeriya JAMB ke yi ya mayar da ɗaliban arewacin kasar ragwaye.

    Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

    Jridar The Cable ta rawaito gwamnan na cewa ko kadan rage makin ba ya taimaka wa yankin da ya jima yana fama da matsalar ilimi tun bayan samun 'yancin cin gashin kai.

    Ya shawarci hukumar ta fasa aiwatar da wannan shiri domin ba abun da zai haifar face sake jefa tsarin ilimin yankin cikin halin wani yanayi a cewarsa.

  14. Jagoran ƴan adawar Guinea ya goyi bayan hamɓarar da shugaba Conde

    Cellou Dalein Diallo

    Jagoran ƴan adawar Guinea ya goyi bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Alpha Conde, yana bayyana hakan a matsayin wata dama ta farfado da kasar.

    Cellou Dalein Diallo ya ce sojojin ƙasar sun ƙarasa gagarumin aikin da masu rajin tabbatar da Dimukradiyya a kasar suka faro.

    Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Ecowas sun yi Alla wadai da juyin mulkin, suna neman a dawo da amfani da kundin tsarin mulkin kasar.

    Sun kuma buƙac a gaggauta sakin shugaba Alpha Conde wanda aka yi wa gani na ƙarshe a ranar Lahadi, yayin da sojoji suka kewaye shi.

  15. Kim Jong Un ya fusata a kan matsalar sauyin yanayi

    Kim Jong Un

    Ran shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ya yi dubu ya ɓaci, kan yadda matsalar sauyin yanayi ke ci gaba da shafar ƙasar.

    Yana magana ne bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da fari, da suka janyo asarar kayan amfanin gona da dama, abun da ya jefa ƙasar cikin tsananin ƙarancin abinci.

    Kamfanin dillacin labaran Koriya ta Arewa KCA ya rawaito shugaban na umartar jami'an gwamnatinsa su fara aiki ka'in da na'in don magance matsalar a sassan ƙasar baki ɗaya.

    Ƙasar wadda ke tunƙaho da makamin Nukiliya na fama da ambaliya da fari a baya bayan nan, yayin da a gefe guda kuma take fadi tashin shawo kan matsalar karancin abincin da take fama da shi.

  16. Taliban ta sa labule tsakanin ɗalibai maza da mata a Jami'a

    Taliban
    Image caption: Akwai ƙarancin ɗalibai a azuzuwan

    Ƙungiyar Taliban ta gabatar da sabbin sauye-sauye a Jami'o'in ƙasar, yayin da ɗalibai suka fara janyewa.

    Ko da yake ɗalibai maza da mata za su ci gaba da zama a aji guda, sai dai an sanya labule a tsakaninsu, da zummar hana kowacce irin mu'amala a tsakani.

    Daga yanzu dole ne kowacce daliba mace ta sanya doguwar riga (Abaya, sannan ta rufe fuskarta da Nikabi.

    Dama an yi hasashen ganin irin waɗannan sauye-sauye, tun bayan da Taliban ta kwace iko.

    Taliban
    Image caption: Taliban ta ce ta yi hakan ne da zummar kare ɓarna
    Taliban
    Image caption: Wani malami yayin da yake bayar da darasi
  17. 'Za mu tsaya kai da fata don kare ƴancin mata na zubar da ciki'

    Joe Biden

    Ma'aikatar sharia a Amurka ta ce za ta ta kare yancin mata na zubar da ciki idan bukatar hakan ta taso.

    Hakan na zuwa bayan da jihar Texas ke shirin yin garambawul kan dokar hana zubar da ciki a jihar.

    A baya Shugaba Joe Biden ya soki kotun kolin Amurka kan kin taka wa Texas birki, a yunkurinta na fito da dokar hana mata yancin zubar da ciki matsawar ya wuce sati shida.

  18. 'Allah zai sake ba wa ƴan Najeriya shugaba irin Buhari'

    Dave Umahi

    Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya yi addu'ar Allah ya sake ba wa ƴan ƙasar shugaba mai kyakkyawar zuciya da kishin kasa kamar shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.

    Jaridar The Punch ta rawaito gwamnan na jinjina wa shugaban ƙasar kan wasu manyan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samar a yankin kudu maso gabashin Najeriya tun bayan hawansa mulki a 2015.

    Yana magana ne jim kadan bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda yace ya je ne domin mika masa godiya ta musamman saboda yadda yake daukar yankin da muhimmanci.

  19. Muna ci gaba da faɗaɗa nasararmu - Taliban

    Kakakin ƙungiyar Taliban
    Image caption: Kakakin ƙungiyar Taliban

    Ƙungiyar Taliban ta ce tana kara samun nasara a gundumar Panjshir, inda a nan ne kawai take fuskantar turjiya a Afghanistan.

    Wakiliyar BBC ta ce ba abun mamaki b ane Taliban ta kwace iko da Panjshir, to amma akwai lungunan da mayakan NRF za su iya fakewa don kai wa kungiyar harin kwanton bauna.

    Daya daga cikin jagororin kungiyar Mullah Hidayat Badar, ya yi kira ga fararen hula da kar su tsorata su zauna a gida babu abinda zai same su.

    Kungiyar mayakan turjiya ta National Resistance Front ta ce har yanzu yaki bai kare ba.

    Makonni uku kenan bayan da ta Taliban ta kwace Afghanistan, to amma har yanzu ba ta bayyana yadda za ta gudanar da gwamnati ba.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce har yanzu bai fara tunanin amincewa da sahihacin gwamnatin Taliban ba.

  20. Buɗewa

    Imam Saleh

    Multimedia Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu ta wannan shafi Assalamu alaikum da fatan kun wayi gari lafiya.

    Imam Saleh ne ke muku maraba zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya kai tsaye.

    Sai ku gyara zama don jin halin da duniyar ke ciki a yau !

    BBC Hausa