Gwamnatin Najeriya ta kasa hukunta jami'an SARS - Amnesty International
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita
Rufewa
To masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku kai tsaye.
Sai kuma ku tara gobe idan Allah Ya kai mu da misalin karfe 9 na safe inda za mu zo muku da sabbin bayanai kan abin da ke faruwa a duniya idan Allah Ya kai mu.
Kuna iya ziyartar shafinmu na BBC Hausa, don karanta wasu labaran.
A madadin Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita, ni Halima Umar Saleh nake cewa mu kwana lafiya.
Kamfanin jiragen sama na Kenya 'zai tafka asarar' dala miliyan 500 a 2020
Asalin hoton, Airteam Images
Kamfanin jiragen sama na Kenya Airways yana sa ran zai tafka asarar fiye da dala miliyan 500 a wannan shekarar sakamakon tabarbarewar kasuwanci da annobar cutar korona.
Kamfanin ya ce yana sa ran zai dauki matakai masu tsanani, da suka hada da rage yawan ma'aikata da sayar da manyan kadarori, baya ga wasu kudi fiye da dala miliyan 70 da gwamnati za ta ware don ceto tattalin arzikin kasa.
Kamfanin ya yi asarar dala miliyan 122 a shekarar 2019 wanda aka alakanta da tsadar abubuwan da suka danganci tsadar abubuwa.
An samu ƙaruwar masu shan ƙwaya a Kano saboda kullen corona
Bayanan bidiyo, Bidiyon hira da Dr Abdullahi Abdul na hukumar NDLEA ta Kano
Hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta ce an sami karin masu tu'ammali da miyagun kwayoyin tun bayan bullar cutar corona a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Kano Dr. Ibrahim Abdul ne ya shaida wa BBC hakan a wata hira ta musamman albarkacin ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya wato World Drug Day.
Dr. Ibrahim Abdul ya ce sun kama tan bakwai na kwaya cikin da tsakanin da jihar ta kasance karkashin dokar kullen cutar korona.
"Mu mun dauka da farko tun da an kulle gari to ba za a samu kamu mai yawa ba, abin mamaki har ofisoshin da suka kasance a rufe an mayar da su wajen shan ƙwaya, kamar ofisoshin gwamnati tun da sun ga ba mutane a wajen.''
An samu ƙarin irin ƙwayoyin da matsa ke hadawa da kansu tun da samu a kemis ya yi wahala don an rufe shaguna.
Ya ce cikin matakan da suke dauka sun hada da na wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fada a taken wannan shekara cewa a bi wato amfani da ilimi.
''Amfani da ilimin nan ya sa muka samu wani mutum da ya dauko kilo 233 na kwaya daga jihar Ondo a Kudancin Najeriya, wanda ya aike shi din kuma yana garin Azare a jihar Bauchi, sai muka yi amfani da ilimi muka dauko na Bauchin muka hada da na Ondon muka kai su kotu,'' in ji shi.
Dr Abdul ya ce ya yi nasarar cafke shi na Bauchin wanda dama ya gagari hukuma wajen kamawa, kuma babu wani dan kwaya da ya kai shi shahara a jihar Bauchin.
'Gwamnatin Najeriya ta kasa hukunta jami'an SARS'
Asalin hoton, PoliceNG_PCRRU/Twitter
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amensty International ta koka kan cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ta kasa ɗaukar mataki kan jami'an rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta ƙasar wato SARS.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, ƙungiyar ta ce duk da dokar da aka amince da ita a ƙasar ta hana azabtarwa a 2017, akwai hujjoji da ke nuna cewa har yanzu hukumar ta SARS na azabtar da waɗanda ake zargi da kuma kashe su ba bisa ƙa'ida ba duk da sunan neman bayanai daga wurinsu.
Ƙungiyar ta ce a kalla mutum 82 da biyu jami'an rundunar suka azabtar tare da kashewa tsakanin Janairun 2017 zuwa watan Mayu na 2020.
Kamfanin Kenya Airways zai yi asarar miliyan $500
Kamfanin jirgin sama na ƙasar Kenya wato Kenya Airways ya bayyana cewa zai yi asarar sama da dala miliyan 500 sakamakon annobar korona.
Kamfanin ya bayyana cewa tsaikon da annobar ta kawo wa kasuwancinsa zai sa ya ɗauki wasu matakai marasa daɗi.
Matakan sun haɗa da korar ma'aikata da kuma siyar da manyan ƙadarorin kamfanin.
Kamfanin jirgin a shekarar bara ya yi asarar dala miliyan 122 sakamakon maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wurin gudanar da harkokin jiragen
Hotunan tattaunawar Buhari da wasu gwamnonin APC
Asalin hoton, Sunday Aghaeze
Asalin hoton, Sunday Aghaeze
Asalin hoton, Sunday Aghaeze
Mutum 580 aka kashe a Mali a 2020 – MDD
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa farar hula 580 aka kashe tun farkon wannan shekarar a yankin tsakiyar Mali.
Shugabar hukumar Michelle Bachelet ce ta bayyana hakan inda ta ce lamarin tsaro a ƙasar na ƙara taɓarɓarewa kuma ƙungiyoyi daban-daban na kashe jama'a.
Hukumar ta bayyana cewa wata ƙungiyar sa kai da aka kafa musamman domin kare ƙabilun Fulani da Dogon sun koma suna kashe mutane tare da satar shanu da ƙona gidaje.
Ana kuma garkuwa da wasu farar hula tare da tursasa musu shiga ƙungiyar, in ji hukumar.
Hukumar ta kuma zargi rundunar soji ta Mali da kisa ba bisa ƙa'ida ba inda ta ce sojojin sun kashe mutum 130 ba bisa ƙa'ida ba kuma akasarinsu Fulani.
Farin Ɗango na neman addabar Gabashin Afrika
Asalin hoton, FAO/AFP
Akwai yiwuwar sake ɓullar farin ɗango a ƙasashen Gabashin Afrika, wanda hakan babbar barazana ce ga samar da abinci.
A farkon wannan shekarar, biliyoyin farin ɗango ne suka lalata gonaki - a halin yanzu, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa ɓullar farin karo na biyu zai zama babban bala'i.
Manoma a Kenya sun bayyana cewa suna dafa ganye su gauraya da hoda sa'annan su zuba inda farin suke. Sai dai sun ce duk da wannan ƙoƙarin nasu farin suna nan.
Ana tunanin cewa lamarin farin a halin yanzu kan iya zama wata babbar matsala da za ta baddabi yankin idan ba a tashi tsaye ba.
Korona ta sake kashe mutum 186 a Birtaniya
Mutum 186 sun sake mutuwa sakamkon cutar korona a Birtaniya.
Ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta bayyana cewa a halin yanzu waɗanda suka mutu sakamkon cutar a ƙasar sun kai 43,414.
A sakamakon da aka fitar a yau Juma'a, mutum 1,006 sun sake kamuwa da cutar bayan an yi gwaji ga mutum 165,665 a jiya.
Masu zaman makoki sun cika filin wasan don bankwana da Nkurunziza
Masu makoki sanye da fararen tufafi sun cika makil a babban filin wasa Gitage, babban birnin Burundi domin yin bankwana da Pierre Nkurunziza shugaban kasar da ya mutu mako biyu da suka wuce sanadin bugun zuciya.
An dauko gawarsa daga asibiti da ke birnin Karuzi, tare da rakiyar jami'an tsaro zuwa filin wasan inda dubban mutane suka tsaya a kan tituna domin ganin lookacin da za a wuce da gawar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya dauko hotunan da ke nuna cewa mutane ba su yi biyayya ga dokar yin nesa-nesa da juna ba.
Asalin hoton, AFP
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mai dakin marigayin, Denise Nkurunziza
Asalin hoton, AFP
Yadda annobar korona ta shafi Nollywood,
Asalin hoton, AFP
Masu harkar fina-finan Nollywood suna fatan komawa bakin aiki nan da wata biyu, da zarar gwamnat ta ba s izinin yin hakan.
Masana sun yi kiyasin cewa masana'antar Nollywood ta yi asarar $30m sakamakon anobar korona.
Har yanzu gwamnati tana yin nazari kan matakan kare kai ga masu harkar fina-finai kafin su koma bakin aiki, kuma masu shirya fim sun ce za a rika kashe karin makudan kudi ajen tabatar da lafiyar 'yan fim da masu taya su aiki.
La Femme Anjola yana cikin fina-finan Nollywood da ake sa ran fitowarsu a 2020. Labari ne na wani mai sayar da hannun jari wanda ya fada kogin soyayya da wata budurwa - kuma fitacciyar 'yan wasan kwaikwayon nan Rita Dominic iat ce ta taka wannan rawa.
Tun da fari an so fitar da fim din a watan Afrilu ama an jinkirta fitar da shi saboda annobar korona da sauran matsaloli.
Mildred Okwo, wadda ta shirya fim din, ta ce an shirya fitar da shi ama gidajen sinima da ke fadn kasar a kulle suke don haka babu yadda za su yi.
"Ban san lokacin da za mu fitar da fim din ba yanzu kuma mun kashe kudi sosai a kansa. Komai ya tsaya cak," a cewarta.
A shekarun baya bayan nan, ana fitar da fina-finai a shafukan intanet irin su IrokoTV da Netflix.
'Yan sandan Kenya sun kashe mutane a kan takunkumin rufe fuska
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan Kenya sun kashe mutum uku lokacin da wasu masu tuƙin tasi suka yi zanga-zanga kan kama abokin aikinsu saboda bai sanya takunkumin kare fuska ba.
'Yan sanda sun yi harbi a tsakiyar masu zanga-zangar a birnin Lessos da ke yammacin kasar bayan sun yi taho-mu-gama, a cewar wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar.
Rundunar ta umarci a kama 'yan sandan da suka kashe mutane.
Gwamnatin jhar Lagos da ke kudancin Najeriya ta ce cutar korona ce ta yi ajalin tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.
A sakon da Kwamishinan Lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi ya wallafa ranar Alhamis, ya ce tsohon gwamnan ya rasu ne a wani asibiti da aka ware domin kula da masu dauke da COVID-19.
"Tsohon gwamnan ya rasu sakamakon aikin da gabobin jikinsa suka daina yi sanadin kamuwa da COVID-19," in ji Farfesa Abayomi.
Sanata Abiola Ajimobi shi ne tsohon gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 2011 - 2019.
Kafin ya zama gwamnan jihar Oyo ya rike mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai a 2003.
Amma Sanata Ajimobi ya fadi zaben kujerar majalisar dattawa ta Kudancin Oyo inda abokin karawarsa na jam'iyyar PDP Kola Balogun ya kayar da shi a 2019.
Ya mutu ya bar mace daya Florence Ajimobi da kuma yara biyar. Daya daga cikin 'ya'yansa Idris Ajimobi ya auri 'yar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Fatima.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An kama wani ɗan damfarar Najeriya a Dubai
Asalin hoton, DUBAI MEDIA OFFICE/TWITTER
Rundunar 'yan sandan Dubai ta ce ta kama wani fitaccen mai amfani da shafin Instagram a Najeriya Raymond Igbalodely, wanda aka fi sani da Hushpuppi, bisa zargin damfarar mutane $435m.
A wani samame da ta kai wanda ta yi wa suna "Fox Hunt 2", ta kama mutum 12 a farmakin da ta kai wurare shida a Dubai.
Rahotanni sun ce mutumin ya damfari kusan mutum miliyan biyu a yankuna daban-daban na duniya.
Mutumin mazaunin Dubai ne kuma ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne.
Rundunar 'yan sandan ta wallafa bidiyo a shafinta na Twitter kan yadda ta kama shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Arsenal ta taya Willian, Arthur na dab da barin Barca
Dan wasan tsakiya naBarcelonada Brazil Arthur, mai shekara 23, yana dab da amincewa da yarjejeniyar fam miliyan £72.5 zuwaJuventus,yayin da kuma dan wasan tsakiya na Bosnia Miralem Pjanic, 30, ke shirin amincewa da yarjejeniyar fam miliyan £54.25 zuwa Barcelona.(Sky Sports)
Dan wasan gaba da Sifaniya Pedro, mai shekara 32, zai komaRomakan yarjejeniyar shekara biyu idan kwangilar shi daChelseata kawo karshe bayan kammala kakar bana.(Sky Sports)
Bayern Munichta janye waManchester Unitedkan matashin dan wasanBirminghammai shekara 16 Jude Bellingham, wanda kuma ya ja hankalinBorussia Dortmund.(Bild, via Sun)
Arsenala shirye ta ke ta biya dan wasanChelseada Brazil Willian, mai shekara 31, fam 250,000 duk mako kafin karshen annobar korona.(Mirror)
An sace ma'aikata goma da ke raba kayan abinci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar.
Kungiyar da suke yi wa aiki, Action and Impact Programme, ta ce 'yan bindiga a kan babura sun kai hari a kauyen da suka je rabon kayan agaji sannan suka bukaci ma'aikatan su bi su. Sun kuma sace motoci biyu na ma'aikatan.
Masu ikirarin jihadi sun kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin wanda ke kusa da iyakokin kasar da Mali da Burkina Faso.
'Yan bindiga sun sace ma'aikatan agaji da dama da kuma ababen hawansu wadanda suke amfani da su wajen kai hare-hare.
Masu ikirarin jihadi sun kashe mutum fiye da 4,000 a cikin shekara daya da ta wuce.
Yadda na daina shan ƙwaya har na kafa ƙungiyar yaki da ita
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar Yaki da shan Kwaya da kuma safararta.
Taken ranar na bana shi ne ''Ilimi mai inganci don samun kula mai kyau,'' wato "Better Knowledge for Better Care."
An kirkiri taken na bana ne don inganta fahimtar yadda matsalar kwaya take a duniya da kuma neman hadin kai kan yadda za a yi yaki da hakan don magance illolinta ga lafiya da kuma tsaro.
A kan haka ne BBC Hausa ta tattauna da wani matashi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya wanda ya tuba daga shan kwayar ya kuma zama mai yaki da ita.
Bayanan bidiyo, Yadda na daina shan kwaya har na kafa kungiyar yaki da ita
Yadda aka kai hari kan ofishin jakadancin Najeriya da ke Indonesia
Gwamnatin Najeriya ta yi tir da harin da 'yan kasar suka kai a ofishin jakadancinta da ke Jakarta, babban birnin Indonesia.
'Yan kasar ta Najeriya sun hari ofishin jakadancin inda suka lalata motocin da ke harabar ofishin.
Sun zargi jami'an ofishin da kin taimaka musu game da zargin musgunawar da jami'an shige-da-ficen Indonesia suke yi musu.
Sun yi zargin cewa wani dan Najeriya ya fado daga kan bene a yayin da yake yunkurin tserewa daga hannun jami'an shige-da-ficen kasar ta Indonesia.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce za a gano wadanda suka lalata ofishin jakadancin kuma a hukunta su.
"Wannan lamari abin kyama ne wanda laifi ne da 'yan dabar Najeriya suka yi," in ji shi.
An rika watsa bidiyon 'yan Najeriyan lokacin da suka isa ofishin jakadancin a shafukan sada zumunta:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Za a binne tsohon shugaban Burundi Nkurunziza
Asalin hoton, Getty Images
Za a yi bikin binne tsohon shugaban Burundi Pierre Nkurunziza - wanda ya mulki kasar tsawon kusan shekara 15 - ranar Juma'a a Gitega, babban birnin kasar.
Gwamnatin kasar ta ce ya rasu bayan ya yi fama da "bugun zuciya" kusan mako biyu da suka gabata.
Gwamnatin kasar ta bukaci masu halartar bikin binne shi su yi layi a kan tituna sannan su yi masa girmamawar bankwana a yayin da za a dauki gawarsa daga asibitin Karusi inda ya mutu, zuwa flin wasa na Gitega, dn nuna girmamawa a gare shi.
Mista Nkurunziza ya jagoranci Burundi tun daga 2005 kuma yana shirin mika mulki ga zababben shugaban kasar, Evariste NDayishimiye a ranar 20 ga watan Agusta.
A shekarar 2015, sanarwar da ya bayar cewa zai tsaya takara a karo na uku ta jefa kasar cikin tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Asalin hoton, AFP
Bayan sauya kundin tsarin mulki, ya samu damar yin takara a karo na huɗu a zaɓen da aka gudanar na watan da ya gabata amma sai ya zaɓi ya yi ritaya a matsayin "wani aikin kishin ƙasa".
Yana gab da karɓar dala dubu 540 a matsayin kuɗin sallama daga aiki da kuma wata fada ta ƙasaita.
Mista Nkurunziza ya hau mulki a shekarar 2005 bayan yaƙin basasa da ya yi ajalin mutum 300,000 a ƙasar.
Barkanmu da Juma'a,
Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da Juma'a.
Muna fatan za ku
kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku
labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke
faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.