Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Najeriya @60: Buhari ya yi amai ya lashe

    ..

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai yi jawabi ga 'yan Najeriya ta talabijin a maimakon Dandalin Eagle wanda aka yi niyyar yi a baya.

    A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana cewa shugaban zai yi jawabin ne da misalin 7:00 na safe a ranar 1 ga watan Oktoba.

    A sabuwar sanarwar, ya ce 'yan Najeriya su yi watsi da sanarwar baya da ta ce shugaban zai yi jawabin a gaban jama'a a Dandalin Eagle.

    Ya kuma ce daga nan shugaban zai wuce Dandalin Eagle wurin taron cika ƙasar shekara 60 da samun 'yancin kai.

  3. An yi wa Sarkin Kuwait jana'iza daga Masallacin Makkah

    A yau ne dai aka gudanar da jana'izar marigayi Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah a ranar Laraba Kuwait.

    Sai dai daga Makkah, an gudanar da Salatul Gaib (sallar da mutum baya nan) ga sarkin.

    Salatul gyab
    Salatul gyab
    Salatul gyab
    Salatul gyab
  4. Ku saurari labaran duniya cikin minti daya da BBC Hausa

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 30/09/2020
  5. MDD na neman ƙasashen duniya su tallafa wa shirin samar da riga-kafin korona

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga ƙasashe da su fara amfani da kuɗaɗensu na yaƙi da annobar korona domin tallafa wa shirin ƙirƙiro riga-kafin cutar.

    Ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar kuɗaɗe a halin yanzu domin kada a rasa damar da ake da ita ta ƙirƙiro riga-kafin.

    Ya ce haɗin kan ƙasashe wurin nemo riga-kafin cutar duk zai taimaki duniya baki ɗaya.

    Kiran da Mista Guterres ya yi na zuwa ne bayan da shugaban ƙungiyar samar da riga-kafi ta duniya, Seth Berkley, ya yi kira ga ƙasashe su bayar da taimako.

    Mista Seth ya ce ana buƙatar dala biliyan biyu zuwa watan Disamba domin samar da riga-kafin cutar ga ƙasashe 92 masu tasowa.

  6. Eden Hazard: Dan kwallon Belgium na fama da jinya a Spaniya

    ..

    Ranar Litinin kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana sunayen 'yan kwallon Real Madrid da za su buga karawa da Valladolid har da Eden Hazard a cikinsu.

    Sai kawai aka sanar da cewar dan kwallon tawagar Belgium ya ji raunin da ba zai buga wasan da Madrid za ta yi ranar Laraba ba.

    Kuma sabon ciwo na daban dan kwallon ya ji da zai yi jinyar mako uku zuwa hudu kafin ya dawo taka leda.

    Ga cikakken labarin a nan:

  7. Lauyoyi na zanga-zanga a Aljeriya

    zanga-zanga a Aljeriya

    Lauyoyi a Aljeriya na gudanar da wata zanga-zanga a fadin kasar ta abin da suka kira karin matsin lambar siyasa ga bangaren shari’ar kasar.

    Ana yin wannan zanga-zangar ta kwana biyu domin nuna goyon baya ga lauyoyin da ke Algeris babban birnin kasar, wadanda suka gama ta su a ranar Lahadi.

    Lauyoyin sun ce ana ta yin kame babu gaira babu dalili, kan kokarin hukumomin kasar na samar da sabon kundin tsarin mulki.

    Zanga-zangar neman kawo sauyi ga shugabancin kasar da aka fara a watan Fabirairun bara, ta matukar girgiza hukumomin kasar.

  8. An yi jana'izar Sarkin Kuwait

    Jana'izar Saekin Kuwait

    An yi jana'izar marigayi Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah a ranar Laraba.

    Gawar sarkin ta isa Kuwait ne a ranar Laraba da rana daga Amurka, kuma sabon sarkin Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah da wasu manyan jami'an gwamnati ne suka tarbi gawar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.

    An rufe tituna da yawa na birnin da rana don bai wa motocin da suka ɗauko gawar sarkin daga filin jirgi hanyar wucewa zuwa babban Masallacin Kuwait, inda danginsa da manyan jami'an gwamnati suka yi sallar jana'izarsa.

    Daga can ne sai aka kai shi maƙabarta.

    Sheikh Sabah ya mutu ne a ranar Talata a Amurka, inda ake duba lafiyarsa tun a watan Yuli bayan wata tiyata da aka yi masa a Kuwait.

    Masallatai a ƙasar sun yi addu'o'i na musamman da magariba ga marigayin.

    Za a bar mutane su kai ziyara kabarin sarkin a ranar Alhamis.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Kuwait da al'ummarta kan rasuwar sarkin nasu.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Shugaba Buhari ya kuma taya sabon sarkin da aka naɗa murna.

  9. Majalisar wakilan Najeriya ta janye ƙudurin doka kan albarkatun ruwa na shekarar 2020

    Majalisar wakilan Najeriya ta janye kudin doka kan mallakar albarkatun ruwa na shekara ta 2020 duk da kasancewar an amince da shi watanni biyun da suka wuce.

    Hakan dai ya biyo bayan adawa mai karfi da wasu 'yan majalisar suka nuna ga kudurin bayan dawowar majalisar daga hutu a jiya, bisa zargin cewa an karya wasu ka'idoji majalisar wajen gabatar da shi.

    Ko da yake masu goyon bayan kudurin sun tsaya kai da fata cewa yana kan ka'ida, kakakin majalisar ya yanke hukuncin cewa a janye kudurin a sake gabatar shi.

    Ku latsa lasifikar da ke asa don sauraron rahoton Haruna Shehu Tangaza:

    Video content

    Video caption: Rahoton Haruna Tangaza kan dokar kudurin ruwa
  10. Real Madrid da Valladoli: Ko Real Madrid za ta hada maki uku kuwa?

    ...

    Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan mako na hudu a gasar La Liga da za su fafata ranar Laraba a Alfredo Di Stefano.

    A kakar bara Real ta hada maki hudu a kan Valladolid, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 ranar 24 ga watan Agustan 2019 a karawar farko.

    A wasa na biyu a La Liga da suka fafata a gidan Valladolid, Real ce ta yi nasara da ci 1-0 ranar 26 ga Janairun 2020.

    Ga cikakken labarin a nan:

  11. An yi wa ayarin motocin Firaiminstan Guinea ruwan duwatsu

    ..

    'Yan adawa masu zanga-zanga a Guinea, sun yi wa ayarin motocin firaiministan ƙasar ruwan duwatsu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    Kamar yadda sanarwar ta ruwaito, Firaiminista Ibrahima Kassory Fofana, na tafiya ne ta yankin Fouta-Djalon da ke arewacin Guinea a yayin da aka kai hari ga sansanin motocinsa, inda aka raunata mutane da dama.

    Shugaban ƙasar mai shekara 82, Alpha Conde, na takarar shugabancin ƙasar karo na uku a zaɓen ƙasar da za a yi 18 ga watan Oktoba bayan ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar da zai ba shi damar zarcewa.

    Wannan ne ya sa 'yan adawa suka fara zanga-zanga tun a shekarar da ta gabata inda aka kashe gwamman mutane.

  12. China za ta kama masu ƙoƙarin tsallake 'bangon duniya'

    ..

    A yayin da lokacin hutu ke ƙaratowa a China, ƙasar ta ce za ta kama masu ƙoƙarin tsallake "Great wall" wanda aka fi sani da bangon duniya a Hausance.

    Wannan wuri ana yawan misalta shi da wani babban wuri wanda aka killace shi daga mutane da kuma masu zuwa yawon buɗe ido.

    Ƙasar ta bayyana cewa za a saka tara mai tsanani ga waɗanda suka karya dokar, inda ake zaton dubban masu zuwa yawon buɗe ido za su je wurin.

    Ƙasar ta ce ga waɗanda suka karya dokar, za a caje su kudi kimanin Yuan 200,00 zuwa 300,000, kimanin Fam 3,430 zuwa 4,404.

  13. An halaka makiyaya biyu a jihar Ebonyi

    Yan sanda

    Ƴan sanda a Ebonyi sun tabbatar da kisan makiyaya biyu a sansaninsu da ke dajin Ukwuachi a yankin Ishieke da ke ƙaramar hukumar Ebonyi.

    Kwamishinan yan sandan jihar, Philip Maku cikin wata sanarwa ya ce makiyayan yan uwan juna ne - Adamu Ibrahim da Jubril Adamu.

    Sanarwar ɗauke da sa hannun kakakin rundunar, Loveth Odah ta rawaito kwamishinan na cewa akwai wasu mutum biyu da aka jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti.

    Jaridar Premium Times ta bayyana cewa kwamishinan yan sandan ya yi tur da harin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar makiyayan - ɗaya ɗan shekara 7 yayin da ɗayan kuma yake da shekara 15.

    Waɗanda kuma suka jikkata suna kwance a asibitin koyarwa da ke Abakaliki.

    Kwamishinan kuma ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin inda ya sha alwashin tabbatar da gaskiya.

  14. Kotu ta yi watsi da ƙarar da ke neman sake maido da iyakar shekarun zabe a Uganda

    Uganda

    Wata kotu a Uganda ta yi fatali da wata kara da ke kalubalantar kudirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul da ya cire iyakar da aka sa kan shekarun wanda yake son yin takarar shugaban ƙasa.

    Wannan na nufin Shugaba Yoweri Museveni zai iya sake neman takara.

    Lauya Male Mabirizi ne ya garzaya kotun da ke zamanta a Tanzania domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da gyaran da aka yi.

    Gyaran da aka yi a shekarar 2017 ya share ka'idar dake cewa sai wanda yake tsakanin shekara 35 da 75 ne zai iya tsayawa takarar shugaban kasa.

  15. Nigeria@60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari sakon taya murna

    Sarauniya

    Sarauniyar Ingila ta aike saƙon taya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari murna yayin da ƙasar ke cika shekara 60 da samun ƴancin kai.

    Mai taimaka wa shugaba Buhari kan kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

    Sarauniyar ta kuma yi wa Najeriya fatan alheri cike da farin ciki da kuma ci gaba.

    View more on twitter
  16. An hana tsohon shugaban Sierra Leone Ernest Bai Koroma fita daga kasar

    Ernest Bai

    Hukumomi a Sierra Leone sun haramta wa tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma da wasu jami'ai da suka yi aiki a gwamnatinsa barin kasar saboda zargin cin hanci.

    Ba za a bar Mr Koroma da fiye da mutum 100 su fita daga kasar ba kuma an umarce su da su mayar da kudaden da aka sace, su bayar da gidajensu, idan ba haka ba za a sake gudanar da bincike a kansu.

    Jam'iyyar hamayya ta Mr Koroma mai suna All People's Congress (APC) ta yi watsi da zarge-zargen.

    Wani lauyan jam'iyyar ya ce za su garzaya kotu domin kalubalantar batun.

  17. Buhari ya rantsar da sabbin manyan sakatarori hudu

    Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Muhammadu Buhari ya rantsar da wasu sabbin manyan sakatarori guda hudu.

    An rantsar da su ne yau kafin fara gudanar da taron majalisar ministoci ta intanet a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

    Sabbin manyan sakatarorin hudu da suka hada da maza uku da mace daya sun zama cikon mutane 16 da aka nada cikin watan Yunin bana wanda daga ciki aka rantsar da mutum 12 sama da wata guda da ya gabata.

    Sabbin manyan sakatarorin su ne Mr James Sule daga Kaduna da Isma'ila Abubakar daga Kebbi sai Mrs Ibiene Patricia Roberts daga Rivers da Mr Shehu Aliyu Shinkafi daga Zamfara.

    Najeriya
    Image caption: Sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha da Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo

    Bayan rantsar da mutanen, wadanda suka halarci taron majalisar ministocin ta intanet sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da Shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

    JaridarVanguardta rawaito cewa ministoci hudu sun halarci taron daga fadar shugaban kasa - ministan shari'a bubakar Malami da ministar kudi da kasafi da tsare-tsare, Dr Zainab Ahmed da ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed da karamin ministan kasafi da tsare-tsare Mr Clement Agba.

  18. Labarai cikin miniti daya

    Video content

    Video caption: Minti Daya Da BBC Na Rana 30 09 2020
  19. Gwamnatin Najeriya ta samar da kayan gwajin cutar korona

    Korona

    Gwamnatin Najeriya ta kirkiro wani sabon kayan gwajin cutar korona wanda zai kara bunkasa gwajin cutar a ƙasar.

    Sai dai har yanzu ba a amince da sabon kayan gwajin cutar ba amma hukumomi sun ce suna fatan za su fara aiki da su nan ba da jimawa ba.

    Kamar sauran ƙasashen Afirka Najeriya tana shigo da mahimman kayan gwajin da ake buƙata amma idan har aka fara amfani da sabon kayan gwajin, hakan zai sa a fadada gwajin cutar.

    Hukumomi sun ce sabon kayan gwajin da aka yi wa lakabi da SARS-COV-2 Isothermal Molecular Assay wanda cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Najeriya ta kirkira zai iya ba da sakamako cikin kasa da minti 40.

    Karamin ministan lafiya na kasar Dr Olurunimbe Mamora ya ce sabon kayan gwajin ya fi sauri sannan bai kai tsarin gwaji na PCR tsada ba wanda kasar take amfani da shi a halin yanzu.

    Shugaban kwamitin shugaban kasa da ke yaki da korona a Najeriya, Boss Mustapha ya fada wa yan jarida cewa wannan abin daɗaɗa rai ne kuma alamu ne cewa Najeriya tana ba da gudummawarta ga yaki da korona da kasashe ke yi.

    Hukumomin lafiya sun ce da zarar an tabbatar da ingancin kayan, za a tura su zuwa yankuna domin bunkasa gwajin cutar a kasar.

    Najeriya dai ta na da fiye da mutum dubu 58 da suka kamu da korona kuma sama da mutum dubu daya sun mutu. Sai dai ana samun raguwar mutanen da suke kamuwa kowace rana.

  20. An rantsar da sabon Sarkin Kuwait

    Kuwait
    Image caption: Sabon Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmed

    Sabon Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah ya karbi rantsuwar kama aiki.

    Hakan ya zo ne kwana daya bayan sanar da rasuwar Sheikh Sabah.

    Sheikh Nawaf - wanda shi ne yarima mai jiran gado a baya - ya sha alwashin yin aiki domin samar da daidaito da tabbatar da tsaro a Kuwait.

    Ba a tsammanin Sheikh Nawaf mai shekara 83 zai kawar da kasar daga manufofin cikin gida da na ƙasashen duniya da magabacinsa ya samar - wanda dan uwansa ne.