Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Mu haɗu da ku idan Allah Ya kai mu domin ɗorawa daga inda aka tsaya.

    Umar Mikail ke muku sallamar fatan alheri a wannan dare na Lahadi.

  2. Labarai da dumi-dumiGobara ta tashi a birnin Legas

    Gobara ta tashi a yankin IddoTerminus da ke Jihar Legas a kudancin Najeriya.

    Ya zuwa yanzu babu bayani kan abin da ya haddasa gobarar.

    Za mu kawo ƙarin bayani idan mun samu.

    View more on twitter
  3. Gwamnonin Oyo da Ondo sun ziyarci wurin rikicin Hausawa da Yarabawa

    Kasuwar Shasha

    Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da takwaransa na Ondo, Rotimi Akeredolu, sun kai ziyara kasuwar Shasha, inda aka yi rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa.

    Akeredolu wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu masu yammacin Najeriya, ya yi kira ga shugabannin Yarabawa na yankin da su gargaɗi yaransu game da ɗaukar doka a hannunsu.

    Yayin ziyarar, wasu matasa sun hana gwamnonin kaiwa ga fadar Sarkin Hausawan Sasa Haruna Mai Yasin domin yi ma sa jaje.

    Matasan cikin sowa da ihu, sun nuna dole sai gwamnonin sun kai ziyara ga fadar sarkin Yarabawa wato Bale kafin a je fadar Sarkin Sasa.

    "Duk girman rashin adalcin da aka aikata wa wata al'umma, ya kamata su kwantar da hankalinsu su bari a tattauna domin doka ta yi aikinta," in ji gwamnan.

    Rikicin na Kasuwar Shasha da ke yankin Ojoo a birnin Ibadan, ya jawo asarar rayukan Hausawa aƙalla 10 tare da ƙona shagunansu da dama.

    Lamarin ya faru ne bayan mutuwar wani Bayarabe a kasuwar Shasha sakamakon hatsaniyar da ta ɓarke tsakanin wani Bahaushe mai turin baro da wata Bayarabiya mai shago a kasuwar ranar Alhamis.

    Dubban 'yan Najerya na kiraye-kirayen "a daina kashe 'yan Arewa" a shafukan zumunta ta hanyar amfani da maudu'in #stopkilingnortherners a Twitter.

    View more on twitter
  4. WHO na shirin tallafa wa Guinea bayan sake ɓullar cutar Ebola

    Hukumar Lafiyar ta Duniya (WHO) na shirin samar da wani taimakon gaggawa ga kasar Guinea, bayan sake bullar cutar Ebola.

    Rahotanni sun ce an samu mutum takwas ɗauke da cutar kuma tuni uku suka mutu.

    Mutanen sun kamu da ita ne yayin halartar wata jana'iza a garin Gouecke, a cewar rahotanni.

    Ɓullar Ebola a Guinea ta sa shugaban Liberia mai makwabtaka, George Weah, ya umurci hukumomi da su ɗauki tsauraran matakin hana shigar cutar kasarsa.

    Sama da mutum dubu11 ne suka mutu bayan kamuwa da Ebola a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016.

    A baya-bayanan Ebola ta bulla a gabashin Demokradiyyar Kongo, inda ta kama akalla mutun hudu.

  5. APC ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Sokoto

    Jam'iyyar APC

    Yayin da ya rage makwanni a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, jam'iyyar APC mai adawa a jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen ba.

    Da yake zantawa da 'yan jarida a hedikwatar jam'iyyar yau Lahadi a birnin Sokoto, shugaban riƙo na jam'iyyar, Isa Sadiq Achida, ya ce jam'iyyar ba za ta shiga "zaɓen da ba za a yi adalci ba".

    A cewarsa, hukumar zaɓen jihar gwamnati take goyon baya, yana mai zarginta da cewa "sun shirya tsaf domin yin abin da gwamna ke buƙata".

    Ya ƙara da cewa "idan har aka gudanar da zaɓen cikin adalci" jam'iyyarsu ce za ta yi nasara.

    Ranar 27 ga watan Maris mai zuwa za a gudanar da zaɓen.

  6. 'Yan Najeriya na kira da 'a daina kashe 'yan Arewa' a shafukan zumunta

    Hoton rikin kasuwar Sasa

    Dubban 'yan Najerya na kiraye-kirayen "a daina kashe 'yan Arewa" a shafukan zumunta biyo bayan rikicin ƙabilanci tsakanin Yarabawa da Hausawa a Jihar Oyo.

    Tun da safiyar yau Lahadi ne masu amfani da dandalin Twitter suka riƙa amfani da maudu'in #stopkilingnortherners wato a daina kashe 'yan Arewa.

    Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an ambaci maudu'in sau fiye da 6,322.

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi tur da "hare-hare a kan 'yan Arewa da ke kasuwancinsu a kasuwar Sasa wanda ya jawo kashe-kashe" sannan ta yi kira da a yi bincike kan lamarin don yin adalci.

    Wani shugaban Hausawan kasuwar Shasha, Alhaji Usman Idris Yako, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu ya tabbatar da mutuwar Hausawa 10.

    "Kisan 'yan Arewa da ba su ji ba ba su gani ba abin takaici ne," a cewar mawaƙi Umar M. Shareef maƙale da maudu'in #stopkilingnortherners.

    View more on twitter

    Shi kuwa Suraj tambaya yake cewa "me ya faru da maganar ƙasa ɗaya dunƙulalliya cikin 'yanci da kwanciyar hankali?".

    View more on twitter

    Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kuma shahararren ɗan jam'iyyar adawa ta PDP, Reno Omokri, ya yi kiran da "kar a yi ramuwar gayya" yana cewa "na sha nuna kaina a matsayin ɗan Arewa, dangina sun zauna a Sokoto tsawon shekara 31 amma ba a taɓa nuna mana ƙabilanci ba".

    View more on twitter
    View more on twitter
  7. Yadda Turawa suka shigo ƙasar Hausa

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi da suka haɗa da yadda Turawa suka shigo ƙasar Hausa da kuma illar da takunkumi ke haifarwa idan ya daɗe a fuskar mutum.

    Mustapha Musa Kaita ne ya gabatar da shi. A yi sauraro lafiya.

  8. Kai-tsaye daga Facebook

    Ku garzaya shafinmu na Facebook domin kallon sharhin wasannin ƙwallon ƙafa kai-tsaye.

    Jabir Mustapha Sambo ne tare da baƙonsa ke yin fashin baƙin game da yadda ƙungiyoyi ke ɓarje gumi a kakar bana.

    View more on facebook
  9. An tsawaita wa'adin haramta shiga Dubai daga Najeriya

    Jirgin Emirates

    Hukumomin Ɗaular Larabawa (UAE) sun tsawaita wa'adin dakatar da saukar jirage daga Najeriya a ƙasar har zuwa 10 ga watan Maris.

    Ƙarin wa'adin na cikin wata sanarwa da kamfanin zirga-zirgar jirgin sama na Emirates ya wallafa a shafinsa, wanda mallakin ƙasar ne.

    Tun farko kamfanin jirgin ya sanar da dakatar da ɗaukar fasinjan Najeriya har zuwa 28 ga Fabarairu kafin a ƙara wa'adin da mako biyu.

    "Bisa umarnin gwamnati, an dakatar da fasinjoji daga Legas da Abuja zuwa Dubai har zuwa 10 ga watan Maris," a cerwar sanarwar.

  10. An saka dimokuraɗiyya cikin wani hali bayan wanke Trump - Joe Biden

    Joe Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce wanke Donald Trump da majalisa ta yi daga zargin haddasa rikicin matasa a zauren majalisar manuniya ce cewa "dimokuraɗiyya na cikin wani hali".

    'Yan majalisar jam'iyyar Republican bakwai ne suka goyi bayan hukunta Trump, abin da ya sa aka kasa samun biyu cikin uku na adadin da ake buƙata domin kama tsohon shugaban da laifi.

    Mista Biden ya ce "akwai hujja" kan tuhumar da ake yi wa Trump kan rikicin 'yan dabar da suka kai hari kan ginin majalisar a watan Janairu, yayin da ya buƙaci a jingine batun.

    Da rinjayen kuri'u 57 suka kada kuri'ar, inda 43 cikinsu suka ki amincewa - cikinsu har da 'yan Republican bakwai d su ka bi sahu takwarorinsu na Democrat - amma ba su sami kuri'u 65 da suke bukata ba.

    Bayan da aka wanke shi daga zargin aikata laifi, Mista Trump ya fitar da wata sanarwa da ke sukar shari'ar, yana cewa "yunkurin neman bata suna ne mafi girma a duniya".

  11. Matuƙa jirgin ruwan da aka sace a ruwan Guinea sun isa Turkiya

    Matuka jirgin ruwan Turkiya da masu fashin teku suka yi garkuwa da su a watan jiya a Najeriya sun isa gida bayan an sake su.

    Sun haɗu da iyalansu a ranar Lahadi bayan sun sauka a filin jirgin saman Santanbul.

    An kashe wani matuƙi jirgin ruwan lokacin da wasu ɗauke da makamai da ba a san ko su wanene ba suka afkawa jirgin da ake kira Mozart mai dauke da tutar Liberia makonni uku da suka gabata.

    Ƴan fashin waɗanda suka nemi kuɗin fansa, sun yi garkuwa da matuka jirgin ruwan a daji yayin da ake tattaunawa.

    Kusan dukkanin jiragen ruwa dari da talatin da biyar da aka sace a duniya a bara an kama su ne a mashigin tekun Guinea, wanda ya taso daga Senegal zuwa Angola.

  12. Masu adawa da takarar Deby za su gurfana gaban kotu

    Kotun Chadi za ta fara shari’ar wasu ƴan adawa 14 da za su gurfana gabanta a ranar Litinin kan zanga-zangar da suka yi ta adawa da matakin shugaban Idriss Deby na sake neman wani wa’adin mulki.

    Shugaba Idriss Deby Itno na neman wa’adina shida ne akan mulki.

    Hukumomi a kasar Chadi na zargin ƴan adawa da taka doka lamarin da ya kai ga za su gurfana a gaban kotu domin bayar da bahasi na bukatar da suka gabatar domin a yi adalci wurin neman mulkin kasa.

    Tuni Amnesty International ta yi Allah wadai da taka hakkokin wadannan 'yan siyasa da ta ce gwamnatin kasar Chadi ta yi.

  13. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jiragen Houthi shaƙe da bama-bamai

    Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya ce ya yi nasararar murƙushe wani hari da ƴan Houthi suka yi shirin kai wa da jirage marar matuki a yankin kudancin ƙasar, kamar yadda kafar talabijin din Saudiyya Al Arabiya ta ruwaito.

    Ƙawancen ya ce ƴan Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun yi niyyar kai harin ne a garin Khamis Mushait kan fararen hula.

    Ƴan Houthi sun tsawwala kai hare-hare a kudancin Saudiyya inda a kwanakin da suka gabata suka kai hari filin jirgin sama a yankin.

    Kuma sun yi barazanar ci gaba da kai hare-hare har Saudiyya ta daina kai hare-hare ta sama.

  14. Shekara ɗaya da ɓullar korona a Afirka

    Cutar korona ta kashe kusan mutum 100,000 a Afrika shekara ɗaya bayan ɓullarta a nahiyar.

    Cutar kuma yanzu na ci gaba da bazuwa a ƙasashe 32 na Afirka.

    A ranar 13 ga watan Fabrairun 2020 aka fara samun ɓullar korona a Masar, kuma wasu da dama sun yi tunanin cutar za ta fi ƙamari a Afrika saboda lalacewar kiwon lafiya a ƙasashen.

    Amma matakan da aka ɗauka da kuma yanayi da al’ummar nahiyar musamman da ke da yawan matasa ya taimaka.

    Hukumar daƙile cutar masu yaɗuwa ta Afrika CDC ta ce cutar ta kashe mutum 98,187, kuma jimillar mutum 3,740,297 cutar ta shafa amma daga ciki mutum 3,280,893 sun warke.

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce wadatuwar rigakafin korona zuwa watan gobe zai taimaka wajen daƙile bazuwar cutar.

    View more on twitter
  15. Kotu ta ɗora tarar dubu 100 kan masu zanga-zanga da aka kama a Legas

    Masuy zanga-zanga a Legas

    Kotu ta bayar da belin masu zanga-zanga da aka kama a Legas da ke shirin ƙaddamar da zanga-zangar neman tabbatar da adalci ga waɗanda da suke zargin an ci zalinsu a zanga-zangar EndSARS da aka yi a 2020.

    An saki dukkanin masu zanga-zanga 40 da yammacin jiya, kamar yadda lauyan da ke kare su ya shaida wa AFP.

    Amma ya ce kotu ta umurci su biya kuɗin beli naira dubu ɗari kan barazana ga zaman lafiya da keta ka’idojin cutar korona.

    A ranar Asabar masu fafutika suka yi kiran ƙaddamar da sabuwar zanga-zanga bayan bayar da umurnin sake buɗe Lekki toll gate, inda ake zargin jami’an tsaro sun harbi masu zanga-zanga a watan Oktoba.

  16. Ɗan Najeriya Kamaru Usman ya kafa tarihi a damben ajin welterweight

    Kamaru Usman

    Ɗan Najeriya Kamaru Usman ya kare kambunsa na UFC, wato wasan da ake dambe da harbi da kafa ajin welterweight nauyin kilo sama da 77 bayan ya doke Gilbert Burns a faɗan da suka yi ranar Lahadi.

    Da farko Usman, mai shekara 33 ya ji jiki hannun abokin dambensa ɗan Brazil wanda tsohon abokin atisayensa ne.

    Amma daga baya ɗan damben na Najeriya ya farfaɗo ya doke abokin karawarsa mai shekara 34 tare da kare kambunsa na UFC a Las Vegas.

    Ya lashe dukkanin damben da ya yi 13 na ajin UFC inda ya kere Georges St-Pierre wanda ya fi yawan nasara a welterweight.

    Kamaru Usman
  17. Ƙungiyar lauyoyi ta yi Allah wadai da kama masu zanga-zanga a Lekki

    Yan sanda na kama masu zanga-zanga

    Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA ta yi Allah wadai da kama masu zanga-zanga da dama da jami’an tsaro suka yi a Lekki toll gate.

    Jaridar Tribune ta ambato shugaban ƙungiyar Olumide Akpata cikin wata sanarwa yana cewa hotuna da bidiyonyadda ƴan sanda suka kama masu zanga-zangar abin tsoro ne.

    Matasan na zanga-zanga ne domin neman tabbatar da adalci kan mutanen da suke zargi an harba a lokacin zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban 2020.

  18. Sudan ta kama mataimakin Omar al-Bashir

    Sudan ta kama tsohon mataimakin shugaban ƙasa Hassabo Abdel-Rahman da wani babban jigo a jam’iyyar NCP da aka haramta bayan hukumomi sun zarge shi da hannu a zanga-zanga da aka gudanar a ƙasar.

    Ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar Mohamed al-Hasan al-Amin ya ce hukumomi kuma sun kama wani jami’in NCP Amin Hassan Omar da kuma wasu ƴan jarida, kamar yadda jaridar Sudan Tribune ta ruwaito

    Daga cikin ƴan jaridar da aka kama har da mawallafin jaridar al-Wan kuma mai gidan talabijin na Omdurman TV

  19. Saudiyya ta rufe Masallatai saboda saɓa ka'idojin korona

    Masallaci a Saudiyya

    Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai bayan an samu cikin masu ibada da suka kamu da cutar korona.

    Ma’aikatar lamurran addini ta ƙasar ta ce masallatai biyar ne aka rufe, huɗu a Riyadh babban birnin ƙasar da kuma ɗaya da ke kusa da kan iyaka a yankin arewaci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito.

    Masallatai kimanin 57 yanzu Saudiyya ta rufe cikin mako ɗaya, yayin da aka buɗe 44 daga cikinsu bayan an yi masu feshi da kuma gindaya sharaɗi ga masallata.

    Gwamnatin ta buƙaci mutane su kiyaye sharuɗɗan korona tare da bayar da rahotanni kan duk masallacin da ya saɓa dokokin.

  20. Gwamnatin Najeriya ta roƙi Masallatai da coci-coci kan kiyaye matakan korona

    Hukumar wayar da kan jama'a ta Najeriya (NOA) ta rubutawa Masallatai da coci-coci wasiƙa inda ta buƙaci su tabbatar da kiyaye matakan daƙile yaɗuwar cutar korona.

    Wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar Garba Abari ya yi kira ga cibiyoyin addinai su janyo hankalin mabiyansu kan buƙatar bin ka’idojin da aka shata na daƙile bazuwar korona a ƙasar.

    “Na rubuta wannan wasiƙa ga dukkanin Masallatai da coci-coci a faɗin Najeriya tare da fatan za a karanta wa mabiya,” in ji shugaban NOA.

    Ya ce sun fahimci cewa ƴan Najeriya da dama ba su bin matakan kariya daga korona inda ya ce dawowar Najeriya yadda take kafin korona ya dogara ne da dukkanin ƴan ƙasar.

    View more on twitter