Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Mun zo ƙarshen rahotannin

    Jama'armu rahotannin sun zo ƙarshe a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe da safe domin sanin yadda duniya ke ciki.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Ina addu'ar Allah kawo ƙarshen ta'addanci a Iraƙi - Fafaroma Francis

    Fafaroma

    Fafaroma Francis ya yi kira da a kawo ƙarshen tashin hankali da ta'addanci yayin ziyarar mutum irinsa na farko a Iraƙi.

    Fafaroman na yin ziyarar ce a karon farko tun bayan ɓarkewar annobar cutar korona.

    Da yake jawabi bayan Shugaban Iraƙi Barham Salih ya tarɓe shi, Fafaroma ya ce ya ji daɗin zuwa ƙasar wadda ya siffanta da "ƙashin bayan al'umma".

    "Ina addu'ar kawo ƙarshen makamai...Allah kawo ƙarshen tashin hankali da ta'addanci da ƙungiyanci da kuma rashin haƙuri da juna!" in ji shi.

    "Iraƙi ta sha fama da yaƙi da ta'addanci da faɗan ƙabilanci akasari saboda tsattsauran ra'ayi, waɗanda ke hana mutane su zauna da juna cikin kwanciyar hankali."

    Cutar korona da kuma matsalolilin tsaro sun sa wannan ziyara tasa ta zama mafi haɗari, sai dai dattijon mai shekara 84 ya haƙiƙance cewa "aikinsa ya je yi".

  3. An yanke wa 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana

    Wasu 'yan Najeriya

    ‘Yan Najeriya biyu za su fuskanci da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙasar Ghana muddin suka kasa ɗaukaka ƙara a cikin kwana 30 daga yau Juma'a.

    Babbar Totu a Sekondi ta yanke wa Samuel Udoetuk Wills da John Oji hukuncin kisa sakamkon samun su da aikata laifin ɓatarwa da kuma kisan wasu ‘yan mata ɗalibai a Takoradi.

    Mai Shari’a Richard Adjei-Frimpong wanda ke jagorantar zaman kotun daukaka kara a Ghanar ne ya karanta hukuncin a yau, yayin da sauran masu taimaka masa su bakwai suka same su ta aikata laifin na kisan ‘yan matan Takoradi guda huɗu.

    Bacewar ‘yan matan Takoradin ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye kafafen yaɗa labaran a Ghana a shekarar 2018 bayan da iyayen ‘yan matan suka kai ƙara caji ofis.

    Hakan kuma ya haifar da gagarumar zanga-zanga da kuma gangami a kafafen yaɗa labaran yankin kan bukatar a nemo duk inda ‘yan matan da aka sace suke.

    Bayan tsananta bincike ne kuma ‘yan sandan Ghana suka gano kwarangwal ɗin wasu daga cikin ‘yan matan a cikin tankin dagwalo na karkashin ƙasa..

  4. Obasanjo ya ce ya kamu da cutar korona

    Obasanjo

    Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya faɗa a yau Juma'a cewa gwajin da ya yi na cutar korona ya nuna cewa ya kamu da cutar.

    Jaridu a Najeriya sun ruwaito cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya domin bikin cikarsa shekara 84 da haihuwa a fadarsa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

    'Za ku sha mamaki cewa na kamu da korona," in ji shi. "Na kira su domin su zo su yi mani gwaji, suka zo ranar Asabar. Ban samu sakamakon ba har sai Laraba kuma suka ce na kamu."

    Tsohon shugaban ya ce da farko ya ɗan damu, abin da ya sa ma ya kira 'yarsa Dr. Iyabo Obasanjo kenan, wadda likitar bin diddigin cutuka ce.

    "Da suka dawo bayan kwana uku suka sake gwada ni, sai suka ce na warke, kwana uku kenan bayan gwaji ya nuna na kamu.

    "'Yata Iyabo wadda likita ce, na kira ta domin na yi mata bayani, sai ta ce babu mamaki na kusa warkewa a lokacin da suka yi mani gwajin."

    Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce an yi masa gwajin har sau uku amma yana nuna cewa ba ya ɗauke da cutar.

  5. Tarayyar Turai ta soki China kan sauya tsarin zaɓe a Hong Kong

    Kungiyar Tarayyar Turai ta soki China kan matakan da take dauka da suka shafi tsarin zabe a yankin Hong Kong.

    Kungiyar ta ce wadanan sauye-sauye za su shafi 'yanci da dimokuradiya.

    Wakilin BBC ya ce daya daga cikin tsarin da China ta bijiro da shi zai bukaci duk wani dan takarar kujerar majalisa a Hong Kong ya nemi amincewar kwamitin da mambobinsa ke biyayya ga ƙasar.

    Sabuwar doka kan tsaron kasa da China ta kakaba a Hong Kong a shekarar da ta gabata na ci gaba da tasiri da rage kaifin adawa ga jam'iyyar kwaminisanci a yankin.

  6. Buhari ya buƙaci hafsoshin soja su dawo da tsaro kafin damuna

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya faɗa wa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar cewa su tabbata sun sauke nauyin da ke kansu na dawo da zaman lafiya "kafin zuwan damuna".

    Buhari wanda ya bayyana haka a yau Juma'a yayin bikin bai wa shugabannin tsaron muƙamansu a fadar Aso Villa, ya umarce su da su "ceto Najeriya daga matsalar tsaro cikin gaggawa."

    Ya ce: "Yayin taronmu kan tsaro na awa huɗu da muka yi ranar Talata, na ɗaura muku alhaki a matsayina na Shuhgaban Tsaro da ku fita filin daga domin ku kare wannan ƙasa.

    "Yan makonni kaɗai gare ku don ku yi hakan saboda damuna. Muna sa ran 'yan ƙasa su samu ƙwarin gwiwar komawa gonakinsu saboda kar mu sake shiga matsala ta barin filin daga kuma mu kasa samar da isasshen abinci ga ƙasa."

    Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, musamman a arewa maso gabas, inda Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare, da kuma arewa maso yamma, inda 'yan fashi ke kashe mutane a kullum.

    A ƙarsen watan Janairu ne Buhari ya sauya hafsoshin tsaron ƙasar tare da maye gurbinsu da sabbi.

    Sabbin hafsoshin tsaron su ne:

    • Janar Leo Irabor - shi ne aka naɗa babban hafsan tsaro
    • Janar I. Attahiru - babban hafsan sojan ƙasa
    • Rear Admiral A.Z Gambo - babban hafsan sojan ruwa
    • Air-Vice Marshal I.O Amao - babban hafsan sojan sama.
  7. 'Yan fashi sun kashe mutum 15 a Jihar Sokoto

    'Yan fashi

    Wasu 'yn bindiga sun kashe mutum 15 a harin da suka kai garin Tara da wasu ƙauyukan da ke kewayensa a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Kazalika ana zargin cewa maharan sun sace wasu dabbobi bayan sun far wa ƙauyukan da tsakar daren Alhamis.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun shammaci mutanen ta wata mashiga, inda suka buɗe wuta a kan jama`a tare da kashe mutum 15 sannan mutum bakwai suka jikkata.

    Cikin wadanda suka rasu har da wata `yar shekara shida da haihuwa.

    Ku karanta cikakken rahoton a nan:

  8. Shugaban Cocin Ingila ya caccaki kalaman da Archbishop na Najeriya ya yi kan 'yan Luwaɗi

    Shugaban Cocin Ingila ya yi Allah-wadai da kalmomin nuna yama kan auren jinsi ɗaya da wani malaman coci ya yi a Najeriya.

    A makon da ya gabata ne Archbishop Henry Ndukuba ya fitar da sanarwa yana mai cewa an shiga yanayi na annobar Luwadi, sannan ya ce akwai tsarin gwamnatocin da ke buɗe kofa ga ƙazamin tsarin ɗabi'ar auren jinsi.

    A wani yanayi da ba a saba gani ba, Justin Welby ya soki malamin cocin yana mai cewa "kalamansa ba su dace ba kuma akwai ƙasƙanci a ciki".

    Sannan ya aike wa Archbishop Henry wasika, inda ya ce kalmominsa ba suyi daidai da koyarwar cocinsu ba.

  9. 'Yan sanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Myanmar

    REUTERS

    Rahotanni daga Myanmar na cewa yansanda sun bude wuta kan masu zanga-zanga a birni na biyu mafi girma a kasar, Mandalay, sun kashe mutum guda, yayinda yan kasar ke cigaba da boren nuna adawa da juyin mulkin sojoji.

    Wakilin BBC ya ce mutanen na cigaba da bijirewa umarni da duk wani yunkuri na hana su fitowa, ana cigaba da gangami a garuruwa da biranen kasar, duk da irin barazanar da masu zanga-zangar ke fuskanta, mutum 38 aka kashe a ranar Laraba.

    Firaministan makawabciyar kasar Singapore, Vivian Balakrishnan, yayi alla-wadai da abin daya kira abun kunya ga kasa, ganin yada sojoji ke amfani da bindiga kan mutane

  10. Ziyarar Fafaroma Iraƙi za ta sabunta al'amura da dama

    REUTERS

    Fafaroma Francis ya soma rangadi irinsa na farko a Iraqi. Ya samu tarba daga manyan shugabanni a tashar jirgin sama Bagadaza, da faretin girmamawa, kade-kade domin yi masa marhaba.

    Wakilin BBC ya ce an bayyana ziyarar a matsayin mafi hadari da shugaban darikar katolikar ke kaiwa kasashen ketare.

    Akwai damuwa kan yanayin tsaro, kuma Iraqi na cikin yanayi na annobar korona. A cewara ziyarar ta zame masa tilas la'akari da irin abubuwan da suka faruwa a kasar tsawon lokaci.

    Zai kuma nuna goyon-baya da karfafa gwiwa da kiristoci tsiraru a Iraqi, da suka rinka fusantar barazanar kisa a hannun mayakan jihadi.

  11. Hotunan yadda shugaba Buhari ya sanya wa sabbin hafsoshin Najeriya anini

    @BashirAhmed
    Image caption: Manjo Janar Leo Irabor - Babban hafsan tsaro yayin da shugaba Buhari ke sanya masa anini
    @BashirAhmed
    Image caption: Manjo Janar Attahiru - Babban hafsan sojan ƙasa lokacin da matarsa take taimakawa shugaba Buhari sanya masa anini
    @BashirAhmed
    Image caption: Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban hafsan sojan sama lokacin da matarsa take taimakawa shugaba Buhari sanya masa anini
    @BashirAhmed
    Image caption: Rear Admiral A.Z Gambo - Babban hafsan sojan ruwa Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban hafsan sojan sama lokacin da matarsa take taimakawa shugaba Buhari sanya masa anini
  12. MDD na neman wanda zai ba da shaidar Gimbiya Latifa na raye

    BBC

    Majalaisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu tana dakon shaida da zai tabbatar da cewa Gimbiya Latifa yar sarkin Dubai da aka kulle na raye.

    Majalisar ta nemi shaida daga gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, kakakinta Rupert Colville ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu babu wani martani da suka samu.

    A wani bidiyo da BBC ta gano kwanakin baya, Gimbiyar Latifa tace ana rike da ita a wani kebeben wuri a Dubai, bayan ta yi kokarin tserewa.

    Sannan a wata wasika ta bukaci a sake bincike kan batar yaruwarta Gimbiya Shamsa, shekaru 20 da suka wuce.

  13. Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dakatar da yin muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman Kano da aka shirya yi.

    A ranar Juma'a ne Mai Shari'a Muhammad Jibrin na Kotun Majistire da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon buƙatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma'aruf Yakasai ya shigar gabanta.

    Barista Yakasai dai ya buƙaci a dakatar da gwamnati daga yin muƙabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukansa a daukacin kafofin yada labaran jihar.

    Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari'a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu muƙabala a ranar Lahadi mai zuwa.

    Ku karanta karin bayani a nan.

  14. Bidiyon mutum na farko da aka yi wa allurar riga-kafin korona a Najeriya

    Video content

    Video caption: Bidiyon mutum na farko da aka yi wa allurar riga-kafin korona a Najeriya
  15. Yau ne za a sanya wa hafsoshin sojin Najeriya anini

    A yau ne ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sanya wa Manyan Hafssoshin ƙasar anini, biyo bayan amin cewa da Majalisar dattijan kasar ta yi da nadin da shugaban ya yi musu.

    :  @BayoOmoboriowo
    Image caption: Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban hafsan sojan sama
    :  @BayoOmoboriowo
    Image caption: Rear Admiral A.Z Gambo - Babban hafsan sojan ruwa
    :  @BayoOmoboriowo
    Image caption: Manjo Janar Attahiru - Babban hafsan sojan ƙasa
    :  @BayoOmoboriowo
    Image caption: Manjo Janar Leo Irabor - Babban hafsan tsaro
  16. Majalisar dokokin Zamfara ta kaɗa kuri'ar yanke ƙauna kan Babagana Mungonu

    MAS

    Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kaɗa kuri'ar yake kauna ga mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Babagana Mungonu, kan gazawarsa game da matsalar tsaron da ke faruwa a jihar.

    Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na majalisar Mustapha Jafaru Kaura, Majalisar da ta yi zamanta a jiya, ta nemi gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan mutanen da ke dakile kokarin tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a jihar.,

    Wannan dai wani martani ne da majalisar jihar ke yi game da ayyana jihar a matsayi wadda aka haramta shawagin jirage a samaniyarta.

    Majalisar ta ce duk wanda aka samu da laifi a yanke masa hukunci ba tare da la'akari da girman matsayinsa ba.

    Wannan matakin ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Faruk Musa Dosara ya gabatar a jiya.

    Yana nuna takaicinsa kan yadda aka sace 'yan matan makarantar Jangebe da ke karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara.

  17. Kwana 100 ana zanga-zangar manoma a India

    Getty Images

    An shiga kwana na 100 ana gudanar da zanga-zangar adawa da dokar da gwamnatin India ta kirkiro ta kawo sauyi a harkokin noman kasar.

    Wani dattijo mai suna Prem Singh mai shekara 65 ya kwashe kimanin wata biyu yana fita wannan zanga-zanga.

    Ya baro kauyensu na Haryana da ke arewacin India a watan Disamba 2020, domin shiga zanga-zangar da dubban manoma a India suka shiga, a kan iyakokin kasar, kan bukatarsu ta sake bibiyar dokar da gwamnatin kasar ta kafa a watan Satumba kan noma.

    Yayin da suke gangamin zanga-zanga a garin Singhu - da ke gefen Delhi - Prem ya ce yana kiran dansa Sanddep mai shekara 34 zuwa gida ko wacce safiya.

  18. Najeriya ta shirya tsaf domin fara yi wa ma’aikatan lafiya rigakafin korona

    A cikin wannan makon ne Najeriya ta karbi rigakafin korona da ake sa ran fara yi wa ma'aikatan lafiya a yau.

    An kuma tsara cewa za a yi wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo ta su rigakafin a ranar Asabar.

    BBC
    Image caption: Wasu ma'aikatan lafiya da shuka shirya domin rigakafin korona a Abuja
    BBC
    Image caption: Katin da za a ba duk wanda aka yiwa allurar riga-kafin kenan
    BBC
    Image caption: Akwatin rigakafin korona
  19. Ba mu yarda da hukuncin kotun kolin Ghana ba - John Mahama

    GETTY IMAGES

    Tsohon shugaban kasar Ghana kuma shugaban 'yan hamayyar kasar John Mahama ya ce bai amince da hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar ba, wadda ta tabbatar da zaɓen shugaba Nana Akufo-Addo.

    A ranar Alhamis ne kotun kolin ta yi watsi da korafin da aka shigar gabanta na cewa an yi magudi a zaben shugabancin kasar da aka yi a watan Disambar da ya gabata.

    Da yake mayar da martani kan hukuncin kotu, Mista Mahama ya nuna rashin jin dadinsa, kan cewa shugaban hukumar zaben kasar Jean Mensa ba ta halarci zaman kotun ba balle ta ba da amsa kan zargin yin magudi.

    Kotun ta yanke hukuncin cewa Mista Akufo-Addo ya samu sama da kashi 50 cikin 100 (51,295) na duka kuri'un da aka kada, kuma dan gyaran da hukumar zabe za ta yi game da sakamakon ba zai wani kawo sauyi ba a ciki.

  20. 'Taron MDD kan sauyin yanayi ka iya zama na shan shayi'

    UN

    Wasu gungun 'yan majalisar dokokin Burtaniya na gargadin cewa taron Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi da za a yi a Glasgow a watan Nuwamba mai zuwa na iya karewa a matsayin taron shan shayi kawai, matsawar ba a aiwatar da manufofin da za a cimma ba.

    Sun ce batutuwan da za a tattauna, wadanda suka hada da yadda za a daidaita yanayi da kuma komawa ga amfani da makamashi na zamani na da muhimmanci sosai.

    To sai dai sun tafka muhawara a kan cewa ya kamata a samar da wani tsari da za a rika yin dubayya a kan irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufofin da za a cimma a taron.

    Wakilin BBC yace yan majalisar sun ce suna son Boris Johnson ya maida hankali kan abin da suka kira matukar bukatar kasashe su amince da muhimman manufofi da za su iyakance dumamar yanayi da akalla maki 1.5 a ma'aunin Celcious.

    Yayin da duniya ke fama da ibtila'i iri-iri da aka yi imanin matsalar sauyin yanayi ne kan janyo su, a yanzu masana na dakon taron na Glasgow, da ake kallo a matsayin dama ta karshe ta tunkarar wadannan masifu.