Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Nan muka kawo karshen wadannan labarai da rahotanni.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Manchester Utd ta tsallaka zagayen 'yan 16 a Champions

    Getty Images

    Manchester United ta samu damar tsallakawa wasannin zagayen 'yan 16, bayan cin kwallaye biyu da ta yi a ragar Villarreal karkashin kocin rikon kwarya Michael Carrick.

    Ronaldo ne ya fara cin kwallo a daidai minti na 78 da fara wasan, inda ya ci shida a wasa biyar na Champions ya zuwa yanzu.

    Jadon sancho ne ya ci ta biyu wadda kuma ita ce kwallonsa ta farko tun bayan zuwansa kungiyar.

    United wadda ta kori kocinta Ole Gunnar Solskjaera ranar Lahadi ita ce ta daya a rukunin F yayin da ya rage saura wasa guda a kammala wasannin rukuni.

  3. Sama da mako biyu hukumar zaben Libya ta gaza fitar da 'yan takara shugabancin ƙasar

    Reuters

    Hukumar zaben Libya ta ce za ta shafe kusan mako biyu kafin ta fitar da jerin yan takarar da suka cancanta su fafata a zaben shugaban kasar da za a yi a watan gobe.

    Yan kasar cassa'in da takwas ne suka yi rajistar neman takara amma ana ci gaba da tafka muhawara kan ka'idojin zaben da kuma wanda ya kamata ya tsaya takarar.

    Ana kuma ci gaba da nuna shakku kan cancantar yan takara uku da suka fi fice. Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC na neman Saiful Islam Gaddafi ruwa a jallo saboda rawar da ya taka a boren da ya janyo hambarar da mahaifinsa shekara 10 da suka gabata.

    Ana zargin Janar Khalifa Haftar da ke da sansanin soji a gabashin Libya da tafka laifukan yaki da cin zarafin bil adama.

  4. 'Ta'azzarar rikicin Ethiopia na barazana ga shirin tsagaita wuta'

    BBC

    Wakilin Amurka na musamman a kusurwar gabashin Afirka ya yi gargadin cewa ta'azzarar rikici a Ethiopia na barazana ga duk wani yunkuri na tsagaita wuta.

    Bayan wata ziyara da ya kai Ethiopia, Jeffrey Feltman ya ce Firaminista Abiy Ahmed da kungiyar yan aware ta TPLF dukkansu na ganin suna gab da samun nasara.

    Jeffery Feltman bai yi karin bayani ba kan irin ci gaban da aka samu a yunkurin da ake na ganin bangarorin biyu da ke rikici da juna sun amince da tsagaita wuta.

    Mista Feltman ya sake gargadin cewa idan yan tawayen Tigray suka shiga babban birnin Addis Ababa, hakan babban bala'i ne kuma ba za a amince da shi ba.

    Yayin da TPLF ke cewa mayakanta na nausawa gaba, Faransa da Jamus sun zama kasashen baya-bayan nan da suka shawarci al'ummarsu da su fice daga Ethiopia ba tare da bata lokaci ba.

  5. EFCC ta tsare Femi Fani-Kayode

    Others

    Hukumar da ke yaki da yi wa arzikin kasa ta'annati ta Najeriya EFCC ta tsare tsohon ministan sufurin harkokin sama Najeriya Femi Fani-Kayode domin yi masa wasu tambayoyi.

    Wasu jami'an hukumar EFCC ne suka tabbatar wa da kafar yada labarai ta Channels haka a ranar Litinin a Legas.

    An gayyaci tsohon ministan ne domin ya amsa tambayoyi game da rahoton asibiti na karya da ya gabatar domin ya ki gurfana gaban babbar kotun tarayya da ke Legas, in ji majiyar.

    Rahotanni sun ce FFK ya je ofishin EFCC ne cikin rakiyar lauyansa da misalin 1 na rana.

    Har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoto ana ci gaba da yi masa tambayoyi.

    EFCC ta ce za ta yi bayani kan sakamakon binciken da ta kammala yi masa tambayoyi.

  6. Faransa na taimakawa Burtaniya wajen hana kwararar baki

    BBC

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta ce ta sayi kayan aiki da motoci na sama da dala miliyan goma sha biyu don taimakawa wajen dakile kwararar bakin haure zuwa Biritaniya.

    Ta ce tuni motoci ashirin ke aiki tare da jami'an 'yan sanda a gabar tekun Faransa.

    Haka kuma za a rarraba jiragen ruwa masu sauri, da na'urorin hangen nesa da na sadarwa.

    Sau uku 'yan ci-rani suna tsallakawa zuwa Burtaniya ta kwale-kwale a bana fiye da adadin da aka samu a bara.

  7. Tsohon shugaban Koriya ta Kudu Chun Doo-hwan ya mutu

    QAL

    Tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Chun Doo-hwan da ya yi mulkin karfa-karfa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 1979 ya mutu yana da shekaru 90.

    A matsayinsa na tsohon kwamandan soji, shi ne ya jagoranci kisan gillar da sojoji suka yi wa dubban masu zanga-zangar neman dimokradiyya a Gwangju a 1980, laifin da daga bisani kotu ta same shi da aikatawa harma ta yanke masa hukuncin kisa.

    Ko da yake shekaru takwas da ya kwashe yana mulki sun kasance na nuna rashin tausayi da danniya da kama karya, duk da haka ya taka muhimmiyar rawa cikin saurin wajen ci gaban Koriya ta Kudu har ma ta zamo ɗaya daga cikin mafiya tattalin arziki a yankin Asiya.

  8. Gwamnonin Najeriya ba sa tsoron zaben 'yar tinke - Badaru

    Video content

    Video caption: Gwamnonin Najeriya ba sa tsoron zaben 'yar tinke - Badaru

    Latsa bidiyon da ke sama domin kallon bidiyon:

    Gwamnan Jigawa da ke arewacin Najeriya Muhammadu Badaru Abubakar ya ce gwamnonin jihohin kasar ba sa jin tsoron gudanar da zaben cikin gida ta hanyar 'yar tinke ko kato-bayan-kato.

    Gwamnan ya shaida wa BBC cewa gwamnonin kasar ba sa adawa da gudanar da zabe ta hanyar 'yar tinke, yana mai cewa tsadar gudanar da shi ne abu da suke so a fahimta.

    Ya kara da cewa ita kanta hukumar zaben kasar za ta sha wahala wajen gudanar da shi baya ga daukar lokaci da kuma tsadar da ke cikinsa.

  9. An kashe mutum 19 a harin da aka kai Burkina Faso

    Sojojin Burkina Faso

    Hukumomi a Burkina Faso sun ce wani hari da aka kai a birnin Foubé da ke arewacin kasar ya yi sanadin mutuwar sojoji tara da farar hula akalla 10.

    A makon jiya kusan sojoji 50 ne suka mutu lokacin wani hari da aka kai a arewacin kasar.

    Mutane suna ci gaba da nuna fushinsu a Burkina Faso saboda hare-haren da masu tsattsauran ra'ayin addin suke kai wa lamarin da ya yi sanadin mutuwart dubban mutane sanna ya raba miliyoyi daga gidajensu tun shekarar 2017.

    An yi ta gudanar da zanga-zana da kuma kiraye-kiraye ga Shugaban kasa Roch Kaboré ya sauka daga kan mulki.

    Ranar Litinin gwamnati ta tabbatar da cewa ta katse intanet na kan wayoyin salula saboda rashin tsaro a kasar.

  10. Gwamnonin jihohi za su goyon bayan cire tallafin man fetur baki daya - El-Rufai

    Ekrufai

    Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, Malam Nasir El-Rufai, ya ce a shirye gwamnatocin jihohi suke su goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur baki daya.

    Jaridar Vanguard ta ambato gwamnan yana bayyana hakan ranar Talata a wajen gabatar da sabbin bayanai na Bankin Duniya reshen Najeriya da aka gudanar a Abuja.

    El-Rufai, wanda ya yi bayani ta intanet, ya ce idan ba a cire tallafin man baki daya ba, watakila jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashi a shekarar 2022 ba.

    A cewarsa, an dade da cire tallafin kalanzir, wanda shi ne ya fi yi wa talakawa amfani ba tare da wata matsala ba, yayin da aka cire tallafi a kan gas wanda manyan motoci suka fi yin amfani da shi .

    “Ce-ce-ku-cen da ake yi kan fetur abu ne da a matsayinmu na kasa dole mu tattauna a kansa sanna mu amince kan yadda za a kawo karshensa," in ji gwamna na jihar Kaduna.

  11. Ba mu gamsu da matakan tsaro da gwamnatin Najeriya take ɗauka ba - ACF

    Kungiyar tuntubar juna ta ‘yan arewacin Najeriya (ACF), ta bayyana hare-hare da sace-sacen fasinjoji da ke ci gaba da faruwa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin wani babban abin kunya ga ƙasa, tare da ayyana hakan da cewa ba abin da za a lamuntaba ne ko kadan.

    A wata sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ACF ta yi Allah wadai da hallaka tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu tare da yin awon gaba da mutanen da har yanzu ba a san adadin su b da harin da ya faru a ranar Lahadi.

    Sakatare janar na kungiyar Alhaji Murtala Aliyu ya shaida wa BBC cewagamsu da matakan da gwamnatin Najeriya ke cewa tana ɗauka ba kan matsalar tsaro.

    Ku saurari hirarsa da wakiliyar BBC Balkisu Babangida

    Video content

    Video caption: Hirar BBC Sakatare janar na kungiyar Alhaji Murtala Aliyu
  12. Gwamnati za ta raba wa ƴan Najeriya N5,000 na rage raɗaɗin tallafin mai da ta janye a 2022

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta raba wa ƴan Najeriya tallafin sufuri na naira 5,000 a madadin tallafin mai da za ta janye gaba ɗaya zuwa 2022.

    Ministar kuɗin ƙasar Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya.

    Ministar ta ce adadin waɗanda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

    “Kafin kammala janye tallafin mai a tsakiyar 2022, muna aiki tare da abokan hulɗarmu kan matakai da suka kamata na rage tasirin janye tallafin ga talakawa.”

    “Ɗaya daga cikin matakan shi ne tsarin biyan tallafin sufuri ta hanyar tura wa ƴan Najeriya tsakanin miliyan 30 zuwa 40 kuɗi,” in ji ta.

    Alƙalumman Bankin Duniya sun nuna cewa kashi 40 na talakawan Najeriya, kashi uku kawai na fetur suke amfani da shi a ƙasar, tare da nuna cewa masu arziki ne suke amfana da tallafin mai da gwamnati ke biya.

    View more on facebook
  13. Ƴan sanda na farautar saurayin da ake zargi ya kashe budurwarsa a Ghana

    Ƴan sandan Ghana sun ce suna farautar wani da ake zargin ya kashe budurwarsa kuma ya ɓoye gawarta cikin firjin a cikin gida.

    An gano gawar ne bayan wari ya dami mutanen da ke maƙwabtaka da gidan saurayin.

    Wasu shedu sun ce sun ga kuɗa na yawo a bakin ƙofa da tagar ɗakin matashin wanda ƴan sanda suka kira ‘Frank’. Dalilin haka ya sa aka ɓalla ɗakin kuma aka samu gawar mace a cikin firjin.

    Nan take maƙwabtan suka sanar da ƴan sanda waɗanda suke ci gaba da gudanar da bincike.

    Maƙwabtan sun gano budurwar da suka bayyana a matsayin Lizzy, amma ƴan sanda sun ce saurayin ya yi ɓatan dabo.

    Mai magana da yawun ƴan sanda ASP Efia Tenge ta ce suna farautar saurayin da ake zargin ya kashe budurwarsa.

    Yan sandan Ghana
  14. Har yanzu ba a san adadin mutanen da ƴan bindiga suka sace ba a hanyar Kaduna zuwa Abuja

    Jami'an tsaro

    Har yanzu ba a san yawan mutanen da ke hannun ƴan bindiga ba bayan harin da aka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba a ranar Lahadi.

    A ranar litinin gwamnatin Kaduna da rundunar ƴan sandan jihar ta ce ta ceto mutum 11 bayan musayar wuta da ƴan sanda da sojoji suka yi da ƴan bindiga.

    Sai dai hukumomin har yanzu ba su tattance adadin yawan mutanen da aka sace ba. Jami’an sun samu motocin matafiya da dama ba kowa a cikinsu, wasu a cikin daji wasu kuma a gefen hanya.

    Harin na hanyar Kaduna zuwa Abuja ya yi ajalin tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

  15. Ƴan Gambia na jimamin mutuwar fitaccen ɗan jaridar da ya tona asirin gwamnatin Jammeh

    Pa Nderry Mbai
    Image caption: Pa Nderry Mbai

    Al’ummar Gambia na jimamin mutuwar ɗaya daga cikin fitattun ƴan jaridar ƙasar.

    Sama da shekara 20, Pa Nderry Mbai ya taka rawa wajen bankaɗo take haƙƙin ɗan Adam da wasu ayyuka na rashin adalci zamanin mulkin tsohon shugaba Yahya Jammeh.

    Ya gudu daga ƙasar zuwa Amurka saboda barazana ga rayuwar shi.

    Mista Jammeh a lokacin ya ayyana cewa karanta jaridar Mista Mbai laifi ne ko kuma sauraren gidan rediyonsa.

    Ƴan ƙasar da dama na ɗaukarsa a matsayin wata hukumar tabbatar da gaskiya a Gambia saboda yadda ya taimaka wajen bankaɗo kashe-kashe da azabtarwa a zamanin mulkin Jammeh.

  16. Kasuwar cinikin ƴan ƙwallo

    PSG ta tuntuɓi Zidane, mai shekara 49, wanda ake sa ran zai karɓi ragamar ƙungiyar idan har Pochettino ya tafi. (ESPN)

    Ƴan wasan Paris St-Germain sun yi imanin cewa kocinsu Mauricio Pochettino zai koma Manchester United kuma suna tsammanin Zinedine Zidane zai maye gurbinsa. (Marca, in Spanish)

    Karanta labarin a nan

  17. Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton binciken rikicin EndSars

    Lai Mohammed

    Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya yi watsi da rahoton kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa kan zargin harbe-harbe da aka yi a kofar shiga unguwar Lekki.

    A wani taron manema labarai da ya kira a Abuja a ranar Talata, Ministan ya kira rahoton a matsayin “jaddada labaran ƙarya da ake yaɗa wa a kafofin sadarwa na intanet tun lokacin da al’amarin ya faru a watan Oktoba, kamar yadda ya shaida

    “Mun yi watsi da batun cewa sojojinmu da ƴan sanda sun halaka ƴan Najeriya da ba su ba su gani ba a Lekki a ranar 20 ga watan Oktoban 2020,” in ji Lai Mohammed.

    Ministan ya ƙara da cewa zargin kisa ba ƙaramin abu ne wanda ba zai dogara kaɗai ba akan zargi yana mai cewa an fitar da rahoton ne da ke yawo a kafofin sadarwa don a kunyata gwamnati da kuma hukumominta ba tare da hujjoji ba.

    Ya ce gwamnati ba za ta taɓa bari hukumominta na tsaro su ci zarafi ko keta haƙƙin ƴan Najeriya ta ko wace irin hanya, “dalilin da ya sa aka soke SARS tare da ƙarfafawa jihohi su kafa kwamitin bincike kan rahotannin take haƙƙin ɗan Adam da ake zargin ƴan sandan SARS sun yi.

  18. An wajabta yin rigakafin korona ga ma’aikatan lafiya na Nijar

    Shugaba Bazoum

    Gwamnatin Nijar ta ce rigakafin korona ta zama wajibi ga dukkanin ma’aikatan lafiya na ƙasar.

    Matakin na zuwa bayan ƙaruwar masu kamuwa da cutar kuma masu mutuwa a ƙasar.

    Ma’aikatar lafiya ta Nijar wacce ta sanar wajibcin ga ma’aikatanta a ranar Litinin ta ce matakin na daga cikin matakan ɗakile bazuwar cutar.

    Kuma daga yanzu dole sai ma’aikacin lafiya ya nuna katin shaidar rigakafi kafin samun izinin zuwa wurin aiki ko kuma damar amfani da kayayyakin lafiya.

    Matakin ya shafi har da ɗaliban koyon aikin likita a Nijar.

    Zuwa yanzu mutum 6851 cutar korona ta shafa a ƙasar yayin da ta kashe mutum 246.

  19. Hatsarin mota ya kashe mutum 46 a Bulgaria

    Bulgaria
    Image caption: Yadda motar bar ta ƙone ƙurmus da ke ɗauke da ƴan yawon buɗe ido a Bulgaria

    Aƙalla mutum 46 da suka haɗa yara 12 suka mutu bayan da wata motar bas ta yi hatsari kuma ta kama da wuta a yammacin Bulgaria, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.

    Lamanin ya faru ne kan babbar hanya tsakiyar dare kusa da Bosnek, kudu maso yamma da Sofia babban birnin Bulgeria.

    Motar bas ɗin mai lambar North Macedonia tana ɗauke ne da masu yawon buɗe ido da suka dawo daga Turkiyya.

    Mutum bakwai sun yi nasarar ficewa cikin motar inda aka ɗauke su zuwa asibiti ɗauke da ƙuna a cikinsu.

    Wani jami’in ma’aikatar cikin gida ta Bulgeria ya ce ba a tantance ko motar ta fara kamawa da wuta ba ne kafin ta yi hatsari ko ta ci gaba da ci da wuta.

    Firaministan Macedonia Zoran Zaev ya yi magana da ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira kuma ya shaida masa cewa fasinjan motar suna bacci lokacin da abin ya faru, ƙarar fashewa ce ta sa suka farka.

  20. Red Cross ta ce duniya ta juya wa Afghanistan baya

    Dominik Stillhart

    Wani babban jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya zargi kasashen duniya da juya wa Afghanistan baya yayin da al'ummarta ke fuskantar matsananciyar yunwa.

    Dominik Stillhart, wanda shi ne daraktan ayyuka na ICRC, ya ce abu mafi muni shi newahalar da mutane ke fuskanta na da nasaba da ayyukan bil'adama.

    Ya ce manufofin da aka tsara don hana kungiyar Taliban kuɗaɗen Afghanistan sun jefa talakawan kasar cikin mummunan yanayi.

    Da yake jawabi bayan ya ziyarci kasar Afghanistan, Dominik Stillhart ya buƙaci masu ba da agaji na kasa da kasa su lalubo hanyar da ya kamata a bi don daƙile matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

    Mista Stillhart ya ce ya kamata ƙasashen duniya su fara tattaunawa da gwamnatin Taliban.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa kimanin ƴan Afghanistan miliyan 22za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a cikin hunturu mai zuwa.