Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Sai da safe

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra’ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Ƙungiyar Leeds ta sallami kocinta Jesse Marsch

    ..

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leeds ta kori kocinta Jesse Marsch ƙasa da shekara guda bayan kama aiki.

    Leeds ta yi rashin nasara da ci 1-0 da Nottingham Forest a ranar Lahadi, wanda wannan shi ne wasa na bakwai a gasar Firemiya da ba su ci ko ƙwallo ɗaya ba.

    Kulob ɗin ne na 17 a kan teburi kuma lokaci na ƙarshe da ya ci ƙwallo shi ne a ranar 5 ga watan Nuwamba.

  3. Aƙalla mutum 2,700 aka tabbatar sun rasu a girgizar ƙasar Turkiyya da Syria

    Adadin waɗanda suka rasu a Turkiyya sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a ƙasar ya ƙaru zuwa 1,762 kamar yadda hukumar kare afkuwar bala'i ta ƙasar ta bayyana.

    Idan aka haɗa jumulla daga girgizar ƙasa ta farko da aka yi da asuba da wadda aka yi da hantsi a Turkiyya da Syria sun haura 2,700 bayan rahotanni daga Syria sun bayyana cewa mutum 1,000 suka rasu.

  4. Kamfanonin Amurka za su zuba jarin dala biliyan 4.2 a yankin tsakiya na nahiyar

    ..

    Gwamantin Amurka ta ce kamfanonin ƙasar sun yi alƙawarin zuba jari na dala biliyan 4.2 a yankin ƙasashen da ke tsakiyar Amurka, a wani yunkuri na haɓaka tattalin arziki da taƙaita ƙaura ta haramtacciyar hanya.

    Manufar hakan ita ce samar da dubban ayyukan yi nan da shekara biyar masu zuwa a ƙasashen Honduras da Guatemala da El Salvador.

    Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ce ke shiga tsakani, bayan da shugaban ƙasar Mexico da sauran shugabanin larduna, ke kira ga gwamnatin Biden da magance dalilan da ke sa mutane masu yawa yin ƙaura, mai makon tsaurara matakai akan iyakokinta.

  5. Hotunan Shugaba Buhari a wurin taron APC a Katsina

    Nigeria Presidency
    Nigeria Presidency
    Nigeria Presidency
  6. EFCC ta kama manajan banki a Abuja kan zargin ƙin loda kuɗaɗe a ATM

    .

    Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta kama wani manajan banki a Abuja kan ƙin loda sabbin kuɗi cikin na'urar ATM duk da cewa akwai miliyan 29 lakadan ajiye a cikin bankin.

    Kafin jami'an na EFCC su yi awon gaba da shi, jami'an na EFCC nan take suka bayar da umarni aka zuba kuɗaɗen cikin na'urorin biyan kuɗin domin biyan kwastamomin da suka ɗauki sa'o'i kan layi suna jira.

    Ko a makon da ya gabata sai da jami'an hukumar ICPC suka kama wasu shuwagabannin banki a Abuja.

    .
  7. An raunata sojoji an kashe mutum shida a harin jihar Benue

    PIUS UTOMI EKPEI

    Rahotanni daga Jihar Benue na cewa sojoji uku sun samu raunuka inda kuma aka kashe mutanen ƙauye shida a loikacin da wasu mutane ɗauke da makamai suka kai hari yankin Ikobi da ke Ƙaramar Hukumar Apa ta jihar.,

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito mazauna garin na cewa an kashe wani soja kuma akwai abokan aikinsa biyu ma da aka raunata a yayin wata arangama da wasu ƴan bindiga waɗanda suka kai hari a Ikobi a ƙarshen makon da ya wuce.

    Sai dai sojoji sun bayyana cewa jami'ansu uku ne kawai aka raunata a yayin musayar wuta da ƴan bindigar.

    Haka ma wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sojoji sun daƙile harin amma daga baya an yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa Agagbe.

  8. Ɗan ƙwallon Ghana Christian Atsu na cikin waɗanda ake fargabar ya maƙale a girgizar ƙasar Turkiyya

    ..

    Masu aikin ceto na ci gaba da neman ɗan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana Christian Atsu wanda ake fargabar ya maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai biyo bayan girgizar ƙasar da aka yi a Turkiyya.

    Kafafen watsa labarai sun bayyana cewa ba a san inda ɗan wasan Hataysport yake ba, haka ma daraktan wasanni na kulob ɗin Taner Savut.

    Girgizar ƙasar ta faru ne a wasu sassa na Turkiyya da Syria da misalin 04:00 agogon Turkiyya.

    Sama da mutum 2,300 aka tabbatar da sun rasu bayan girgizar ƙasar.

  9. Labarai da dumi-dumiAƙalla mutum 2,300 aka tabbatar sun rasu a Turkiyya da Syria

    ..

    Adadin mutanen da suka rasu a Turkiyya ya ƙaru sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a yau inda adadin ya kai 1,498, kamaryadda hukumar kare afkuwar bala'i ta ƙasar ta bayyana.

    Idan aka haɗa jumulla da na girgizar ƙasar da aka yi da asubahi da kuma wadda aka yi da hantsi adadin ya kai 2,300, bayan an sake tabbatar da mutuwar mutum 810 a Syria, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

    Ƙasashe da dama a faɗin duniya dai suna ta jajantawa ƙasashen Turkiyya da Syria tare da yi musu tayin bayar da agaji.

  10. Miliyoyin 'yan Habasha na kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba-gardama

    Referundum

    Miliyoyi mutane na ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba gardama a yankin kudancin Habasha domin yiyuwar kafa lardinsu ko kuma kasancewa a inda suke a ƙasar.

    Kimanin mutum miliyan uku da ke rajista ake sa ran za su iya kaɗa ƙuri'a a zaɓen wanda ke nuna yadda ƙabilanci ke ci gaba da yin tasiri a tsarin fedaraliyyar ƙasar.

    Habasha ta shafe sama da shekara 30 tana fama da rikicin ƙabilancin da ya kai ga karkasa ƙasar har zuwa larduna tara ta la'akari da ƙabila.

    Sai dai ana samun ƙarin wasu ƙabilu da ke neman a ba su cin gashin kansu, kamar yadda kundin tarin mulki ya ba su dama.

  11. Sauya fasalin kuɗi: Jam'iyyu 13 sun yi barazanar ƙaurace wa zaɓe 2023

    zabe

    Jam'iyyun siyasa 13 daga cikin jam'iyyu 18 a Najeriya sun yi barazanar kaurace wa babban zaɓen ƙasar da ke tafe matukar Babban Bankin Ƙasar ya ƙara wa'adin amfani da tsoffin kuɗi a ƙasar.

    Jam'iyyun sun ce ba za su shiga zaɓen ba matuƙar CBN ya sake tsawaita wa'adin amfani da tsoffin takardun kudin.

    Gamayyar ƙungiyar shugabannin jam'iyun, waɗanda suka yaba wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, sun dage cewa dole a tabbatar da tsarin.

    Shugaban Jam'iyyar Action Alliance A.A Kenneth Udeze, wanda ya yi wa manema labarai jawabi, ya ce ''muna bayyana cewa akalla jam'iyyu 13 daga cikin jam'iyyun ƙasar nan 18 ba za mu shiga zaɓen da ke tafe ba matuƙar aka dakatar ko a aka soke ko aka tsawaita wa'adin fara amfani da sabbin takardun kuɗi''.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara suka kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙolin ƙasar, suna neman kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da tsarin wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi.

    Matakin da gamayar jam'iyyun suka yi watsi da shi.

    A makon da ya gabata ma dai gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki suka gana da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa.

    Inda suka buƙace shi da ya sake tsawaita wa'adin amfani da sabbin takardun kudi, sakamakon wahalhalun ƙarancin kudin da jama'ar ƙasar ke fuskanta.

    To sai dai a martanin da ya mayar, shugaban ƙasar ya alƙawarta duba tare da magance matsalar cikin kwanaki bakwai.

  12. Yunkurin gurfanar da AA Zaura a kotu ya sake gamuwa da cikas

    AA Zaura

    Yunkurin hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, na gurfanar da ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Kano AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura kan zarge-zargen tafka damfara ya sake fuskantar cikas a kotu.

    Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kanon ta ɗage gurfanar da A.A Zaura don bai wa sabon lauyansa dama ya je ya shirya don tunkarar shari’ar.

    EFCC na zargin sa ne da damfarar wani ɗan ƙasar Kuwait kuɗi fiye da dala miliyan daya, zargin da ya sha musantawa.

    Duk da kasancewar EFCC ta sami nasarar kawo AA Zaura gaban kotun tarayyar amma kotun ta ɗage zaman shari'ar saboda sabon sauyansa Basil Hemba bai shirya ba, inda yace yana buƙatar nazarin yadda zai tunkari batun kasancewarsa sabo kan shari'ar.

    Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ta nemi kotu ta ci gaba da sauraron shari'ar saboda ta ce sun shirya kuma sun kawo wanda ake zargin kotu, sai dai sabon lauyan AA Zaura ya ce bai shirya ba kasancewar jiya ya karɓi kunshin Shari'ar.

    Wannan shi ne karo na shida da ake ƙoƙarin gurfanar da AA Zaura, amma har yanzu ba a kai ga karanto masa zarge-zargen da EFCC ke masa a gaban babbar kotun tarayyar ba.

    Saboda a cewar Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ana ta gabatar da uzuri iri daban-daban.

    Mai Shari'a Muhammad Nasir Yunusa ya ɗage zaman kotun zuwa 1 ga watan Maris, don bai wa sabon lauyan damar nazartar ƙunshin Shari'ar.

    Bayanai na cewa wata babbar kotun tarayya a 2020 ta sallami AA Zaura tare da wanke shi kan da duk wani zargi da EFCC ke masa, abin da yasa EFCCn sake gabatar da zargin zamba da ake yi masa tun da farko a kotu.

  13. Mali ta kori jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya

    ...

    Gwamnatin mulkin soji ta ƙasar Mali ta bai wa shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wa'adin kwana biyu ya fice daga ƙasar.

    A wata sanarwar da aka karanta a kafar talabijin ta gwamnatin ƙasar, mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce shugaban dakarun, Guillaume Ngefa-Atondoko Andali ya aikata ayyuka na zagon-ƙasa a wajen zaɓen shaidun da aka gabatar domin yin bayani a gaban kwamityin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

    A watan jiya, wani mai hanƙoro na wata ƙungiyar fararen hula wanda ya yi bayani a zauren kwamitin tsaron na MDD, ya yi zargin cewa ana take hakkin bil'adama ƙarƙashin ayyukan soji na haɗin gwiwa da Mali ɗin ke yi da Rasha.

  14. Kotun Ƙolin Najeriya ta bai wa Ahmad Lawan takarar sanatan Yobe ta Arewa

    Ahmad Lawan

    Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan matsayin halastaccen ɗan takarar kujerar sanata ta Yobe ta arewa.

    Da yake yanke hukuncin alƙalin kotun mai shari'a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Damaturu hujjar - baka ta zargin aikata maguɗi a zaɓen fitar da gwanin - da ya sa ake gayyatar ɓangaren Ahmad Lawan zuwa kotun.

    Jam'iyyar APC ce dai ta ƙalubalanci Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ɗan takara.

    A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam'iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

    Peters ya ce ba jam'iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami'in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

    Ya shaida wa kotun cewa jam'iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen, inda a cewarsa kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

    To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

    Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam'iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

    Sanata Ahmad lawan dai bai shiga takarar fitar da gwani na farko da jam'iyyar ta gudanarar ranar 28 ga watan Mayun 2022, kasancewar ya shiga takarar shugabancin ƙasar.

  15. Buhari ya yi Allah-wadai da kisan 'yan Najeriya a Burkina Faso

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan 'yan ƙasar waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa ziyarar ibada garin Kaulaha na ƙasar Senegal.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce shugaban ya samu mummunan labarin harin da aka kai wa 'yan ƙasar a kan haryarsu ta zuwa garin Kaulaha na ƙasar Senegal hari.

    Wasu 'yan bindiga ne dai suka far wa ayarin motocin da ke ɗauke da mutanen a ƙasar Burkina Faso, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wasu da dama.

    Shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, tare da addu'ar samun kariya da waɗanda suka maƙale a can.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta hanyar ofishin jakadancin ƙasar da ke Burkina Faso na aiki da hukumomin ƙasar domin yin bincike game da faruwar lamarin, tare da tabbatar da kamo tare da gurfanar da waɗanda suka aikata lafin gaban shari'a.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnatin Najeriya za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin mayar da gawarwakin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa ƙasar.

  16. Sauya fasalin kuɗi: Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai gwamnatin tarayya ƙara

    Kudi

    Gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙolin ƙasar, suna neman kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da tsarin wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi.

    Sakamokon matsalar ƙarancin sabbin kuɗin da suka ce ya jefa al'umominsu cikin mawuyacin hali.

    Buƙatar da lauyan jihohin uku, AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN) ya gabatar wa kotun, ta nuna cewa jihohin arewacin ƙasar uku na buƙatar Kotun Ƙolin da ta tsayar da gwamnatin tarayya da CBN da bankunan ƙasar aiwatar da tsarin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi zuwa wa'adin 10 ga watan Fabrairu da CBN ɗin ya saka.

    Masu shigar da ƙarar sun haɗar da kwamishinonin shari'a na jihohin uku, inda ministan shari'a na ƙasar Abubakar Malami (SAN) ke wakiltar gwamnatin tarayya a shari'ar.

    Masu shigar da ƙarar su ce tun bayan bayyana fara amfani da sabbin takardun kuɗin, ake samun matsalar ƙarancin sabbin kuɗin a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara,.

    Sun kuma ce mutanen da suka kai tsoffin takardun kuɗin nasu bankuna, na shan matuƙar wahala kafin samun kuɗaɗen daga bankunan, a wasu lokutan ma ba sa samun kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau-da-kullum.

    Sun ƙara da cewa wa'adin kwana 10 da gwamnatin tarayya ta ƙara ba zai isa ba wajen warware matsalar da ake fuskanta ta ƙarancin takardun kuɗin.

    A ƙarshen mako ne dai Gwamnan Babban Bankin ya jaddada cewa CBN ɗin ba zai ƙara wa'adin da ya saka ba a wani taron manema labarai da ya gabatar a birnin Legas.

  17. MDD ta yi Allah- wadai da kisan jami'inta a DR Kongo

    Gutteres

    Babban Sakatare Janar na Majaliar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah -wadai da kisan jami'in wanzar da zaman lafiya na majalisar a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

    Wani jami'in majalisar ya samu raunuka a lokacin da jirgin da suke ciki ya kama da wuta a lokacin da ya doshi lardin Kivu na arewacin ƙasar.

    Kawo yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin.Faɗa na ƙara ƙamari a yankin inda sojojin Kongo ke yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a ƙasar sun ce jami'in da aka kashen ɗan ƙasar Afirka ta Kudu ne.

    Jirgin dai ya kama da wuta ne jim kaɗan bayan tashinsa daga birnin Beni.

    Inda kuma ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Goma babban birnin lardin arewacin Kivu.

    Kawo yanzu dai ba a san wanda ya harbo jirgin ba, to amma yanki na fama da ƙungiyoyin 'yan tayar da ƙayar baya waɗanda ke faɗa da dakarun gwamnati a 'yan watannin nan.

    Ɗaruruwan mutane ne aka kashe, tare da raba dubbai da gidajensu sakamakon rikicin.

    A cikin ƙarshen mako ne shugabannin ƙasashen gabashin Afirka suka yi wani taro a Burundi domin sabunta kiraye-kirayensu na gaggauta dakatar da buɗe wuta daga duka ɓangarorin da ke yaƙi da juna a gabashin ƙasar.

  18. Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari'ar Ahmad Lawan da Bashir Machina

    Ahmad Lawan da Bashir Machina

    A yau ne kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci game da rikicin takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa na jam'iyyar APC.

    Jam'iyyar APC na ƙalubalantar Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa.

    Jam'iyyar ta kafe cewa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne halastaccen ɗan takararta a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam'iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

    Peters ya ce ba jam'iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami'in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

    Ya shaida wa kotun cewa jam'iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen.

    Ya kuma ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

    To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce yana fatan Kotun Ƙolin za ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin ƙwararan hujjoji, kasancewar Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

    Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam'iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

  19. Matsalar tsaro za ta yi cikas ga zaɓen Najeriya na 2023 - HRW

    'Yan bindiga

    Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ƴancin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023.

    A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al’ummar Najeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa, tare da na 'yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi.

    An dai yi ta samun barazanar tsaro game da zaɓen daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar, ciki har da ƙungiyoyin 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke yunƙurin daƙile yiyuwar zaɓen.

    Tarihin zaɓukan Najeriya ya nuna yadda zaɓukan ke cike da rigingimu da sauran laifukan zaɓe.

    Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce zaɓen Najeriya na 2015 wanda ya bai wa shugaba mai ci Muhammadu Buhari nasara a matsayin ɗan takarar jam'iyyar adawa na farko da ya yi nasara zaɓen ƙasar shi ne ake gani wanda aka yi cikin kwanciyar hankali.

    To amma an samu 'yar hatsaniya a zaɓen 2019, ciki har da amfani da jami'an tsaro wajen yin barazana ga masu kaɗa ƙuri'a da kuma 'yan dabar siyasa da ke yi wa 'yan siyasa aiki.

  20. Cutar Kansa na kashe mutum 700,000 duk shekara a Afirka – WHO

    Tedros

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a kowacce shakara akan samu kusan mutum miliyan 1.1 da ke kamuwa da cutar Kansa a nahiyar Afirka inda kusan mutum 700,000 ke mutuwa sakamakon cutar.

    Daraktar hukumar mai lura da kasashen Afirka Dakta Matshidiso Moeti, ce ta bayyana haka ranar Lahadi a wani jawabi da ta gabatar a bikin ranar yaƙi da cutar ta duniya mai taken 'Inganta Hanyoyin Yaki da Cutar: Mu haɗa muryoyinmu domin ɗaukar mataki'.

    Ta ce hasashen da aka yi yanzu na nuna cewa akwai barazanar samun kashi 50 cikin ɗari na yaran da ake haihuwa da cutar a nahiyar Afirka zuwa shekarar 2050.

    Ta ƙara da cewa alkaluman sun nuna cewa akwai hasashen samun ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar kansa zuwa kusan miliyan ɗaya a kowacce shekara zuwa 2030, idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

    Dakta Moeti ta ce ƙasashe 12 ne a nahiyar Afirka ke da kyakkyawan shirin yaƙi da cutar.

    Jami'ar ta WHO ta ce Hukumar na taimaka wa ƙasashe 11 domin samar da ko inganta shirye-shiyensu na yaƙi da cutar.