Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya tare da fatan za mu haɗu gobe a wani sabon shafin na labarai kai-tsaye.

  2. Ku ji daga bakin gwarazan gasar Al-Ƙur'ani ta 2021 a Najeriya

    Video content

    Video caption: Danna hoton sama ku kalli bidiyo

    A ɓangaren mata, wata 'yar Kano mai suna Nusaiba Shuaibu Ahmad ce ta zo ta ɗaya daga Jihar Kano.

    Muhammad Auwal Gusau, shi ne gwarzon musabaƙar a bangaren maza, kuma ya fito ne daga Jihar Zamfara - duka a arewa maso yammacin ƙasar.

    Kuna iya karanta bayanai game da rayuwarsu a nan:

  3. Sauya shugabannin tsaro zai taimaka mana a yaƙi da Boko Haram - Idris Deby

    Buhari da Idris Deby

    Shugaban Chadi, Idris Deby Itno, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa dakarun haɗin gwiwa na ƙasashe huɗu da ke yaƙi da Boko Haram (MNJTF) za su kawo ƙarshen ƙungiyar.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Asabar jim kaɗan bayan ya gana da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Shugaban mai muƙamin soja na Marshal ya ce sababbin salon yaƙi da rundunar ke ɗauka, ciki har da sake shugabanninta a kowane mataki, za su taimaka wajen daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi.

    "Ganin sabbin matakan tsaro da ake ɗauka da sabbin shugabannin tsaron, ba a Najeriya kaɗai ba har a rundunar Multinational Joint Task Force wadda ita ma ta yi sababbin kwamandoji, za mu iya kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram baki ɗaya," in ji shi.

    "Abin baƙin ciki shi ne, dagewar da Boko Haram da IS ke yi a yankin Tafkin Chadi na da yawa sosai. Ana ba su horo da makamai daga Libya.

    "MNJTF ta samu gagarumin ci gaba a 'yan kwanakin nan. Samuwar sabon shugaban rundunar MNJTF za ta taimaka mana kawo ƙarshen Boko Haram."

    Sojojin Chadi na da ƙwarewa sosai a yaƙi da masu iƙirarin jihadi a tsakanin ƙasashen Najeriya da Nijar da Benin da Kamaru, waɗanda ke cikin rundunar ta ƙasa da ƙasa.

  4. Najeriya ta samu gurbin shiga gasar Kofin Afirka ta 2021

    Super Eagles

    Najeriya ta samu gurbin shiga gasar Kofin Afirka ta 2021 bayan Lesotho da Sierra Leone sun buga canjaras a wasansu a rukunin L.

    Sakamakon wasan ne ya bai wa tawagar ta Super Eagles damar shiga gasar tun kafin take wasanta da Benin a yau Asabar.

    Najeriya ta doke Benin 0-1 a wasan da suka take da ƙarfe 5:00, abin da ya sa ta samu maki 11, Benin na da bakwai, Sierra Leone na da huɗu sai kuma Lesotho mai uku a rukunin.

    Ƙasashen da suka ƙare a mataki na ɗaya da na biyu ne za su halarci gasar a Kamaru, wadda ƙasashe guda 24 za su fafata a karo na 33.

    Benin da Najeriya ne suka samu gurbin shiga gasar daga rukunin na L.

    Tawagar Super Eagles ta lashe kofin gasar sau uku a tarihi.

    Sauran ƙasashen da suka fito zuwa yanzu:

    • Algeria
    • Burkina Faso
    • Kamaru
    • Comoros
    • Egypt
    • Equatorial Guinea
    • Gabon
    • Gambia
    • Ghana
    • Guinea
    • Ivory Coast
    • Mali
    • Morocco,
    • Senegal
    • Tunisia
    • Zimbabwe
  5. Sojojin Najeriya sun 'kashe 'yan Boko Haram 48', sun ceto mutum 11

    Sojojin Najeriya

    Dakarun sojan Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram guda 48 tare da ceto mutum 11 a Jihar Borno, a cewar mai magana da yawun rundunar.

    Wata sanarwa da Birgediya Mohammed Yerima ya fitar a yau Asabar ta ce dakarun rundunar 28 a ƙarƙashin shirin Lafiya Dole sun kashe 'yan bindiga tara a wata fafatawa a yankin Chibok zuwa Damboa.

    Kazalika ya ce an ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su tare da ƙwace bindigar AK-47 guda bakwai.

    Ya ce dakarun nasu sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri da ke cewa an ga mayaƙan na tserewa sakamakon luguden wutar da ake yi musu a Dajin Sambisa.

    A wani kwanton ɓauna na daban, sojojin sun kashe 'yan Boko Haram 39 a garin Askira sannan suka ceto mutum takwas da suka yi garkuwa da su.

    Haka nan, sojoji sun sake yin nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda takwas.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da sojojin suka kai waɗannan hare-hare ba sannan kuma ko wani soja ya ji rauni ko rasa rai.

    Amma ta ce ɗaya daga cikin mutanen da aka ceto ya ji rauni kuma yana kwance a asibitin sojoji.

    View more on twitter
  6. Rwanda ta yi maraba da rahoton da ya 'fallasa' hannun Faransa a kisan kiyashi

    Rwanda ta yi maraba da wani rahoto da ya gano cewa Faransa ta ba da gudummawa a kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994.

    Rahoton wanda shugaba Emmanuel Macron ya gabatar bai bayyana ko Faransa tana da hannu dumu-dumu a kashe-kashen ba.

    Amma ya ce gwamnati a lokacin tana da kusanci da mulkin da ya karfafa kisan kiyashin.

    Kimanin yan Rwanda 800,000 - akasarinsu yan kabilar Tutsi ne - suka mutu.

    A cewar wakilin BBC, sojojin Faransa suna Rwanda daga shekarar 1990 lokacin da aka soma kisan kiyashin a 1994.

    Sakamakon kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar a lokacin, Faransa ta ci gaba da tallafa wa gwamnatin.

    Gwamnatin Rwanda da ta kawo karshen lamarin ta dade tana zargin Faransa da hannu a lamarin.

  7. Facebook ya rufe shafin shugaban Venezuela

    Facebook

    Facebook ya rufe shafin Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, bayan ya wallafa cewa maganin gargajiya ka iya magance cutar korona.

    Sai dai shugaban bai bayar da wata hujja ba game da iƙirarin nasa.

    Wani mai magana da yawun Facebook ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa Maduro ya karya dokar dandalin ta yaƙi da satar basira ko zamba.

    A watan Janairu, shugaban na Venezuela ya ce maganin gargajiya ka iya maganin cutar amma likitoci sun yi watsi da iƙirarin nasa.

    Shi ma Facebook ya yi watsi da kalaman nasa cewa ana iya magance cutar da maganin gargajiya.

  8. 'Yan wasan da za su buga wa Najeriya wasa da Benin a yau

    @NGSuperEagles

    Da ƙarfe 5:00 agogon Najeriya, ƙungiyar ƙwallon ƙafar Super Eagles ta ƙasar za ta ɓarje gumi da takwararta ta Benin a wasan neman shiga gasar Kofin Afirka ta 2021.

    Tuni mai horarwa Gernot Rohr ya fitar da sunayen 'yan wasa 23 da suka isa ƙasar ta Benin don buga wasan.

    Tawagar 'yan ƙwallon Najeriyar ta isa Benin ne a jiragen ruwa.

    Kamaru ce za ta karɓi baƙuncin gasar karo na 33.

    'Yan wasan su ne:

    • Okoye
    • Aina
    • Balogun
    • Ekong
    • Ndidi
    • Chukwueze
    • Aribo
    • Onyekuru
    • Iheanacho
    • Osimhen

    Sai kuma 'yan benci:

    • Uzohoh
    • Noble
    • Collins
    • Etebo
    • Abdullahi
    • Onuachu
    • Awaziem
    • Ebuehi
    • Ajayi
    • Musa
    • Iwuala
    • Adekunle
    View more on twitter
    View more on twitter
  9. An kai wa tawagar ceto hari a Mozambique

    Mozambique

    An kai wa wata tawaga da ke yunƙurin ceto mutanen da suka maƙale a wani otel a Mozambique hari, waɗanda faɗa tsakanin 'yan bindiga da dakarun gwamnati ya ritsa da su.

    Mutum fiye da 170 ne ke cikin otel ɗin Amarula da ke Palma, inda dakaru ke fafatawa da masu tsattsauran ra'ayin Musulunci.

    Wani mai aikin ceto ya faɗa wa BBC cewa an ceto mutum kusan 100.

  10. Sharhin wasanni tare da Jabir Mustapha Sambo

    TC

    A yau ne tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta kece reni da Jamhuriyar Benin a wasan share fagen zuwa gasar cin kofin nahiyar Africa.

    Menene hasashenku kan wannan wasa?

    Ya kuma ku ke ganin za ta kaya a sauran wasannin na kasa da kasa da za'a yi a yau?

    Ku kasance da sashes Hausa na BBC a wannan shafi na Facebook da misalin karfe 4:00.

    Jabir Mustapha Sambo ne zai gabatar ku kasance tare da shi domin bayyana ra'ayoyinku.

    TC
  11. Ana tattaunawar sirri tsakanin Buhari da shugaban Chadi Idriss Deby

    Google

    Shugaba Muhammadu Buhari na wata tattaunwar sirri tsakaninsa da takwaransa na na Chadi Idriss Deby a fadarsa da ke Abuja babban birnin kasar.

    Rahotanni sun ce da misalin 12 na rana Shugaba Deby ya isa fadar Shugaban Najeriya, yayin da ya tarbesa tare da wasu mukarrabansa.

    Ba dai a bayyana dalilin wannan ziyara ta shugaban na Chadi ba.

    Sai dai ana sa ran zai tattauna da manema labarai bayan ya kammala tattaunawa da shugaba Buhari.

    Masu lura da al'amuran yau da kullum na hasashen cewa, tattaunawar ta su ba za ta rasa nasaba da ,matsalar tsaro ba da ta'addabi kasashen, wadda ta hada da matsalar Boko Haram da kuma yadda za a kiyaye bakin tafkin kogin Chadi.

    Ana kuma sa ran Deby zai bayyanawa Buhari aniyarsa ta neman takarar shugabancin Chadi karo na shida a tarihi, zaben da za a yi a ranar 11 ga watan Afrilu mai zuwa.

    Deby ya shugabanci Chadi na tsawon shekara 30, kuma ya fara yakin neman zabensa ne tun ranar 13 ga wannan wata na Maris.

  12. 'Yar Kano ce ta lashe musabakar kur'ani ta mata dan Zamfara ya lashe ta maza

    BBC

    A yau ne aka kammala musabakar Al-kur'ani mai girma ta kasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

    An fara musabakar ne kwanaki takwas baya, inda a yau kwana na tara aka kammala ta.

    Muhammad Auwal Gusau shi ne gwarzon musabakar ta bana bangaren maza, kuma ya fito ne daga jihar Zamfara.

    Ya kara da masu karatu da yawa in da a karshe ya samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri.

    Sai Nusaiba Shuaibu Ahmad daga bangaren mata, wadda ita ma ta zo ta daya a bangaren izu 60, kuma yar asalin jihar Kano ce.

    BBC

    A yayin bikin an nadawa Muhammad Auwal Gusau rawani, cewa ya zama kangaran kuma zakaran gwajin dafi a tsakanin gwanayen al-Kur'ani mai girma.

    Man yan makaranta ne suka halarci taron daga sassa daban-daban na Najeriya.

    Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya halarci wurin rufe wannan gasa ta karatun al-Kurani.

    Haka kuma mafi yawan wadanda ba su samu nasara ba tun daga matakin farko na gasar har zuwa karshe sun halarci taron rufe gasar.

    BBC
  13. Motoci bakwai wani hadari ya rutsa da su a gadar Otedola a Legas

    @LagosRescue

    Wani mummunan hatsari da ya afku ya haifar da gobara a kan gadar Otedola a kan titin Legas zuwa Ibadan a yankin kudancin Najeriya da safiyar Asabar.

    Hukumomin ba da agajin gaggawa da suka hadar da hukumar kashe gobara ta jihar Legas da sauransu tuni suka isa wurin tare da girke jami'ansu domin kashe wutar da kuma saukaka cunkoson ababan hawa.

    View more on twitter

    Hukumar kiyaye cunkoson ababan hawa LASTMA ta ce hadarin ya rutsa da ababan hawa biyar, ciki har da motocin mai biyu da wasu manyan motoci biyu da kuma karamar mota daya.

    Amma daga baya hukumar kashe gobarar ta jihar ta ce hadarin ya rutsa ne da motoci bakwai maimakon biyar.

    @LagosRescue
    @LagosRescue
  14. An kama wani babba jigo a kungiyar ISIL a Kabul

    moi

    Ma'aikatar cikin gida ta Afghanistan ta ce dakarunta na musamman sun yi nasarar kama wani ƙusa kuma mamba a kuniyar ISIL a wani samame da suka kai a Kabul babban birnin kasar.

    Ma'aikatar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter cewa an kama wani babban mamban ISIS tare da wasu makamai da kuma wasu wasu kayan aikin soji da suka kwace.

  15. Saurari cikakkiyar hirar BBC da Rabi'u Musa Kwankwaso

    Video content

    Video caption: Latsa ka saurari shirin Gane Mani Hanya hirar da BBC ta yi da Rabi'u Musa Kwankwaso

    A Najeriya, duk da cewa da sauran tafiya dangane da babban zaben kasar na shekara ta 2023, za a iya cewa an fara kada gangar siyasa.

    Kuma a halin da ake ciki, manyan jam`iyyun siyasar kasar biyu, APC da PDP na neman yadda za su tunkuri batun shiyyar da za su ba da takarar shugaban kasa.

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Senata Rabi`u Musa Kwankwaso, jigo ne a jam`iyyar PDP, wanda kuma kan yi gaba-gadi wajen fadar ra`ayinsa na siyasa.

    A filin gane-mani-hanya na wannan makon, Ibrahim Isa ya tatattauna da tsohon gwamnan na Kano a kan maganar takarar shugaban kasa, musamman ma shiyyar da ya kamata jam`iyyar PDP ta kebe wa kujerar.

    Amma ya fara ne da bayyana ra'ayinsa a kan wadansu batutuwa da suka shafi jihar ta Kano, musamman ma shirin rancen naira biliyan ashirin da gwamnatin jihar za ta karba domin gina wata gada da za ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil, da ya ce ba dai-dai ba ne:

  16. Babban Hafsan sojan kasa lokacin Jonathan ya shiga jam’iyyar APC

    APCTWITTER

    Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC A Najeriya ya ce komawar tsohon babban Hafsan sojan kasar lokacin Jonathan, Azubuike Ihejirika jam'iyyarsu zai kara sanya a ci gaba da damawa da yankin kudu maso gabas

    Ihejirika dai tsohon babban Hafsan sojan kasa ne a lokacin Jonathan,ya kuma bayyana komawarsa APC tun ranar 16 ga watan Fabirairu a mazabarsa ta Isuikwuato da ke karamar hukumar Abia ta arewa.

    Sai dai a yammacin Juma'a ne jam'iyyar ta karbe shi a hukumance.

    An gabatar da Ihejirika gaban shugaban riko na jam'iyyar Abubakar Badaru wanda kuma shi ne gwamnan Jigawa da kuma Faruka Aliyu.

    Mai Mala Buni ya bayyana wannan komawar ta Ihejirika a matsayin babbar nasara ga jam'iyyarsu.

    Shafin jam'iyyar ne ya fara wallafa hoton shugabannin da kuma tsohon hafsan sojin lokacin da aka gabatar da shi.

    View more on twitter
  17. 'Faransa ta ba da gudummawa a kisan kiyashin da aka a Rwanda a 1994'

    AFP

    Rwanda ta yi maraba da wani rahoto da ya gano cewa Faransa ta ba da gudummawa a kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994.

    Rahoton wanda shugaba Emmanuel Macron ya gabatar bai bayyana ko Faransa tana da hannu dumu-dumu a kashe-kashen ba.

    Amma ya ce gwamnati a lokacin tana da kusanci da mulkin da ya karfafa kisan kiyashin.

    Kimanin yan Rwanda dubu dari takwas - akasarinsu yan kabilar Tutsi ne suka mutu.

    A cewar wakilin BBC, sojojin Faransa sun kasance a Rwanda daga shekarar 1990.

    Lokacin da aka soma kisan kiyashin a 1994 sakamakon kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar a lokacin, Faransa ta ci gaba da tallafawa gwamnatin.

    Gwamnatin Rwanda mai ci da ta kawo karshen lamarin ta dade tana zargin Faransa da hannu a lamarin.

    AFP
  18. Babu wanda zai rubuta jarrabawar UTME sai mai lambar NIN - JAMB

    FACEBOOK/JAMB

    Hukumar shirya jarrabawar shiga jami'a JAMB ta ce sai dalibi yana da lambar NIN zai iya yin rijistar jarrabawar UTME ta 2021.

    Wannan wajibcin ya shafi masu shiga jami'a kai tsaye daga kwalejin kasar ko kuma makarantun gaba da sakandire.

    Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.

    "A wannan shekarar za mu yi aiki kafada da kafada da hukumar dake ba da lambaar NIN.

    Duk wanda yake son yin rijista da mu sai ya tabbatar yana da Lambar NIN, saboda a wannan shekarar farkon abin da muke bukata ita ce lambar NIN.

    Oloyede ya ce duk lambar da aka yi amfani da inda wajen yin rijistar NIN to dole da ita za a ci gaba da amfani ga wanda yake neman gurbin karatu.

    Ya kuma ce amma ga daliban da basu da layin waya kuma suna son yin rijista za a iya daga musu kafa.

  19. An kashe masu zanga-zanga kimanin 59 a Myanmar

    Reuters

    Rahotanni daga Myanmar na cewa jami'an tsaro sun bude wuta kan masu zanga-zanga a birnin Yangon a ranar da ake bikin tunawa da yan mazan jiya.

    Masu adawa da juyin mulkin sun nemi a gudanar da zanga-zanga a yau duk da barazanar da sojoji suka yi cewa za a yi amfani da karfi kan masu bore.

    A wani taro da aka gudanar a babban birnin kasar, Jagoran gwamnatin mulkin soji a Myanmar ya kare matakin hambarar da gwamnatin da aka zaba wata biyu da ya gabata inda ya nanata alkawarin gudanar da wani sabon zabe.

    Reuters

    Wakilin BBC ya ce jagoran juyin mulkin ya kuma soki masu zanga-zanga inda ya zarge su da hannu a tashin hankalin da aka samu a 'yan makwannin da suka gabata.

    Jami'an tsaro sun fito da karfinsu damin dakile zanga-zangar musamman a yankin Yangon.

    Reuters

    Abu ne dai mai wuya a iya tantance mutum nawa ne suka mutu ya zuwa yanzu.

    Amma rahotanni sun ce an kashe mutu 59 ciki har da wasu kananan yara uku da kuma wasu 28 a wasu wuraren na daban.

    Myanmar ta ce a kalla an kashe mutum 50, ciki har da wasu hudu a wajen ofishin 'yan sanda dake yankin Dala a lardin Yangon.

    EPA

    Ana ta samun rahoton mace-mace a Mandalay, birni na biyu mafi girma a kasar, yayin da masu zanga-zangar suka dauki tutocin jam'iyyar NLD, wato jam'iyyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi da ake tsare da ita.

    Wani dan jarida ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, jami'an tsaro na amfani da harsashi domin tarwatsa masu zanga-zangar a yankin arewa maso gabashin birnin Lashio.

  20. 'Yan bindiga sun sace kimanin mutum takwas a Kaduna

    Facebook

    'Yan bindiga sun sace kimanin mutum takwas mambobin wata coci a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a maraicen Juma'a.

    Rahotanni sun ce mutanen na cikin motar cocinsu ne a kan hanyarsu ta zuwa aiki na musamman lokacin da aka sace su.

    Tun a daren ranar Juma'a aka fara samun wasu hotuna a kafafen sada zumunta da ke nuna hoton motar da aka sace su a yashe.

    An sace duka fasinjojin da ke cikin motar a kan hanyar Kachia kilomita 63 daga Kaduna, kamar yadda rahotanni suka ce.

    Tsohon Sanata a Jihar Shehu sani ya wallafa faruwar lamarin a shafinsa na Twitter, yana mai nuna bakin cikinsa kan yadda jihar ta zama wajen baje hajar yan bindiga.

    View more on twitter

    Ya ce kafin a saki wadanda aka sace sai kaji an kara sace wasu, mutane sun zama abin farauta.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da aka shiga kwana na 17 da sace dalibai 39 na makarantar Afaka dake jihar.

    Da yawan mutane a kafafen sada zumunta na ta kiraye-kirayen gwamnati ta kara kaimi domin ganin ta dakile wannan abu da ke faruwa a kai-akai a Jihar Kaduna.