Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

    Za ku iya zuwa har kasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a yinin Juma'a.

  2. Likitoci na neman tallafi don raba tagwayen da aka haifa a manne a Yemen

    Likitoci a babban birnin Yemen, Sanaa, sun yi kiran taimakon gaggawa don ceton rayukan wasu tagwaye da aka haifa a manne da juna a ranar Alhamis.

    Shugaban asibitin (Al-Sabeen) inda aka haifi tagwayen ya ce suna cikin mawuyacin hali kuma suna bukatar tiyatar da ba za a iya yin ta ba a Yemen sai an fita ƙasar waje.

    An rufe tashar jirgin saman da ke Sanaa ga jiragen da jigilar fasinja saboda rikicin ƙasar da aka shafe shekaru ana yi.

    Hukumomin kiwon lafiya na cikin gida sun yi kira ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ke Yemen da su samar da jirgin da zai ɗauki tagwayen.

    Wasu tagwaye sun taɓa mutuwa a Yemena bara, makwanni biyu da haihuwarsu.

    Tagwayen da aka haifa a Yemen a manne da juna
    Image caption: Tagwayen da aka haifa a Yemen a manne da juna
  3. Sabbin matakan da gwamnatin Legas ta ɗauka kan korona

    Gwamnatin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kafa sabbin dokoki domin daƙile annobar korona da ta ƙara bazuwa a jihar.

    Daga cikin sabbin matakan sun haɗa da rufe makarantu a faɗin jihar, sannan ƙananan ma'aikata zuwa matakin aiki na GL14 za su ci gaba da aiki a gida.

    Sauran matakan sun hada da:

    • Taƙaita lokacin ibada da masallatai da coci coci zuwa awa biyu da yawan masu ibada zuwa kashi 50.
    • Dokar hana fita daga tsakiyar dare zuwa ƙarfe 4 na dare.
    • Amfani da abin rufe fuska a ofisoshi da kasuwanni da kantina.
    • An haramta taron bukukuwa da wurin cashewa da dare a faɗin Legas

    Gwamnatin ta ce duk wanda ya saɓa dokokin za a rufe wurinsa kuma tare da cin shi tara.

    View more on twitter
  4. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin yunwa a Sudan ta Kudu

    Yunwa a Sudan ta kudu

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu a yankin Jonglei domin bayar da dama a shigar da kayan agaji ga mutane.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen yankin Pibor su ne suka fi fuskantar matsananciyar yunwa.

    Rikicin ne ya ƙara sa matsalar ta fi ƙamari da kuma annobar korona da ambaliyar ga kuma tabarbarewar tattalin arziki.

    Hukumomin sun ce mutum miliyan shida da rabi a Sudan ta Kudu na fuskantar matsanancin rashin abinci, ana kuma hasashen adadin zai iya karuwa a shekara mai zuwa

  5. Wani ya kai iyayensa kotu kan watsar masa da hotunan batsa

    Wani alƙalin kotun jihar Michigan ta Amurka ya yanke hukuncin cewa dole iyaye wani su biya shi diyya bayan sun zubar da ɗinbim hotunansa na batsa.

    David Werking mai shekara 42, ya dawo yana zama da iyayensa bayan aurensa ya mutu kuma daga baya ya nemi hotuna da fina-finansa na batsa ya rasa.

    Ya ce yawansu darajarsu ta kai dala 25,000kuma lauyansa ya ce ba za a iya “samunsu ba.”

    Iyayen sun gargaɗi Mista Werking kan shigowa da hotunan batsa amma alƙalin kotun ya ce matsayinsu na masu gida da suka ba shi haya, ba su da ƴancin watsar masa da kayansa da suke kyama.

  6. Gwamnati Legas ta gargaɗi masu gwajin korona na bogi

    Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu bayar da sakamakon gwajin korona na bogi.

    Sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na Twitter ta ce ta gano yadda wasu cibiyoyin gwaji ke haɗa baki da wasu suna bayar da sakamakon gwajin korona na bogi.

    Gwamnatin Legas ta ce za ta hukunta duk wanda ta kama tare da rufe cibiyar da ake gwajin.

    Legas ta ce jihar cutar korona ta fi yaɗuwa a Najeriya. Gwamnatin jihar ta ce ta fi kowace jiha yawan gwaji a Najeriya.

    View more on twitter
  7. Garba Shehu ya nemi afuwa kan cewa ɗalibai 10 aka sace

    Mai taimakawa shugaban Najeriya kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya nemi afuwa kan bayanin da ya bayar cewa ɗalibai 10 ne kawai aka sace a makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina.

    "Ina neman afuwa kan kuskuren bayanai da aka gabatar cewa dalibai 10 ne aka sace a makarantar kimiya ta Kankara.

    "Wani ne wanda ya kamata ace ya sani ya bayar da bayanan kan adadin ɗaliban. Adadin kuma yanzu ya ci karo da waɗanda aka gani.

    "Don Allah a fahimci cewa bayanan ba an bayar da su ba ne domin rage muhimmancin yanayin da aka shiga," in ji Garba Shehu.

    View more on twitter
  8. Motoci 1,000 sun maƙale a cikin dusar ƙanƙara a wani babban titi a Japan

    japan cars snow

    Masu aikin ceto suna ta ƙoƙarin tserar da fiye da motoci 1,000 da suka maƙale a kan wani babban titi tsawon kwana biyu bayan zubar dusar ƙanƙara a Japan.

    Hukumomi sun rarraba abinci da man fetur da barguna ga direbobin a kan titin na Kanetsu, wanda ya haɗa babban birnin ƙasar Tokyo da kuma Niigata da ke arewaci.

    Dusar ƙanƙarar da ta fara zuba ranar Laraba, ta jawo cushewar ababen hawa a kan titin.

    Lamarin ya sa fiye da gidaje 10,000 a arewa da yammacin ƙasar sun rasa wutar lantarki.

    Kafar yaɗa labarai ta Kyodo ta ruwaito cewa an samu cunkoso a ɓangarori daban-daban na babban titin Kanetsun.

    Cunkoson ya fara ne bayan da wata babbar mota ta maƙale a cikin dusar ƙanƙarar ranar Laraba da daddare.

    Wasu kafofin sun ce cunkoson ababen hawan ya kai har tsawon kilomita 16.5km a kan titin.

    Jami'ai sun yi ta amfani da na'urori da dama don ciro motocin da suka maƙale ɗaya bayan ɗaya, amma kusan motoci 1,000 har yanzu suna nan maƙale a kan titin har zuwa ranar Juma'a da rana.

  9. Habasha ta sa tukwicin $500,000 ga wanda ya ba da bayanin shugabannin an tawayen Tigray

    Shugaban Habasha

    Hukumomin Habasha sun sanya tukwicin dala dubu 500 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama shugabannin ‘yan tawayen yankin Tigray.

    Sun kuma fitar da wata lamba da za a kira domin bayar da bayanan.

    An bayar da umarnin kama shugabannin TPLF sama da 60, wadanda suke ta rikici da gwamnatin tarayya tun watan jiya.

    Babu dai wanda ya san ida shugabannin ‘yan tawayen suke, ko kafafen yada labarai ba sa samunsu sama da makonni biyu

  10. Buhari yana ganawa da ɗaliban Kankara a Katsina

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana ganawa da ɗaliban makarantar Kankara kwana ɗaya bayan sakinsu da ƴan bindiga suka yi.

    Shugaban na ganawa ne da ɗaliban a fadar gwamnatin Katsina.

    View more on facebook
  11. Ɗakin taron da Shugaba Buhari zai gana da ɗaliban Ƙanƙara da aka ceto

    ..

    Ana sa ran cewa a yau Juma'a Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da ɗaliban Ƙanƙara da aka ceto a jiya

    ..
  12. Wasu 'yan Najeriya na baƙin cikin ceto yaran Ƙanƙara – Hadimin Buhari

    ..

    Mai tamaka wa shugaban Najeriya kan harkokin sada zumunta, Bashir Ahmed, ya yi zargin cewa wasu daga cikin 'yan Najeriya ba su ji daɗin ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 da aka yi ba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce " a lokacin da aka sace yaran, wasu sun nuna farin cikinsu a fili, a yanzu kuma sun nuna baƙin cikinsu a fili bayan ceto su".

    Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa duka yaran 344 da aka ceto na cikin ƙoshin lafiya.

    A baya dai an ta samun bambancin adadin ɗaliban da aka sace, inda tun a farko aka ce sama da 600 aka sace.

  13. WHO ta sanar da odar riga-kafin korona biliyan biyu

    Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ta yi odar riga-kafin korona biliyan biyu da niyyar taimaka wa al'ummomi waɗanda suka fi fuskantar haɗari.

    Hukumar ta bayyana cewa za ta karɓi rukunin farko na riga-kafin a watannin ukun farko na shekara mai zuwa.

    Shirin WHO na COVAX na da niyyar tabbatar da cewa riga-kafin korona ya wadatu a faɗin duniya.

    A farkon makon nan ne jami'an WHO suka yi gargaɗin cewa kuɗin tallafin da hukumar za ta bai wa ƙasashe masu tasowa zai ragu sakamakon amfani da za a yi da su wurin sayen riga-kafin na korona.

  14. Harin bam ya kashe mutum 15 a Afghanistan

    Aƙalla mutum 15 suka mutu sakamakon wani bam da ya tashi a Afghanistan, akasarin waɗanda suka mutu yara ne.

    Ministan harkokin cikin gida na ƙasar ya bayyana cewa akwai wasu mutum 20 da suka samu rauni a lamarin da ya faru a lardin Ghazni.

    Bama-bamai ne da aka ɓoye a cikin mota suka fashe a kusa da wani wuri da ake taron karatun Al-Qur'ani.

    Babu wani tabbaci ko wurin taron ne maharan suka so su kai wa hari. Ana ta kai hare-hare a Afghanistan a 'yan kwanakin nan a daidai lokacin da ake sulhu tsakanin 'yan Taliban da gwamnatin ƙasar a Qatar.

  15. 'Yan bindiga sun kai wa Sarkin Ƙauran Namoda hari, sun kashe 'yan sanda uku da fadawa

    ..

    Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai wa tawagar Sarkin Ƙauran Namoda, Sanusi Muhammad Asha hari inda suka kashe 'yan sanda uku da wasu fadawa da ƙanin sarkin.

    Majiya daga gwamnatin Zamfara ta tabbatar mana da cewa lamarin ya faru ne a hanyar garin Funtua yayin da sarkin ke komawa Ƙauran Namoda daga Abuja.

    An kuma tabbatar wa BBC da cewa sarkin ya tsira daga harin ba tare da samun rauni ba.

    A bana aka naɗa Sanusi Muhammad Asha, mai shekara 40 a matsayin Sarkin Ƙauran Namoda bayan rasuwar mahaifinsa Muhammad Asha.

    Mun tuntuɓi rundunar 'yan sandan Zamfara domin jin ƙarin bayani kan lamarin, sai dai ba su ɗaga waya ba.

    A jiya ne dai aka ceto ɗaliban Ƙanƙara sama 344 daga dajin na Zamfara, bayan sun kwashe kwanaki a hannun 'yan bindiga.

  16. MINTI ƊAYA DA BBC - 18/12/2020 - LABARAN RANA

    Video content

    Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
  17. MDD na gargaɗin kan ƙara taɓarɓarewar rayuwar al'umma a Mozambique

    ..

    Majalisar Ɗinkin Duniya na gargaɗin ƙara taɓarɓarewar rayuwar bil'adama a arewacin Mozambique, wurin da masu iƙirarin jihadi suka tilasta wa dubu ɗaruruwan mutane barin gidajensu.

    Wata babbar jami'a daga hukumar MDD da ke kula da ƴan gudun hijira, Angele Dikongue-Atanga, ta bayyana cewa ta'addanci ne ya jawo akasarin matsalar da ake ciki a yankin.

    Amma a yayin wata ziyara da ta kai yankin Cabo Delgado, ta ce akwai rashin adalci a yankin wanda cibiya ce da ake samun iskar gas.

    Ana dai caccakar gwamnatin Mozambique kan ƙoƙarinta na daƙile wannan rikici, inda ake zarginta da take haƙƙin bil'adama.

  18. Amurka na daf da amincewa da samfari na biyu na riga-kafin korona

    ..

    Rahotanni daga Amurka na cewa ƙasar na daf da amincewa da samfari na biyu na riga-kafin annobar korona.

    Wani kwamiti na ƙwararru a ƙasar ya amince da riga-kafin na kamfanin Moderna inda suka ce amfanin da riga-kafin ke da shi ga matasa ƴan 18 zuwa sama ya fi illolinsa yawa.

    Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan an ƙaddamar da fara amfani da riga-kafin Pfizer/BioNTech a ƙasar.

    A yanzu dai, masana sun bayyana cewa riga-kafin na da inganci na kashi 94 cikin 100.

  19. Ethiopia za ta bayar da ladar dala 256.000 ga wanda ya taimaka aka gano jagororin Tigray

    ..

    Ministan tsaro na Ethiopia ya sanar da cewa ƙasar za ta ba da ladar dala 256,000 ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga kama shugabannin yankin Tigray.

    Laftanar Janar Asrat Denero ya shaida cewa za a bayar da wannan kyauta ne domin taimakawa a kama wadanda ake nema cikin gaggawa.

    A watan da ya gabata, an bayar da takardun sammaci ga sama da manyan shugabannin Tigray 60.

    Daga baya kuma an sake bayar da wasu takardun sammacin ga gwamman jami'an tsaro na ƙasar, masu ci a yanzu da waɗanda suka ajiye aiki.

  20. Ɗaliban Ƙanƙara da aka ceto sun isa Katsina

    .
    ..
    ..