Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Asuba ta gari

    Karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Manyan kwamandojin mu na goyon bayan karfafa wuraren da suke dakile hare-haren sojin Rasha - Zelensky

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce manyan kwamandojin sojojin Ukraine na goyon bayan karfafa wuraren da suke dakile haren haren sojoji Rasha, a garin Bakhmut da aka yi wa ƙawanya da ke gabashin ƙasar.

    Dakarun Rasha sun yi wa garin kofar rago ta bangarori uku tare da kai hare hare ta sama na tsawon watani.

    Sai dai sun kasa karya lagwon sojojin Ukraine duk da cewa rahotani sun ce watakila sojojin Ukaraine ɗin sun fara shirin janyewa daga garin.

    Wakilin BBC ya ce shugaba Zelensky ya gana da manyan kwamadojinsa kuma ofishinsa ya ce sun yi magana kan bukatar ganin cewa sun ci gaba da kare kasarsu.

    Masu sharhi sun ce garin Bakhmut ba shi da wani muhimmanci, amma ya kasance wurin da manyan kwamandojin Rasha su ke gwagwamayar ganin cewa sun isar da labari mai dadin ji ga fadar Kremlin.

  3. Saudiyya na shirin tallafa wa Turkiyya da $5bn

    Salman and Erdowan

    Saudiyya ta ce za ta saka dala biliyan biyar a babban bankin Turkiyya domin tallafa wa tattalin arzikin kasar.

    Sanarwar da Saudiyya ta ftar ta ce gudumuwar wata shaida ce kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

    A bara ne aka sasanta shugaba Rajib Dayyib Erdowan da yerima mai jiran gado sarautar Saudiyyar Mohammed Bin Salman bayan tsawon shekarun da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu.

    A shekarar 2018 aka kashe Jamal Khashogi a birnin Santabul wanda dan kasar Saudiyya ne kuma dan jarida mai sukar gwamnatin Saudiyyar wanda Tukiyya ta dora alhakin mutuwarsa akan shugabancin Saudiyya.

    Turkiyya na matukar bukatar tallafi bayan girgizar ƙasa da ta afkawa ƙasar a makon da ya gabata.

  4. Mashaƙo ta hallaka mutum 61 a Kano

    Mashaƙo

    Cutar mashaƙo ta hallaka mutum 61 a jihar Kano. Manajar kula da cutuka a jihar, Dakta Salma Suwaid ce ta bayyana waɗannan alkaluman a wani taro da cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya ta shirya.

    Dakta Suwaid ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kwantar da marasa lafiya 783 a asibitin, inda mata 360 da maza 423.

    Ta kuma jaddada bukatar ɗaukar matakan rigakafi cikin gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar.

    Ta ce barkewar cutar ta samo asali ne saboda ƙarancin allurar rigakafi a cikin al’ummomin da abin ya shafa, inda ta ce mutane da yawa ba su sami allurai da suka dace ba, wanda hakan ya sa suka kasance cikin haɗari na kamuwa da cutar.

    Dakta Suwaid ta ƙara da cewa akwai yiwuwar bullar cutar a Kano sakamakon ƙarancin allurar rigakafi.

    Cibiyar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta ba da fifiko ga kokarin samar da rigakafin cutar don hana ci gaba da yaduwa da ta ke yi.

  5. Rundunar sojin Najeriya ta soma bincike kan sojan da ya halaka kansa da abokan aikinsa

    .

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta soma gudanar da bincike bayan wani mummunan lamari da ya kai wani soja halaka kansa da abokan aikinsa a Rabbah da ke jihar Sokoto.

    Lamarin ya faru ne ranar Lahadi inda aka tura sojoji domin gudanar da aikin tsaro a yankin kuma a cewar rundunar, binciken zai bayar da damar sanin ainahin abin da ya faru.

    Wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar sojin, Onyema Nwachukwu ya sanyawa hannu ta ce ba a iya gano abin da ya kai shi ga yin aika-aikar ba saboda sojan ya kashe kansa bayan halaka abokan aikin nasa.

    Babban kwamandan rundunar ta takwas a rundunar sojin Najeriya wanda kuma shi ne kwamandan rundunar Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut da wasu manyan jami'an soji sun kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda ya mika sakon ta'aziyya kan mutuwar sojojin.

    Ya kuma bukace su da su zama masu kulawa da junansu sannan su kai rahoton duk wani abin zargi da suka lura a tare da abokan aikinsu domin kare afkuwar irin haka a gaba.

    Kwamandan ya nemi su kwantar da hankalinsu su kuma dukufa wajen gudanar da ayyukansu.

  6. Ana ci gaba da fuskantar ƙarancin man fetur a sassan Najeriya da dama

    Ibrahim Isa, BBC Hausa

    Petrol Scarcity

    A Najeriya, 'yan ƙasar na ci gaba da nuna takaicinsu dangane da matsalar ƙarancin mai da ta ki ta ki cinyewa a sassa da dama, ciki har da Abuja, babban birnin ƙasar.

    Mahukunta na danganta matsalar da dakatar da zirga-zirga da aka yi a lokacin zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala a makon jiya.

    Amma wasu kungiyoyin farar-hula na zargin cewa matsalar cin hanci da sakacin gwamnati ne suka haddasa matsalar.

    Gwamnati dai ta daɗe tana alwashin magance matsalar amma babu abin da ya sauya a birane da kauyakun ƙasar.

    Abin da ke ɗaure kan `yan ƙasar game da wannan ƙarancin man shi ne iƙirarin da gwamnatin ke yi cewa a kowane wata tana kashe naira biliyan ɗari huɗu a kan tallafin man fetur.

    Amma Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar da ke yaki da rashawa ta Transparency International a Najeriya ya yi zargin akwai rashin gaskiya a cikin lamarin saboda wasu ne ke sama da faɗi da dukiyar kasa kuma an kasa hukuntasu.

    Sai dai hukumar da ke kula da sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur ta Najeriya, cikin wata sanarwar da ta fitar ta ce dakatar da zirga-zirgar da aka yi a lokacin zaben shugaban kasa da aka kamala a makon jiya, shi ne babban dalilin da ya janyo jinkirin wajen kai man wasu sassan kasar.

    Amma masanin ya ce wannan ba hujja bane saboda tun kafin lokacin zaɓe ake samun matsalar ƙarancin man fetur.

    Gwamnatin shugaba Buhari dai na tutiya da dokar man da aka zartar a zamaninta, tana saka dokar a cikin gadon da za ta bar wa `yan Najeriya, amma masu lura da al`amura na cewa wannan matsala ta rashin man fetur idan ba a magance ta ba, tana iya dusashe nasarori da dama da gwamnatin ke alfahari ta samu.

  7. Gwamnatin Yobe ta ɗage haramcin hawa babura a wasu yankunan jihar bayan shekara 11

    Okada Riders

    Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya sanar da ɗage haramcin amfani da babura a faɗin ƙananan hukumomi bakwai na jihar.

    Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam ya fitar wadda kuma aka raba wa manema labarai a Damaturu a yau Litinin.

    A cewarsa, baburan za su yi aiki daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a kowace rana. Ya ce baburan ba za su ɗauki mutum fiye da ɗaya ba ko yin achaba.

    Ya kuma yi kira ga dukkan waɗanda ke da babura a ƙananan hukumomin da abin ya shafa, da su tabbatar da cewa sun yi musu rajista.

    Gwamnatin jihar ta kuma bai wa masu baburan umarnin cewa su yi aiki a iya ƙananan hukumomi da suke ba tare da shiga wasu wurare ba, inda ta ce duk wanda aka samu da laifin take umarnin, zai fuskanci hukuncin da ya kamata.

    A shekara ta 2012 ne dai lokacin gwamnatin Ibrahim Gaidam, aka sanya haramci kan amfani da babura a faɗin jihar ko achaba da nufin dakile yunkurin amfani da su wajen aikata muggan ayyuka, musamman lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a jihar.

    Sai dai gwamna Mai Mala Buni ya ɗage haramcin a kan wasu ƙananan hukumomi 10 cikin 17 na jihar a watan Janairun 2022.

  8. Tanzania ta haramta wa yara 'yan ƙasa da shekara 10 zuwa makarantun kwana

    Gwamnatin Tanzania ta haramta wa yara 'yan ƙasa da shekara 10 zuwa makarantun kwana musamman ma na firamare, inda ta ce tayi haka ne don bai wa yaran damar kasancewa da iyayensu - domin su ƙara sanin al'adunsu da kuma tsare-tsare na ƙasar.

    Kwamishinan harkokin ilimi na ƙasar, Lyabwene Mtahabwa, ta ce kulawar da ake bai wa yaran da basu haura shekara 10 ba irin na makarantun kwana, za ta kawo karshe a watan hudu, inda yta ce za su ci gaba da zuwa na jeka-ka-dawo har sai sun kai wani mataki na gaba.

    Sai dai, ta ce za a iya yi wa yaran da iyayensu suka karɓi dama ta musamman da za ta hana umarnin ya shafe su.

    Ms Mtahabwa ta ce duk makarantar da aka samu ta karya wannan umarni, za ta fuskanci hukunci.

    Makarantun kwana sun kasance sanannu a faɗin Tanzania, inda gwamnati da mutane masu zaman kansu ke da irin waɗannan makarantu.

    Yawancin makarantu da abin da zai shafa za su kasance masu zaman kansu, saboda ba kowace makarantar firamare mallakin gwamnati ke karɓar yara a makarantunsu ba.

  9. Ƙasashen Yamma ne suka hana Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zaman lafiya - Touadéra

    Faustin-Archange Touadéra

    Shugaban ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya zargi ƙasashen yamma da hana ƙasarsa zaman lafiya da gangan, kwanaki kaɗan bayan ganawarsa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron.

    Shugaba Touadéra ya ce ƙasar ta fuskanci wahalhalu daban-daban tun samun yancin kai kama daga satar kuɗin ƙasar da ƙasashen yamma suka yi sanadiyar rashin tsayayyar gwamnati ko kuma amfani da kamfanoninsu wajen taimaka wa kungiyoyin ta da ƙayar-baya wanda yawancin jagororinsu suka ƙasance daga waje.

    An zargi dakarun ƙasar da wasu sojojin haya na kungiyar Wagner daga Rasha da ta ke hakkin ɗan adam, wanda ya janyo Tarayyar Turai ta saka wa wasu manyan jami'an kungiyar takunkumi.

    A taron MDD da ake gudanarwa a Qatar, shugaban ya ce ƙasashen yamma sun mayar da ƙasarsa wurin tasa na albarkatun ƙasa, inda ya ce hakan ya sanya ƙasar da kuma wasu rashin dogaro da kai da kuma samun zaman lafiya mai ɗorewa.

  10. 'Yan siyasa na shirin amfani da 'yan banga don tayar da hargitsi a zaɓen gwamnoni a Kano'

    Kano Police to prosecute thugs

    Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta samu bayanai da ke nuna cewa wasu 'yan siyasa na shirin shigo da 'yan bangar siyasa zuwa jihar domin tayar da hatsaniya a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki da ke tafe.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mamman Dauda shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, inda ya ce 'yan siyasa da ke ganin za su fadi, tuni suka shirya tayar da tarzoma a zaɓen da ke tafe a ranar Asabar.

    Sai dai, Mamman Dauda, ya gargaɗi dukkan 'yan bangar siyasa da wasu ɓata gari cewa kada su kuskura su ta da fitina saboda a shirye 'yan sanda suke wajen hukunta duk wanda aka kama da laifi.

    CP Dauda ya kuma ce rundunar tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro a jihar za su tabbatar da cewa an kama dukkan waɗanda ake zargi, inda ya ce duk ɗan bangar siyasa da aka kama, za a tura shi zuwa kotu tare da waɗanda suka saka su aikin.

  11. Kotu ta ba da belin Alhassan Ado Doguwa

    Kotu

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano, ta bayar da belin Alhassan Ado Duguwa.

    Kakakin kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce hakan ya dace da tsarin shari'a, amma za a ci gaba da sauraron shari'ar zargin kisan kai da ake yi masa.

    Ya ce Kotun ta kalubalanci rundunar 'yan sanda saboda kai Alhassan Doguwa gabanta saboda ba ta da hurumin sauraron irin laifin da ake tuhumarsa da shi.

    Yan sandan dai na kuma zargin sa da hannu a harbin wasu mutane da bindiga kwana ɗaya bayan kammala jefa ƙuri'a a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudun wada a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya.

    Ana kuma tuhumar ɗan majalisar da laifin kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu guda takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.

    Kotun tarayyar ta bayar da belinsa bisa wasu sharuɗa ciki har da gabatar da manyan sakatarori biyu waɗanda suke aiki a gwamnatin jiha da sarki mai daraja ta ɗaya da kuma ajiye fasfo ɗin sa a kotun.

    Mai shari’a Muhammad Yunusa na babbar kotun tarayyar ya ɗage zaman zuwa ranar 22 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

    A gobe ne aka tsara komawa gaban kotun majisteret ɗin da ta tura shi zuwa gidan yari, don a saurari shawarar da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano za ta gabatar game da batun.

  12. Hukumar kula da kafofin yaɗa labaran Najeriya ta haramta sanya batutuwan addini da na ƙabilanci a shirye-shiryen siyasa

    NBC

    Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Najeriya ta ce ta lura da yadda ake sanya abubuwan da suka shafi addini da ƙabilanci da kuma kalaman tunzura jama'a a shirye-shiryen siyasa da yaƙin neman zaɓe a yayin da ake fuskantar zaɓen gwamnoni a ƙasar.

    A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce yin hakan ba zai zame wa ƙasar alkairi ba.

    Hukumar ta ce doka ta tanadar da cewa dole kafofin yaɗa labarai su taimaka wajen jaddada hadin kan ƙasa tare da taimaka wa wajen inganta dimokradiyya.

    Haka kuma sanarwar ta yi kira ga kafofin yaɗa labaran ƙasar da su yi amfani da kafofin nasu wajen daƙile wannan aƙida, da kuma kalaman tunzura jama'a da za su iya kawo barazana ga haɗin kai da dimokraɗiyyar ƙasar.

    A cewar sanawar duk da cewa ana ƙarfafa wa kafofin yaɗa labarai gwiwwa wajen bai wa 'yan ƙasa damar bayyana ra'ayoyinsu, waɗanda ba kalaman ƙiyayya ko na cin zarafin juna ko na tunzura jama'a ba, ya kamata kafofin yaɗa labaran su san cewa za su yi hakan ne kawai ta hanyar da ta dace.

  13. Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP a zamfara

    Dauda Lawan Dare

    Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da Dauda Lawan Dare a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP qa jihar Zamfara.

    Hukuncin kotun na zuwa ne kawana hudu kafin zaɓen gwamnonin jihohin ƙasar da za a gudanar ranar 11 ga watan Maris.

    A hukuncin da suke yanke alƙalan kotun biyar ƙarƙashin jagoranci alƙalan mai shari'a Adamu Jauro, duka sun amince da yin watsi da ɗaukaka ƙarar da Dakta Ibrahim Gusau ya shigar gabanta yana ƙalubalantar takarar dauda.

    Kotun ta ce ta amince da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ke Sokoto ta yi ranar 6 ga watan Janairun da muke ciki, wanda ya amince da zaɓen fitar da gwani na biyu da aka yi wanda a shi ne Dauda Lawan ya yi nasara.

    A zaɓen Dauda Lawan ya samu nasara da ƙuri'a 442 a kan abokan takarar tasa.

  14. 'Yan sanda sun tsare malamar makarantar kan zargin neman jinsi a Uganda

    'Yan sanda a Uganda suna tsare da wata malamar makaranta tare da wata ƙawarta saboda zargin alaƙar neman jinsi a birnin Jinja da ke gabashin ƙasar.

    A ƙarƙashin dokokin Uganda laifi ne neman jinsi, kuma a baya-bayan nan majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wani ƙuduri da ya jaddada haramcin neman jinsi a ƙasar.

    A ranar Juma'a ne iyayen ɗalibai suka yi wa wata makarantar 'yan mata a ƙasar ƙawanya, domin cire 'ya'yansu daga makarantar sakamakon zarge-zargen yaɗa aƙidar neman jinsi ɗaya da aka riƙa yi wa malamar a shafukan sada zumunta.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yankin Kiira James Mubi ya shaida wa BBC cewa suna gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa malamar.

    Ƙawar tata mai shekara 30, ba ɗalibar makarantar ba ce kuma ba ma'aikaciyar makarantar ba ce.

    Ya ƙara da cewa ba su samu ƙorafi daga ɗaliban makarantar ba kan yunƙurin malamar na nemansu, to amma ya ce ya zama wajibi su ci gaba da riƙe ta tare da ƙawar tata har zuwa lokacin da za su kammala bincike.

    Fiye da mako guda kenan babbar kotun musuluncin ƙasar ta yi kira ga musulman Jinja da kewaye da su yi zanga-zanga kan abin da suka kira yunƙurin yaɗa aƙidar auren jinsi a ƙasar.

  15. An samu haɗuran babur 377 a shekara guda a Gombe – FRSC

    jami'an kiyaye haɗura

    Hukumar kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya ta ce an samu haɗuran babur 377 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022 a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    A tatatunawarsa da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, babban jami'in hukumar mai lura da jihar Gombe Mista Felix Theman ya ce alƙaluman haduran sun nuna cewa an samu haɗuran babur da na babura masu ƙafa uku a birnin Gombe kimanin 377.

    Theman ya ce laifi ne yara masu ƙananan shekaru su riƙa hawa ababen hawa ''kuma mun ɗauki matakai domin magance wannan matsala''.

    “Mun samu rahotonnin ƙananan yara masu hawa babur da shekarunsu ba su kai shekaru 18 da doka ta tanadar kafin yaro ya hau abin hawa, iyayensu na barinsu suna yin tuƙin ganganci a kan tituna, lamarin da ke janyo haɗura, musamman a cikin gari''.

    “Mun ƙara haɓaka ayyukanmu ta yadda muka buɗe kotunan tafi-da-gidanka ta hanyar haɗin gwiwwa da ɓangaren shari'ar jihar'', in ji shi.

    Theman ya ce sun kama mutane da dama musamman ƙananan yara da laifin tuƙin ganganci a jihar.

    Daga ƙarshe ya gargaɗi iyayen yara da su sanya ido kan 'ya'yansu musamman kan aikata laifukan da suka saɓa wa dokokin titi.