Abdulkadir Balarabe Musa: Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya rasu

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, An tsige Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa daga kujerar gwamnan Kaduna a 1981

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna da ke Najeriya Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu.

Ya rasu ne a birnin Kaduna yana da shekara 84 a duniya.

Ɗaya daga cikin 'ya'yansa ya tabbatar wa BBC da wannan labari.

Za a yi jana'izarsa da misalin karfe hudu a agogon Najeriya a masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna.

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa - wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar ta Kaduna - ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Marigayin na cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokradiyya.

Ya zama gwamna ne 1979 a karkashin jam'iyyar PRP, ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa'adinsa.

Amma duk da haka ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra'ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya.

A wata hira da ya taba yi da BBC Hausa, marigayi Balarabe Musa ya ce naira 741,000 ake biyansa a matsayin fansho a kowane wata.

Kauce wa Twitter, 1
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

A shekarar 2003 Abdulkadir Balarabe Musa ya tsaya takarar shugaban Najeriya a karkashin jam'iyyar PRP.

Yadda ake alhinin rasuwarsa

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu manyan mutane suka soma bayyana alhininsu kan rasuwar fitaccen an siyasar.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya ambato shugaban kasar yana jinjina wa marigayin inda ya ce 'yan Najeriya za su yi rashin mutumin da ya yi "aiki tukuru wajen ganin an rika jin duriyar marasa karfi."

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamna El-Rufai, ya ce za a tuna Alhaji Balarabe Musa a matsayin "dan siyasa mai son ci gaba wanda ya yi kokarin inganta rayuwar marasa galihu."

Kauce wa Twitter, 2
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Daya daga 'ya'yan jam'iyyar PRP, Sanata Shehu Sani, wanda ya tsaya takarar dan majalisar dattawan Najeriya a jam'iyyar a 2019, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon gwamnan.

Kauce wa Twitter, 3
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3