Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan mun sha ruwa lafiya tare da fatan mu yi sahur lafiya daga nan BBC.

  2. Bazoum ya naɗa sabon hafsan sojojin Nijar

    Bazoum Twitter

    Shugaban Nijar, Muhammad Bazoum ya naɗa sabon babban hafsan dakarun sojin ƙasar, daidai lokacin da Nijar ke fafutukar murƙushe ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

    Kawo yanzu, gwamnati ba ta yi bayani a kan dalilan maye gurbin Janar Salifou Mody da Janar Abdou Sidikou Issa ba, wanda a baya ya riƙe manyan muƙamai a ɓangaren na sojoji.

    Akwai ƙungiyoyi da dama na masu iƙirarin jihadi a Nijar ciki har da Boko Haram wadda ta samo asali daga Najeriya mai maƙwabtaka.

    Mali da Nijar sun amince a farkon watan nan su yi aiki tare domin murƙushe ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS.

    ActuNIger
  3. Iran na shirin tabbatar da kafa dokar tilasta sa hijabi

    BBC

    Hukumomi a Iran na yunƙurin kafa dokar tilasta wa mata sanya hijabi.

    Wannan mataki na zuwa ne watanni bayan zanga-zangar da aka gudanar ta neman a kawo ƙarshen irin wannan mataki.

    Masu ra'ayin riƙau a majalisar Iran ne suka yi kira ga kotu ta ɗauki matakin hukunci a kan matan da suka karya dokar sanya hijabi nan da kwana biyu.

    An kawo ƙarshen zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar ne cikin watan Satumba ga masu nuna turjiya ga dokar ta hanyar amfani da ƙarfi.

    Amma har yanzu wasu matan na karya dokar wajibta sa hijabin a bainar jama'a.

    Hotuna da bidiyoyi da ake wallafawa a shafukan sada zumunta na nuna tsananin ɓacin rai da ke ci gaba da ruruwa a zukatan mafi yawan Iraniyawa.

  4. Pakistan ta sanar da kashe dakarunta hudu a kan iyaka da Iran

    AFP

    Pakistan ta ce sojojin sa-kai a Iran sun kashe dakarunta da ke aikin ceto a kan iyaka, a wani hari da aka kai musu cikin yankin kudu maso yammacin ƙasar.

    Wata sanarwa da rundunar sojin Pakistan ta fitar, ta ce hukumomin Pakistan na tattaunawa da takwarorinsu na Iran don kare faruwar irin wannan lamari a gaba.

    Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi awon gaba da makaman dakarun tsaron kan iyakar na Pakistan.

    Babu dai wata ƙungiya da ta auki alhakin kai wannan hari ya zuwa yanzu.

  5. Shugaba Ruto ya yi magana kan zanga-zangar da 'yan adawa ke yi a Kenya

    BBC

    Shugaban Kenya, William Ruto, ya yi magana a kan rayukan da aka kashe da kuma dukiyoyin da aka lalata sakamakon zanga-zangar siyasa - da aka shirya ranar Alhamis, karo na uku kenan.

    A cewar jaridar Daily Nation ta ƙasar, babu shakka tsarin mulkin Kenya ya ba da damar a gudanar da zanga-zanga don nuna ra'ayi, in ji Shugaba Ruto amma hakan bai zama hujja ta kashe rayuka ba.

    Duk da cewa 'yancinku ne, amma bai kamata a hana mutane gudanar da kasuwancinsu ba, ko kuma su kawo tangarɗa ga harkokin ilimi a cewar shugaban.

    Tsarin mulki ya yarda a samu mabaMbantan ra'ayi, amma bai amince da asarar rayuwa ba.

    Ya kamata mu yi farin ciki da 'yancin da aka ba mu cikin tsarin mulki, a mutunta wasu mutanen kada a lalata dukiyoyinsu.

    Shugaban ya ce kada wani yaro ya sake zuwa makaranta matuƙar ana gudanar da zanga-zangar.

    An kashe 'yan Kenya da dama ciki har da 'yan sanda a yayin zanga-zangar, an kuma sace kayayyaki a shaguna da yawa.

  6. Ukraine ta zargi shugaban cocin Orthodox da goyon bayan Rasha

    BBC

    Jami'ai a Ukraine sun binciki gidan shugaban cocin Orthodox da ke Kyiv, bayan zargin da aka yi masa na goyon bayan dakarun Rasha da suka mamaye ƙasar.

    Pavel Lebed ne yake shugabantar cocin mafi muhimmanci a ƙasar ta Ukraine.

    A shekarun baya, sanannen abu ne cewa reshen wannan coci yana da kyakkyawar alaƙa da malaman Moscow.

    Masu gabatar da ƙara a Kyiv sun ce ana zarginsa da ingiza mutane da kuma haifar da gaba ta addini.

    Hukumomin Kyiv na ƙoƙarin fitar da shi daga cikin cocin mai muhimmanci tare da mabiyansa.

    Lokacin da ya bayyana a gaban kotu ranar Asabar, babban limamin cocin ya ce shari'ar cike take da siyasa, kuma a cewarsa "bai taba nuna goyon baya ga masu mamaye ba - duk da yake bai ambaci sunan Rasha ba.

    BBC
  7. Jami'an fasa ƙwauri sun kama kwantena 27 a jihar Rivers

    ss

    Jami'an hukumar hana fasa-ƙwauri ta Najeriya reshen jihar River a kudu maso kudancin Najeriya sun kama wasu Kwantena 27 kan zargin saɓa ƙa'ida wajen shigar da su cikin ƙasar.

    Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar jihar Baba Imam ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a garin Onne na jihar Rivers.

    Imam ya ce an kama kwantenonin ne bisa laifukan da suka shafi yin ƙarya a takardun mallakarsu, da rashin cikakkun takardu, da rashin samun takardar izini daga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasar NAFDAC, da kuma sauran laifuka.

    Babban jami'in ya ce hukumar tasa ta kama kwantenonin ne cikin wata uku da suka gabata.

    Ya kuma tabbatar wa 'yan ƙasar cewa rundunarsu da ke aiki a Rivers ƙarƙashin za ta ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da kare lafiya da hana shigar da kayayyaki cikin ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

  8. Ra'ayi Riga :Sauƙin ƙarancin takardun kuɗi

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  9. Man City ta casa Liverpool da ci 4-1

    Man City

    Manchester City ta casa Liverpool da ci 4-1 ranar Asabar da rana a filin wasa na Etihad, duk da rashin zaƙaƙurin ɗan wasanta na gaba Erling Haaland.

    Haaland - wanda ya ci wa Man City ƙwallo 42 a kakar wasa ta bana - yana fama da rashin lafiya.

    Sai dai, duk da haka ƙungiyar ta nuna irin ƙarfin da take da shi bayan ta farke ƙwallon da Liverpool ta fara jefa mata a raga.

    A cikin minti na 17 da take wasa, Liverpool zura wa City ƙwallo ta hannun Mo Sallah.

    To amma a minti na 27, Julian Alvarez - wanda ya fara wasan a madadin Erling Haaland - ya farke wa City, bayan Jack Grealish ya bugo ƙwallon ta gefe.

    A cikin daƙiƙa 53 bayan komawa hutun rabin lokaci ne kuma, Kevin De Bruyne ya zura ƙwallo ta biyu, lokacin da Mahrez ya tura masa ƙwallo

    Ana minti na 53 kuma, Ikay Gündogan ya ƙara ta uku, bayan ya tsinci wani ƙwallo da Alvarez ya buga a da'irar yadi na 18.

    Kafin daga bisani Jack Grealish - wanda ya kasance gwarzon ɗan wasa a karawar - ya zura tasa ƙwallon bayan Kevin De Bruyne ya gara masa bal.

  10. Gane Mini Hanya: Hira da Rabi'u Kwankwaso

    Ɗaya daga cikin'yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 25 ga watan Fabrairu da ya wuce a Najeriya, ya ce jam'iyyarsa ta NNPP ta yi rawar gani a zaɓen duk da yake, shi ne ya zo na huɗu a cikin abokan takararsa.

    Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce sakamakon zaɓen zai bai wa jam'iyyarsa damar amfani da darussan da ta koya a zaɓen da kuma gyara kura-kuren da ta yi.

    Kuma kamar yadda za ku ji a cikin wannan hira ta musamman da Yusuf Ibrahim Yakasai, Rabiu Kwankwaso ya ce, da NNPP ta samu jajirtattun shugabanni a jihohin ƙasar, da ta samu nasara irin wadda ta cimma a Kano, wato mahaifarsa.

    Sai dai Yusuf Yakasai ɗin ya fara da tambayar Kwankwaso kan yadda ya kalli zaɓen.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  11. Rasha ta karɓi shugabancin kwamitin tsaro na MDD

    Rasha

    Rasha ta karɓi shugabancin kwamitin taro na Majalisar Ɗinkin Duniya duk da ƙoƙarin Ukraine na ganin hakan bai tabbata ba.

    Duka mambobin kwamitin 15 sukan jagoranci kwamitin tsawon wata guda a wani tsarin shugabancin kwamitin na karɓa-karɓa.

    Rabon da Rasha ta jagoranci kwamitin tun a watan Fabrairun 2022, lokacin da ta ƙaddamar da mamaya a Ukraine.

    Hakan na nufin a yanzu kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya na ƙarƙashin jagorancin ƙasar da shugabanta ke fuskantar yiwuwar kamu kan zargin laifukan da suka shafi yaƙi.

    A watan jiya ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wadda ba a ƙarƙashin Majalisar Dinkin Duniya take ba - ta ba da sammacin kama shugaban Rasha Vladimir Putin.

    Duk da ƙorafin da Ukraine ta yi, Amurka ta ce ba za ta iya hana Rasha - wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin tsaron - ɗarewa kan shugabancinsa ba.

    Sauran ƙasashen da suke da kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun haɗar da Birtaniya da Amurka da Faransa da kuma China.

  12. DSS ta kama jagoran Igbo da ya yi barazanar kai IPOB Legas

    IPOB

    Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Najeriya sun kama jagoran ƙabilar Igbo mazauna rukunin gidajen Ajao a Legas, kudu maso yammacin Najeriya.

    Fredrick Nwajagu ya yi barazanar gayyatar 'yan kungiyar a-ware ta IPOB zuwa Legas don ƙwato wa al'ummar Igbo kadarorinsu a jihar.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa, an kama jagoran Igbo ne da safiyar Asabar a wani samamen haɗin gwiwa tsakanin jami'an DSS da 'yan sanda.

    bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun nemi kama shi a fadarsa, amma sai ya gudu, inda suka riƙa bin sawu har suka kama shi a wani otal.

    A ranar Juma'a ne, Mista Nwajagu mai shekara 49 ya yi barazanar gayyatar 'yan a-waren IPOB zuwa jihar Legas domin kare 'yan ƙabilar Igbo mazauna jihar daga hare-haren da ya ce ana kai musu.

  13. NBC ta ci tarar Channels TV naira miliyan biyar

    s

    Hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin a Najeriya (NBC) ta ci tarar gidan talbijin na Channels, naira miliyan biyar saboda saɓa doƙar yaɗa labarai a wata hira da ya yi da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour a zaɓen da ya wuce.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar wato NAN ya ruwaito cewa matakin na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da shugaban hukumar ta NBC, Balarabe Shehu Illelah ya sanya wa hannu, kuma aka aika wa gidan talbijin ɗin.

    Hukumar ta ce ta yi nazarin hirar da Channels ɗin ya yi da Datka Datti Baba-Ahmed ranar Laraba 22 ga watan Maris.

    ''A cikin hirar, Datti ya ce saɓa wa tsarin mulkin Najeriya ne, a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu saboda kura-kuran da ya ce an samu a zaɓen watan Fabrairu'', kamar yadda yake ƙunshe a wasiƙar.

    Ya ƙara da cewa hirar, za ta iya tunzura jama'a tare da kawo hargitsi a ƙasar, don haka a cewar hukumar, ta saɓa wa dokokin yaɗa labarai.

    lllelah ya ci gaba da cewa a lokuta da dama, hukumarsa ta sha faɗa wa gidan talbijin ɗin ya riƙa la'akari da zaman lafiyar Najeriya, kafin yaɗa kowanne irin shiri.

    Don haka ya ce hukumar ta sanya wa gidan talbijin ɗin tarar naira miliyan biyar a kan wannan saɓa ƙa'ida, tare da gargaɗin Channels TV ya kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba.

  14. Shin kun san hantara na janyo tsumburewar yaro?

    Shirin namu na wannan mako ya duba batun tsumburewar yara,

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce matsalar tsumburewa tana shafar miliyoyin yara. A cewarta, yara kimanin miliyan 162 ne ke fama da wannan matsala a faɗin duniya.

    To sai dai, matsalar ta fi ƙamari a nahiyar Afirka da yankin Latin da Karebiyan

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  15. Abba Gida-gida ya shawarci masu bai wa gwamnatin Kano bashi su dakata

    Abba Gida-gida

    Zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi a wannan lokaci, su dakata.

    A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan mai jiran gado ya shawarci masu ba da bashi na cikin gida da na ƙetare ga gwamnatin Kano mai barin gado, su dakatar da hakan daga 18 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Mayu.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa sabuwar gwamnatin ba za ta yi la'akari da bashin da jihar ta karɓa ba, matuƙar ba a sanar da ita game da hakan ba.

    Ta kuma ce masu bin gwamnatin jihar bashi, su kwan da sanin cewa za a sake nazarin ƙa'idojin bashin da suka bai wa gwamnati mai barin gado, bayan kammala bincike a kan duk bashin da ake bin Kano.

    A tsakiyar wannan mako ma, zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar da irin wannan sanarwa da ya ce shawara ce ga masu gine-gine a filayen gwamantin jihar, inda ya nemi su dakata.

    Sai dai, washe gari da fitar da shawarar, gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani, yana cewa ya kamata gwamnan mai jiran gado ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara.

    A sanarwar da ya fitar, kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi, tamkar ba da umarni ne a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, a daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu ke da cikakken iko.

    Lamarin da ka iya zama riga mallam masallaci.

  16. Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta yi Allah-wadai da masu shirin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya

    Tambuwal

    Ƙungiyar gwamnoni ta Najeriya ta yi Allah-wadai cikin kakkausar murya ga masu yunƙurin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, maimakon rantsar da shugabannin da aka zaɓa a ƙasar.

    A wata sanarwa da ta fitar da sa hannun shugabanta, kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ƙungiyar ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin kare martabar dimokraɗiyyar Najeriya.

    Haka kuma, ƙungiyar ta ce ba za ta goyi bayan duk wani abu da ya saɓa wa tsarin mulkin ƙasar ba.

    Gwamnonin sun ce fitar da sanarwar cewa akwai masu yunƙurin kafa gwamnatin riƙo, ba tare da sanar sunayen masu maƙarƙashiyar ba, abu ne da zai iya haifar da ruɗani da fargaba a ƙasar.

    Don haka gwamnonin suka yi kira ga hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta gaggauta kamawa tare da gurfanar da mutanen da ke da hannu a yunkurin kafa gwamnatin riƙo a gaban kotu.

    Ƙungiyar ta kuma taya mambobinta da aka sake zaɓa a karo na biyu, murna.

    Tana cewa duk da kura-kuran da aka samu a zaɓukan da suka gabata, ƙungiyar ta yi alƙawarin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don inganta dimokraɗiyya da harkokin zaɓen ƙasar.

  17. TUC ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan cire tallafin man fetur

    Fetur

    Ƙungiyar ƙwadogo ta TUC a Najeriya ta gargaɗi gwammatin tarayya ta guji janye tallafin man fetur, a daidai wannan lokaci da ta ce talakawan ƙasar na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.

    Ƙungiyar na ganin matuƙar gwamnati ta janye tallafin man fetur, to hakan zai ƙara wa jama'ar ƙasar ɗumbin wahalhalu da kuma matsin rayuwa.

    Abin da kuma ita ƙungiyar ta TUC ke cewa ba za ta amince da shi ba.

    A tattaunawarsa da BBC, mai magana da yawun ƙungiyar, Kwamared Nuhu Toro ya ce babu yadda za a yi, a cire tallafin man ba tare da an zauna an tattauna batun tsakanin masu ruwa da tsaki ba.

    Ya ce matuƙar aka cire tallafin, to farshin man fetur zai yi tashin gwauron zabo, abin da kuma zai shafi farashin sauran kayan masarufi da buƙatun rayuwa a ƙasar.

    Kwamared Toro ya ce cire tallafin man fetur, ba shi ne mafita wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya ba a yanzu.

    Ga yadda tattaunawarsa da wakilinmu Abdulsalam Ibrahim Ahmed ta kasance

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron hirar
  18. Mahaukaciyar guguwa na ci gaba da ɓarna a Amurka

    US Tonadoes

    Mahaukaciyar guguwa ta ɗaiɗaita wasu jihohin kudancin Amurka da tsakiyar ƙasar, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin kai tallafi.

    Ana ta aikin kwashe tarkace da ɓaraguzan gine-gine da suka ruguje a Little Rock, babban birnin jihar Arkansas.

    Gwamnar jihar Sarah Huckabee ta ce mahukunta sun haɗa karfi-da-ƙarfe tun farkon fara guguwar don taƙaita yawan ɓarnarta.

    Ta kuma ce an ba da umarnin a fitar da kuɗaɗe daga asusun kar-ta-kwana don aukuwar wani bala'i kamar wannan a taimaka wa mutane.

  19. Kamala Haris ta buƙaci ƙasashen duniya su yafe wa Zambiya bashi

    Kamala Harris

    Mataimakaiyar shugaban Amurka Kamala Harris, ta yi kira ga masu bin Zambiya bashi su sassauta mata, ta hanyar yafewa ko rage kuɗin da suke bin ƙasar, musamman bashin da Zambiya ta gaza biya a lokacin annobar korona.

    Da take jawabi a birnin Lusaka na Zambiya, cikin rana ta ƙarshe a rangadin da ta shafe kusan mako guda tana yi a nahiyar Afirka, Kamala Harrris ta ce Zambiya ta ɗauki matakai don farfaɗo da tattalin arziƙinta.

    Kuma a yanzu buƙatarta, ita ce ƙasashen duniya su tallafa mata.

    China ce ƙasar da ke kan gaba wajen bin Zambiya ɗumbin basuka, amma Misis Harris ta ce ba wai tana katsalandan a kan tasirin da China ke da shi a Zambiya ba ne, abin da take yi, ƙoƙari ne kawai na inganta alaƙa tsakanin Amurka da ƙasar ta Afirka.

    A baya dai, ita ma China ta sha kira ga manyan cibiyoyin kuɗi da IMF da Bankin Duniya su rage wa zambiya raɗaɗin matsin tattalin arziƙi, kuma su yafe mata wani kaso na basukan da suke binta.