Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma yanzu a madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Buhari ya aike da saƙon ta'aziyya ga Shaykh Sharif Saleh

    BUHARI

    Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh al-Hussaini, shugaban kwamitin Fatwa na kwamitin ƙoli na addinin musulunci, wanda aka fi sani da Shaykh Sharif Saleh, kan rasuwar babban ɗansa Alhaji Musa Alkasim.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya aike da saƙon ta'aziyarsa da shehin malamin da gwamnati da kuma ilahirin al'umma jihar Borno, kan rasuwar Alhaji Musa Alkasim.

    Shugaba Buhari ya ce ya 'kaɗu' da jin labarin rasuwar Alhaji Musa wanda ya bayyana a matsayin wata ''majingina'' ga shehin malamin.

    Buhari ya bayyana marigayi Alhaji Musa Alkasim mai shekara 59 a matsayin mutum mai halin dattako wanda za a daɗe ba manta da shi ba.

    Daga ƙarshe ya yi addu'ar neman gafara a gare shi , tare da bai wa iyalansa da al'ummar Borno haƙurin jure rashinsa.

  3. Girke-girken Ramadan: Yadda ake dafa chicken doughnut

    Tare da Rahama Sanusi Mato, wadda aka fi sani da Mato favourite disheses a fashin Instagram

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon
  4. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  5. NDLEA ta kama wani mutum ɗauke a hodar ibilis a cikin kwaroro-roba

    Jami'an NDLEA

    Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wani mutum ɗan ƙasar Suriname da ke yankin kudancin Amurka, bisa laifin safarar hodar ibilis a Najeriya.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama Dadda Lorenzo Harvey Albert da hodar ibilis ɗin da nauyinta ya kai kilogiram 9.9, wadda ya ƙunshe a cikin kwaroron-rabo tare da saka ta cikin ƙwalaben turare.

    Hukumar ta ce ta kama mutumin mai shekarar 34 a filin jirgin saman birnin Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya, a lokacin da ya shiga ƙasar da ƙulli 117 na hodar ibilis.

    Hakan na zuwa a daidai lokacin da hukumar ta ce ta ƙwace kilogiram 1,559.3 na tabar wiwi a faɗin jihohin ƙasar biyar, tare da ƙwace ƙwayar tramadol kimakin 648,050 a jihohin legas da imo da kuma taraba.

    View more on twitter
  6. Amsoshin Takardunka

    Shin mene ne asalin Tatsuniya?, kuma mene ne ya sa aka ba ta sunan Tatsuniya?

    Domin amsa wannan tambaya BBC ta tuntuɓi Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

    Zulaiha Abubakar Kibiya ce ta gabatar da shirin

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  7. Dan ƙasar Masar ya lashe musabaƙar Ƙur'ani ta duniya

    BBC

    Wani matashi ɗan ƙasar Masar ya lashe gasar musabaƙar Al-Ƙur'ani mai girma ta duniya da aka yi a Tanzania.

    Omar Mohammad Hussein, Ya samu nasarar zama zakara tsakanin abokan karawarsa 23 daga ƙasashe 23 na ciki da wajen nahiyar Afirka.

    Omar ya lashe miliyan 23 na kudin Tanzania daidai da dalar Amurka dubu 10, kwatankwacin naira miliyan bakwai da ɗari hudu a kuɗin Najeriya.

    .
    .
  8. Kwale-kwalen 'yan cirani ya nutse da mutum 27 a Tunisia

    ,

    Mutum 27 ne suka mutu yayin da wasu kwale-kwalen 'yan cirani suka nutse a gaɓar tekun Tunisia.

    Kwale-kwalen farko ya bar Tunisia ne a ranar Juma'a inda ya nufi Italiya ɗauke da mutum 37.

    Mutum 20 sun bata yayin da aka ceto wasu 17 na daban, in ji kakakin kotun birnin Sfax.

    A ranar Asabar, an gano gawarwaki huɗu a bakin ruwa bayan kwale-kwale na biyu ya nutse.

    An ceto mutum 36 a kwale-kwale na biyu, a cewar kakakin mutum uku na daban sun ɓata.

    Kakakin Faouz Masmoudi ya ce duka kwalekwalen na roba ne.

    Tun farkon watan Maris an samu nutsewar jiragen 'yan cirani bakwai a wannan gaɓar kogin.

    Wata gaɓar tekun a Tunisia ba ta fi nisan kilomita 150 zuwa Lampedus ba, wani tsuburi a Italiy, wanda duk wanda ya isa nan ana masa kallon yana cikin Italiya.

  9. Amurka ta nemi China ta nuna dattako a tsakaninta da Taiwan

    BBC

    Amurka ta buƙaci China ta nuna dattako, bayan fara atisayen soja a kusa da Taiwan, jim kaɗan bayan Shugaba Thai Ing-wen ta koma gida daga ziyarar da ta kai Amurka.

    Mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta sake nanata cewa ƙofa a buɗe take tsakanin Amurka da China matuƙar tana buƙatar hakan.

    Beijing ta gargaɗi 'yan majalisar dokokin Amurka kada su gana da Thai Ing-wen lokacin da ta kai ziyara ƙasar, amma suka yi biris da hakan.

    Wannan shi ne dalilin maida martanin China.

    China dai na kallon Tsibirin Taiwan a matsayin mallakiarta, ta kuma nuna aniyar ƙwato shi ta kowacce hanya.

  10. Tanzania za ta shirya musabaƙar Ƙur'ani da ƙasashe irin su 'yan Najeriya

    .

    Dubban mazauna birnin Dar es Salaam da ƙauyukan da ke zagaye da shi ne suka yi fitar ɗango a filin wasan kwallon ƙafa na ƙasar domin shaida musabaƙar karatun al-Ƙurani mai girma a ranar ta ƙarshe.

    Gasar wadda ita ce ta 23, mutum 23 ne za su fafata a cikinta daga ƙasashe 23 na ciki da wajen nahiyar Afrika.

    Cikin ƙasashen akwai na Gabashi da kuma Yammacin Afrika irinsu Najeriya

    Karon farko cikin tarihin gasar za a samu masu fafatawa daga yankin Asia, daga ƙasashe irin su Saudiyya, da kuma wasu ƙasashen irinsu Amurka da Birtaniya.

    .

    Duk wanda ya yi nasara a gasar zai lashe kudin Tanzaniya miliyan 23 daidai da dalar Amurka dubu 10, kimanin naira miliyan miliyan bakwai da dari 400.

    Na biyu kuma zuwa na biyar za su samu miliyan 15 zuwa miliyan hudu.

  11. 'Yan bindigar da suka sace gomman yara a zamfara sun yi magana

    bbc

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa 'yan fashin dajin da suka sace gomman yara da mata a ƙauyen Wanzamai na jihar Zamfara sun nemi a biya kuɗin fansa.

    Iyaye da dangin waɗanda aka yi garkuwar da su, sun shaida wa BBC cewa a ranar Alhamis ne aka sace aƙalla mutum 90 lokacin da suke daji da kuma aiki a gonakin bayan gari.

    Wata majiya ta ambato wani shaida daga Wanzamai yana cewa a cikin waɗanda aka sace har da fiye da mutum 20 daga ƙauyuka maƙwabta.

    Hukumomin jihar Zamfara har yanzu ba su ce uffan ba kan rahotannin sace waɗannan yara da mata na ƙauyen Wanzamai.

  12. Jami'an Saudiyya sun isa Iran da Yemen don sake ƙulla hulɗa

    BBC

    Jami'ai daga Saudiyya sun isa Iran da Yemen sakamakon yarjejeniyar da aka ƙulla a watan jiya ta maido da alaƙar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Iran.

    A Iran, ayarin Saudiyya ta isa ƙasar domin tattauna tsare-tsaren da za a bi wajen sake buɗe ofishin jakadancinta da ke can shekaru bakwai bayan Saudiyyan ta yanke hulɗar diflomasiyya.

    Rahotanni na cewa jami'an Saudiyya sun isa Sanaa, babban birnin Yemen inda za su haɗu da masu shiga tsakani daga Oman a ƙoƙarin cimma matsaya game da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da jagororin ƴan tawayen Houthi.

  13. Shugaban sojin Ƙurdawa a Syria ya ce Turkiyya ta nemi hallaka shi

    .

    Kwamandan sojin Kurdawa na SDF da ke jagorantar dakarun Syria, ya zargi Turkiyya da ƙoƙarin hallaka shi ta hare-haren jirgi maras matuƙi.

    Janaral Mazloum Abdi, ya ce harin ya faru a lokacin da ya ke filin jirgin Sulaymaniyah da ke yankin Ƙurdawa a Iraqi, kuma tawagarsa ta ƙunshi sojojin Amurka cikin jerin gwanon motocin da suke ciki.

    Sai dai Turkiyya ta musanta hannu a harin, wanda ya haddasa tashin gobara amma babu wanda ya jikkata.

    Mayaƙan SDF dai manyan aminan ƙawancen sojin Amurka da ke yaƙar mayaƙan ƙungiyar IS a Syria.

  14. Iran za ta sa kyamara a ko'ina don kama matan da ba sa yawo da hijabi

    B

    Hukumomin Iran sun fara kafa kyamarori a wuraren da mutane ke taruwa domin gano matan da ke yawo ba tare da hijabi ba, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

    Duk macen da aka samu ba ta sanya hijabi ba za a "aika mata saƙon jan kunne," in ji 'yan sanda.

    Wanda haka a cewarsu "zai rufe bakin masu adawa da wannan doka".

    Zanga-zanga ta mamaye Iran a bara, bayan an zargi 'yan hizba da sanadin mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini, wata Baƙurdiya da aka zarga da karya dokar sanya hijabi.

    Tun bayan mutuwar Mahsa, mata da yawa ke sanya hijabi musamman waɗanda ke zaune a manyan birane.

  15. Matar Aminu Ɗantata ta rasu a Saudiyya

    Family

    Mai ɗakin hamshaƙin ɗan kasuwar nan na jihar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata ta rasu.

    Hajiya Rabi Aminu Ɗantata wadda aka fi sani da Mama Rabi ta rasu ne a jiya Asabar a wani asibiti da ke birnin jidda na Saudiyya.

    Mama Rabi ta rasu tana da shekaru 70 a duniya, bayan wata doguwar jinya da ta yi fama da ita.

    Mama wadda ita ce mace ta biyu (kwari) a gidan fitaccen attajirin, ta mutu ta bar 'ya'ya shida ciki har da Tajudden Ɗantata, wani ɗan kasuwa mai tashe, da Batulu Dantata da Hafsa Dantata da Jamila Dantata sai kuma Aliya Dantata.

    Ta rasu kuma ta bar maigidanta, Alhaji Aminu Ɗantata da jikoki da dama.

  16. Isra'ila ta yi luguden wuta a Syria

    BBC

    Isra'ila ta ce jiragen yaƙinta sun kai hare-hare, bayan harba makaman roka cikin iyakokin da take iko da su daga Siriya.

    Tun da farko, kafar yaɗa labaran Syria ta ce an ji ƙarar fashewar wani abu a kusa da birnin Damascus, yayin da rahotanni ke cewa Isra'ila na kai hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa a kan birnin.

    An yi amfani da motocin atilare da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare kan wani ginin sojoji a Siriya da kuma bindigogin harba rokoki, bayan harba makaman roka shida daga cikin Siriya a yankin Tuddan Golan.

    Jami'ai sun ce rokoki guda uku sun faɗa cikin iyakar Isra'ila. Guda biyu sun dira a wani fili sai na uku wanda sojoji suka katse masa hanzari.

    Dakarun tsaron Siriya sun yi iƙirarin cewa na'urorin tsaro na sama sun mayar da martani kan hare-haren kuma cikin nasara sun tarbe wasu daga cikin makamai masu linzami da aka harba.

    Ta ƙara da cewa ba a samu rahoton wani mutum da ya mutu ko jikkata sanadin hare-haren na Isra'ila ba, illa dai ɓarnar da suka yi a kan dukiya.

    Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ruwaito cewa mayaƙan Al-Quds Brigade - wani ɓangaren masu gwagwarmaya da makamai daga ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad mai samun goyon bayan Iran - sun yi iƙirarin cewa su ne da alhakin kai hare-haren.

    A cikin wata sanarwa da sanyin safiyar Lahadi, Dakarun Tsaron Isra'ila sun ce "suna kallon ƙasar Siriya a matsayin wadda ke da alhaki kan duk al'amuran da ke faruwa a cikin iyakokinta kuma ba za su bar duk wani yunƙuri na keta 'yancin iyakokin Isra'ila ya tafi a banza ba".

    A lokaci guda, Jordan - wadda ta haɗa iyaka da Isra'ila da kuma Siriya - ta ce wata roka ta fashe a sama da yammacin Asabar kuma tarkacenta sun faɗo ƙasa cikin iyakar ƙasar.

    Ba ta ce ga daga inda aka harba rokar ba.

    Tarkacen waɗanda suka faɗa cikin yankin Wadi Aqraba, ba su yi sanadin mutuwa ko rauni ba, a cewar sanarwar rundunar sojin Jordan.

    Isra'ila ta ƙwace Tuddan Golan ne mai girman murabba'in kilomita 1,200, wanda a baya ke ƙarƙashin ikon Siriya a lokacin Yaƙin Kwana Shida cikin 1967 inda ta haɗe shi da ƙasarta a 1981, wani mataki wanda mafi yawan ƙasashen duniya ba su amince da shi ba.

    Hare-haren na zuwa ne daidai lokacin da tunzuri ke ƙaruwa a yankin.

    A ranar Juma'a, Isra'ila ta kai hare-hare kan wurare da dama a kudancin Lebanon, waɗanda mallakar ƙungiyar Falasɗinawa 'yan ta-da-ƙayar-baya ta Hamas ne, wadda ta ɗora wa alhakin rokoki guda 34 da aka harba arewacin Isra'ila ranar Alhamis.

    A kwanakin nan, mayaƙan Hamas sun yi ta harba makaman roka cikin Isra'ila daga Falasɗinu da Lebanon, yayin da ita kuma take maida martani da luguden bama-bamai ta sama.

    Can a wani wurin kuma, ɗaruruwan Falasɗinawa ne suka katange kansu a Masallacin Al-Aqsa da ke Gabashin Birnin Ƙudus, yankin da ke ƙarƙashin mamaya, abin da ya sake jefa fargabar arangama da 'yan sandan Isra'ila.

  17. An sake kama mutumin da yake yi wa mata fyaɗe ta hanyar amfani da Facebook

    .

    Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce an yi nasarar sake kamo wani mutum da ya yi ƙaurin suna wajen aikata fyaɗe da kisa wanda ya tsere daga gidan yari bayan ya yi ƙaryar ya mutu.

    Jami'ai sun ce an kama Thabo Bester tare da budurwarsa da wani mutum a ranar Juma'a a Tanzania.

    An yi wa Bester laƙabi da mai fyaden Facebook saboda yadda yake amfani da shafukan sada zumunta wajen ɗana wa mutanen da yake yaudara tarko.

    An yi tunanin ya mutu a wata gobara da ta tashi a gidan yarin cikin shekarar da ta gabata amma gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da cewa gawar da aka gani, ba ta shi bace.

    Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Afirka ta Kudu - ƙasar da aka fi samun yawan laifukan cin zarafi ta hanyar lalata a duniya.

  18. An kai wa 'yan mata a makarantu hari da iska mai guba a Iran

    BBC

    Rahotanni daga Iran na cewa ƴan mata da yawa ne a ƙasar suka shaƙi iska mai guba bayan komawarsu makarantu a wani lamari mai ban mamaki da ya tayar da hankula.

    Wani likita ɗan Iran ya ce cikin kwanaki biyun farko bayan ɗalibai sun koma makaranta, ɗalibai mata kimanin ɗari bakwai da goma sha bakwai ne aka kai wa hari.

    Hotuna da bidiyo sun nuna yadda gurbatacciyar iskar ta yi wa ɗaliban illa a makarantu da ke Khuzestan da Ardabil da Urmia.

    Hukumomi sun ƙaddamar da bincike inda jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce ya kamata a yanke hukunci mai tsanani ga waɗanda aka samu da laifi.

    Sai dai Iraniyawa suna zargin hukumomi da hannu a lamarin.

  19. An kashe mutum 44 a wasu tagwayen hare-hare a Burkina Faso

    .

    Hukumomi a Burkina Faso sun ce an kashe farar hula 44 a wasu hare-hare biyu da aka kai yankin Sahel da ke arewacin ƙasar tsakanin ranar Alhamis da Juma'a da dare.

    Sun ce maharan sun afka wa ƙauyukan Kourakou da Tondobi amma a cewarsu, an daƙile su bayan hare-haren.

    Rahotanni sun ce sojoji na ƙoƙarin daidaita al'amura a yankin.

    Tun shekarar 2015 ne Burkina Faso ke yaƙar ayyukan masu iƙirarin Jihadi.

    Tashin hankalin ya ɗaiɗaita dubun dubatar mutane a ƙasar.