PDP ta naɗa sabon shugaban riƙo na ƙasa

...

Asalin hoton, FACEBOOK/Umar Iliya Damagum

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya amince da naɗin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar na ƙasa.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya yi ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne don yin biyayya ga hukuncin babbar kotun jihar Binuwai.

A ranar Litinin ne kotu a Binuwai ta haramta wa Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari ƙarar da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka shigar gabanta.

Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam'iyyar ya ce sun ɗauki matakin naɗa Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP.

Debo Ologunagba ya ce "Bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la'akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewa, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar".

Dakatar da Iyorchia Ayu

Matakin na zuwa ne bayan, babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ta sanar da dakatar da Dr Iyorchia Ayu, bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amana.

Shugabannin PDP a matakin gundumar Ayu da ke ƙaramar hukumar Gboko cikin jihar Benue ne suka ɗauki matakin dakatar da shi.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan sun kaɗa ƙuri'ar dawowa daga rakiyar shugabancinsa.

A lokacin da ya karanta matsayar da suka cimma, sakataren jam'iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasan da Ayu da kuma makusantansa suka yi wa PDP ne ya ja mata faɗuwa a zaɓe cikin gundumar da kuma jihar Binuwai baki ɗaya, a zaɓen gwamna.

Binuwai dai na cikin jihohin da suka kuɓuce daga hannun babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya a zaɓukan da aka yi cikin watan Maris ɗin 2023.

Bayan sanar da sakamakon zaɓukan gwamna a cikin jiha 26, PDP a ƙarƙashin jagorancin Iyorchia Ayu ta ƙare ne da samun gwamnoni guda 9, inda ta yi asarar wasu muhimman jihohinta kamar Sokoto da Binuwai da kuma Abia.

Haka zalika, PDP ta yi rashin nasara a babban zaɓen Najeriya, inda ɗan takararta Atiku Abubakar ya zo na biyu da adadin ƙuri'a 6,984,520.

Masharhanta sun ce da PDP ta shiga zaɓukan 2023 da cikakken haɗin kai, mai yiwuwa da ta samu nasarar ƙwace gwamnatin ƙasar daga hannun APC.

An daɗe ana kai ruwa rana

PDP ta fara tsunduma cikin rikici ne tun bayan zaɓen fitar da gwani a ƙarshen watan Mayun 2022, inda Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi nasarar zama ɗan takarar jam'iyyar na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

An jima ana kai ruwa rana tsakanin PDP da gwamnanta na jihar Ribas, Nyesom Wike mutumin da ya nemi takarar shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar, amma bai yi nasara ba.

Bayanai sun ce gwamnan mai ƙarfin faɗa-a-ji a PDP ya gindaya sharuɗɗa kafin ya ci gaba da zama a jam'iyyar, da kuma mara wa Atiku Abubakar baya, cikinsu har da sai lallai Iyorchia Ayu ya sauka daga shugabancin PDP.

Ya dai kafa hujjar cewa babu adalci, kuma ya saɓa da tsarin raba-daidai, PDP ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga ɓangaren da shugabanta na ƙasa ya fito.

Sai dai a wani martani yayin zantawa da BBC, Iyorchia Ayu ya ce ba zai sauka daga kan muƙamin nasa ba, don kuwa an zaɓe shi ne bisa dokokin da jam'iyyar PDP ta shimfiɗa.

Ya dage a kan cewa an zaɓe shi tsawon wa'adin shekara huɗu, kuma don kawai wasu ba sa son ganin sa a kan muƙamin shugaban PDP, hakan ba ta zama hujjar da zai sauka ya bar kujerarsa ba.

''Maganar zaɓen Atiku ba ta shafi muƙamin Shugaban jam'iyya ba. Ni na ci zabe. A cikin kundin tsarinmu muka yi wannan," in ji Ayu.

''Ba wani laifi da na yi, ina gyara jam'iyya ne, hayaniyar da ake yi wallahi ba ta dame ni ba,'' ya faɗa wa BBC.

Iyorchia Ayu

Asalin hoton, PDP

Tun da farko a ranar Alhamis 23 ga watan Maris, jam'iyyar PDP ta sanar da miƙa sunan gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortum gaban kwamitin ladabtarwarta na ƙasa don ɗaukar mataki a kansa.

Mista Ortum yana cikin gwamnonin PDP biyar waɗanda suka yi wa kansu laƙabi da Gungun 'yan biyar wato G5, da suka yi tawaye ga ɗan takarar jam'iyyar na shugaban ƙasa.

A cikin sanarwar da PDP ta fitar game da buƙatar a ladabtar da Samuel Ortum, jam'iyyar ta kuma ce ta dakatar da wasu jiga-jiganta irinsu Ibrahim Shehu Shema da Ayodele Fayose dukkansu tsoffin gwamnoni, sai Dr. Anyim Pius Anyim, tsohon shugaban majalisar dattijai.

Akwai kuma Prof. Dennis Ityavyar daga jihar Binuwai da Dr Aslam Aliyu ta jihar Zamfara, dukkansu kuma jam'iyyar ta zarge su ne da yi mata zagon ƙasa a zaɓukan da suka gudana.