Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Mustapha Musa Kaita

    Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan wasu labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Buhari ya bayar da umarnin fatattakar yan bindigar da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja

    ...

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma na wasu sassan ƙasar.

    Jaridar Daily Trust a Najeriyar ta ruwaito ministan harkokin cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola yana sanar da hakan a yau Alhamis bayan taron majalisar tsaro ta tarayya wanda shugaban ƙasar ya jagoranta a fadarsa.

    Ya bayyana cewa shugaban ya ba dukkannin jami'an tsaron ƙasar umarni da kada su yi ƙasa a gwiwa su tabbatar sun kawar da duk wasu ɓarayi da masu garkuwa da mutane da duk wasu nau'uka na laifuka.

    Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ta zama tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake yawan samun ƴan bindigan na yi wa matafiya kwantar ɓauna.

    Ko a makon nan sai da ƴan bindigan suka sace gwamman mutane da kuma kashe wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriyar.

  3. Barazanar korona a Belgium ta wuce yadda ake tunani - Firaiminista

    ..

    Firaiministan Belgium ya bayyana cewa ƙara ɓullar cutar korona ta baya-bayan nan da kuma irin barazanar da asibitocin ƙasar ke ciki ya wuce inda ake tunani.

    Alexander De Croo ya yi gargaɗin cewa akwai buƙatar a sake ɗaukar wasu matakai - duk da cewa ƙasar ta saka wasu matakai a makon da ya gabata.

    A yanzu haka ana fuskantar ɓullar cutar korona karo na huɗu a Turai duk da cewa an gudanar da riga-kafi sosai a ƙasar.

    Ƙasashe da dama sun dawo da dokoki domin a dakatar da bazuwar cutar inda ake buƙatar mutane su ƙara karɓar ƙarin riga-kafin.

    A halin yanzu, an tabbatar da mutuwar mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar a Nahiyar Turai.

  4. Binciken Bangladesh ya gano wasu magunguna sun daina tasiri da kashi 50 cikin 100

    Wani bincike da aka gudanar a Bangladesh ya gano cewa tasirin magungunan da ke kashe kwayoyin cututtuka ya ragu da fiye da kashi 50 cikin 100.

    Binciken ya nuna cewa annobar korona ta janyo ƙaruwar amfani da irin magungunan saboda jita-jitar da ake yaɗawa cewa magungunan na iya kashe ƙwayar cutar korona.

    Jami'an Lafiya sun ce lamarin abin tada hankali ne saboda biyar daga cikin muhimman magungunan da hukumar lafiya ta duniya ta bayyana na ci gaba da rasa tasirinsu.

  5. An kashe mutum 43 a yankin Darfur na Sudan cikin mako guda - MDD

    ..

    Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa bayan shafe kwanaki da dama ana rikicin ƙabilanci a yankin Darfur na Sudan, aƙalla mutum 43 ne suka rasa rayukansu inda kuma dubban mutane ne suka rasa muhallansu.

    Rikicin ya ɓarke ne a makon da ya gabata tsakanin Larabawa makiyaya da kuma manoma daga ƙabilar Misseriya Jebel.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da ƙauyuka 40 aka ƙona da kuma sace-sacen kayayyaki. Mutane da dama ne aka bayar da rahoton cewa sun ɓacce ciki har da ƙananan yara.

    An ta samun ɓarkewar rikici a yankin Darfur tun bayan da aka saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a bara, lamarin da ya sa sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya suka janye daga yankin,

  6. An kashe mutum huɗu a wajen haƙar zinare a Congo

    ..

    Mutum huɗu ciki har da ƴan ƙasar China biyu aka kashe a wani harin yan tawaye a wani wurin haƙar zinare a arewa maso gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

    Wani mai magana da yawun sojin ƙasar ya ɗora alhakin kai harin kan wata ƙungiyar haɗin kai da ci gaban Congo mai suna CODECO inda aka kai harin a Damblo da ke lardin Ituri.

    Watanni shida da suka gabata, Felix Tshisekedi ya sa an yi ƙawanya a lardin Ituri da lardin Kivu mai makwaftaka - wanda wannan wani yunƙuri ne na ƙara wa sojoji ƙarfi. Duk da wannan matakin da gwamnati ta ɗauka, an ci gaba da kisan kiyashi da kuma garkuwa da mutane.

    Ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama na ƙasa da ƙasa ciki har da ƙungiyar Save The Children da Norwegian Refugee Council duk sun bayyana cewa wani sabon nau'in hare-haren ƴan tawaye ya sa sun rage ayyukan da suke yi a Ituri, lamarin da ya ja dubu ɗaruruwan mutane ba su samun agaji.

  7. Buhari ya mayar da Najeriya mabaraciya, in ji shugaban PDP mai jiran gado

    Sanata Iyorchia Ayu

    Zababben shugaban babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya PDP ya ce yawan ciyo bashin da shugaban kasar Muhammadu Buhari yake yi ya sa kasar ta zama mabaraciya.

    Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana haka ne a wurin taron manema labaran da sabbin shugabannin jam'iyyar suka yi bayan taron karawa juna sani da suka yi a Abuja ranar Talata.

    Ya ce a wajen taron da suka yi na kwana biyu sun gano cewa gwamnatin Buhari ta raba mutum miliyan 30 da ayyukansu, yana mai cewa gwamnatin ta gaza wajen samar da tsaro.

    Haka matsalar tattalin arziki ta mayar da Najeriya cibiyar talauci a duniya, a cewar shugaban na PDP.

    Ya ce PDP ta shirya tsaf don ceto Najeriya daga kanshin mutuwar da APC ta yi mata.

  8. Dubban mutane sun yi zanga-zanga kan kulla yarjejeniya da sojoji a Sudan

    Masu zanga-zanga

    Dubban mutane ne a babban birnin Sudan, Khartoum, da ma wasu birane suka gudanar da zanga-zanga domin matsa lamba kan shugabannin sojojin kasar.

    A birnin Omdurman, jami'an tsaro sun fesa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa kwalla wadanda ke adawa da juyin mulkin da aka yi a watan jiya.

    Sun yi gangami domin jinjina wa mutanen da jamia'n tsaron Sudan suka kashe a makonnin baya bayan nan.

    Kazalika sun yi tir da yarjejeniyar da aka kulla da sojoji a kwanakin baya wadda ta bayar da damar komawa da Firaiminista Abdalla Hamdok kan mukaminsa.

    Fitattun jam'iyyun siyasa da kuma kungiyoyi masu karfi da ke yin zanga-zanga a Sudan sun yi watsi da matakin da Mr Hamdok ya dauka na sanya hannu kan yarjejeniyar da sojoji suka mika masa..

    Wasu daga cikinsu sun ce ya watsa musu kasa a ido yayin da wasu suka ce hakan ya halasta juyin mulkin da sojoji suka yi.

    Masu gangami
  9. Kotu ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar

    Wata Babbar kotun Shari'ar Musulunci ta Kofar Kudu a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

    Lawyan Abduljabbar Nasiru kabara, Muhammad A Mika’il ne ya gabatar da bukatar gaban mai Shar'ia Ibrahim Sarki Yola gabanin kammala zaman kotun a yau.

    Gwamnantin jihar Kano ce dai ta ke karar Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin batanci ga Manzon Allah da kalaman da ke tunzura jama'a.

    Ibrahim Miniyawa ya tuntubi wakilinmu na Kano, Khalifa Shehu Dokaji, domin jin karin bayani kan zaman kotun.

    Latsa hoton da ke kasa domin sauraren karin bayanin:

    Video content

    Video caption: Kotu ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar Kabara
  10. Najeriya ta karɓi ƴan ci-rani 330 da suka maƙale Libya da niyyar haurawa Turai

    Hukumar NEMA mai bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce ta karɓi adadin ƴan Najeriya 330 da aka dawo da su gida ta hannun ƙungiyar Tarayyar Turai da ta ɗauki nauyin dawo da su gida.

    Yawancinsu ƴan Najeriyar sun maƙale a yankuna daban-danban da ke a ƙasar Libya a yunƙurinsu na tsallaka wa zuwa Turai domin samun rayuwa mai nasibi.

    Ku saurari rahoton Umar Shehu Elleman

    Video content

    Video caption: Rahoton Elleman
  11. Za a ɗage dokar haramta wa masu ciki zuwa makaranta a Tanzania

    Mai ciki

    Gwamnatin Tanzania ta ce za ta ɗage dokar haramta wa mata masu ciki zuwa makaranta.

    Ministar ilimi ta ƙasar, Prof Joyce Ndalichako wacce ta sanar da matakin ta ce ɗalibai da dama da suka daina zuwa makaranta saboda wasu dalilai da suka hada da ɗaukar ciki yanzu za a bari su dawo karatu.

    Gwamnatin ta ce ta fito da wani tsari na daban ga ƴan makaranta mata masu juna biyu, inda hukumomi suka ce zai zama kariya gare su.

    Dokar da ta hana masu juna biyu zuwa makaranta ta ce za a kori su daga karatu saboda aikata laifin aikata “mummunan aiki a wajen aure.”

    An daɗe masu fafutikar kare ƴancin mata na bayyana adawa da dokar tare da kira ga gwamnati ta sauya dokar.

    Shugaban ƙasar ya ce duk namijin da aka kama ya yi wa mace ciki za a ɗaure shi shekara 30.

  12. Buhari na jagorantar taron majalisar ƙoli kan tsaro

    Taron majalisar koli

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar koli kan harakokin tsaro a fadarsa a Abuja inda ake sa ran za a sanar da shi halin da ake ciki game da tsaro a ƙasar.

    Taron ya ƙunshi mataimakinsa Yemi Osinbajo da shugaban ma'aikatan fadarsa Chief Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro Manjo General Babagana Monguno da kuma babban hafsan sojin Najeriya Janar Leo Irabor.

    A wajen taron ne Shugaban ya ƙara wa babban dogarinsa Laftanar Kanal YM Dodo girma zuwa matsayin Kanal.

    buhari
  13. Manyan makarantun Najeriya sun ɗauki ɗalibai 706,189 ba bisa ka’ida ba – Jamb

    Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta ce makarantun gaba da sakandare sun ɗauki ɗalibai 706,189 ba bisa ka’ida.

    Jaridar Premium Times ta ambato shugaban hukumar JambIs-haq Oloyedena cewa duk da gargaɗi ga makarantun amma jami’o’i da kwalejojin ilimi sun ci gaba da ɗaukar ɗaliban ba bisa ƙa’ida ba.

    Ya ce makarantu 137 da bayar da digiri sun dun ɗauki ɗalibai 706,189 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020.

    Shugaban hukumar ya yi gargaɗi ga makarantun da suka ƙunshi jami’oi na gwamnati da masu zaman kansu su daina kaucewa tsarin ɗaukar ɗalibai na CAPS (Sentral Admission Processing System)

  14. Sojojin Denmark sun yi artabu da ƴan fashin teku a Najeriya

    Yan fashin teku

    Rundunar sojin Denmark ta ce ma'aikatan daya daga cikin jiragen yakinta na ruwa da ke aiki a yammacin Afirka sun kashawasu 'yan fashin teku hudu a wani artabu da suka yi da su.

    Sanarwar ta ce jirgin ruwan Esbern Snare tare da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya tunkari wani jirgin ruwa da ke gudu a kudancin Najeriya ranar Laraba.

    Mutum takwas ne a cikin jirgin da kuma tsani da sauran kayan aikin da 'yan fashin ke amfani da su wajen shiga jiragen ruwa.

    Sanarwar ta ce an yi harbi sama domin tsorata ƴan fashin amma ƴan bindigar suka buɗe wuta kan sojojin Denmark.

    Sojojin sun ce hudu daga cikin ‘yan fashin sun mutu sannan daya ya jikkata; ba a samu asarar rayuka a ɓangaren sojojin Denmark.

    Kasashe da dama sun tura jiragen ruwa zuwa yankin bayan da aka sace sama da ma'aikatan ruwa 130 daga cikin jiragen ruwa a yankin a bara.

  15. An hana Saif al-Islam ɗan Gaddafi tsayawa takara a Libya

    Getty Images

    Hukumar zaben kasar Libya ta cire sunan dan Gaddafi Saif al-Islam,daga cikin wadandsa za su yi takarar shugabancin kasar a babban zabe da za a watan gobe.

    Daurin da aka yi masa a baya na cikin dalilan da aka kafa na daukar wannan mataki.

    A 2015 wata kotu a tripoli ta yanke wa Saif al-Islam hukumcin daurin kisa saboda tashin hankalin da ya faru a 2011, rikicin da ya hambarar da gwamnatin mahaifinsa.

    Bayan shekaru kokarin Majalisar Dinkin Duniya na ganin an bai wa dimokradiyya mazauni ya kawo karshen yakin basasar.

    Za a yi zaben shugaban ƙasa a Libya a ranar 24 ga watan Disamba a karon farko cikin shekara 10.

    Getty Images
  16. NLC ta ce maganar rabawa 'yan Najeriya ₦5000 'abin dariya ne'

    NLC

    Kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin kasar na yunkurin kara farashin man fetur, in da ta ce ba za ta fada gadar zaren da gwamnatin ƙasar ke neman shiryawa mutanenta ba.

    Cikin wata sanarwa da NLC ta fitar shugaban kungiyar Kwamared Ayuba Wabba ya ce sanarwar da shugaban NNPC Malam Mele Kyari ya yi ta kara farashin man fetur zuwa 340 daga watan Fabirairu ba ta yi wa 'yan kasar dadi ba.

    Cikin sanarwar NLC ta ce cewa za a rabawa 'yan Najeriya miliyan 40 naira 5000 domin rage musu radadin karin farashin man fetur 'abin dariya ne', inda ta ce idan aka lissafa kudin sai ya haura na tallafin man fetur din da ake bayarwa a kasar.

  17. Harin kunar bakin wake kan jami'an tsaro ya kashe mutum takwas a Somalia

    BBC

    'Yan sanda a Somalia sun tabbatar da kisan fararen hula takwas a wani harin kunar bakin wake da aka kai Mogadishu babban birnin kasar.

    Wasu mutum 17 na daban sun jikkata, ciki har da yara 13 na wata makaranta da ke kusa da wurin da aka kai harin.

    Harin da al-Shabab suka kai a wata mota, sun yi nufin kai shi ne kan wani jerin gwanon motocin jami'an tsaron wani kamfani da yake kare Majalisar Dinkin Duniya.

    'Yan sanda sun ce babu wani wakilin MDD da harin ya shafa.

    Rahotanni sun ce an kai harin ne da safe lokacin da ake saurin tafiya wuraren aiki.

    Tuni al-Shabab ta dauki nauyin kai harin.

  18. Farashin man fetur a Ghana ya kai sidi 7 kwatankwacin ₦560

    Video content

    Video caption: Saurari tattaunawar Fahad Adam da Sarki Imrana Ashiru Dikeni,

    Ana ci gaba da samun hauhawar farashin man fetur a Ghana, inda farashin ya yi tashin gwauron zabi a yanzu lita daya ta kai kusan sidi 7 wato sama da dala daya kwatankwacin ₦560 a kudaden Najeriya.

    Lamarin dai ya sa direbobin motocin haya bai wa gwamnati daga nan zuwa ranar Litinin mai zuwa don ta janye wasu haraje-haraje a kan man fetur da dangoginsa, ko su tsunduma yajin aiki gadan gadan.

    Haraji nau'i takwas ake da shi a kan man fetur, amma waɗanda suke ci wa direbobin tuwo a kwarya, guda uku ne don haka suka ce gwamnati ta janye su da nufin kawo sauƙi ga rayuwar al'ummar Ghana.

    Sarki Imrana Ashiru Dikeni, wani masanin harkokin kudi da tattalin arziki ya fara da bayani kan mafarin matsalar a hirarsu da Fahd Adam

  19. An haramta gudanar da bukukuwan Kirismeti a Indonesia

    History

    Gwamnatin Indonesia ta haramatawa kab ma'aikatan gwamnati da na 'yan kasuwa zuwa hutu a karshen shekara domin bukukuwan Kirismeti da Sabuwar shekara a kokarin rage yaɗuwar annobar korona.

    An kuma hana ɗaliban makarantu daukar ƙarin kwanakin hutu a lokacin bukukuwan.

    Hutu da aka yi a baya ya taka rawa wajen kara yaduwar annobar saboda tafiye-tafiyen mutane a sassan kasar.

    Akwai kiristoci akalla miliyan 30 a Indonesia - a kasar da Musulmi ke da rinjaye. Tun bayan watan Yuli ana samu ragin masu kamuwa da annobar yanzu haka a ƙasar.

  20. An kama mutumin da ya yi yunkurin sayar da 'ya'yansa biyu kan ₦700,000 a Najeriya

    Video content

    Video caption: Latsa nan ka saurari rahoton Umar Shehu Elleman

    Rundunar tsaro ta Sibil Difense a jihar Akwa-Ibom Najeriya, ta damke wani mutum mai suna Mista Elisha Adet Iffiong ɗan shekara arba'in.

    An kama shi a lokacin da ya yi yunƙurin sayar da ‘ya’yansa mata guda biyu akan kuɗi naira dubu ɗari bakwai. Anan gaba ne za a gurfanar da shi a gaban kotu.