NIN: Hukumar NIMC mai yin katin ɗan ƙasa ta samar da manhajar da za ku saka katin ɗan ƙasa a waya

NIMC Mobile app download

Asalin hoton, NIMC

Hukumar da ke rajistar katin ɗan ƙasa a Najeriya, NIMC, ta fara kira ga ƴan ƙasar da su sauke manhajar ta NIMC a wayoyinsu, bayan hukumar ta ƙaddamar da ita domin ƴan ƙasar su iya yin tozali da katinsu a wayoyinsu ba wai lallai sai a zahiri ba.

NIMC ta bayyana cewa manhajar da ta fito da ita ba ta da wuyar amfani, haka kuma duk wanda zai yi amfani da ita lallai sai yana da lambar NIN.

Kamar yadda hukumar ta NIMC ta bayyana, hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayyana cewa mutum zai iya haɗa lambarsa ta NIN da lambobin layi bakwai - waɗanda aka yi musu rajista da sunansa.

Ta yaya mutum zai sauke manhajar NIMC a wayar?

A farko dai, za ku iya sauke manhajar daga Google Play Store idan kuna amfani da waya ƙirar Android, haka kuma ga masu amfani da iPhone za su iya zuwa Apple Store domin duba manhajar domin su sauke.

NIMC Mobile app download
  • Bayan kun sauke manhajar a wayarku, sai ku shiga cikinta ku je ƙasa ku latsa Skip (tsallake) domin ku ci gaba
  • Sai ku saka lambobi 11 na NIN ɗinku, ku latsa Next (na gaba), sai kuma ku latsa I Agree (na yarda)
  • Bayan nan, lambar da kuka yi amfani kuka yi rajistar NIN ɗinku za ta fito tare da tambaya biyu:
  • Ina amfani da wannan lambar har yanzu
  • Ba na amfani da wannan lambar a halin yanzu
  • Sai ku latsa abin da ya dace game da waɗannan tambayoyin domin zuwa mataki na gaba
  • Idan kuna amfani da lmbar da ta fito, za ku saka wata lamba ta sirri da za a turo muku a waya a daidai lokacin, sai ku saka lambar tare da latsa mataki na gaba
  • Amma idan ba kwa amfani da ita, dole ne ku je ɗaya daga cikin ofisoshin NIMC da ke kusa domin bayar da sabuwar lambar wayarku, wanda hakan zai ba ku dama ku samu katinku