Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance da mu gobe Laraba inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye.

  2. An kama wani mutum da akwati cike da hawainiya

    Hawainiya

    An kama wani mutum da akwati cike da hawainiya a filin jirgin sama na birnin Vienna da ke Austria.

    An gano hawainiyar ne bayan da aka sa akwatin a na'urar daukar hoton cikin akwati kuma nan aka gan hawainiya 74 an ɓoye ta a cikin safa da ƙananan akwatuna.

    Muyumin mai shekara 56 na hanyarsa ta komawa gida ne daga Tanzania kuma nan take aka kama shi.

    Jami'ai sun ce ana sayar da hawainiyar ne a kasuwar bayan fage.

    Ana tunanin za a ci tarar mutumin Euro 6,000.

    Uku daga cikin hawainiyoyin sun mutu yayin da aka kai sauran wani gidan ajiye namun daji inda ake ba su kulawa ta musamman saboda sun jikkata a lokacin da aka ɓoye su a cikin akwatin.

  3. Lauyan Yari ya ce kuɗin da gwamnati ta kwace a banki bai wuce naira dubu 15 ba

    Tsohon gwamnan Zamfara

    Lauyan tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, Mahmud Abubakar Magaji ya ce kuɗin da ke cikin asusun ajiyar da gwamnati ta kwace bai wuce naira dubu 15 ba, kuma ya mallake su ne tun kafin ya hau mulki.

    Ya ce zancen kwace kudi naira miliyan 23 ba shi da tushe, tare da alƙawarin ɗaukaka ƙara.

    A ranar Talata ne babbar kotun tarayya a Abuja ta ba da umarnin ƙwace wasu kuɗaɗe da ke asusun ajiyar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari.

    Kotun ta ce kuɗaɗen da aka ajiye a wasu bankunan kasuwanci biyu na Nijeriya, sun ƙunshi sama da naira miliyan 23 da kuma fiye da dala dubu 700, kwatankwacin naira miliyan 330.

    Hukumar ICPC, ta tabbatar wa BBC cewa ba shakka maganar ta koma gaban kotu a ranar Talata, sai da ba za ta iya ba da ƙarin haske ba har sai ta ji bayanin abin da ya faru daga lauyoyinta.

    Tun da farko kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta shigar da ƙara tana zargin cewa an samu kuɗaɗen ne ta haramtacciyar hanya.

    Kuɗaɗen a cewar NAN, sun ƙunshi na wani asusu da ke ɗauke da fiye da dala dubu 56 da kuma wata kusan naira miliyan 13 a wani asusun na daban sai sama da naira miliyan 1.

    Aakwai wani asusun da dala 301 da 319 da kwabbai da kuma naira dubu 217, 388, Sai kuma wata dala 311 da 872.

    Kuma an ajiye kuɗin ne da sunan Abdulaziz Yari da kamfanoninsa.

    A wani hukunci da ta gabatar, Mai shari'ah Ijeoma Ojukwu ta ce tsohon gwamnan na Zamfara bai iya yi mata gamsasshen bayani kan dalilin da ya sa ba za ta bai wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa damar karɓe kuɗaɗen ba.

    Hukumar ta shigar da ƙara ne inda ta roƙi kotun ta nemi jin dalilin da ya sa kuɗaɗen waɗanda ake bincike kansu, ba za a karɓe su kwata-kwata a damƙa wa gwamnatin tarayya ba.

    Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa Abdulaziz Yari da kamfanoninsa guda biyu ciki har da Ƙayatawa Nigeria Ltd da B.T Oil and Gas Nigeria Ltd ne cikin wannan ƙara.

    A watan Agustan bara ne, Mai Shari'ah Taiwo Taiwo ya ba da umarnin karɓe kuɗaɗen a matakin wucin gadi bayan buƙatar da lauyan hukumar ta ICPC ya shigar.

  4. Korona: Mutanen da suka mutu a Burtaniya sun haura 100,000

    Annobar Korona

    Sama da mutum 100,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar korona a Burtaniya bayan mutum 1,631 sun mutu cikin kwanaki 28 da sanin suna ɗauke da cutar.

    Firayi Minista Boris Johnson ya ce ya dauki dukkan alhakin matakan da gwamnati ta dauka yana mai cewa: "Mun yi dukkan mai yiwuwa."

    "Ina matuƙar nadamar ko wace mutuwa," a cewarsa.

    Burtaniya ce ƙasa ta farko a Turai da ta wuce wannan adadin mutanen da suka mutu.

    Mista Johnson ya ce yana miƙa ta'aziyya ga dukkan waɗanda suka yi rashi a wannan annoba ta korona.

  5. Biden ya ce yana da aniyar dawo da tallafin Amurka ga Falasdinawa

    Sabon wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya ce gomatin shugaba Biden nada anniyar sake dawo da tallafin da take ba Falasdinwa wanda tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dakatar.

    A jawabin da ya yiwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yayin wata muhawara Richard Mills ya ce Amurka za ta ci gaba da kokarin ganin cewa an samu Karin kasashe musulmi da za su dawo da alakar da ke tsakaninsu da Isra'ila.

    Sai dai ya ce wannan ba zai maye gurbin shirin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Israi'la ba.

  6. Kotu ta ba da umarnin ƙwato kuɗin Abdulaziz Yari da ke bankuna

    Abdulaziz Yari

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin kwace kuɗaɗen tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari waɗanda ke ajiye a bankunan Zenith da Polaris a Najeriya.

    NAN ta ruwaito cewa kuɗin sun kai dala 56 a bankin Polaris sai kuma Naira miliyan 12.9 da Naira miliyan 11.2 da dala 30,309.99 da Naira 217, 388.04 da dala 311, 872.5 da aka adana a bankin Zenith da sunan tsohon gwamnan da kamfanoninsa.

    Alƙalin da ya yanke hukuncin ya ce bai ga dalilin da zai sa a hana Hukumar ICPC da ta shigar da ƙarar damar karɓe kuɗaɗen ba.

    ICPC ta ce tana zargin Abdulaziz Yari ya samu kuɗin ne ta haramtacciyar hanya.

  7. Ana zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Tunisia

    Ɗaruruwan mutane ne ke zanga-zanga a Tunis babban birnin Tunisia, don nuna ƙin jinin gwamnati da ƴan sanda.

    Sun yi tattaki zuwa majalisar dokokin ƙasar inda ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fusata da yadda gwamnatin ta tafi da tashin hankali da ya faru a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a makon da ya gabata.

    Matasa masu zanga-zanga sama da dubu ne aka tsare bisa zargin lalata gidaje da sata.

  8. Gwamnatin Najeriya ta wallafa hotunan sabbin manyan hafsan soji

    Bayan sanar da sauke manyan hafsan sojin Najeriya da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi, ofishinsa ya wallafa hotunan sabbin da aka naɗa da suka maye gurbinsu.

    Janar Leo Irabor, ne aka naɗa babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru, a matsayin babban hafsan sojan ƙasa.

    Rear Admiral A.Z Gambo, aka naɗa babban hafsan sojan ruwa sai Air-Vice Marshal I.O Amao, a matsayin babban hafsan sojan sama.

    View more on twitter
  9. Labaran BBC Hausa cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Daya Da BBC Na Rana 26/01/2021
  10. Labarai da dumi-dumiBuhari ya ƙori manyan hafsoshin tsaron Najeriya

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙori manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

    Sannan ya naɗa wadanda za su maye gurbinsu domin ci gaba da gudanar da harkokin bai wa ƙasa tsaro.

    Mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter.

  11. Yadda ƙasashe masu arziki ke rabon rigakafin korona abin alla-wadai ne - Ramaphosa

    Shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramophosa , ya yi Alla-wadai da yadda ƙassahen duniya masu karfin tattalin arziki ke nuna kansu kawai suka sani game da alurar rigakafin cutar korona.

    A jawabin da ya yi ta intanet a taron tattalin arziki na duniya, ya ce wasu gwamnatoci sun bada odar allurar rigakafin fiye da wanda suke bukata.

    Ba tare da ambatan sunan wata ƙasa ba, shugaba Ramophosa, ya yi kira ga ƙasashen akan su fitar da ƙarin alurar da suka ajiye domin sauran ƙasashe su amfana.

    Kawo yanzu Afrika ta kudu wadda ita ce ƙasar da cutar korona ta fi kamari a nahiyar Afrika ba ta samu allurar rigakafin cutar koronar ba.

    Sai dai tana sa ran samun allurar kamfanin AstraZeneca miliyan ɗaya daga ƙasar Indiya a ƙarshen watan da mu ke ciki.

  12. Abin da ya tunzura manoma suka yi ba-ta-kashi da 'yan sanda a Indiya

    india

    Manoma sun tsallake shingayen da aka sanya sannan suka jurewa hayaki mai sa kwalla da aka rika fesa musu har sai da suka shiga Delhi babban kasar a ranar hutu ta kasar wadda ake kira India's Republic Day.

    Dubban manoma ne suka isa birnin a kan motocin tantan ko tarakta domin yin zanga-zanga a kan sabbin sauye-sauyen da gwamnatin kasar ta yi kan harkokin noman kasar.

    A wasu wuraren, manoma sun kakkarya shingayen sannan suka kauce daga kan hanyoyin da 'yan sanda suka amince su bi.

    Gangamin da suke yi ranar Talata yana cikin jerin zanga-zanga da suka kwashe wata da watanni suna yi, wadda daya ce daga cikin manya-manyan zanga-zanga da manoma suka yi a tarihin India.

    Shiga nan domin samun ƙarin bayyani

  13. Biden zai sanya hoton mace bakar-fata a takardar kuɗin dala

    Harriet Tubman

    Gwamnatin Biden ta ce zata ƙarfafa shirin sanya hoton ƴar fafutikar nan da ta yi gwagwarmayar yaƙi da bautarwa, Harriet Tubman a takardar kuɗin ƙasar na dala 20.

    Tun a shekara ta 2020 aka yi tunanin za a aiwatar da wannan shiri, na sanya hoton Ms Tubman da aka haifa a matsayin baiwa a 1820 a takardar kuɗin.

    Ma'aikatar baitul-malin ƙasar ta ce hoton Tubman zai maye gurbin tsohon shugaba, Andrew Jackson, wanda ya mallaki bayi.

    Sai dai wannan yunƙuri ya fuskanci tsaiko ƙarƙashin mulkin tsohon shugaba Donald Trump, wanda ya sanya siyasa a cikin batun.

    Yanzu shugaba Biden ya sake farfado da shirin, kamar yadda mai magana da yawun fadar White House, Jes Psaki ta shaidawa manema labarai.

    Jen ta ce nan bada jimawa ba za a aiwatar da wannan canji.

    Idan hakan ya tabbata, Ms Tubman za ta kasance bakar-fata ƴar Afirka da za a buga hoton ta a jikin takardar kuɗi na dala 20, kuma mace ta farko a tarihi Amurka da ke samun wannan matsayi a cikin sama da shekaru 100.

  14. MDD na fama da ƙarancin kuɗin yaƙi da farin ɗango a gabashin Afirka

    locust

    Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa jiragen da take amfani dasu wajen yaƙi da farin ɗango a gabashin Afirka za su daina aiki, idan ta gaggara samun tallafin dala miliyan 38.

    Yanzu haka dai ƙwarin na barazana a ƙasashen da suka kutsa irinsu Habasha, da Kenya da Somalia tare da barazana ga milyoyin manoma da dama annobar korona da ambaliyar ruwa ta kassara.

    Sabon rahoton hukumar ya nuna cewa farin sun farwa ƙasashe 11 na Afirka da suka hada da Kenya, sannan yanzu haka sun doshi wasu yankunan da suka hada da Tanzania.

  15. Korona na tafka ɓarna a Afrika ta Kudu

    SA

    Korona na ci gaba da zama barazana a Afirka ta Kudu inda mutum miliyan 1.4 suka kamu, 40,800 suka rasa rayukansu.

    Afirka ta Kudu ce kan gaba a Nahiyar afrika da yawan masu dauke da ita da kuma yaduwarta.

    Rahotanni daga ƙasar na cewa an cike asibitoci sannan har inda ake adana gawa a cike suke yayinda ake ci gaba da samun ƙaruwar masu mutuwa saboda annobar.

    Halin da ƙasar ta tsinci kanta na sake tsanani musamman a wannan lokaci da masana suka sake fahimtar cewa an sake samun bullar sabon nau'in annobar da tafi illa a ƙasar.

    Yanzu haka ƙasashe da dama ciki har da Amurka sun haramtawa baƙi daga Afirka ta Kudu shiga ƙasarsu.

  16. Shafin sada zumuntar da ya zama matattarar samari da ƴan matan arewa

    TIKTOK

    Shafin sada zumunta na Tik Tok ya samu karɓuwa sosai a wurin samari da ƴanmata a arewacin Najeriya. Kusan a iya cewa ma yana daga cikin shafukan sada zumunta da ke samun ƙaruwar masu amfani da shi.

    Babu mamaki a lokacin da kuke shawagi a shafin Instagram ko Twitter, kun ci karo da wani bidiyo mai ɗauke da alamar TikTok da wata budurwa ko saurayi suna ta bin waƙar Hausa ko ma ta turanci.

    Babu mamaki ba ku taɓa ganin budurwar ko saurayin ba, amma kun ga sun burge ku musamman yadda bidiyon ba shi da tsawo — ɗan gajere ne amma ya ƙayatar.

    Wataƙil ma wannan ne ya sa ku ma kuka sauke manhajar TikTok a wayoyinku don ganin wainar da ake toyawa a wannan shafi mai miliyoyin bidiyo.

    Mafi yawa masu amfani da shafin TikTok matasa ne masu neman nishaɗi — wato ku su nishaɗantar ko su nishaɗantu. Shi ya sa ma kusan duka bidiyon da ke wannan shafi yana ɗauke da waƙa ko rawa ko kwaikwayo ko kuma duka

    Latsa nan domin karanta cikakken labarin

  17. An samu ɓullar sabon nau'in annobar korona ta Burtaniya a Najeriya

    NCDC

    Shugaban hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu ya shaida cewa an samu ƴan ƙasar hudu dauke da sabon nau'in annobar korona mai haɗari irin ta Burtaniya.

    Ihekweazu, ya ce daga cikin wadanda aka samu dauke da cutar uku ƴan ƙasar ne da suka dawo daga balaguro, sai kuma ɗaya da bai je ko ina ba.

    Ya shaida cewa ba abin mamaki bane samun bullar wannan nau'in a ƙasar la'akari da yada ake tafiye-tafiye tsakanin Burtaniya da Najeriya.

    NCDC ta ce zata cigaba da daukan matakai da fadada ayyukanta da hadin-gwiwar da take samu, ganin cewa rufe ko hana jiragen ƙetare sauka a ƙasar a yanzu da wuya.

  18. Na tafka asarar miliyan 50 a gobarar gidana - Sunday Igboho

    GOBARA

    Mutumin da ya umarci Fulani makiyaya su fice daga yankin kudu maso yammacin Najeriya, Sunday Igboho ya ce ya tafka asarar miliyan 50 a gobarar da ta tashi a gidansa.

    Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na asubahin yau Talata wasu mutane suka cinna wuta a gidan Sunday Igboho.

    Sai dai ba ya gidan saboda ya tashi daga can inda ya koma wani gidan, amma dai gidan da aka cinna wa wuta shi ne babban gidansa da ke birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet da wasu jaridun Najeriya sun nuna yadda wasu bangarori na gidan suka kone.

    Latsa nan domin karanta cikakken rahoton

  19. Gwamnatin Ganduje ta yi barazanar hukunta shugabannin makarantun kwana

    BBC

    Gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar soma hukunta shugabannin makaratun sakandare na kwana, kan ƙin kwana a makarantar da suke kula da ita.

    Kwamishinan Ilimin jihar, Muhammad Sunusi Kiru ne ya shaida hakan ga manema labarai a Jihar, bayan samun rahotannin da ke nuna cewa akasarin shugabannin basa kwana a cikin makarantu.

    Ana dai zargin muggan laifuka da dabi'u da ake samu a wasu makarantun na faruwa ne saboda ƙin mayar da hankali da wasu shugabanni ke nuna wa wajen kula da ɗalibai da kuma kasance da su a makaranta.

    Muhammad Kiru ya gargaɗi malamai da shugabannin makarantu wajen mayar da hankali da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na bai wa ɗalibai kulawa da ilimi mai inganci.

  20. Gwamnati ta yi barazanar sake rufe sansanonin NYSC

    NYSC

    Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar sake rufe sansanonin masu yiwa ƙasa hidima wato NYSC, a jihohin da ke karya ka'idojin kare kai daga kamuwa da korona.

    Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya shaida hakan ne a lokacin taron da kwamitin yaƙi da annobar wato PTF ke gudarwa a Abuja.

    Kwamitin ya ce masu yiwa ƙasa hidima 700 a wannan rukunin na yanzu haka sun kamu da annobar.

    Minista ya ce ya zama wajibi a rinka bin dokoki, sannan masu yiwa ƙasa hidima da aka samu dauke da annobar an dakatar da su daga sansanonin da ake basu horo zuwa lokacin da za su samu lafiya.