Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Ban kwana

    An muka kawo karshen labarai da rahotannin namu sai kuma gobe

  2. An nemi gwamnan Legas ya sauka daga mukaminsa

    Video content

    Video caption: Latsa domin sauraron rahoton Umar Shehu Elleman

    Wata kungiyar gina sabuwar Naijeriya ta New Nigera Network ta yi kira ga gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sauka daga kan kujerar gwamna.

    Wannan ya zo a lokacin da wata kungiya ta daban, ta Access To Justice ta nemi Ministan watsa labarai a kasar, Alhaji Lai Muhammad ya sauka daga mukaminsa na minister.

    Sun bukaci haka kamar yadda suka ce rahoton kwamitin da gwamnatin jihar Legas ta kafa ya samu jami’an tsaro da laifi.

    Bayan wasu mambobin kwamitin sun shiga gidan talbijin suna fadin abinda suka gabatar.

    Wani lauya kuma wakililin gwamnatin Jihar Legas a zaman kwamitin, yace abinda wasu daga cikin membobin kwamitin suka aikata sun saba alkawarin da suka dau rantsuwa cewa ba zasu fadawa kowa game da rahoton a mataki na farko ba.

  3. Yan sanda sun ce sun kashe 7 cikin wadanda ake zargi da kai harin Kampala

    BBC

    'Yan sanda a Uganda sun ce sun kashe mutum bakwai tare da kama sama da 106 yayin wadandu samame na musamman biyo bayan hare-haren da aka kai Kampala babban birnin kasar, a makon jiya.

    kungiyar ISIS ta yi ikrarin kai na ranar 16 ga watan Nowamba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai, ciki har da 'yan kunar bakin wake uku ya kuma raunata mutane da dama.

    Wani jami'in dan sanda na cikin mutane hudu da aka kashe, kuma 27 cikin 37 da suka raunata yan sanda ne.

  4. An yi jana'izar tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara da 'yan bindiga suka kashe

    Mahalarta jana'iza

    An yi jana’izar Alhaji Sagir Hamidu, tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara wanda ‘yan bindiga suka kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

    An kashe Alhaji Sagir Hamidu a lokacin da ‘yan bindiga dauke da makamai suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

    A cikin wadanda suka halarci jana’izar har da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da kuma tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

    Malam Mohammed Sirajo Hamidu ƙanin marigayin ne kuma ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun buɗe wuta ne lokacin da direban yayansa ya yi ƙoƙarin juyawa domin komawa Kaduna bayan da suka fahimci cewa sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane.

    "Masu garkuwa da mutane ne suka tare hanya kuma suna zuwa sai suka tarar da abin da ke faruwa, ganin haka sai suka yi sauri suka juya, suna juyawa za su koma Kaduna sai wasu mutum uku suka fito daga cikin daji suka tsaya a gabansu su ka buɗe wa motarsa wuta, harsashi daya ya same shi a ƙirji, daya kuma a kafarsa," a cewarsa.

    Ya kuma ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da jami'in dan sanda daya da ke tsaron lafiyar marigayin ya yin da dirbarsa ya kubuta.

    Mahalarta jana'iza
  5. Rikici ya barke tsakanin Falasdinawa da dakarun Isra'ila

    rikici

    Rikici barke tsakanin matasan Falasdinawa da sojojin Isra'ila a yankuna daban-daban a gabar yanna da kogin Jordan, a safiyar yau.

    Jami'an Isra'ila sun kama Falasdinawa 12 a yamma da gabar kogin Jordan a gabashin birnin Kudus, kamar yadda kungiyar gidajen yarin Falasdinawa ta bayyana.

    Shugabannin sojojin Isra'ila sun bayar da umarnin girke wasu sojoji na ko ta kwana ganin yadda zaman dardar ke karuwa a yankin, biyo bayan wani dan Isra'ila da aka kashe a wani harbe-harbe a tsohon birnin Kudus.

    Kafafen yada labarai na cikin gida sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari gidan gwamnan Falasdinawa a birnin Kudus Adnan Ghaith tare harba wani abin fashewa a gidansa.

  6. 'Yan bindiga sun kashe mutum 12 a wani hari a sansanin 'yan gudun hijira

    Wani hari da 'yan bindiga suka kai a sansanin 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 12.

    Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun ce adadin mutanen da aka kashe ya zarta haka nesa ba kusa ba.

    Wata kungiya da ke sa ido ta ce 'yan bindiga ne da ke ikirarin kare al'ummar Lendu ta kai harin a arewa maso gabashin lardin Ituri.

    Galibin mazauna sansanin 'yan gudun hijirar al'ummar Hema da ke hamayya da al'ummar Lendu.

    An zargi kungiyar 'yan bindiga mai suna Cooperative for the Development of Congo (Codeco) - wadda galibin mambobinta 'yan kabilar Lendu - da kisan daruruwan farar hula da ke Ituri a shekaru biyun da suka gabata.

  7. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yiwuwar durkushewar bankunan Afghanistan

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gaggauta daukar matakin kare tsarin banki a Afghanistan da ke cikin hadarin durkushewa.

    Majalisar Dinkin Duniyar na ba da shawarar bijiro da tsarin inshora domin cire kokwanto a zukatan masu ajiya da kuma samar da sauki kan bayar da lamuni bisa hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya.

    Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta ce akwai bukatar a yi hakan domin inganta abubuwan da Afghanistan ke iya samarwa da kuma bunkasa ayyukan jinkai.

    Tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko a Afghanistan cikin watan Agusta, an samu koma-bayan kayayyakin jinkai sannan an kwace biliyoyin daloli na kadarorin kasar.

  8. Labarai da dumi-dumiAPC za ta gudanar da babban taronta na kasa a watan Fabrairun 2022

    APC

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce za ta gudanar da babban taronta na kasa a watan Fabrairun shekarar 2022.

    Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar ta APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labaran da ke fadar shugaban kasa ranar Litinin bayan ganawa da Muhammadu Buhari.

    Shugaban kungiyar gwamnonin na APC ya gana da shugaban kasar ne tare da rakiyar shugaban riko na jam'iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Malla Buni da kuma gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

    Gwamna Bagudu ya ce sun zabi gudanar da taron a watan Fabrairu ne domin bayar da dama ga jihohi hudu su kammala zabukansu na cikin gida sannan kuma 'yan kasar su samu damar kammala bukukuwan Kirsimieti da na sabuwar shekara.

    A yayin da yake jawabi, Gwamna Buni ya ce ba su tsayar da ranar gudanar da taron ba ne saboda su samu damar sanar da hukumar zabe mai zaman kanta da kuma duk wasu masu ruwa da tsaki.

  9. An nemi Ganduje ya mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama Sule filayenta da ya 'sayar'

    Video content

    Video caption: An nemi Ganduje ya mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama Sule filayenta da ya 'sayar'

    Latsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton Khalifa Shehu Dokaji:

    Kungiyoyin kare fararen hula a jihar Kano sun bukaci gwamantin Kano da ta gaggauta mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama Sule filayen da ke harabar makarantar da ta sayar.

    Kungiyoyin kare fararen hular na wannan furuci ne dai karkashin gammayar kungiyoyin kare fararen hula a da ke Kano, inda suka ce abin takaici ne gwamantin ta Kano ta taba filayen jami'ar bayan nan da wasu lokuta za ta iya neman filayen da za su yi gine-gine don amfanin dalibai.

    Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin Kungiyar mallaman jami’o’i reshen Jami’ar ta Yusuf Maitama Sule suka koka dangane da yadda gwamantin ta Kano ke sayar da filaye da ke gefan harabar makarantar tare da wasu da ke cikin makarantar.

  10. Wata ta watsa wa saurayinta asid saboda ya fasa aurenta

    asid

    An kama wata mata ƴar shekara 35 mahaifiyar ƴaƴa biyu kan zargin watsa wa wani saurayinta asid saboda ya fasa aurenta, kamar yadda ƴan sanda suka tabbatar a cewar kamfanin dillacin labarai na PTI a Indiya.

    An kama matar ne a ranar Asabar, kuma an bayyana mutumin a matsayin Arun Kumar wanda ke jinya a asibiti.

    Ƴan sanda sun ce mutumin mai shekara 28 yana fuskantar barazanar rasa idonsa ɗaya sakamakon sanadarin asid da matar mai suna Sheeba ta watsa masa.

    Ƴan sandan sun shaidawa PTI cewa sun haɗu ne a Facebook, daga baya kuma mutumin ya fahimci cewa tana da aure kuma har tana da ƴaƴa biyu. Ya nemi ya kawo ƙarshen soyayyarsu, amma sai ta yi ƙoƙarin tozarta shi tare da neman ya biya ta kuɗi.

    Sun ce Kumar tare da ɗan uwansa da abokinsa sun tafi wata coci kusa da Adimali inda suka haɗu da ita da nufin ya ba ta kuɗin da ta nema.

    Amma na’urar kamara da ke sa ido a cocin da aka fitar a yau Litinin ya nuna yadda Sheeba da ke tsaye kusa da Kumar ta matso kusa ta watsa masa asid a fuska, ko da yake ita ma ta samu rauni, a cewar ƴan sandan.

    Yan sandan sun ce suna tsare da matar yanzu haka.

  11. Ƴan sandan Kaduna sun ce sun ceto mutum 11 daga cikin waɗanda aka ɗauke a hanyar Abuja

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto mutum 11 daga cikin matafiyan da ƴan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi.

    Kwamishinan ƴan sandan Kaduna ya ce jami’an ƴan sanda da sojoji sun yi ƙoƙarin korar ƴan bindiga kuma sun yi nasarar kuɓutar da mutum 11.

    A ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

    Sun kuma kashe wasu ciki har da wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

    Zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana yawan mutanen da aka kashe ba da kuma yawan waɗanda aka sace.

    Lamarin ya jefa jama’a musamman direbobi da fasinjoji masu yawan bin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano cikin fargaba.

    Yan sanda
  12. WhatsApp ya sauya ka'idojin kiyaye sirri bayan tarar da aka ci shi

    Whatsapp

    WhatsApp na sake sauya ƙa'idojin kiyaye sirri a sakamakon gagarumar tarar kare bayanai da aka ci kamfanin a farkon shekarar nan.

    Karanta labarin a nan

  13. Ana zanga-zangar kyamar dokar kullen korona a Turai

    zanga-zanga

    Belgium ta zama ƙasa ta baya bayan nan da ta fuskanci mummunar tarzomar nuna ƙin jinin dokar kullen korona.

    Masu zanga-zangar a Brussels sun yi arangama da ƴan sanda bayan wani tattaki na fiye da mutum dubu 30.

    Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaro inda suka dinga jifan jami’an tsaron da duwatsu. Su kuwa jamai'an sun harba musu barkonon tsohuwa.

    Neitherlands ma ta gamu da rikici mafi muni a ƙarshen mako lokacin da masu tada hatsaniya suka mamaye birnin Rotterdam suna cinna wa ababen hawa wuta, kamar yadda ta faru a birnin Heague.

    A Austria da Croatia da Denmark ma mutane sun tunzura, sakamakon sake sabunta dokar kullen koronar a ƙasashen.

    zanga-zanga
  14. Yankin da ya fi ko ina sanyi a Najeriya

    Gembu

    An yi imanin cewa tsaunin Mambila shi ne wuri mafi sanyi a duk fadin Najeriya.

    A tsaunin da wuya ake amfani da na'urorin bayar da sanyi kamar su firji da fanka da na'urar sanyaya ɗaki saboda ba a buƙatarsu.

    Karanta labarin a nan

  15. Taliban ta haramta wa mata fitowa wasannin kwaikwayo a talabijin

    Afghanistan

    Gwamnatin Taliban ta haramta wa mata fitowa wasannin kwaikwayo a gidajen talabijin na Afghanistan ƙarƙashin wasu sabbin dokoki da ta kafa.

    An kuma tilasta wa mata ƴan jarida da masu gabatar da labarai su dinga amfani da abin rufe kai, ko da yake ba a fayyace nau’in abin rufe kai da matan za su yi amfani da shi ba.

    Sabbin dokokin guda takwas na Taliban sun haɗa da haramta nuna film da ya saɓa wa shari’a da al’adun Afghanistan.

    Haka kuma an haramta wa maza nuna tsaraicinsu.

    An haramta duk wani wasan kwaikwaiyo ko nishaɗi na cin mutuncin addini ko kuma wanda ke nuna cin mutuncin ƴan Afghanistan.

    Sannan duk wani fim da ke tallata al’adun wasu ƙasashe ba za a nuna shi ba a ƙasar.

  16. Aisha Buhari za ta jagoranci taron matan shugabannin Afrika a Abuja

    Nan gaba a yau Litinin za a buɗe taron ƙoli na ƙungiyar Matan Shugabannin ƙasashen Afirka a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Yayin wannan taro da matan shugabannin ƙasashen Afirka za su halarta, ana sa ran Uwargidan shugaban Najeriya kuma mai masaukin baƙi, Aisha Buhari za ta aza harsashin gina Sakatariyar Dindindin ta ƙungiyar.

    Taron zai ƙunshi liyafar tara gundunmuwa don bunkasa sakatariyar kungiyar

    Matan shugabannin Afrika masu yawa ne da manyan ƴan kasuwa masu masana’antu da abokan ƙawance ne ake sa ran za su halarci taron.

    Tuni matan shugabannin Afrika kamar ta Burundi da Congo Brazzaville da Sao Tome da Saliyo suka sauka a Abuja, kamar yadda Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Facebook.

    Asiah Buhari
    Aisha Buhari

    Ana sa ran ƙarin matan shugabanni irinsu na Ghana da Cote d’Ivoire da Nijar da Liberia za su iso Abuja a ranar Litinin.

    Sanarwar da ofishin yada labarai na uwargidan shugaban Najeriya ya fitar a ƙarshen mako ta ce an kafa ƙungiyar tabbatar da zaman lafiya ta shugabannin matan Afrika 1997 a matsayin wani reshe ga matan shugabannin ƙasashen Afrika don bayar da gudunmuwar goyon baya ga Tarayyar Afrika da ƙungiyoyin ƙasashen yankin da kuma gwamnatoci da nufin inganta zaman lafiya da rage rikice-rikice da illolinsa a nahiyar Afrika

  17. Ƙasashen duniya sun yi maraba da dawo da Hamdok a Sudan

    Sudan

    Kasashen duniya sun yi maraba da sabuwar yarjejeniyar da ta ba Firaministan Sudan Abdallah Hamdok damar komawa kujerarsa, ko da yake ƴan adawa na kallon hakan a matsayin cin amana.

    Kungiyar Tarayyar Afirkata EU da Birtaniya da Canada da Saudiyya sun yi maraba da yarjejeniyar a matsayin wani mataki na komawa kan tsarin mulkin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.

    Amurka ta kira matakin a matsayin mai ƙarfafa gwiwa, amma ta gargaɗi jami'an tsaron Sudan da kada su yi amfani da ƙarfi fiye da kima kan masu zanga-zangar lumana.

    Labarin yarjejeniyar ya gaza hana dubban mutane ci gaba da zanga-zanga a kan tituna.

    Masu sukar yarjejeniyar na shakkun cewa da wuya sojoji su bai wa Firaministan da aka mayar da majalisar ministocinsa ta kwararru damar sakewa su yi abin da ya dace.

  18. Wizkid ya lashe kyautar mawaƙa ta Afrika

    Wizkid

    Mawakin Najeriya mai salon kiɗan Afrobeats ya lashe kyautar mawaƙa ta AFRIMA 2021 a bikin da aka gudanar a ranar Lahadi.

    Wizkid ya lashe kyautar mawaƙin shekara, waƙar shekara da kuma waƙar haɗin gwiwa da ta fi shahara.

    Mawaƙin NajeriyaFireboy DML ne ya karɓi kyautar masoya yayin da mawaƙiyar Kenya Nikita Kering ta karɓi kyautar gwarzuwa a salon waƙar RnB.

    An gudanar da bikin ne a birnin Lagos, kudancin Najeriya.

  19. Ana fatarar kwaroron roba a Kenya

    kwaroron roba

    Gwamnatin Kenya ta buƙaci ƴan ƙasar su yi amfani da wasu hanyoyi yayin da ake fama da ƙarancin kwaroron roba.

    An bayyana cewa ƙasar na fama da ƙarancin kwaroron roba, inda alƙalumma suka nuna cewa kwaroron miliyan 1.6 gwamnati ta samar maimakon miliyan 455 da ya kamata a samar a shekara.

    A cewar Star Kenya, wani rahoto da asusun yaƙi da cutar AIDS da tarin fuka da maleriya ya nuna cewa kwaroron roba miliyan 20 aka raba a ƙasar.

    Jaridar ta ambato ma'aikatar lafiya ta ƙasar na cewa gwamnati za ta yi ƙoƙarin magance matsalar fatarar ƙwaroron roba da ake yi a ƙasar.

    Lamarin dai ya haifar da muhawara musamman a kafofin sadarwa na intanet, saboda yadda wasu ke la'akari da manufar amfani da kwaroron roba domin kare cutuka da kuma hana ɗaukar ciki.

    Rahotanni dai sun nuna cewa an samu ƙarancin ne sakamakon haraji da gwamnati ta saka wa kayayyaki.

  20. Hatsarin mota ya halaka mutum 159 a Abuja a 2021

    Tasi a Abuja

    Hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya FRSC ta ce jimillar mutum 156 suka mutu daga hatsarin mota 850 na ababen hawa da suka faru a Abuja a shekarar 2021.

    Adadin mutum 1,572 suka ji rauni a hatsurran. Alƙalumman sun shafi daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba.

    Kwamandan hukumar na Abuja Oga Ochi ne ya bayyana haka a ranar Asabar.

    Ya kuma ɗora alhakin yawan hatsurran ga yawan saɓa dokokin tuƙi da kuma rashin haƙuri daga masu ababen hawa.

    Kuma a cewarsa yawan mugun gudu ne ya fi haddasa hatsarin a Abuja.