Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a yinin Lahadi.

  2. Ana ƙarancin magani a yankin Tigray – Red Cross

    Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce asibitoci a yankin Tigray da ke arewacin Ethiopia na fama da karancin magani, biyo bayan makonni uku da aka shafe ana gwabza rikici.

    Da ta ke bayani a Addis Ababa babban birnin kasar, Shugabar kungiyar Red Cross a Ethiopia Maria Soledad ta ce kimanin kashi 80 na marasa lafiya a Makelle na fama da matsalar damuwa.

    Sai dai gwamnati a gefe guda na ikirarin karbe iko da babban birnin yankin, kamar yadda sakatariyar yada labaran Firaministan kasar Billeni Seyom ta bayyana wa BBC.

    Billeni ta ce “zan iya tabbatarwa dakarun kasarmu sun karbe iko da birnin Mekkele tun ranar Asabar, tare da mamaye wurare masu mahimmanci kamarsu filin jirgin sama da asibitoci.”

  3. Fitaccen ɗan ƙwallon Senegal Papa Bouba Diop ya mutu

    Tsohon ɗan wasan Senegal Papa Bouba Diop ya mutu, kamar yadda hukumar Fifa ta sanar a ranar Lahadi.

    Bouba Diop wanda ya fara cin ƙwallo a gasar cin kofin duniya ta 2002 a Koriya-Japan, ya mutu ne yana da shekara 42.

    "Fifa ta ƙadu da samun labarin mutuwar Papa Bouba Diop," kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta sanar a shafinta na Twitter.

    View more on twitter

    Tsohon ɗan ƙwallon Super Eagles na Najeriya kuma tsohon kocin Super Eagles ya ce Afirka ta yi babban rashin ɗaya daga cikin manyan ƴan ƙwallonta.

    View more on twitter
  4. Ana zargin likitan Maradona da kashe ɗan ƙwallon

    Maradona

    Ana binciken likitan Diego Maradona da zargin yin kisa, bayan mutuwar shahararren ɗan ƙwallon Argentina a ranar Laraba.

    Ƴan sanda a Buenos Aires sun kai samame gidan Leopoldo Luque domin bincike da kuma wani asibiti mai zaman kansa don samun shaidar ko ya yi sakaci, bayan da ƴaƴan Maradona mata suka yi koken rashin nuna kulawa ga rashin lafiyar mahaifinsu.

    Maradona ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a ranar Laraba yana da shekara 60.

    A farkon watan Nuwamba, an yi nasarar yi masa tiyata kan daskarewar jini a kwakwalwarsa kuma ana diba lafiyarsa kan hana shi dogaro da barasa.

    A tsawon rayuwarsa ya yi fama da shan ƙwaya kuma ya yi fama da rashin lafiya dab da ƙarshen rayuwarsa.

    Maradona shi ya jagoranci Argentina ga nasarar lashe kofin duniya a 1986.

    Kuma ana ɗaukar shi ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallon da babu kamarsu a duniya.

    Maradona
  5. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum 110 aka kashe a Borno

    Gawawwakin mutane

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin mutum 110 aka kashe a harin da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka kai wa manoma kusa da garin Maiduguri a ranar Asabar.

    A cikin wata sanarwa, mai kula da ayyukan jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniyar Edward Kallon ya ce manoma ne aka kashe a harin da ya kira mummunan tashin hankali.

    Bayan kisan, gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya yi kira ga matasa su shiga aikin ƴan banga ko sa-kai domin yaƙi da ta’addanci.

    Babagana Zulum ya yi wannan kiran ne yayin ziyarar jaje a yankin Zabarmari da aka kai harin.

  6. Messi ya sadaukar da ƙwallon da ya ci Osasuna ga Maradona

    Lionel Messi ya karrama Diego Maradona bayan da ya ci kwallo a karawar da Barcelona ta doke Osasuna 4-0 a gasar La Liga a ranar Lahadi.

    Messi, mai shekara 33, ya saka rigar tsohuwar ƙungiyarsa da Maradona Newells Old Boys - bayan ya ci wa Barca ƙwallo ta huɗu a ragar Osasuna.

    Messi kuma ya kwaikwayi hoton Maradona da aka nuna a majigi a fili inda ya ɗaga hannu sama kamar Maradona.

    Bayan da ya ci ƙwallon Messi ya ɗaga rigarsa ta Newell's Old Boys mai lamba 10, wadda shi ma Maradona ya saka a lokacin da yana kulub din a 1993.

    Martin Braithwwaite da Antoine Griezmann da Philippe Coutinho suka ci wa Barcelona sauran ƙwallayen.

    A ranar Laraba ne Maradona ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallon duniya ya mutu yana da shekara 60

    Kafin wasan Barcelona ta ware minti ɗaya domin karrama Maradona, tsohon ɗan wasanta tsakanin 1982 zuwa 1984.

    View more on instagram
  7. PDP na son Buhari ya gaggauta zuwa Zabarmari inda aka kashe mutum 43 a Borno

    Kisan mutum 43 a Zabarmari
    Image caption: Buhari ya yi Allah wadai da kisan manoma 43 a Borno

    Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi Allah wadai da kakkausar murya da yankan ragon da ƴan ta’adda suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari na jihar Borno.

    Cikin sanarwar da ta aika wa BBC, Jam’iyyar PDP ta jajantawa al’ummar jihar Borno tare da bayyana ɗanyen aikin a matsayin zalunci, wanda ta ce dole a ɗauki mataki.

    “Irin wannan mummunan kisan ya ƙara nuna gazawar gwamnatin Buhari na tabbatar da tsaron ƙasa da rayuka da kuma dukiya a ƙasarmu.” In ji PDP.

    Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana ɓacin ransa tare da yin Allah wadai da kisan manoman a Zabarmari, wanda ya bayyana a matsayin hauka.

    PDP ta ce ta damu kan gazawar gwamnatin Buhari na kasa ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki duk da koke-koken gwamnan Borno Babagana Zulum kan matsalar tsaro a jiharsa.

    Jam’iyyar kuma a cikin sanarwar ta ce “ Buhari ya gaggauta zuwa Zabarmari a jihar Borno domin jajantawa mutanen Borno da ƴan uwan waɗanda aka kashe, sannan ya kuma jagoranci yakin tabbatar da tsaro da yankin.”

  8. Zulum ya roki matasa su shiga aikin sa-kai a Borno

    Gwamna Zulum

    Gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya roƙi matasan jihar su shiga aikin sa-kai domin taimakawa a kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.

    Gwamna Zulum ya yi wannan kiran ne bayan kisan da wasu da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka yi wa manoma 43 a wani ƙauyen da ke kusa da garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

    Gwamnan kuma ya yi wannan kiran e lokacin da je ta’aziya da jaje ga mutanen garin Zabarmari da lamarin ya faru.

    Sojojin Najeriya sun kasa kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram a arewa maso gabas, inda aka kashe sama da mutum dubu goma.

    A makon da ya gabata sojoji shida rahotanni suka ce an kashe a wani harin kwanton ɓauna a Borno.

  9. An kashe jami’an tsaron Afghanistan 30 a wani mummunan hari

    Aƙalla jami’an tsaron Afghanistan 30 aka kashe a wani harin bam da aka kai da mota a kan wani sansanin soja da ke Ghazni, a gabashin kasar.

    Ana ganin wannan shi ne hari mafi muni da aka kai a cikin ƴan watannin nan kuma ya zo ne duk da shirin zaman lafiya tsakanin gwamnati da ƴan Taliban.

    A ranar Asabar, wani mai magana da yawun Taliban ya ce ɓangarorin biyu - da ke ganawa a Doha - sun amince da tsarin tattaunawar. Amma gwamnati na taka-tsantsan.

    Masu sharhi na nuna cewa shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani, yana adawa da wasu sharuddan.

    Shugaban a yau ya gana da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Dr Abdullah Abdullah, shugaban ƙungiyar da ke kula da tattaunawar sulhun, a wani mataki na ƙoƙarin warware saɓanin.

  10. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram biyar

    Wani wuri da aka ƙona

    Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe 'yan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda biyar ranar Juma'a a Jihar Borno.

    Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar, Benard Onyeuko, ya fitar ta ce dakarunsu sun fafata da 'yan bindigar a garuruwan Garal da Bulankesa, inda suka kashe mayaƙa biyu sannan wasu suka tsere da raunuka.

    A dai ranar Juma'ar, an yi wata fafatawar a yankin Ashigashiya, abin da ya yi sanadiyyar kashe wasu mayaƙan ƙungiyar biyu sannan aka ƙwace kayayyakin abinci daga sansaninsu tare da lalata shi.

    Kazalika, sojoji sun kashe wani ɗan Boko Haram a yankin Doksa, inda suka ƙwato bindigar AK-47 ɗaya da wayar salula biyu da kuma katin shaidar Boko Haram.

    A yau Lahadi ne aka yi jana'izar wasu manoma 43 da 'yan Boko Haram ɗin suka yi wa yankan rago a gonakinsu da ke Zabarmari ta jihar Borno.

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce akwai mata guda 10 da ba a san inda suke ba bayan harin, waɗanda ke aiki a wata gonar shinkafa da ke garin Koshebe na Zabarmari.

    Mutum 16 daga cikin waɗanda aka kashe 'yan gudun hijira ne, in ji Amnesty.

    Mazauna yankin sun faɗa wa Gwamna Zulum, wanda ya jagoranci jana'izar, cewa har yanzu ba su gama tantance yawan waɗanda aka kashe ba.

    View more on twitter
  11. Da gaske ministan matasan Najeriya ya nemi miliyan 81 don nome ciyawa a filin wasa?

    Sunday Dare

    Ministan Wasanni da Matasa a Najeriya, Sunday Dare ya musanta rahotannin da ke cewa ya ce ma'aikatarsa na buƙatar naira miliyan 81 domin sharewa tare da nome ciyayin da ke filin wasa na Abuja.

    Jardar Daily Trust ta ruwaito ministan yana bayyana haka ne yayin wani taron ƙara wa juna sani da ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta shirya a Abuja.

    "Mun nemi hukumar kula da mahalli ta birnin Abuja ta zo ta duba yadda za a yi game da nome ciyawa a filin wasan, sai suka faɗa mana cewa za a kashe naira miliyan 81," a cewar ministan kamar yadda jaridar ta ruwaito.

    A cikin rahoton, ministan ya ce "ba mu da wannan kuɗi, shi ya sa muke haɗa kai da masu zuba jari domin yin gyararraki". "Idan muka faɗa wa 'yan Najeriya cewa mun kashe miliyan 81, wadda ma ba mu da ita, za a yi ƙaorafi."

    A martaninsa, Mista Dare ya ce bai faɗi haka ba, yana mai cewa an gurɓata kalaman nasa.

    Sai dai jaridar ta sauya kanun labarin nata daga cewa ministan ne ya faɗa zuwa cewa hukumar kula da mahalli ta birnin Abuja ce ta faɗa.

    Rahoton na Daily Trust ya jawo mutane da dama sun soki ministan a shafukan zumunta, inda wasu suka riƙa kwatanta shi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal, wanda Buhari ya kora daga aiki samakaon zargin kashe maƙudan kuɗi wurin nome ciyawa a sansanin 'yan gudun hijirar Boko Haram.

    View more on twitter
  12. Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 29/11/2020

    Video content

    Video caption: Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 29/11/2020
  13. 'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da saka abin fashewa a coci a Rivers

    Jihar Rivers

    An kama mutum biyu a Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya bisa zargin saka abin fashewa a cocin mahaifin Gwamna Nyesom Wike na jihar.

    Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a jiya Asabar a cocin mai suna Christian Universal Church International da ke Fatakwal, inda masu bauta suka yi rige-rigen fita amma ba tare da an ji rauni ba.

    Matasan yankin ne suka kama mutanen biyu da ake zargi da dasa ababen fashewar kafin 'yan sanda su isa wurin.

    'Yan sandan sashen kwance bam sun tare hanyar shiga cocin yayin da suke aikin kwance abubuwan a lokacin da tawagar BBC Pidgin ta isa wurin.

    Jihar Rivers
  14. Messi v Maradona

    Shin Messi zai iya shafe tarihin marigayi Maradona a duniyar ƙwallon ƙafa?

    View more on twitter

    A wannan bidiyon na sama, Awwal Ahmed Janyau ya yi nazari kan taurarin wasa biyu da wasu ke ganin babu kamarsu a tarihin ƙwallon ƙafa baki ɗaya.

    Ku latsa hoton da sama domin ganin abin da Awwal ya zaƙulo bayan mutuwar Diego Maradona ranar Laraba yana da shekar 60.

    Kamanceceniya tsakanin Messi da Maradona

    • Dukkaninsu 'yan Argentina ne
    • Tsawonsu ɗaya
    • Dukkaninsu lamba 10 suke sakawa
    • Dukkaninsu kyaftin ne
    • Dukkaninisu sun buga wa Barcelona wasa
  15. Abin da ake nufi da mazgaye, dama da hauni, sunkuye ga sarakunan gargajiya

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari shirin na Amsoshin Takardunku

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambaya ne game da yadda aka samo kirari irinsu gyara kintsi, mazgaye, dama da hauni, sunkuye waɗanda ake yi wa sarakunan gargajiya.

    Farfesa Tijjani Muhammad Naniya na Jami'ar Bayero ta Kano ne ya amsa tambayoyin a cikin shirin da Nabeela Muktar Uba ta gabatar.

  16. Labarai da dumi-dumiRikicin ƙabilanci ya ɓarke a Jos na Jihar Filato

    Rahotanni daga Bukur na Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato na cewa ana arangama tsakanin ƙabilun yankin.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa yanzu haka jami'an tsaro na harbi a sama domin tarwatsa matasan da ke jefe-jefe da duwatsu.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Jihar Filato Uba Gabriel bai tabbatar da faruwar lamarin ba amma ya ce zai bincika.

    An fara rikicin ne tsakanin al'ummar Hausawa da kuma sauran ƙabilun yankin bayan zargin juna da fara aikata kisa.

    Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu...

  17. Najeriya: 'Na'urorin tantance kaya na hukumar Kwastam a Apapa ba sa aiki'

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari shugaban Kwastam na gaɓar ruwan Apapa, Muhammad Abba Kura

    Hukumar yaƙi da fasa ƙwauri a Najeriya ta Kwastam ta ce na’urorin da ke tantance kayayyaki da ake shigo da kuma fita da su waɗanda ake kira Scanners a gabar ruwan Apapa ba sa aiki.

    Shugaban Kwastam na shiyyar Apapa, Muhammad Abba Kura, ya ce lamarin zai iya haifar da tsaiko wurin tantance cunkoson sunduƙan kwantenoni.

    Sai dai kuma ya ce suna samun nasarar daƙile matsaloli da ake samu a gabar tekun na Apapa.

  18. Eden Hazard ya sake jin rauni

    Eden Hazard

    Eden Hazard ya sake jin rauni a wasan da Alaves ta doke Real Madrid 2-1 har gida a daren Asabar.

    Hazard wanda wasa uku kawai aka fara da shi a Laliga ta bana, an sauya shi minti 28 kacal da fara wasan bayan ya turguɗe ƙafa.

    Lucas Perez ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Madrid daga bugun finareti bayan ƙwallo ta taɓa hannun Nacho.

    Daga baya Joselu ya ƙara ta biyu sakamakon kuskuren da Thibaut Courtois ya yi na ba shi ƙwallo a ƙafarsa kafin daga bisani Casemiro ya farke guda ɗaya.

    Rashin nasara ta uku kenan da tawagar Zidane ta yi, abin da ya sa take a matsayi na huɗu da tazarar maki shida tsakaninta da Real Sociedad da kuma Atletico Madrid, jagororin teburin La Liga.

    Wasa 27 kacal Hazard mai shekara 29 ya buga tun bayan komawarsa Real Madrid a 2019 kan kuɗi fan miliyan 150.

  19. 'Cutar korona za ta ci gaba da kashe mutane a Amurka'

    Amurka

    Ƙwamitin kar-ta-kwana kan annobar korona da zababben shugaban Amurka Joe Biden ya kafa ya yi hasashen karuwar alkaluman masu kamuwa da korona da mace-mace bayan hutun cikaciki na Thanksgiving.

    Daya daga cikin mambobin kwamitin Celine Gounder ta shaida wa tashar CBS cewa akasarin Amurkawa da ke bikin Thanksgiving tare da iyalai da abokansu za su ƙare a asibiti bayan Kirsimeti da bukukuwan sabuwar shekara.

    Ta ce su ma jami'an lafiya da suka shafe watanni suna yaki da wannan cuta na son a ba su damar hutu su je su kasance da iyalansu a wannan lokaci.

    Milyoyi sun yi balaguro zuwa hutu duk da gargadi da rokon su zauna a gida.

    Sama da mutum 200,000 ne suka sake kamuwa da korona a fadin Amurka a ranar Juma'a.

  20. Zan isar da saƙonku ga Buhari kan Boko Haram – Isa Pantami

    Dr. Isa Ali Pantami

    Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Intanet a Najeriya, Isa Ali Pantami, ya ce zai isar da saƙon al'umma ga Shugaba Muhammadu Buhari game da kisan mutum 43 da 'yan Boko Haram suka yi.

    A jiya Asabar ne aka samu rahoton 'yan bindiga sun shiga gonakin mutanen kuma suka yi musu yankan rago a yankin Koshebe na Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno.

    Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter bayan wani mai amfani da shafin ya roƙe shi da ya yi hakan.

    "Ya Sheikh @DrIsaPantami - muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban qasa magana. Mutum arba’in da hudu (43) ko a movie aka kashe lokaci daya abun da ban tsoro. Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai abun ya fara yawa," a cewar Boss Mustapha (@__yellows).

    Shi kuma Isa Pantami ya mayar masa da martanin cewa: "Muna yin hakan kuma za mu ci gaba da yi. Zan isar masa da wannan kamar yadda na yi magana da Gwamna Zulum ɗazun nan. Allah Ya ji ƙansu kuma Ya kawo ƙarshen wannan masifa."

    Yankin arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro baya ga Boko Haram da suka haɗa da 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

    Rahotanni na cewa an yi garkuwa da mutum fiye da 1,500 a yankin tare da biyan kuɗin fansa masu ɗimbin yawa.

    Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa ran mutum fiye da 36,000 sannan an rusa gidaje fiye da kashi 30 cikin 100 na Jihar Borno baki ɗaya.

    View more on twitter