Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Sarauniya Elizabeth ba za ta samu damar halartar buɗe majalisa ba

    .

    Gidan sarautar Birtaniya ya sanar da cewa Sarauniya Elizabeth ba za ta samu halartar buɗe majalisa a birnin London ba.

    Fadar Buckingham ta ce har yanzu sarauniya na fama da rashin lafiya don hakan ba za ta iya halartar bikin ba da za ayi gobe.

    Fadar ta kara da cewa Yarima Charles ne zai yi jawabi a madadin mahaifiyar tasa.

    A cikin jawabin ne ake bayyana shirye-shirye masu zuwa da gwamnatin Birtaniya za ta yi.

  3. Putin ya yi ƙarin bayani kan matakinsa na kutsawa Ukraine

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana matakinsa na kutsawa Ukraine a matsayin wanda ke bisa ka'ida.

    Shugaban ya bayyana haka ne yayin gagarumin faretin murnar nasara kan dakarun Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.

    Putin daga bisani ya zargi NATO da yin gangamin soji a kasashen da ke makwabtaka da Rasha.

    Ya kuma fada wa sojojinsa cewa suna yaki ne kan abin da wadanda suka gabace su suka yi a lokacin yakin duniya na biyu, wato tsaron kasa.

    To amma a martaninsa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Mr Putin na maimaita ta'asar da Adolf Hitler na Jamus yayi ne kawai.

  4. Labarai da dumi-dumiWasu ƙungiyoyin arewacin Najeriya sun saya wa Jonathan fom a APC

    ,.

    Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ƙungiyoyin arewacin ƙasar sun haɗa hannu inda suka saya wa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan fom din takarar shugabancin ƙasar

    Duk da cewa Jonathan ba ɗan Jam'iyyar APC bane, amma ana ta ce-ce-ku-ce a kwanakin baya kan cewa yana daf da sauya sheƙa daga PDP ya koma APC.

    A 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Jonathan a zaben ƙasar, amma tun bayan nan Jonathan ya ci gaba da gudanar da ayyukan ƙungiyar ECOWAS inda ya rinƙa zuwa sasanci a wasu ƙasashen Afrika.

  5. Firaiministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya yi murabus

    ..

    Firaiministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya yi murabus yayin da kasar ta tsunduma cikin rikici tsakanin masoya da masu adawa da gwamnatinsa.

    Akalla mutun biyar suka mutu 150 kuma suka jikkata a taho mu gamar da aka yi. Kazalika an kona gidajen yan siyasar da ke tare da iyalan Rajapaksa.

    Yanzu haka Sri Lanka na karkashin dokar ta baci, kuma an hana fita a fadin kasar. Rikicin ya biyo bayan boren kin jinin gwamnati saboda matsin tattalin arziki da kasar ta samu kanta.

    Ana sa ran kafa sabuwar gwamnati da ake fatan ta farfado da tattalin arzikin na Sri Lanka.

  6. 'Kada a kuskura a dawo da jirgin ƙasa sai an ceto ƴan uwanmu'

    ..

    Iyalan mutum 62 da aka sace a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun yi gargaɗi kada a kuskura a dawo da jigilar fasinjoji har sai an ceto musu yan uwansu.

    Sun bayyana haka ne a Kaduna a ranar Litinin a yayin wani taron manema labarai inda suka buƙaci a gaggauta ceto musu yan uwansu cikin ƙoshin lafiya.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun duka iyalan da aka sace a jirgin ƙasan inda yake zargin hukumar gudanar da ayyukan jiragen ƙasa ta Najeriya wato NRC da yin biris da umarnin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na haɗa hannu da su iyalan wajen tsara yadda za a ceto ƴan uwansu.

    Ya ce NRC ba ta tuntuɓi kowa daga cikin iyalan waɗanda aka sace ba domin ba su labari kan wani ci gaba da aka samu.

  7. Mutum 11 sun ɓace a Ghana bayan jirgin ruwa ya nutse

    ..

    An soma neman mutum 11 waɗanda suka ɓace bayan wani jirgin ruwa na kamun kifi ya nutse a cikin teku a Ghana.

    Masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin gano gawar matuƙin jirgin wanda ɗaya ne daga cikin mutum shida waɗanda ƴan China ne da ke cikin jirgin.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da ma'aikatan jirgin ke ƙoƙarin ɗauko ragar kamun kifi wadda ke cike maƙil da kifaye da kuma rashin kyawun yanayi waɗanda duk sun taimaka wurin nutsewar jirgin.

    Wasu daga cikin ma'aikatan jirgin sun yi ƙoƙarin ninƙaya zuwa wani jirgin ruwa da ke kusa wanda ya cece su.

    Masu kai agaji ciki har da rundunar sojin ruwan Ghana da ta sojojin sama da sauran jiragen kamun kifi na ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.

  8. An kama matasan da suka ci zarafin mata yan yawon bude ido a Masar

    .

    Masu shigar da kara a Masar, sun bada umarnin tsare wasu yara maza 13 da aka kama kan zargin cin zarafin mata biyu 'yan yawon buɗe ido a wurin dalar Giza.

    Masarawa sun fusata a makon da ya wuce bayan bullar wani bidiyo da ya nuna gungun matasan na yi wa matan 'yan kasashen waje da suka je kasar. Sanarwar masu shigar da kara na cewa an kama matasa mazan, masu shekaru 13 zuwa 15.

    Sun yi ikirarin kawai suna son daukar hoto da 'yan matan ne, ba su zo da niyyar yi musu wulakanci ba. Ana kuma zargin yaran da durawa matan ashariya, da kokarin taba su kamar yadda wanda ke yi wa matan rakiya ya shaida wa jami'an tsaro.

    Za a ci gaba da tsare yaran a gidan kangararrun yara, kafin a kammala bincike, kamar yadda sanarwar ta karkare.

    Cikin bidiyon mai sakan 35, ana iya jin muryar dan rakiyar matan na korafin yara mazan na bin matan da gudu, ya na kuma son ministan da ke kula da fannin ya dauki mataki akai.

  9. An saya wa Sanata Ahmad Lawan fom din takarar shugaban kasa

    Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya

    Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun saya wa shugaban majalisar takardar takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki.

    A yau Litinin ne 'yan majalisar suka saya wa Ahmad Lawan takardar, inda wasu daga cikin 'yan majalisar da suka hada da Sanata Bello Mandiya da Sanata Barau Jibrin da Sanata Yusuf A. Yusuf suka je sakatariyar jam'iyyar domin sayen fom din.

    Sanata Ahmed Lawan shi ne, mai mukami mafi girm a majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya, saboda haka ana kallon shiga takarar tasa a matsayin wani babban abu.

    A baya dai wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da ministoci da wasu gwamnoni sun sayi takardar neman takarar, wadda jam'iyyar ke sayarwa a kan naira miliyan 100.

  10. Kotu ta ki amsa bukatar Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan takarar shugaban kasa

    Godwin Emiefele
    Image caption: Emiefele na son neman takarar shugabancin Najeriya ne ba tare da ya ajiye mukaminsa ba

    Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ki yarda da bukatar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emiefele ta ba shi kariyar neman takarar shugaban kasa ba tare da ya sauka daga kujerarsa ba.

    Mista Emiefele dai ya gabatar da bukatar kotun ta ayyana cewa yana da damar neman takarar shugabancin a karkashin duk jam'iyyar da yake so, yayin da yake rike da mukamin gwamnan bankin.

    Tun da farko a yau Litinin lauyan Emiefele, Mike Ozekhome, ya bukaci kotun da ta amsa bukatarsu ta bayar da umarni na wucin-gadi na hana Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) da Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari'a na Tarayya daga hana shi shiga zaben fitar da gwani na duk jam'iyyar da yake so.

    Da yake zartar da hukunci, alkalin kotun Ahmed Mohammed, ya ayyana cewa, maimakon haka sai dai ya umarci hukumar zaben da Babban Lauyan su bayyana a gabanta ranar 12 ga watan Mayu domin su bayar da bahasinsu kan dalilin da suke ganin kotun bai kamata ta amsa bukatar Mista Emiefele ba.

    A zaman na yau Litinin, lauyan gwamnan ya ce zuwa ranar Laraba 11 ga watan Mayu, wa'adin karbar takardar bayyana sha'awar yin takarar shugaban kasar zai kare

    A ainahin karar da lauyan Gwamnan Babban Bankin ya gabatar ranar biyar ga watan Mayu, 2022, lauyan ya ce babu wata dokar kasar da ta hana Mista Emiefele takara yana rike da kujerar shugabancin bankin.

    Ana matsa wa Mista Emefiele lamba ne da ya sauka daga mukami tun bayan da bayanai suka bayyana na aniyarsa ta neman takarar shugabancin kasar a jam'iyya mai mulkin kasar, APC, a farkon shekarar nan.

    A watan Fabrairu na shekara mai zuwa ne 2023, za a yi babban zaben kasa a Najeriya, inda za a zabi wanda zai gaji Shugaba Muhammdu Buhari wanda zai kammala wa'adinsa na biyu na shekara hudu-hudu.

  11. Iyalan wadanda aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi zanga-zanga

    Masu zanga-zanga
    Image caption: Iyalan na cikin damuwa sosai kan kasa ceto 'yan uwan nasu

    'Yan uwa da iyalan wadanda aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi zanga-zangar lumana a titunan kaduna a yau Litinin domin nuna damuwarsu kan rashin ceto ko sakin wadanda aka sacen.

    Haka kuma a Abuja ma babban birnin kasar, wasu iyalai da 'yan uwan wadanda aka sacen sun gudanar da taron manema labarai a kan lamarin.

    A ranar 28 ga watan Maris ne, wasu 'yan bindiga suka tayar da bam a kan layin dogo na jirgin, sannan kuma suka bude wa jirgin da ke cike da fasinjoji wuta, inda suka hallaka wasu sannan suka yi awon gaba da wasu.

    Zuwa yau Litinin, kwana 42 kenan bayan harin har yanzu ba a sako wadanda aka sace din ba, inda bayanai suka nuna cewa wadanda suka sace su sun gabatar wa da gwamnatin kasar wasu bukatu kafin su saki mutanen.

    Hukumomin Najeriya na dora alhakin harin a kan 'yan kungiyar Boko Haram.

  12. Shugabar Tanzania ta yi taron gaggawa don shawo kan tashin farashin mai

    Shugaba Samia Hassan
    Image caption: Shugaba Samia Hassan ta nemi da a gaggauta samo hanyar magance tashin farashin

    Shugaba Samia Hassan ta Tanzania ta yi wani taron gaggawa na majalisar ministocinta a kan matsalar tashin farashin mai a kasar.

    Shugabar ta kira taron ne wanda ta jagoranta cikin daren da ya gabata na Lahadi domin tattauna yadda za a bullo wa tashin farashin, wanda hukumar da ke kula da makamashi da ruwa ta sanar da tashin farashin wanda ta ce ba a taba gani ba, a makon da ya gabata.

    Shugabar kasar ta bayar da umarni ga wadanda suka halarci taron da su gaggauta lalubo hanyar da za a bi domin shawo kan matsalar tashin farashin man.

    Taron majalisar zartarwar da aka yi a birnin Dar es Salaam na gabar teku ya samu halartar Firaminista Kassim Majaliwa da ministan makamashi da na kudi da sauransu.

  13. Dubbai sun kaurace wa karbar maganin cutar kanjamau a Mozambique

    Maganin rage kaifin cutar kanjamau
    Image caption: Yawanci sun daina zuwa karbar maganin ne saboda tsangwama

    Hukumomi a Mozambique sun ce masu dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki sama da dubu 14 sun daina zuwa karbar maganin rage kaifin cutar a watanni uku na farkon shekara a lardin Zambézia na tsakiyar kasar.

    Shugabar shirin yaki da cutar a yankin, Dr Cheinaze Veríssimo, ta ce, yawancin wadanda suka daina zuwa karbar maganin maza ne.

    Ya dora alhakin yawan kauracewar a kan tsangwama da kyama da ake nuna wa masu cutar.

    Sama da mutane dubu 300,ne ke karbar maganin rage kaifin cutar da AIDS ko SIDA a lardin na Zambézia.

    Likitan ya ce matsalar da suke fuskanta ita ce, idan mutum ya daina shan maganin, bayan ya fara, hakan zai sa kwayar cutar ta kara karfi, abin da zai iya sa mutum ya kamu da rashin lafiya sosai har ma a wni lokaci abin ya kai ga rasuwa.

    Dr Veríssimo ya ce yanzu jami'an lafiya za su rika kai maganin har gida ga jama'a, ga wadanda ba za su iya zuwa asibiti ba, saboda rashin lafiyar ko kuma gudun tsangwama.

  14. Firaministan Sri Lanka ya sauka saboda zanga-zangar ƙin gwamnati

    Sri Lanka PM

    Hukumomin Sri Lanka sun ce firaministan kasar, Mahinda Rajapaksa, ya sauka daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar kin gwamnati ta gama-gari da ake yi da kuma tsadar rayuwa.

    Mista Rajapaksa, ya ajiye aiki ne yayin da aka sanya dokar hana zirga-zirga bayan mummunan tashin hankalin da aka samu tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma masu goyon bayan firaministan da dan uwansa, Shugaba Gotabaya Rajapaksa.

    Rahotanni daga wani asibiti a babban birnin kasar Colombo, sun nuna cewa an jikkata akalla mutum 78 a tashin hankalin da aka gwabza a wajen fadar shugaban kasar.

  15. An haramta wa mata wasu na'ukan gyaran jiki da suka haɗa da halawa da dilka a Iran

    Matan Iran

    An hana wasu daga cikin nau'ukan kwalliyar mata a birni na biyu mafi girma a Iran, wato Mashshad.

    Shugabar kungiyar masu gyaran gashi ta birnin ta ce, abubuwan da aka haramta sun hada da gyaran jiki na mata irin su halawa da dilka da karin farce da zane a jiki na wuta ko aska (tattoo) da gyaran fuska na maida-tsohuwa-yarinya.

    Ta ce an dauki matakin ne saboda haramci na addini, kuma hakan ya tilasta wa wuraren gyaran jiki da kwalliyar mata da dama sun rufe.

    Shugabar ta kuma sanar da cewa ana gudanar da sintiri a sassan birnin domin tabbatar da bin dokokin.

    Birnin Mashhad babbar cibiya ce ta ziyarar ibada, inda miliyoyin jama'a ke ziyartar hubbaren Imam Reza, a kowace shekara.

  16. An dakatar da rusau a unguwannin Musulmi a India saboda zanga-zanga

    Matan Indiya Musulmai

    Hukumomin India sun dakata da wani aiki na tsawon kwana 10 na rushe gine-gine da suka ce an yi su ba bisa ka'ida ba, a babban birnin kasar, Delhi, bayan da daruruwan masu zanga-zanga suka datse tituna domin hana manyan motoci na rusau wucewa.

    Gwamnati ta shirya rushe gine-ginen shaguna da duk wasu gidaje da aka gina ba bisa ka'ida ba, a filayen hukuma a yankin Shaheen Bagh da wasu yankuna na kusa.

    Sai dai mazauna unguwannin sun zargi gwamnatin jam'iyya mai mulki ta BJP da harar yankin da Musulmi suka fi yawa.

    Wani daga cikin manyan 'yan jam'iyyar ta BJP, Adesh Gupta, ya zargi jam'iyyun hamayya da shiga zanga-zangar, inda ya ce hakan ya nuna goyon bayan da suke yi wa Musulmi 'yan Rohingyas da 'yan Bangladesh.

  17. Najeriya ba ta dauki mataki ba wata shida bayan rahoton zanga-zangar #ENDSARS - HRW

    Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch ta zargi hukumomin Najeriya da kin daukar matakin tabbatar da adalci ga masu zanga-zangar neman kawo karshen zaluncin 'yan sanda wato #ENDSARS, a jihar Lagos a 2020, bayan wata shida da kwamitin binciken da aka kafa ya zargi jami'an tsaro da cin zarafin mutane a lokacin.

    A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Litinin, ta bukaci gwamnati da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar a dauka a kan wadanda aka zarga da aikata laifi.

    Kungiyar ta ce, ba zai yiwu a kawar da kai a kan rahoton ba, ba tare da wani abu ya biyo bayan hakan ba a kan wadanda ake zargi da kisa da kuma jikkata masu zanga-zangar.

    Ta ce muddin ba a dauki mataki ba a kan shawarwarin kwamitin, hakan zai harzuka wadanda abin ya shafa, tare kuma da karfafa wa jami'an tsaro guiwa kan cin zarafi.

    A watan Oktoba na 2020 daruruwan matasa suka kwarara a titunan biranen wasu jihohin Najeriya, suna zanga-zangar neman a rushe rundunar 'yan sanda ta musamman mai yaki da 'yan fashi da makami, wato SARS, wadda ta yi kaurin suna da cin zarafin jama'a, tare kuma da kawo karshen zaluncin da 'yan sanda ke yi, abin da ya janyo jami'an tsaro suka mayar da martani da karfin da ya wuce kima.

    Daya daga cikin inda lamarin ya fi kamari shi ne na mashigar Lekki da ke Lagos wato Lekki Toll Gate, inda aka bayar da rahoton cewa sojoji da 'yan sanda sun bude wuta a kan masu zanga-zangar, har suka kasahe tare da jikkata mutane, abin da su kuma suka musanta.

  18. Yakin Ukraine: Harin bam ya kashe mutum 60 a makaranta - Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce wani bam da aka harba ya fada wata makaranta ya hallaka kusan mutum 60 a gabashin kasar.

    Tun da farko, gwamnan yankin Luhansk, Serhiy Haidai, ya ce mutum 90 ne ke zaman mafaka a ginin makarantar da ke Bilohorivka, kuma an ceto 30.

    Mista Haidai ya ce wani jirgin saman yaki na Rasha ne ya jefa bam din a ranar Asabar, sai dai Rasha ba ta ce komai ba a kan lamarin.

    Ana mummunar musayar wuta a Luhansk, yayin da dakarun Rasha tare da mayakan 'yan aware ke kokarin yi wa sojin gwamnatin Ukraine kawanya.

    Mafi yawan yankin na karkashin ikon 'yan aware masu samun goyon bayan sojojin Rasha, a shekara takwas da ta gabata.

    Harin ya rushe ginin, wanda ya kama wuta, abin da ya dauki 'yan kwana-kwana sa'a uku kafin su kashe wutar, kamar yadda gwamnan yankin ya bayyana a shafinsa na Telegram.

    Ya ce wanda ya ce kusan dukkanin mazauna kauyen sun fake ne a ginin karkashin kasa na makarantar, ya kara da cewa ba za a san yawan wadanda suka mutu ba sai bayan an kwashe baraguzan ginin.

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce mummunan harin ya tayar masa da hankali, inda ya ce dole ne a rika tabbatar da kare fararen hula a lokacin yaki.

  19. BBC ta gano inda aka kashe sojoji ango da amarya a kudancin Najeriya

    Ango da amarya da aka kashe
    Image caption: Hukumomin Najeriya sun zargi 'yan kungiyar a-ware ta Biyafara da yi wa sojojin kisan gilla

    Sashen gano gaskiyar labari na BBC ya gano cewa an kashe amarya Private Gloria Matthew, da angonta Warrant Officer Linus Musa Audu (mai ritaya), da kuma wasu danginsa biyu a yankin Orlu da ke jihar Imo, a kudu maso gabashin Najeriya.

    Hoton bidiyon kisan sojojin, ango da amarya wanda ya karade shafukan intanet a makon da ya gabata, ya janyo maganganu, inda har wasu suke karyata shi da cewa ba na gaskiya ba ne, wasu kuma suke cewa ba a Najeriya ba ne, a Kamaru ne.

    A binciken kwakwaf da BBC ta yi ta gano cewa hoton bidiyon na gaskiya ne ba hada shi aka yi ba.

    Wani daga cikin dangin ma'auratan da ke da cikakkiyar masaniya kan abin da ya faru, ya sheda wa BBC cewa wasu matasa ne hudu dauke da makamai suka yi musu kwanton-bauna a lokacin da ma'auratan ke hanyarsu ta zuwa garin amaryar, a karamar hukumar Nwekere ta jihar Imo, daga Lagos domin gudanar da al'adarsu ta aure, da aka shirya yi ranar Litinin biyu ga watan Mayu, 2022.

    Mutumin ya ce, maharan sun kama su ne a wani wuri kusa da mahadar Banana a Orlu da ke jihar Imo, inda suka shiga daji da su suka hallaka su, inda suka daddatse musu kai.

    Dangin ya ce, angon wato Audu ya fito ne daga kudancin Kaduna amma yana zaune a Makurdi. Ita kuwa amarya Gloria, 'yar kabilar Igbo tana aikin soji ne a Sokoto.

    Mutumin ya ce, jagoran 'yan bindigar ya sa an harbe 'yan uwan mijin biyu a ranar da aka kama su 30 ga watan Afrilu, saboda wai makiyansu ne, Hausawa.

    Ya ce an kashe su a gaban 'yar Gloria mai shekara 10 da mahaifiyart, in ji dangin nasu.

    Hukumomin sojin kasa na Najeriya, da Shugaba Muhammadu Buhari sun zargi kungiyar 'yan aware ta Biyafara da laifin kisan. abin da ita kungiyar ta musanta.

  20. Kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya sun fasa yajin aiki

    Kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya sun janye aniyarsu ta dakatar da aiki a fadin kasar, da suka tsara yi a yau Litinin.

    Shugaban kungiyar kamfanonin (AON), Abdulmunaf Sarina, ya bayyana a wata sanarwa ta hadin guiwa da suka sanya wa hannu cewa sun dauki matakin ne domin gudun jefa tattalin arzikin kasar cikin wani haloi, tare kuma da la'akari da halin tsaro da ake ciki a Najeriyar.

    A ranar Juma'a kungiyar ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aikin saboda tashin farashin man jirgi, wato JetA1, inda kamfanonin ke sayen man a kan naira 700 farashin da kusan ya ninka a wannan shekara, ta wani bangare saboda yakin da Rsaha ke yi a Ukraine, lamarin da ya sa kudin da kamfanonin ke kashewa a harkarsu ya karu da kusan kashi 95 cikin dari.

    Gwamnatin Najeriya ta roki masu kamfanonin jiragen da su yi la'akari da abin da yajin aikin nasu zai iya haddasawa ga kasar, su hakura.