Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Imam Saleh

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Imam Saleh

    Multimedia Broadcast Journalist

    A nan za mu dasa aya wajen kawo muku labaran duniya kai tsaye sai kuma gobe idan da yawan rai.

    Amma kafin nan za ku iya komawa ƙasa don samun labaran da muka kawo muku a tsawon wannan rana.

    Nine Imam Saleh. Allah ya sada mu da alkairi.

  2. Gobara ta lalata ilahirin ginin Majalisar Wakilan Afrika Ta Kudu

    Afrika Ta Kudu

    Hukumomin kasar Afirka ta Kudu sun ce wata gagarumar gobara da ta tashi a cikin ginin majalisar da ke birnin Cape Town ta lalata majalisar dokokin kasar gaba daya.

    Ƴan sanda sun kama wani da ake zargi, tare da gurfanar da shi da laifin fasa gida, da sata.

    Wani mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta kasar ya shaida wa gidan talabijin na Afirka ta Kudu cewa gobarar ta sa rufin babban ginin majalisar ya ruguje.

    Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda tun da farko ya ziyarci wurin, ya bayyana gobarar a matsayin mummunan al'amari.

  3. An kusa kawo ƙarshen Bello Turji - Tambuwal

    Aminu Waziri Tambuwal

    Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya sha alwashin cewa ya kusa kawo fitaccen ɗan fashin dajin nan Bello Turji, wanda ke ci gaba da addabar jihar Sokoto duk da farautarsa da jami’an tsaro ke yi.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a wani taro da shugabannin al’umma, sa’o’i kadan bayan da wasu gungun ‘yan bindiga suka kashe wani dan kasuwa a yankin tare da yin garkuwa da mutane biyar a Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birnin Jihar.

    ‘’Dab ake da a kawo ƙarshensa, kuma gwamnati ta ɗauki matakan da suka kamata don yi hakan da ma kawo ƙarshen yan bindigar da suka hana jama’a zaman lafiya’’ kamar yadda Premium Times ta rawaito shi yana faɗa.

  4. Daga sama aka ƙaƙaba wa Kanawa Ganduje a 2019 - Kwankwaso

    RABIU MUSA KWANKWASO

    Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake jaddada abun da ya sha faɗa a baya, cewa wasu manya ne daga sama suka tursasa wa al'ummar Kano gwamnan da yanzu yake kan mulki Abdullahi Umar Ganduje duk da cewa ya faɗi zaɓe a 2019.

    Yayin wata hira ta musamman da jaridar Punch Kwankwaso ya ce ''Na tabbatar yanzu wadanda suka yi hakan suna da na sanin abun da suka yi wa Kano. Duk jama'ar Najeriya sun san cewa Ganduje ya fadi zaɓen nan, amma haka suka tursasawa mafi yawan jama'a ra'ayin wadanda ba su taka kara sun karya ba wanda shi ne babban laifin da wani zai aikata''.

    Ya ƙara da cewa abun takaici ne yadda wasu tsiraru suka kasa ganin abun da talakawa suka hango wa kansu.

    ''Muna da ƙarin da iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma sai muka yi la'akari da cewa idan muka biye musu hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, don haka muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari'a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi'' inji Kwankwaso.

    A halin da ake ciki dai ana raɗe-raɗin sasantawa tsakanin tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje, bayan ziyarar ta'aziyya da Gandujen ya kai wa Kwankwaso.

  5. Zan wanke taɓargazar Nasir El-Rufai idan na zama gwamnan Kaduna a 2023 - Shehu Sani

    SHEHU SANI

    Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2023.

    Yayin hira da wani gidan rediyo a jihar, sanatan ya yi alkawarin wanke abun da ya kira ''tabargazar gwamnan jihar mai ci Nasir El-Rufa'i'' idan ya yi nasara.

    ''Duk wanda ya musguna wa jama'a ya ƙuntata musu bai cancanci ya samu kowacce irin dama ba, domin duka addinanmu sun girmama ɗan adam''.

    Shehu Sani ya ƙara da cewa a yanzu ya rage wa jam'iyyar PDP ta haɗe kan ƴaƴanta don ƙwatar mulki a hannun APC.

  6. Lionel Messi ya kamu da korona

    .

    Ɗan wasan gaban Pairs St-Germain Lionel Messi ya kamu da cutar korona.

    Ɗan wasan gaban na Argentina ya kasance ɗaya daga mutum huɗu na kulob ɗin da suka kamu da cutar.

    Sauran mutanen da suka kamu da cutar sun haɗa da Juan Bernat da Nathan Bitumazala da Sergio Rico.

    An tabbatar da sun kamu da cutar kwana guda kafin karawar kulob ɗin da Vannes a gasar French Cup.

    Ana sa ran ƴan wasan za su killace kansu har sai sun samu sauƙi.

    Shugaban na PSG Mauricio Pochettino ya bayyana cewa Messi zai ci gaba da zama a Argentina kuma ba zai bar ƙasar ba har sai ya warke.

  7. Jami'an tsaro a Sudan sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga

    .

    Jami'an tsaro sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa dubban masu zanga-zanga da ke adawa da mulkin soja a ƙasar waɗanda ke tattaki zuwa Khartoum inda suke so a kawo ƙarshen mulkin na soji.

    Tuni aka katse layukan sadarwa gabannin soma wannan zanga-zanga inda ƴan sanda ɗauke da makamai suka rufe gadoji da tituna da ake shiga birnin.

    Wannan zanga-zangar ita ce babbar zanga-zanga ta 12 da ake gudanarwa tun daga watan Oktoban bara bayan sojoji sun yi juyin mulki ga gwamnatin Firaiminista Abdallah Hamdok.

  8. Ƴan bindiga sun harbe mutum biyar a Igabi da Zangon Kataf

    ..

    Hukumomi a Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kashe mutum huɗu da kuma raunata ɗaya a wani hari da suka kai a Ƙaramar Hukumar Igabi da ke jihar.

    A wani saƙo da ma'aikatar harkokin cikin gida da tsaro ta jihar Kaduna ta wallafa a shafin Facebook, ƴan bindigan sun afka garin ne inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi tare da kashe mazauna garin huɗu.

    Mutanen da aka kashe sun haɗa da Lado Shuaibu da Usman Haruna da Ayuba Muntari da Jafar Abdullahi.

    Haka kuma an raunata wani Mamuda a yayin da ƴan bindigan suka sace babura da abinci a garin.

    Haka kuma wasu rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kashe wani mai suna Joshua Kawu bayan harbinsa da suka yi a ƙirji a Unguwan Rimi-Afana da ke Zangon Kataf.

  9. Akwai yiwuwar za a benca Lukaku a wasan Chelsea da Liverpool

    ..

    Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Chelsea kuma ɗan asalin Belgium zai zama ɗan kallo a wasan da ƙungiyarsa ta Chelsea za ta kara da Liverpool a yau Lahadi.

    A wata hira da aka naɗa makonni da dama da suka gabata amma aka saka ta a ranar Alhamis, ɗan wasan mai shekara 28 ya bayyana cewa ba ya jin daɗin irin rawar da yake takawa a Chelsea ƙarƙashin jagorancin Thomas Tuchel a farkon kaka.

    Ya bayyana cewa yana so ya koma Inter Milan ɗin da ya bari a watan Agustan bara a nan gaba.

    Sai dai kocin Chelsea Tuchel ya ce waɗannan kalaman sun jawo ce-ce-ku-cen da ba a buƙata.

    Ana ganin wannan hirar ta jawo masa matsala tsakaninsa da ƙungiyar tasa.

    Lukaku ya ci ƙwallaye bakwai a wasanni 18 da ya buga tun bayan da ya koma Chelsea a wannan kakar.

    Haka kum ya samu rauni tare da yin rashin lafiya a baya kuma a wasu lokutan ma ana benca shi duk da yana da lafiya.

  10. Zanga-zanga: Hukumomi a Sudan sun toshe layukan sadarwa

    .

    Hukumomi a Sudan sun toshe layukan sadarwa a daidai lokacin da masu zanga-zanga ke taruwa a wasu biranen ƙasar domin soma zanga-zanga ta farko a bana.

    Jami'an tsaron ƙasar sun sa shingaye inda suka rufe wasu hanyoyi a Khartoum babban birnin ƙasar.

    Masu zanga-zangar dai na neman sojojin ƙasar su bar siyasa su miƙa mulki ga farar hula.

    Wannan zanga-zangar ita ce babbar zanga-zanga ta 12 da ake gudanarwa tun daga watan Oktoban bara bayan sojoji sun yi juyin mulki ga gwamnatin Firaiminista Abdallah Hamdok.

    Sai dai sojojin sun mayar da shi kan muƙaminsa bayan wata guda amma daga baya an ci gaba da zanga-zanga.

    Sama da mutum 50 aka kashe tun bayan da aka soma wannan zanga-zanga.

  11. Ƴan bindiga sun sace matan aure da ƴan mata a Kaduna

    ..

    Aƙalla mutum 18 ƴan bindiga suka sace tare da kashe mutum guda a Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani jagora a wurin da lamarin ya faru inda ya ce cikin waɗanda aka sace har da matan aure da ƴan mata.

    An bayyana cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin 12:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi a garin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

    BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Kaduna Mohammed Jalige domin jin ƙarin bayani sai dai bai amsa kiranmu ba.

    Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ƴan bindiga suka addaba inda suke ci gaba da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa da kashe su a wani lokacin.

  12. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari kan mayaƙan Hamas

    ..

    Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a wasu wurare mallakar mayaƙan Hamas a kudancin birnin Gaza.

    Wannan harin na zuwa ne a matsayin martani bayan Falasɗinawan sun harba rokoki biyu ga Isra'ilar a jiya.

    Muhimman wuraren da mayaƙan Hamas ke zama domin sa ido na daga cikin wuraren da Isra'ilar ta harba wa bindigar atilari.

    Sojojin Isra'ilar sun bayyana cewa jiragen yaƙi da masu saukar ungulu sun kai hari a wani wurin da ake haɗa rokoki na Hamas.

    Rediyon Hamas ta tabbatar da rahoton cewa an kai hari ga wasu wuraren ta, ciki har da sansanonin horas da mayaƙa ta hanyar amfani da jirage da tankokin yaƙi.

    Wannan harin na zuwa ne bayan Hamas sun harba rokoki biyu a safiyar Asabar inda rokokin suka faɗa a tekun Mediterranean a kusa da birnin Tel Aviv.

  13. Labarai da dumi-dumiSarkin Ibadan Saliu Adetunji ya rasu

    ..

    Rahotanni daga Jihar Oyo a Najeriya na cewa Sarkin Ibadan ko kuma Olubadan, wato Oba Saliu Adetunji ya rasu.

    Oba Saliu ya rasu yana da shekara 93.

    Wani da ke a fadar sarkin wanda ba ya so a fadi sunansa ne ya tabbatar wa BBC da rasuwar sarkin.

    An bayyana cewa ya rasu ne a wani asibiti da ke Ibadan a safiyar Lahadi.

    A watan da ya gabata ne shi ma Sarkin Ogbomosho Jimoh Oyewumi ya rasu yana da shekara 95.

  14. Majalisar Dokokin Afrika Ta Kudu ta kama da wuta

    ..

    Gobara ta tashi a Majalisar Dokokin Afrika Ta Kudu wadda ke a birnin Cape Town.

    Wani bidiyo ya nuna yadda baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya tare da balbalin wuta da ke fitowa daga kan rufin ginin majalisar.

    Gwamman masu kashe gobara na wajen domin kashe wutar, haka kuma babu tabbaci kan abin da ya jawo gobarar.

    Wannan gobarar na zuwa ne sa'o'i bayan jana'izar Archbishop Desmond Tutu da aka yi a Cocin St George's Catheral da ke kusa da majalisar.

    Ginin majalisar dai ya kasu kashi uku, inda mafi daɗewa a ciki an gina shi tun a shekarun 1884. Sai kuma sabbin ɓangarorin an gina su ne a shekarun 1920 da kuma shekarun 1980.

    Ko a bara sai da gobara ta ƙona babban ɗakin karatu na Jam'iar Cape Town wanda ke ɗauke da takardu na tarihin Afrika.

  15. Ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan takarar gwamnan Filato

    ....

    Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Filato a zaɓen 2019, Nkemi Nicholas Nashe.

    Mista Nashe wanda jigo ne a Jam'iyyar PDP, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙaramar Hukumar Shendam a baya.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa wani makusancin Mista Nshe ɗin na cewa jama' na zaman ɗar-ɗar tun bayan faruwar wannan lamari a Shendam.

    Shi kansa gwamnan jihar mai ci a yanzu Simon Lalong ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Shendam.

    Sace Mista Nshe na zuwa ne ƙwanaki kaɗan bayan sakin wani basarake a jihar ta Filato da aka sace, Charles Mato Dakat.

    Sai dai sojoji da ke jihar sun bayyana cewa sun kama mutum takwas da suke zargi da hannu a sace basaraken.

  16. Barkanmu da safiya

    Mustapha Musa Kaita

    Multi-Media Broadcast Journalist

    Jama'a barkanmu da safiyar Lahadi, 2 ga watan Janairun 2022.

    A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.