Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotanni da muke kawo muku tsawon yini.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu za mu kawo muku labaran abubuwan da za su fara a duniyar.

    Mu kwana lafiya.

  2. Nasa ta sake fitar da bidiyon saukar mutum-mutuminta a Mars

    Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka Nasa, ta sake fitar da wani sabon bidiyo na saukar mutum-mutuminta na Perseverance a duniyar Mars.

    Nasa ta aika Perseverance ne zuwa Mars haɗe da kyamarori har bakwai, inda bakwai daga cikinsu aka dasa su don ɗaukar sauƙar mutum-mutumin kawai.

    Hotunan da kyamarorin za su turo su ne za su bai wa injiniyoyi damar ganin abin da ya kamata su inganta ta fannin fasaha don gano diddigin abin da suke bi a Jar Duniyar.

    Video content

    Video caption: Sabon bidiyon da Nasa ta fitar na isar mutum-mutumin Perseverance duniyar
  3. An kashe jakadan Italiya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo

    Luca Attanasio was travelling in a UN convoy in the east of the country
    Image caption: Luca Attanasio yana tafiya ne tare da tawagar MDD

    An kashe jakadan Italiya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo a wani hari da aka kai a gabashin ƙasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin waje ta faɗa.

    Luca Attanasio mai shekara 43 ya mut ne a asibiti ranar Litinin bayan da aka buɗe wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya wuta, wacce yake tafiya tare da ita a kusa da Goma, kamar yadda sanarwa ta faɗa.

    Tawagar dai ta Hukumar Shirin Abinci Ta MDD ce (WFP).

    Wani jami'in ɗan sanda na Italiya da wani direba ɗan Congo su ma sun rasa rayukansu a harin.

    An yi amannar cewa an kai harin na yankin Arewacin Kivu ne da zummar sace mutane, kamar yadda jami'ai a kusa da Gandun Namun Daji na Virunga suka ce.

  4. 'Najeriya ta yi rawar gani a yaƙi da cutar Aids'

    Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/Aids a Najeriya ta ce kasar ta yi rawar gani ta fuskar yaki da cutar da babu wata kasa a duniya da ta taɓa yi.

    Sai dai a lokaci guda ta ce akwai masu ɗauke da cutar sama da miliyan ɗaya da ba sa kan magani, kuma hakan wani babban kalubale ne a yakin da ake yi da cutar.

    Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wata bita kan nasarori da kuma kalubale tare da masu ruwa da tsaki yau a Abuja.

    Bayanai na cewa kasashe da dama a duniya shirinsu na kawar da cutar ya durkushe saboda cutar korona, sai dai a cewar Dr Gambo Aliyu shugaban hukumar, Najeriya da wasu kasashe shida sun dawo kan turbar fafutukar yaki da cutar gadan-gadan a bara.

  5. Mohamane Ousmane ne kan gaba da yawan ƙuri'u a zaɓen Nijar

    Mahamane Ousmane na RDR Tchanji
    Image caption: Mahamane Ousmane na RDR Tchanji

    Sakamakon zaɓen Nijar zagaye na biyu ya nuna cewa Mahamane Ousmane na RDR Tchanji ne ke kan gaba da yawan kuri'a fiye da abokin takararsa na jam'iyya mai mulki Mohamed Bazoum

    Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta fitar ya zuwa yanzu sun nuna cewa dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane yana da kuri'u 847, 435.

    Dan takarar PNDS Tarayya mai mulki Mohamed Bazoum kuma yana da kuri'u 803, 301 daga sakamakon da hukumar zaɓen ta bayyana kawo yanzu.

    Tazarar ƙuri'a 44,134 Mohamane Ousmane ya ba Mohamed Bazoum kawo yanzu.

    Wakiliyar BBC ta ce sakamako gundumomi 111 CENI ta bayyana yayin da ya rage saura gundumomi 150.

    Mahamane Ousmane ya samu yawan kuri'u ne a jihohin Yamai da Tilaberi yayin da ake ganin Bazoum zai iya kere shi idan aka bayyana sakamakon Tahoua da sauran sakamakon jihar Zinder da yake da ƙarfi.

    A ranar Lahadi aka gudanar da zaben zagaye na biyu inda aka fafata tsakanin Mohammed Bazoum da abokin karawarsa na jam'iyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane.

    Nan ba da jimawa ba ake sa ran sanar da sakamakon zaben.

  6. ISWAP ta yi iƙirarin kashe sojojin Najeriya 10

    Sojojin Najeriya

    Ƙungiyar IS mai da’awar jihadi reshen Afrika ta yi ikirarin kashe sojojin Najeriya 10 a wani hari da ta kai ƙarshen mako.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, IS ta ce “mayaƙanta sun yi wa sojin Najeriya kwantan ɓauna a kan hanya tsakanin Kava da Gorgi” a jihar Borno inda ta ce ta kashe sojoji 10 da jikkata wasu 20.

    Sannan ta lalata motocin sojojin tare da ƙwace makamai.

    Sai dai babu wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin Najeriya game da ikirarin na ISWAP.

    ISWAP wani ɓangare ne da ya ɓalle daga Boko Haram.

    A kwanan nan ne Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bai wa dakarun soja wa'adin kwana biyu domin su fatattaki 'yan ƙungiyar Boko Haram daga garin Marte da wasu garuruwa biyu na Jihar Borno.

  7. Lai Mohammed ya umarci yin yaren bebaye a gidajen talabijin

    Lai Mohammed

    Ministan watsa labaran Najeriya da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya umarci hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasar NBC ta awaitar da tanadin dokar hukumar da ta buƙaci gidajen talabijin yin yare bebaye a labaransu domin amfanin masu lalurar.

    Ministan ya bada wannan umarnin ne ranar Litinin lokacin da tawagar cibiyar masu buƙata ta musamman ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja.

    Ya ce ya tabbata daga gobe za a fara aiki da umarnin da ya bayar a gidajen talabijin tare da alkawalin cewa ba da dewa ba za a ga sauyi.

  8. An miƙa wa Ganduje rahoton muƙabala da Sheikh Abduljabbar

    Ganduje

    Kwamitin da gwamantin Kano ta kafa kan yadda za a gudanar da muɓabala da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman ya mika rahotonsa gaban gammana Abdullahi Umar Ganduje.

    Kwamishinan harkokin addini a jahar Malam Muhammad Tahar Adam da aka fi sani da Baba Imposible ya ce cikin buƙatun da kwamitin ya gabatar wagwamanan jahar sunhaɗa da gayyato manyan malaman da ake da su a kasar daga ɓangaren Izala da Tijjaniya da Ƙadiriya tare da wakilci daga fadar sarkin Musulmi.

    Amma kuma Baba Impossible ya ce har yanzu gwamanatin jahar bata tsayar da ranar da zaa gudanar da muƙabalar ba.

  9. Buhari ya yi sabon babban dogari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sabon dogari Laftanar Kanal YM Dodo wanda ya maye Kanal Muhammad Lawal Abubakar

    An nuna hoton yadda shugaban ya yi bankwana da dogarin nasa da kuma yin maraba da sabon dogarin.

    View more on twitter
  10. Kotu ta ɗaure matashin da ya damfari Ba’amurke da sunan soyayya

    EFCC

    Wata babbar kotun Ibadan a jihar Oyo yankin kudu maso yammacin Najeriya ta ɗaure wani matashi bayan kama shi da laifin damfarar wani ɗan Amurka.

    Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da shi gaban kotun inda kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin wata shida.

    A sanarwar da ta fitar a Twitter, EFCC ta ce matashin wanda ya ce ɗalibin Jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola ne ya yi amfani da sunan mace ya damfari Ba’amurke inda ya karɓi dala 1,200.

    “Ya yi masa ƙarya cewa shi ɗan Amurka ne mai suna Amanda da ke matuƙar ƙaunarsa,” a cewar EFCC.

    Ya kuma amsa laifin da ake tuhumarsa a gaban alƙalin kotun inda kuma kotun ta buƙaci ya mayar wa Ba’amurken kuɗinsa da ya damfara.

  11. Ashraf Ghani ya yi maraba da matakin NATO kan janye dakaru a Afghanistan

    Ashraf Ghani

    Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya yi maraba da sanarwar da ƙungiyar tsaro ta NATO ta yi cewa ba ta yanke hukunci na ƙarshe ba game da janye dakarunta daga Afghanistan.

    Da yake magana da BBC, Mista Ghani ya ce matakin NATO zai sake ƙarafa guiwa wajen hanzarta batun yin sulhu da ƙungiyar Taliban.

    Ya buƙaci ƙungiyar ta Taliban da ta nemi a yi sulhun. Mista Ghani ya ce ya yi matuƙar farinciki da alaƙarsa da sabuwar gwamnatin Amurka.

    Gwamnatin Biden tana sake nazari kan yarjejeniyar da aka cimma shekarar da ta gabata tsakanin Amurka da Taliban wadda ta mayar da shugaban Afghanistan saniyar ware.

  12. Kamfanin Boeing ya ba da shawarar dakatar da amfani da jirginsa ƙirar 777

    Kamfanin ƙera jirgin sama na Boeing da ke Amurka ya bayar da shawarar dakatar da tashin jirginsa ƙirar 777 har sai an kammala bincike.

    Injin jirgin mallakar United Airlines ya kama da wuta kuma ya faɗo a kusa da Denver a Colorado jiya Lahadi.

    Wata sanarwa da hukumar kula da sufuri ta Amurka ta fitar ta bayyana cewa an samu matsala kuma fankokinsa biyu sun ƙarye.

    Hukumar da ke kula da sufurin jirgin sama a Amurkar ta bayar da umarnin a yi bincike kan samfurin jiragen.

    Japan ta nemi dukkanin jiragen saman da ke amfani da injin da su ƙaurace wa sararin samaniyarta.

  13. Dubun dubatar masu zanga-zanga sun sake fitowa a Myanmar

    Myanmar

    Dubu daruruwan masu zanga-zanga ne suka hau kan tituna a ci gaba da nuna bacin rai kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Myanmar.

    An rufe shagunan kasuwanci sannan ma’aikata ma sun shiga macin, duk da gargadin da sojojin suka yi cewa masu zanga-zangar "na wasa da rayuwarsu".

    'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a babban birnin ƙasar, Nay Pyi Taw, kuma an ga motar ruwa na ƙarasawa wurin taron mutanen.

    An shafe makwanni ana zanga-zanga a Myanmar tun bayan juyin mulkin na ranar 1 ga watan Fabarairu.

    Tawagar sojoji ta tumɓuke zaɓaɓɓiyar gwamnatin Aung San Suu Kyi kuma suka yi mata ɗaurin talala, suna masu tuhumarta da mallakar wayar tarho ta jami'an tsaro ba bisa ƙa'ida ba da kuma karya dokar kare afkuwar bala'o'i ta ƙasar.

  14. Adadin mata ma'aikatan gwamnati ya ninka sau 25 a Saudiyya

    Mata a Saudiyya

    Adadin mata ma'aikatan gwamnati a Saudiyya ya ninka sau kusan 25 cikin shekara 10, a cewar wani rahoton binciken da Family Affairs Council ta gudanar.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito rahoton na cewa adadin matan da suka shiga aikin harkokin tsaro da na soja sun kai 9,408 ya zuwa ƙarshen 2019.

    Kazalika, wasu mutum 500 na neman aikin soja yanzu haka.

    Jumullar adadin mata ma'aikata a Saudiyya ya ƙaru zuwa 484,000 a 2019 daga 21,000 a 2010, abin da ya kai kusan ninki 25 a cikin shekara 10.

    Matan da ke aiki a rundunar soja, su ne kashi biyu cikin 100 na dukkan matan da ke aikin gwamnati a Saudiyya.

    Sai dai an taƙaice ayyukan mata sojoji da na ɓangaren tsaro a ofis-ofis da kuma bayar da taimako kawai.

  15. Kalli bidiyon mutane na taka sayyada a Kano saboda yajin aikin masu adaidaita sahu.

    Video content

    Video caption: Mutane na taka sayyada a Kano saboda yajin aikin masu adaidaita sahu.

    Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta kama mutum biyu da take zargi da shirya zanga-zangar da direbobin babur mai ƙafa uku wato adaidaita-sahu suka yi niyyar yi a yau Litinin.

    Ɗalibai da 'yan kasuwa da ma'aikata sun shiga tasku a Jihar Kano yayin da aka wayi gari da yajin aikin da 'yan adaidaita-sahun suka fara.

    Tun farko dai direbobin sun shirya gudanar da zanga-zanga ne kafin daga baya 'yan sanda su haramta musu yin hakan.

  16. Labarai cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya da BBC na Rana 22/02/2021
    • Hukumar zaɓe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta fitar da sakamakon zaben gunduma 38 daga cikin 266 na zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi jiya Lahadi. Alkaluman da hukumar ta fitar ya zuwa yanzu sun nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki Mohammed Bazoum ne ke kan gaba da kuri’a 191,543, yayin da Mahamane Ousmane na RDR Tchanji ke da 161,972
    • Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum biyu da take zargi da shirya zanga-zangar da direbobin babur mai ƙafa uku wato adaidaita-sahu suka yi niyyar yi a yau Litinin. Ɗalibai da 'yan kasuwa da ma'aikata sun shiga tasku a Jihar Kano yayin da aka wayi gari da yajin aikin da 'yan adaidaita-sahun suka fara kan harajin naira 100 da gwamnati ta dawo da shi a kullum
    • Dubban daruruwan masu zanga-zanga ne suka hau kan tituna a ci gaba da nuna bacin rai kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar. An rufe shagunan kasuwanci sannan ma’aikata ma sun shiga macin, duk da gargadin da sojojin suka yi cewa masu zanga-zangar na wasa da rayuwarsu ne.
    • Labaran rana kenan
  17. Ɗaliban makarantar Kagara na dajin Birnin Gwari - Gwamna Matawalle

    Bello Matawalle

    Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana inda 'yan fashin daji ke tsare da ɗaliban Sakandaren Kimiyya ta Kagara, waɗanda aka sace ranar Laraba da ta gabata.

    Da yake magana da kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Lahadi, gwamnan ya ce ɗaliban tare da sauran waɗanda aka sace na cikin Jihar Kaduna.

    "An hangi ɗaliban Kagara a kusa da yankin Birnin Birnin Gwari da ke Kaduna kuma na yi imanin nan gaba kaɗan za su koma gida," a cewar gwamnan.

    Gwamna Matawalle ya sake nanata batun haɗin kai tsakanin mahukunta, abin da ya ce ya yi imanin shi ne sirrin nasarar samun galaba kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.

    A daren Talata ne 'yan bindiga suka shiga makarantar ta Kagara da ke Jihar Neja sanye da kakin sojoji, inda suka kashe ɗalibi ɗaya sannan suka yi awon gaba da mutum 42, ciki har da ɗalibai da malamansu da iyalai da kuma ma'aikata.

  18. Indiya da China sun janye dakaru daga filin yaƙi

    Indiya da China

    Ƙasashen Indiya da China sun kammala janye dakarunsu daga yankin Himalaya, inda suka shafe lokaci suna rikici.

    Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaro ta Indiya ta bayyana cewa dakarun sun fice ne daga yankin Kogin Pangong Tso ranar Asabar.

    Rikicin na kan iyaka ya jawo mutuwar sojoji 24 a watan Yunin da ya gabata.

    Tun 11 ga watan Fabarairu ƙasashen suka sanar da shirin janye dakarunsu daga yankin. A ranar Asabar ne kuma kwamandojinsu suka haɗu domin duba yadda shirin ke tafiya.

    Sau tara ana yin zaman tattaunawa kafin a cimma wannan mataki, a cewar hukumomi.

  19. Mohamed Bazoum ne ke kan gaba a zaɓen Nijar

    Muhammad Bazoum

    Hukumar zaɓe ta Nijar, CENI, ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar jiya Lahadi.

    Alkaluman da hukumar ta fitar ya zuwa yanzu sun nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki Mohamed Bazoum ne ke kan gaba.

    Kawo yanzu hukumar zaben ta fitar da sakamakon zaben gunduma 38 daga cikin 266.

    Zaɓen Nijar

    A ranar Lahadi aka gudanar da zaben zagaye na biyu, inda aka fafata tsakanin Mohammed Bazoum da abokin karawarsa na jam'iyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane.

    Sakamakon ya nuna cewa Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da kuri'a 191,543, yayin da Mahamane Ousmane ke da 161,972.

    Nan ba da jimawa ba ake sa ran sanar da sakamakon zaben.

  20. 'Yan sandan Imo sun sako Sanata Rochas Okorocha

    Rochas Okorocha

    Rundunar 'yan sandan Jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta ce ta saki tsohon gwamnan jihar kuma sanata, Rochas Okorocha, bayan ya shafe awanni a hannunta.

    Kakakin rundunar Orlando Ikeokwu ne ya bayyana haka yayin wata hira da kafar talabijin ta Channels a safiyar yau Litinin.

    Ya ce an saki Okorocha ne a daren Lahadi bayan sun "gayyace shi" domin amsa wasu tambayoyi game da sake buɗe wani rukunin gidaje mallakar matarsa Nkechi, wanda 'yan sanda suka kulle.

    "An sake shi cikin dare," in ji shi. "Duk wanda aka samu da laifi za a kai shi kotu. Idan bincike ya nuna ya aikata laifi (Okorocha) za a gurfanar da shi a gaban kotu."

    Tun farko Jaridar Punch ta ruwaito yadda tsohon gwamnan ya isa unguwar a safiyar Lahadi tare da magoya bayansa da 'yan sanda da sojoji da dakarun kiyaye zaman lafiya, inda ya bayar da umarnin buɗe su.

    Wasu bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda aka riƙa tinja-tinja tsakanin 'yan sanda da tawagar tsohon gwamnan a lokacin da suke ƙoƙarin tafiya da shi.

    View more on twitter