Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau, Badariyya Tijjani Kalarawi da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na www.bbchausa.com barkanmu da shan ruwa.

    A nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke wallafa muku kai tsaye a kowace rana tun safe.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Halima Umar Saleh da Badriyya Tijjani Ƙalarawi da Awwal Janyau ke muku fatan asuba ta gari.

  2. An sanar da ranar jana'izar Shugaba Idris Deby

    An sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar da za a yi wa Shugaba Idris Deby Itno jana’izar ban girma, wanda ya rasu yayin fafatawa da ‘yan tawaye da ke arewacin kasar.

    Za a fara da macin soji, daga nan dan marigayin, kuma wanda sojoji suka sanar zai mulki kasar wato Janar Mahamat Kaka zai gabatar da jawabi.

    Sanarwar ta ce an gayyaci shugabannin wasu kasashe wajen jana’izar.

    Takardar yadda jana’izar za ta gudana dai an yada ta tare da sa hannun fadar shugaban kasa.

    Chad Presidency
    Chad Presidency
  3. Mutuwar Idriss Deby za ta bar gagarumin giɓi a yaki da ta'addanci - Buhari

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

    Yayin da yake bayyana kaɗuwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban giɓi a ƙoƙarin hadin gwiwa da ake yi na murƙushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP.

    Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da kaɗuwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ƙoƙarin da yake yi na kare kasarsa.’’

    Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya.

    "Sannan ya sanya hannu a yakin da kasar ke yi da Boko Haram, wadanda suka haddasa matsalar tsaro ba a Najeriya ba har da kasashen ta makofta musamman ita kan ta kasar Chadi, da Kamaru da jamhuriyar Nijar," in ji sanarwar shugaban.

    Yayin da yake yi wa al’ummar Chadi da sabon shugaban kasar ta’aziyyar babban rashin da suka yi, Shugaba Buhari ya yi kiran su hada karfi da karfe wajen murkushe masu ta da kayar baya.

  4. Shugaban Kamaru ya aike sakon ta'aziyyar rasuwar Idris Deby

    Shugaban Kamaru Paul Biya ya ce mutuwar shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno gagarumin rashi ne ga tsakiyar Afirka da ma nahiyar baki daya, wadda ya yi wa aiki tuƙuru ba tare da gajiyawa ba.

    Shugaba Biya shi ne shugaba na baya-bayan nan da ya aike sakon ta’ziyyar rasuwar shugaba Deby, da kuma aka wallafa a shafinsa na Twitter.

    Ya kuma aike da sakon ta’aziyya ga maidakin mamacin Hinda Deby Itno na babban rashin da ta yi.

  5. An naɗa janar din soji 15 da za su mulki Chadi

    An sanar da wadanda za su jagoranci gwamnatin riƙo a kasar Chadi ta tsawon watanni 18, bayan mutuwar katsahan da Shugaba Idris Deby Itno ya yi a ranar Talata.

    Tuni sojojin suka sanar cewa dan marigayin janar Mahamat Idris Deby Itno, wanda ake kira da Mahamat Kaka mai shekara 37- shi ne zai jagoranci kasar.

    Janar Mahamet ya fitar da wata sanarwar, tare da jera sunayen masu muƙamin janar din soji 14 da za su hadu don jan ragamar kasar

    Wata ma'aikaciyar sashen BBC Monitoring ta wallafa kwafin sanarwar a shafinta na Twitter.

    View more on twitter
  6. MDD ta bukaci UAE ta ba da cikakkiyar shaidar da za ta tabbatar Gimbiya Latifa ‘Al Makhtoum na raye

    Latifa

    Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba da cikakkiyar shaidar da za ta tabbatar Gimbiya Latifa ‘Al Makhtoum ‘yar shugaban kasar da ake tsare da ita ta na raye.

    A wata sanarwa da aka fitar a Geneva a ranar Talata, kwararru kan kare hakkin dan dam na Majalisar, sun ce ya kamata a sake ta ba tare da bata lokaci ba.

    Gimbiya Latifa ta yi kokarin tserewa daga Hadaddiyar Daular Larabawa a shekarar 2018. A wani bidiyo da BBC Panorama ta samu, Lafita ta ce jami’an tsaron fadar mahaifinta sun dirka mata kwayoyin da suka bugar da ita ka na su ka tafi da ita inda ake tasare da ita.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar ayi ma ta cikakken bayani kan halin da ta ke ciki.

    A baya, masarautar Dubai ta ce gimbiya Latifa ta na cikin koshin lafiya ana kula da ita a gida.

    A ranar 5 ga watan Maris, majalisar dinkin duniya ta ce har lokacin ta na jiran bayanai daga kasar, makwanni biyu bayan bukatar rahoton da zai tabbatar da cewa Latifa ta na raye.

    A karo na biyu ranar Talata, sanarwar da kwararru na majalisar dinkin duniya suka fita ta yi kira ga gwamnatin hadaddiyar daular larabawa su ba da shaidar da za a san makomar gimbiyar ba tare da bata lokaci ba.

    Sun kuma bukaci bincike mai zaman kan sa da zai tabbatar da halin da Latifa ta ke ciki, da inda ake tsare da ita da gaggauta sakin ta.

    Sanarwar ta ce a wanna halin da ake ciki, ba su aminta da sanarwar da masarautar ta fitar ba, na cewa ta na cikin koshin lafiya tun da babu wata kwakkwarar shaida da za ta tabbatar da hakan.

  7. Abin da ya jawo rikici tsakanin ƙabilun Lungudo da Waja na Gombe da Adamawa

    Kura ta lafa bayan wani hari da ake sa ran an kai wa ƴan ƙabilar Lungudo da ke zaune a yankin jihar Gombe.

    Rahotanni sun ce an rasa rayuka da dukiyoyi a harin, wanda ya zo bayan zaman sulhu da aka yi tsakanin ƴan ƙabilar ta Lungudo da kuma ƙabilar Waja da ke yankin jihar Adamawa.

    Al’ummomin sun shafe shekaru suna maƙwabtaka da juna, kafin wani rikici mai nasaba da ikon mallakar gonaki ya haifar da tsamin dangantaka a tsakaninsu.

    Jabir Mustapha Sambo ya tattauna da Sarkin Lungudo mai martaba Kuruhaye Dishon Dan Sanda na II, inda ya fara da bayanin musabbabin rikicin na baya-bayan nan.

    Video content

    Video caption: Hirar Jabir Mustapha Sambo da Sarkin Lungudo Kuruhaye Dishon Dan Sanda na II
  8. Mutane sun tsere saboda fargabar harin ramuwa daga rundunar sojin Myanmar

    Ɗaruruwan mutane a yankin tsakiyar Sagaing a Myanmar sun tsere cikin daji bisa fargabar harin ramuwa daga rundunar soji bayan da aka kashe wasu sojoji biyu ranar Litinin.

    Mutanen yankin sun ce sojoji sun shigo ƙayukansu da ke kusa da garuwuwan Kani da Yin Mar Bin a cikin motoci, bayan kisan sojojin.

    Wasu sojoji uku sun sha da ƙyar a lokacin harin na ranar Litinin amma sun bar makamansu.

    Mutanen yankin sun ce sojojin sun dawo su hukunta ƴan ƙauyen ne sannan su nemi bindigoginsu da suka bari.

    A ƙalla mutum huɗu aka kashe a cikin kwanaki biyu a lokacin da suka kara da sojojin.

    Dama dai yankin na fuskantar tashe-tashen hankula tun farkon wannan watan na Afrilu.

  9. Rasha ta yi kira ga ƙasashen yamma su daina tsanarta

    putin

    Mai magana da yawun gwamnatin Rasha, Dmitri Peskov, ya ce ƙasashen Yamma su watsar da abin da ya kira tsananin ƙin jinin Rasha bayan korar ramuwa kan wasu jami'an diflomasiyya.

    A ranar Talata ne Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa jakadanta na Rasha zai koma gida don tattaunawa, matakin da Rasha ta buƙaci a yi a makon da ya wuce.

    Wakiliyar BBC ta ce "Shawarar da Rasha ta bayar ta cewa Jakadan Amurka ya koma gida don tattaunawa ba abu ne da aka saba gani ba.

    Ba kora ba ce, amma mataki ne da ba za a iya kauda kai daga shi ba.

    "Wasu jami'an diflomasiyyar Bulgaria biyu sun zama na baya-bayan nan da aka kora daga Rashar, kuma an kori jakadan jamhuriyar Czech da Poland cikin kwanaki biyar da suka gabata.

    Mista Peskov ya bayyana cewa dangantaka tsakanin Rasha da ƙasashen Yamma ta yi tsami, kuma ya ce wannan na da nasaba da rashin kirkin da ake nuna wa ƙasarsa.

  10. Shugaba Macron ya yi ta'aziyyar rashin Deby

    Marigayi Idris Deby

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ofishin shugaban Faransa Emmanuel Macron ya na jinjinawa marigayi shugaba Idris Déby, inda ya kira shi da "babban aboki " kuma "jarumin soja".

    Mista Macron ya kara da cewa kasar Chadi ta na bukatar zaman lafiya da mika mulki cikin kwanciyar hankali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito,

  11. Gwamna Sanwo Olu zai kafa hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Legas

    Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya rattaba hannu kan dokar kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

    Hukumar a cewar gwamnan jihar za ta binciki jami’an gwamnati da ‘yan kwangila tare da dakile barnata dukiyar jihar.

    Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu kan dokar, kwanaki kadan bayan majalisar dokokin Legas ta amince da wannan kudirin.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko mana da wannan rahoto.

    Video content

    Video caption: Rahoton Elleman kan bude hukumar cin hanci a Legas
  12. An rusa gwamnati, tare da sanya lokacin zabe

    Sojojin Chadi sun sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a watanni 18 masu zuwa, bayan mutuwar Shugaba Idris Deby.

    An rusa gwamnatin Chadi, sannan dan marigayi Idris DEby mai shekara 37 Mahamat Kaka, wanda janar din soja ne shi zai jagoranci gwamnatin hadin kan kasa.

    Kwararru sun shaida BBC da sauran kafafen yada labarai cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin kasar, kuma a ƙa'ida kakakin majalisar dokoki ya kamata ya jagoranci kasar har zuwa lokacin da za a shirya yin zabe a Chadin.

  13. Sojoji 'sun yi wa kundin tsarin mulkin Tchadi hawan kawara'

    Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa Dakta Evariste Ngerlem Tolde ya shaidawa BBC cewa sanar da sunan dan marigayi Idris Deby a matsayin shugaban kasa ya yi wa kundin tsarin mulki hawan kawara, wanda ya bai wa shugaban majalisar dokoki maye gurbin shugaban idana ka samu gibi.

    Ya kara da cewa kundin tsarin mulki ya bukaci kakakin majalisar dokoki ya tsara shirya zaben shugaban kasa wanda shi ba ya daga cikin wadanda za su tsaya takarar.

  14. 'Yan majalisar dokokin Nijar na son a tsawaita dokar ta ɓaci

    A jamhuriyyar Nijar, 'yan majalisar dokokin kasar ne suka amince da tsawaita dokar ta ɓaci a wasu yankunan kasar da ke fama da matsalolin tsaro.

    Sai dai masu adawa a ƙasar ba su amince da tsawaita dokar ba suna masu cewa ba wani amfanin da ta yi.

    Daga Yamai ga rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko mana.

    Video content

    Video caption: Rahoton Tchima kan tsawaita dokar ta ɓaci a Nijar
  15. Me zai faru nan gaba a Chadi?

    Idriss Déby babban jarumi ne – wanda ya shafe shekaru talatin yana mulki.

    Babban kwamandan soja ne a yankin Tafkin Chadi wanda ya tura sojoji domin taimakawa Najeriya yaƙar Boko Haram, babban mai taka rawa a ƙasashe biyar na Sahel mai ƙunshe dakarun Mali da Nijar kuma babban mai tasiri sosai kan rikicin da ke faruwa a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

    A cikin ƙasar, alamu ya nuna bisa tsarin ne yayin da ɗansa yanzu ke jagorantar ƙasar.

    Amma babu tabbas kan makomar ƙasar.

    Ba a daɗe ba da aka sake zaɓen Deby a zaɓen da ƴan adawa suka kira haramtacce a tsarin dimokuraɗiyya.

    Babu tabbas ko wanda ya gaje shi zai iya ci gaba da tafiyar da tsarinsa da ake gani na mulkin danniya.

    Rikicin siyasa da kuma gaba tsakanin ƙabilarsa ta Zaghawa wani abin dibawa ne.

    An ruwaito cewa Idris Deby ya ji mummunan rauni ne a wajen fagen yaƙi da ƴan tawaye a yankin Kanem, nisan kilomita 400 da birnin N'Djaména fadar gwamnatin Chadi.

    Ayyukan ƴan tawayen ya kasance a yankin arewa mai nisa cikin sahara kuda da iyaka da Libya.

    Amma hakan na nufin rashin zaman lafiya ya koma kudanci sosai.

    Akwai manyan ƙalubane na siyasa da zamantakewar al'umma da ci gaba a cikin Chadi waɗanda da Déby ya runguma a tsawon mulkinsa waɗanda ba a magance ba.

    Yanzu komi zai dogara ne ga sabon shugaban sojan Chadi Mahamat Deby ɗan marigayi Idriss Deby kan yadda zai buɗe babin siyasarsa da kuma ko zai nemi tattaunawa da kuma neman yarjejeniya kan ciyar da ƙasa gaba musamman ko ƙasar za ta ci gaba tafiya kan tafarkin salon mulkin Deby da kuma kundin tsarin mulkinsa.

    Sojojin Chadi
  16. An saka dokar hana fita da rufe iyakokin Chadi

    Sabuwar Gwamnatin sojin Chadi ta sanar da rusa majalisa da rufe kan iyakokin ƙasar.

    Sannan an kafa dokar hana fita a faɗin ƙasar wacce za ta fara aiki daga ƙarfe shida na yamma zuwa biyar na safe.

    Wannan na zuwa bayan mutuwar shugaban ƙasar Idriss Deby a ranar Talata, sakamakon raunikan da ya samu a lokacin da ya jagoranci yaki da ƴan tawayen ƙasar.

    An kafa dokar hana fita a Chadi
  17. Dubban ƴan gudun hijira sun tsere wa rikicin CAR

    Ƴan gudun hijirar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya kimanin 2,000 ne suka tsere wa rikici zuwa Chad, kamar yadda hukumar ƴan kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

    Hukumar UNHCR ta ce ƴan gudun hijirar sun tsere ne sakamakon faɗan da ake gwabza wa tsakanin dakarun gwamnati da kuma na ƴan tawaye a arewacin CAR.

    Hukumar ta ce sun shiga mawuyacin hali na rashin abinci da ruwan sha da kuma matsuguni.

    Ƙasar ta faɗa cikin rikicin ƴan tawayen da tsohon shugaban ƙasa François Bozizé ke jagoranta da kuma sojojin ƙasarda ke samun goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (Minusca) da kuma sojojin Rasha.

  18. Ɗan Idriss Deby Janar Mahamat Deby ya zama sabon shugaban Chadi

    Janar Mahamat Idriss Deby Itno
    Image caption: Janar Mahamat Idriss Deby Itno

    An naɗa Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙo a kasar Chadi.

    Matakin ya biyo bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby a yau Talata sakamakon raunukan da ya ji a kusa da kan iyakar Chadi da Libya inda ‘yan tawaye ke bore.

    Shugaban na riko na da shekaru 37 a duniya kuma Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi.

    A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi "ya ja numfashinsa na ƙarshe a yayin da yake kare martabar ƙasar a fagen daga".

    Janar Mahamat Idriss Deby Itno

    Majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18 karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby

    Mista Déby ya ɗare mulkin ƙasar ne tuna shekarar 1990.

    A ƙarshen mako ne ya je fagen daga don kai wa dakarun da ke yaƙi da ƴan tawaye ziyara a kusa da kan iyakar Libiya.

    Deby ya rasu ne yayin da yake kan hanyar lashe zaɓe wa’adi na shida sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar 11 ga watan Afrilu.

  19. Labarai da dumi-dumiIdriss Deby ya mutu

    Sojojin Chadi sun ce shugaba Idriss Deby ya mutu sakamakon raunin da ya samu a artabun da ya jagoranta da ƴan tawaye.

    Sojojin Chadi na ƙoƙarin fatattakar ƴan tawayen da suka ƙaddamar da farmaki a N'Djamena fadar gwamnatin ƙasar.

    Deby na kan hanyar lashe zaɓe wa’adi na shida sakamakon zaɓen a ranar 11 ga watan Afrilu.

    Karanta ƙarin bayani a nan

  20. Pakistan za ta kori jakadan Faransa

    Gwamnatin Pakistan za ta gabatar da wani kuɗiri gaban majalisar dokokin ƙasar kan matakin korar jakadan Faransa.

    Matakin ba zai kasance doka ba illa ƙoƙarin kwantar da tarzoma da hankalin ƴan jam’iyyar Islama ta TLP.

    Ƴan jam’iyyar sun fusata kan yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna goyon baya ga ƴancin yin zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

    Gwamnatin Pakistan tana tattaunawa da jam’iyyar TLP kuma ta ce a shirye take ta janye tuhumar ta'addanci da ake yi wa fafutukarta.

    Wasu shugabannin TLP, duk da haka, sun ce za su ci gaba da zanga-zangarsu, tare da shirin yin tattaki zuwa Islamabad da yammacin Talata.

    A makon da ya gabata ne Firaministan Pakistan, Imran Khan, ya yi kira ga gwamnatocin ƙasashen yamma da su ɗauki mataki a kan mutanen da ke furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW, kamar yadda suke yi a kan waɗanda suka musanta kisan kiyashi da aka yi wa yahudawa.

    View more on twitter

    Imran Khan ya ce Musulmi ba za su lamunci rashin girmama Manzon Allah ba.