Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na www.bbchausa.com barkanmu da shan ruwa.

    A nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke wallafa muku kai tsaye a kowace rana tun safe.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya komawa ƙasan shafin don karanta wadanda aka wallafa tun safe.

    Halima Umar Saleh da Badriyya Tijjani Ƙalarawi da Awwal Janyau ke muku fatan asuba ta gari.

  2. Sufetan ‘yan sanda ya ba da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga EFCC

    IG Police  Usman Baba

    Mukaddashin sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin janye manyan jami’an ‘yan sanda masu mukamin Cif Sufuritandan da suke aiki tare da jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

    A wata wasika mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Idowu Omohunwa, wacce ya aike wa hukumar EFCC a ranar 15 ga watan Afirilu, mukaddashin sufeton ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan su dawo bakin aiki a ranar Laraba.

    Wasikar ta ci gaba da cewa ‘’Bisa umarni sufeton ‘yan sanda, ina mai farin cikin sanar da shugaban hukumar EFCC cewa maigida ya ba da umarnin janye manyan ‘yan sanda masu mukamin Cif Sufuritanda da ke aiki ƙarƙashin hukumarku.

    An dauki matakin ne saboda bukatar hakan da ta taso, muna bukatar ka ba da umarnin dawo da jami’an ‘yan sandan bakin aikinsu a ranar Laraba 21 ga watan Afirilu.’’

  3. 'Yan kasuwa sun tafka asara bayan hatsaniyar da aka yi a Liberia

    An girke jami’an tsaro, kuma lamura sun fara daidaita a birnin Ganta da ke arewa maso gabashin kasar Liberia, bayan hatsaniyar da ta faru a ranar Talata.

    Sufetan ‘yan sandan birnin, Patrick Sudue, ya shafe daren Talata yana sanya ido kan aikin zaman lafiya da jami’an tsaro ke yi tare da gargadin kar a sake ta da wata tarzomar.

    Sai dai yawancin ‘yan kasuwa sun fara bayyana irin asarar da suka tafka, bayan wasu ɓata gari da ba a san ko su waye ba, sun ɓalle wuraren ajiyar kayayyakinsu na haɗaka tare da banka musu wuta.

    Tashin hankalin ya ɓarke ne bayan wasu daga cikin ‘yan kasuwa da ke shari’a a kan wasu shaguna suka yi rashin nasara, inda kotu ta ba da umarnin a rushe shagunan domin a mayar wa wadanda suka yi nasara a shari’ar filinsu.

    Wanna ya janyo tashin hankali tsakanin bangarorin biyu, a bangare guda kuma rikicin addini da kabilanci ya barke a wajen. Tuni aka rufe makaruntun da ke birnin Ganta, sakamakon yadda mutane ke tserewa.

    Daman dai Ganta yanki ne ya yi suna wajen tashe-tashen hankula, tun lokacin da Liberia ta fada yakin basasa shekaru 17 da suka gabata, kuma a Ganta ne rikicin ya fara barkewa a shekarar 1989.

  4. Kashin farko na riga-kafin cutar korona ya isa yankin 'yan tawayen Syria

    vaccine syria

    Kason farko na allurar riga-kafin cutar korona ya isa arewa maso gabashin kasar Syria.

    Shirin duniya na Covax ne ya bai wa Syria riga-kafin cutar korona 54,000 wanda Oxford-AstraZeneca suka samar, kuma an fara kai wa yankin Idlib ta hanyar amfani da iyakar Bab al-Hawa da ke tsakanin kasar da Turkiyya.

    Jami’an lafiya da ke yankunan da gwamnati da ‘yan tawaye ke iko da su a arewa maso gabashin kasar sun bukaci akai musu isasshiyar allurar riga-kafin da za ta yi wa akalla kashi 20 cikin dari na al’ummar yankin, wadda za ta yi wa mutum 855,000.

    Ana sa ran za a fara yi wa kashin farko na mutane allurar a watan Mayu mai zuwa, inda za a fara ta kan jami’an lafiya da tsofaffi masu shekara 60 wadanda ke fama da wata lalura.

    Sama da mutum 20,000 ne suka kamu da cutar korona wasu 640 sun mutu a arewa maso gabashin Syria tun bayan ɓarkewar annobar. A halin da ake ciki kuma ana ci gaba da samun ƙaruwar wadanda suka kamu da cutar korona a kasar.

    Yankin Idlib shi ne wuri na karshe da ya rage a hannun ‘yan tawaye da mayakan jihadi, wadanda ke ƙoƙarin hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad tun a shekarar 2011.

    A ƙalla mutum kusan miliyan uku ne suka rasa muhallansu tun bayan fara yakin basasa a Syria, ciki har da yara kusan miliyan daya da ke gararamba a sansanin ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin hali da tsakananin bukatar taimakon abinci da ruwan sha da magani.

    Yankin Idlib ya dan samu kwanciyar hankali a watan Mayun 2020, lokacin da Rasha babbar aminiyar Shugaba Assad, da Turkiyya mai goyon bayan ‘yan adawa suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

  5. An kashe mutum ɗaya a satar daliban Jami'ar Greenladn da ke Kaduna

    Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya suna tabbatar da mutuwar mutum daya a harin da masu satar mutane suka kai Jami'ar greenfield da ke kan hanyar Abuja ranar Laraba da safe.

    Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da hakan ya kuma ce wani mutum ɗayan yana asibiti sakamakon raunin da aka ji masa.

    Ya ce ko da sojoji suka je sun samu tuni an kwashe ɗaliban. "A yanzu mun rufe makarantar mun kwashe ɗaliban da ba a sace ba, mun miƙa su ga iyayensu.

    "A yanzu haka muna ƙoƙarin tantance yawan waɗanda aka sace ɗin.,' a cewar Aruwan.

    Ga dai cikakkaiyar hirarsa da Jabir Mustapha Sambo a ƙasa:

    Video content

    Video caption: Hirar Jabir Sambo da Samuel Aruwan kan sace daliban Jami'ar Greenfield
  6. Jirgin ruwan yaƙin Indunusiya ya yi ɓatan dabo a arewacin Bali

    Indonesia

    Jami’an Sojin ruwan Indunusiya sun ce jirgin yaƙinsu ɗauke da fasinjoji 53 ya yi ɓatan dabo.

    Jirgin yana aikin haƙa ne a tsuburin Bali da ke arewacin kasar a ranar Laraba, amma sai ya gagara dawowa kuma duk wata hanyar sadarwa ta ɗauke.

    Shugaban sojin Indunusiya ya ce tuni aka aike da jiragen yaƙi domin neman jirgin mai lamba Nanggala-402.

    Jami’ai sun yi kira ga kasashen Australia da Singapore su taimaka wajen neman jirgin, sai dai har yanzu kasashen ba su ce uffan ba kan hakan.

    An yi amanna jirgin ƙirar kasar Jamus ya ɓace ne cikin ruwa, daga nisan kilomita 100 daga gabar tekun Bali da safiyar ranar Laraba.

    Wasu rahotanni na cewa sadarwa ta yanke tsakanin jirgin da ma’aikatan da ke kan tudu, bayan an bai wa jirgin damar ya kara nutsawa kasan uwa. Jirgin daya ne daga cikin biyar da kasar Indunusiya ke aiki da su.

  7. Ɓulewar iskar shaƙa ta oxygen ta hallaka masu cutar korona 22 a Indiya

    oxygen  tanker

    Akalla masu fama da cutar korona 22 ne suka mutu a wani asibiti a Indiya sakamakon hujewar da iskar shaka ta Oxygen ta yi.

    Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, a lokacin da tankar da ta kawo iskar shakar take zubawa a asibitin Zakir Hussain da ke Nashik.

    Babu tabbacin yadda lamarin ya faru da abin da ya janyo aka dakatar da bai wa marasa lafiyar iskar shaƙa.

    Sai dai jami’ai sun ce iskar ba ta isa cikin bututun da marasa lafiyar ke shaƙa har na tsahon minti 30, lamarin da ya janyo mutuwarsu.

    Kwamishinan birnin Kailash Jadhav ya ce "za mu yi kwakkwaran bincike a kan lamarin da daukar mataki."

    Asibitin dai sun kira masu tankar iskar shaƙar a lokacin da wadda suke da ita ta fara ƙarewa.

    Asibitoci a Indiya na fadi tashi saboda karancin iskar shaka, ga kuma ƙaruwar masu kamuwa da cutar korona a kasar.

    Wani matashi mai suna Vicky Jadhav, wanda kakarsa ke cikin wadanda suka suka mutu, ya ce tana samun sauki a lokacin da ya bar asibitin domin zuwa gida ya ɗauko mata abinci.

    Yankin Maharashtra, inda asibitin yake daya ne daga cikin wuraren da cutar korona ta fi yin muni a jihohin kasar da kuma suke fama da karashin iskar shaƙa.

    Kawo yanzu sama da mutum 200,000 ke kamuwa da cutar korona a kowacce rana a Indiya.

    Lamarin da ya janyo karancin ban a iskar shaka kadai ba har da gadaje a sibitocin kasar da na magunguna.

  8. Faɗan ƴan daba ne ya sa muka hana tashe a Kano - Ƴan sanda

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta hana yin tashe a jihar ne saboda yadda wasu ɓata- gari ke amfani da lokacin tashe wajen yin faɗace-faɗacen daba.

    A cewar kakakin 'yan sandan ta Kano, DSP Abdulahi Haruna Kiyawa, hana yin tashe mataki ne na kare al’adar da masu shaye-shaye, da fadan daban ke san lalatawa.

    Tashe dai dadaddiyar al'adace da aka shafe shekaru masu yawa ana yi a kasashen Hausa, a cikin watan azumi.

    Ga dai karin bayanin da DSP Abdullahi Haruna Kiyawan ya yiwa Khalifa Shehu Dokaji kan matakin da suka dauka:

    Video content

    Video caption: Hirar Khalifa Dokaji da DSP Abdullahi Haruna Kiyawa kan hana tashe a Kano
  9. An fara bincike kan yadda 'yan sanda ke gudanar da aikinsu a Amurka

    george floyd

    An fara bincike kan yadda 'yan sanda ke gudanar da aikinsu a birnin Minneapolis, kwana daya bayan da aka samu wani jami'in 'yan sandan yankin da laifin kisan George Floyd.

    Attorney General din Amurka Merrick Garland, ya ce zai duba ko 'yan sanda na amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima lokacin tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi.

    Hakan ya biyo bayan fusatar da duniya ta yi kan kisan baƙar fatar nan da ba ya ɗauke da makami George Floyd, da dan sanda Derek Chauvin ya yi.

    A ranar Talata ne aka samu tsohon jami'n 'yan sandan da laifin kisa.

    An dauki bidiyon Chauvin ya sanya gwiwarsa a wuyan Floyd har tsawon minti tara a lokacin da suka kama shi a watan Mayun shekarar 2019.

    Sa'o'i kadan da kama Mista Floyd aka sanar da mutuwarsa.

    Bidiyon ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta tare da janyo zazzafar zanga-zanga a sassa daban daban na Amurka tare da kiraye-kirayen yin sauyi a aikin 'yan sanda.

  10. Ƴan adawa na son a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta farar hula a Chadi

    Jam'iyyun adawa a Chadi sun yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da farar hula za su jagoranta, inda suka yi Allah wadai da abin da suka kira juyin mulki, bayan rasuwar shugaban ƙasar Idris Deby a jiya Talata.

    Bayan dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, sojojin kasar sun ce ɗan Idris Deby Mahamat ne zai jagoranci kasar har lokacin da za a gudanar da zabe.

    A wata sanarwa, kusan ƙungiyoyin adawa 30 ne suka yi kira ga jama'ar kasar da kada su goyi bayan abin da suka kira matakin karya doka da gwamnatin riƙon ƙwarya ta soji ta ɗauka.

    A yanzu dai an sanar da sake buɗe iyakokin ƙasar da aka rufe da kuma sassauci kaɗan ga dokar hana fita ta dare.

    Ƴan adawar kuma sun yi gargaɗi ga ƙasar Faransa da ka da ta tsoma baki a harkokin siyasar ta Chadi.

  11. Ana bai wa mutanen da aka yi wa riga-kafin korona tukwuicin wiwi

    Wiwi

    Ana bai wa duk wanda aka yi wa allurar riga-kafin korona kyautar tabar wiwi a birnin New York na kasar Amurka.

    Mazauna birnin na New York r wadanda aka yi wa allurar riga-kafin Covid-19 sun samu kyautar da ba su yi tsammani ba inda aka mika musu wiwi.

    Masu fafutukar ganin an halasta amfani da a jihar New York an rika mika daurin tabar wiwi a ga duk wanda ya tabbatar an yi masa riga-kafin na Manhattan akalla sau daya.

    "Wannan ne karo na farko da za mu iya zama sannan mu halasta amfani da wiwi," a cewar Michael O'Malley, daya daga cikin mutanen da suka shirya ba da wiwin ga wadanda aka yi w riga-kafin a Union Square.

    Ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa: "Muna goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na yin allurar riga-kafin. Kuma muna kokarin mu karfafa gwiwarsu domin su halasta amfani da ganyen wiwi a fadin kasar nan."

  12. An bayar da belin 'yar fim da ta nuna tsiraicinta kan $13,900

    Rosemond Brown

    Wata kotu a Accra babban birnin Ghana ta bayar 'yar fim din kasar Rosemond Brown da aka kama saboda ta wallafa hoton tsiraicinta a shafukan sada zumunta.

    Kotun ta umarci Brown, wadda aka fi sani da Akuapem Poloo, ta biya cedi 80,000, kwatankwacin $13,900 a matsayin kudin beli, har zuwa lokacin da za ta daukaka kara kan daurin kwana 90 da aka yanke mata bisa wallafa hoton nata a shafukan zumunta.

    Alkalin kotun Christiana Cann ta bukaci 'yar wasan kwaikwayon ta rika kai kanta gaban 'yan sanda duk bayan mako biyu sannan ta mika fasfo dinta. Kazalika za ta yi tafiya ne kawai bisa umarnin kotu.

    An bayar da belinta ne saboda wannan ne karon farko da ta aikata irin wannan laifi kuma ta nemi gafara bayan da ta amince da aikata laifin, a cewa alkalin.

    Kotun ta yi ka'akari da halin da danta zai iya shiga ciki idan aka ki bayar da belinta.

    A makon jiya ne 'yar fim din ta fashe da kuka lokacin da aka daure ta.

    Lauyoyi a kotu
  13. Minti Ɗaya da BBC na Rana 21/04/2021

    Video content

    Video caption: Labaran BBC cikin minti ɗaya
  14. Putin ya ja kunnen ƙasashen yammaci

    Vladimir Putin

    Shugaba Putin ya yi gargadin cewa duk ƙasar da ta keta iyaka da Rasha za ta yi nadama, a daidai lokacin da ƙasarsa zaman doya da manja da kasashen Yammacin duniya.

    A cikin jawabinsa na tsawon minti 90 da ya saba yi wa ƴan ƙasa duk shekara , ya ce Rasha za ta yi gaggauwar mayar da martani mai girma kuma mai tsauri.

    Ya ce Rasha za ta bayyana inda ta shata iyaka.

    Ya zargi wasu ƙasashe da shiga hancin Rasha, abin da ya kira kuraye kusa da damisa.

    Amma ya ce Rasha na son yin kyakkyawar alaƙar kasashen duniya.

  15. An yi gagarumar zanga-zanga a Ethiopia kan rikicin kabilanci

    An gudanar da gagarumar zanga-zanga a akalla garuruwa bakwai da ke yankin Amhara na kasar Ethiopia, ciki har da babban birnin yankin Bahir Dar, inda ake kira a kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa 'yan kabilar Amhara.

    An yi jerin zanga-zangar ne bayan an lalata garuruwa biyu sannan aka raba dubban mutane da muhallansu sakamakon rikice-rikicen kabilanci.

    An kai hare-haren ne a gabashin lardin Amhara inda akasarin al'ummar Amhara suke zaune tare da al'ummar Oromo wadanda tsiraru ne.

    Gwamnatin lardi ta zargi 'yan tawayen OLF Shane da kai hare-haren, sai dai kungiyar ta musanta.

    An kai hare-hare a kan akalla yankuna hudu kuma an kwashe kwana biyar ana hatsaniya wadda aka soma ranar Laraba.

    An dakatar da kai hare-haren ranar Litinin bayan sojoji sun bude ofishinsu a yankin.

    Mutanen da suka tsira daga hare-haren sun shaida wa BBC Amharic cewa akalla mutum 20 sun mutum, sai dai jami'ai sun ce mutane da dama ne suka mutu ba tare da bayyana adadin mutanen ba.

  16. Ƙungiyoyin Ingila sun janye daga European Super League

    Ƙungiyoyin Ingila

    Kungiyoyi shida da ke buga wasan Firimiyar Ingila da ke cikin sabuwar gasar da aka ƙirkira ta European Super League sun sanar da janyewa daga gasar.

    Arsenal da Liverpool da Manchester United da Tottenham su bi sahun Chelsea da Man City, da suka sanar da janyewarsu tun da fari.

    Barazanar kafa gasar ta manyan ƙungiyoyin Turai ta ja hankali tare da martani daga hukumomin ƙwallon ƙafa da shugabannin Turai.

    Gasar da aka ƙirƙira a ranar Lahadi,jagoran gasar ya ce zai duba yadda zai sake sabunta shirin.

    Hukumar kwallon kafa ta Uefa ta yi maraba da matsayin kungiyoyin.

    Manyan kulob mafi arziki 12 a Ingila da Sifaniya da Italiya da suka ɓalle domin kafa wannan league din sun sha Allah wadai daga magoya bayansu da gwamnatoci.

    Shugaban Uefa ya yi alƙawalin haɗa kan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ta Turai bayan janyewar ƙungiyoyin na Ingila.

    A cikin wata sanarwa Aleksander Cerefin ya yaba wa ƙungiyoyin na Ingila da ya ce sun fahimci kuskurensu.

  17. Allah Ya yi wa direban Sardauna Ali Sarkin Mota rasuwa

    Direban Sardauna Ali Sarkin Mota rasuwa

    Allah Ya yi wa Alhaji Ali Sarkin Mota rasuwa direban Sardaunan Sakkwato Firimiyan arewa Sir Ahmadu Bello.

    Wani makusancinsa wanda ya tabbatar wa BBC da labarin ya ce ya rasu ne a yau Laraba a Kaduna.

    Ya ce za a yi jana’izarsa idan an jima bayan Sallar Azahar.

  18. Najeriya ta yi tayin shiga tsakani a rikicin Chadi

    Shugaba Buhari na Najeriya

    Najeriya ta bayyana damuwa kan halin da ƙasar Chadi ke ciki inda ta yi kiran kai zuciya nesa tare da hawa teburin tattaunawa.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar mai ɗauke da sa hannun ministan harakokin wajen Najeriya Geoffery Onyeama, Najeriya ta yi tayin shiga tsakani domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

    Najeriya ta ce za ta yi jagorancin tattaunawar ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afrika Ecowas da kuma Tarayyar Afrika AU.

    "Ya kamata gaggauta dawo wa kan mulkin dimokuraɗiyya ya zama babbar manufar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Chadi da ƙasashen gabashin Afrika da na ƙasashen yammacin Afrika da kuma yankin Sahel," a cewar sanarwar.

    View more on twitter
  19. Ma'aikatan kotuna a Najeriya sun lashi takobin ci gaba da yajin aiki

    Ƙungiyar ma'aikatan kotuna a Najeriya ta lashi takobin ci gaba da yajin aikin sai-baba-ta gani da ta fara tun farkon watan nan.

    Wannan matakin na zuwa kwana guda bayan wani taro da kungiyar gwamnoni ta yi da shugabanin majalisun jihohi da shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa inda suka ce sun cimma matsaya kan bukatar ancin cin gashin kan bangaren shari'a.

    A ranar Talata ne aka shirya wani zaman karshe da nufin kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin suka shiga a ofishin ministan kwadago, sai dai zaman bai yiwu ba.

    Kwamared Musa Jimoh ma'ajin kungiyar ma'aikatan kotuna na kasa ya ce ba su samu damar ganawa da ministan kwadago Chris Ngige ba.

    "An sa mana karfe uku a yi zama, kuma mun hadu karfe biyu da rabi muna zaune muna jiran minista na kwadago, ba mu gan shi ba har ƙarfe hudu da rabi''.

    Ya ce a lokacin ne hanakalin mutane ya tashi suka ce ba za su iya jiran shi ba domin ba bu sako game da rahin zuwan shi.

    Sai dai a sanarwar da ofishin ministan kwadago ya fitar ta ce an dage taron ne domin bangaren gwamnati su samu damar yin nazari a kan batutuwan da aka tattaunawa da kungiyar ma'aikatan kotuna da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki.

    Mambobin ƙungiyar ma'aikatan shari'a a Najeriya (JUSUN) sun shiga yajin aiki ne tun daga ranar 6 ga watan Afrilu inda suka rufe dukkan kotuna a duk fadin kasar, don nuna adawa da rashin aiwatar da 'yancin cin gashin kai na bangaren gwamnati na uku a matakin jiha.

    Kotu a Najeriya
  20. Da gaske an harbe ɗan Idriss Deby?

    Mahamat Idriss Déby Itno
    Image caption: Mahamat Idriss Déby Itno aka bayyana a matsayin shugaban riƙo a Chadi bayan mutuwar mahaifinsa

    Kafofin yaɗa labarai na Chadi sun ba da rahotanni masu karo da juna game da zargin harbe-harbe a fadar shugaban kasar Chadi a N’Djamena kan wata taƙaddama tsakanin iyalin marigayi Idriss Déby game da naɗin ɗansa Mahamat Idriss Déby Itno a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa.

    A wasu jerin saƙwanni daga shafin Twitter na kafar Tchadinfos ta ambato majiyoyi da dama da ba ta bayyana suna ba musanta cewa an yi harbe-harben.

    Amma a nata ɓangaren kafar Toubou ta ambato majiyoyin tsaro da ke cewa Mahamat ya ji rauni a harbe-harben sakamakon saɓanin da aka samu.

    Tchadifos ta ce "Shugaban riƙon kwarya yana raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Babu wani harbi da aka yi kuma babu wani saɓani tsakanin Mahamat da ɗan uwansa Zakaria."

    Marigayi Déby yana da ƴaƴa da yawa, ya yi aure da yawa, kuma yana da yara da ba a san yawansu ba.

    A nata labarin kuma Jaridar Alwahida Info mai goyon bayan gwamnati ta ce an ji ƙarar harbin bindiga a Ati, da ke nisan kilomita 378 da gabashin N'Djamena bayan fursunoni sun yi ƙoƙarin tserewa .

    Amma Jaridar ta ce “ƙura ta lafa” bayan tura sojojin a yankin.

    An sanar da mutuwar Idriss Deby a ranar Talata inda aka ce ya mutu sakamakon raunika da ya samu a filin daga
    Image caption: An sanar da mutuwar Idriss Deby a ranar Talata inda aka ce ya mutu sakamakon raunika da ya samu a filin daga