Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    A nan muka zo karshen labarai da rahotanni da muke ba ku kai-tsaye a wannan shafi.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu inda za ku samu sabbin labarai da bayanai masu kayatarwa.

    Amma kuna iya lekawa kasa domin karanta bayanan da muka kwashe tsawon ranar Talata muna ba ku.

    Sannan kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a kodayaushe a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Mun gode

  2. Gwamna Zulum ya yi wa 'yan gudun hijirar Monguno ruwan naira

    Gwamna Zulum ya yi rabon kudi

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya raba N325m da kayan abinci ga magidanta sama da 100,000 wadanda kungiyar Boko Haram ta raba da muhallansu.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Isa Gusau, ya fitar ya ce Gwamna Zulum ya dauki matakin raba kudi da kayan abinci ga mutanen ne saboda sun rasa gonaki da harkokin kasuwancinu da saurna harkokin rayuwa sakamakon rikicin Boko Haram.

    An raba kudu da kayan abincin ne ga mutanen da suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Monguno, wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kukawa, Marte, Ngnazi da Guzamala, a cewar sanarwar.

    Ya kara da cewa an raba dubban buhunan kayan abinci da sikari da zannuwa ga magidanta maza 65,000 da kuma mata 35,000.

    Gwamna Zulum ya yi rabon kudi
    Gwamna Zulum ya yi rabon kudi
  3. AFCON qualifier: Super Eagles ta lallasa Lethoso da ci 3-0

    Minti bakwai a tashi daga wasan ne Paul Onuachu ya saka kwallo ta uku a ragar bakin.

    Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta lallasa Lethoso da ci 3-0, a wasan karshe na share fagen zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a birnin Legas.

    Dan wasan gaban Napoli Victor Osimhen ne ya fara saka kwallo a raga a minti na 23 da soma wasa, kafin Oghenekaro Etebo ya saka ta biyu jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Minti bakwai kafin a tashi daga wasan ne Paul Onuachu ya saka kwallo ta uku a ragar bakin.

    Wannan nasara ta sa Najeriya ta zama zakara a rukunin na L da maki 14 a cikin wasanni shida.

    Ta kuma shiga jerin sauran kasashe 24 da suka samu tsallakewa zuwa gasar da za a yi a Kamaru a watan Janairun shekarar 2022.

    Yanzu haka ana karawa tsakanin Benin da Sierra Leone, kuma duk wadda ta ci za ta raka Najeriya zuwa gasar.

    A sauran wasanni Ivory Coast ta doke Habasha da ci biyu, yayin da Niger da tashi da Madacascar babu ci.

    Hakan na nufin an yi waje rod da Niger da Madacascar yayin da Ivory coast da Ethiopia suka tsallake.

  4. Jirgin sojin Faransa ya 'kashe mutane da ke halartar daurin aure'

    Dakarun Faransa sun kwashe shekara da shekaru a Mali
    Image caption: Dakarun Faransa sun kwashe shekara da shekaru a Mali

    Wani hari ta sama da dakarun Faransa suka kai a kan wani taron daurin aure a watan Janairu a Mali ya yi sanadin mutuwar farar hula 19 da 'yan bindiga uku, a cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

    Ma'aikatar Tsaron Faransa ta musanta rahoton, tana mai cewa an kai harin na ranar 3 ga watan Janairu ne kan "kungiyar 'yan ta'adda".

    Faransa tana da dakaru 5,100 a yankin Sahel wadanda ke yaki da kungiyoyin 'yan bindiga masu alaka da kungiyar al-Qaeda da Islamic State.

    Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike ne bayan mazauna yankunan da harin ya shafa sun yi zargin cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya bude wuta kan masu halartar daurin aure a kusa da kauyen Bounti da ke tsakiyar Mali.

    Binciken ya gano cewa an daura aure kuma akwai "fararen hula kusan 100 a wurin da aka kai harin", a cewar rahoton na Majalisar Dinkin Duniya wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato.

    'Yan bindiga kimanin biyar ne, wadanda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda, suka halarci wurin daurin auren, a cewar rahoton.

  5. Za a kyale sojoji mata su rika sanya dan kamfai a Switzerland

    Wasu sojoji mata
    Image caption: Daga watan gobe za a soma bai wa mata sojoji dan kamfai

    Kafafen watsa labarai a Switzerland sun ce kasar za ta soma kyale sojoji mata su rika sanya dan kamfai da sauran kaya irin su singileti a karon farko a yunkurin kara samun masu son shiga aikin soja.

    A halin yanzu, kakin sojan da ake bai wa sojoji sun hada ne kawai da dan kamfai na maza.

    Daga watan gobe za a soma bai wa mata dan kamfai iri biyu, wanda zai dace da lokacin zafi da wanda zai dace da lokutan sanyi.

    Mata su ne kashi 1 cikin dari na sojojin kasa na Switzerland, sai dai kasar tana fatan samun kashi 10 cikin dari na mata da za su shiga aikin soja nan da 2030.

    Marianne Binder, mamba a majalisar kasa ta rundunar sojin Switzerland, ta ce bai wa mata damar sanya dan kamfan da ya dace da su zai karfafa gwiwarsu wajen shiga aikin soja.

    "An dinka tufafin ne domin su dace da maza, amma idan ana so mata su ji dadin aiki a rundunar sojin kasa, ya kamata a dauki matakan da suka dace," in ji ta.

  6. Bola Tinubu ya yi amai ya lashe kan daukar jami'an tsaro miliyan 50

    Tinubu

    Jagoran jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ce suɓutar baki ya yi game da kiran da ya yi wa gwamnatin Najeriya da ta dauki matasa miliyan hamsin a fannin tsaron kasar.

    Mai magana da yawun tsohon gwamnan na jihar Lagos, Tunde Rahman, ya shaida wa jaridar P.M. NEWS da ake wallafawa a shafin intanet cewa uban gidan nasa yana nufin gwamnati ta dauki matasa miliyan biyar domin magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

    A ranar Litinin ne Mr Tinubu ya kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauki matasa miliyan 50 domin yaki da 'yan fashin daji da mayakan Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

    Ya yi kira ne a lokacin da yake jawabi domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa a birnin Kano.

    Sai dai kalaman nasa sun fuskanci suka daga wajen 'yan kasar da dama wadanda ke ganin babu kasar da za ta iya daukar kashi daya cikin hudu na 'ya'yanta domin su magance matsalolin tsaronta.

  7. Kungiyar Izala ta goyi bayan NDLEA kan yaki da miyagun kwayoyi

    Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'iqamatis Sunnah ta bayyana goyon bayanta ga hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA.

    A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce kungiyar Izala ta nuna goyon baya game da yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi ne lokacin ziyarar da shugabanninta suka kai wa shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ranar Talata a ofishinsa da ke Abuja.

    Sanarwar ta ambato shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau yana neman goyon bayan hukumar NDLEA game da yadda za su isar da sakon yaki da miyagun kwayoyi ga miliyoyin mabiya kungiyar.

    View more on twitter

    Sheikh Bala Lau ya ce Izala za ta taimawa sosai wajen isar da sakon yakin da miyagun kwayoyi ta hanyar amfani da masallan Juma'arta fiye da 15, 000 da kuma makarantun firamare da na sakandarenta sama da 10,000 da ke fadin Najeriya, da ma gidan talbijin dinta na Manara Sat TV.

    A nasa bangaren, shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, ya sha alwashin kai ziyara ga kungiyoyi irin su Izala da zummar neman goyon bayansu wajen yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi.

    View more on twitter
  8. 'Yan bindiga sun kashe ma'aikatan rigakafin Polio a Afghanistan

    Jami'ai a Afghanistan sun ce 'yan bindiga sun kashe ma'aikatan lafiya uku da ke aikin rigakafin Polio a birnin Jalalabad da ke gabashin ƙasar.

    Rahotanni sun ce ma'aikata mata aka kashe a hare-hare biyu cikin kasa da sa'a 1.

    A ranar Litinin aka soma gangamin bayar da rigakafin na wannan shekarar a ƙasar.

    Afghanista da makociyarta Pakistan, su ne kadai kasashen duniya biyu da har yanzu ake da sauran masu dauke da cutar ta Polio.

  9. Labarai da dumi-dumiAn kwaso ƙarin 'yan Najeriya 395 da suka maƙale a Saudiyya

    Ƙarin 'yan Najeriya 395 daga Saudiyya sun isa Abuja, babban birnin ƙasar a yau Talata.

    Mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 12:18 na rana, a cewar hukumar kula da harkokin 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta NiDCOM.

    Da wannan adadi, jumillar waɗanda aka kwaso daga ƙasar sun zama 650 bayan 255 sun isa ƙasar ranar Litinin.

    Mai magana da yawun shugabar hukumar ta faɗa wa BBC cewa mutum 1,000 ne jumillar waɗanda ake sa ran za a kwaso ɗin.

    Hukumar ta ce za a killace su a sansanin alhazai na Abuja tsawon mako biyu, kamar yadda dokokin yaƙi da cutar korona suka tanada.

    Akasarin mutanen na tsare ne a gidajen yarin Saudiyya sakamakon zargin su da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    View more on twitter
  10. Ganduje ya ware biliyan 9 don gina gadar 'Muhammadu Buhari'

    Gada

    Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe naira biliyan kusan tara (N8, 980, 303, 460.63) domin gina gada mai suna Muhammadu Buhari a kan Titin Maiduguri da ke ƙwaryar birnin na Kano.

    Majalisar ta amince da kashe kuɗin ne jim kaɗan bayan kammala zamanta na mako-mako a ɗakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar.

    Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya ce wannan yunƙuri na cikin burin gwamnatin Abdullahi Ganduje na gina tituna da hanyoyi domin mayar da Kano "hamshaƙin birni" da kuma haɓaka harkokin kasuwanci.

    A cewarsa: "Kasancewarsa birni mai tasowa kuma cibiyar kasuwanci a Najeriya, Kano na samun ƙaruwar 'yan kasuwa da ke shigowa, abin da ya sa ake buƙatar sake tsarawa da haɓaka tituna don ya iya ɗaukar masu zirga-zirga a cikinsa."

    A makon da ya gabata ne tsohon gwamna kuma jagoran adawa a jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki aikin gadar, yana mai cewa "mutanen Kano sun fi buƙatar ilimi" ba gada ba.

    Kazalika, kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kashe naira miliyan 44,300,000 domin yi wa Kwalejin Harkokin Noma ta Audu Bako da ke Ƙaramar Hukumar Dambatta kwaskwarima.

  11. Zaman lafiya ya dawo bayan rikicin Hausawa da Yarabawa a Oyo

    'Yan sanda

    Rundunar 'yan sandan jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta ce ta dawo da zaman lafiya a yankin Apata na birnin Ibadan bayan an samu rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa.

    Mai magana da yawun rundunar a jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, yana mai cewa "ɗan sabani" ne aka samu.

    Kakakin 'yan sandan ya ce babu wanda ya jikkata a hatsaniyar kuma sun shawo kan lamarin.

    Sai dai mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sun ji ƙarar harbe-harbe yayin da ɓangarorin biyu ke kai wa juna hari.

    Wani mazaunin unguwar Sabo ya ce: "Ina kwance kawai na ji mutane sun rugo a guje, da har zan gudu sai na ga daji ne a gabana. Daga baya aka ce Hausawa da Yarabawa ne ke faɗa.

    "Na ji harbin bindiga amma dai ban ga wanda aka harba ba da idona."

    Wata ɗaya kenan da makamancin wannan lamari ya faru a kasuwar Shasa da ke birnin na Ibadan, inda aka kashe Hausawan fiye da 10 tare da lalata dukiyoyi.

  12. Yau Talata za a ci gaba sauraron shari'ar kisan George Floyd

    George Floyd

    An shafe rana ta farko a shari’ar da ake yi wa dan sandan nan da ake zargi da kisan George Floyd a birnin Minneapolis na Amurka bayan da bangarorin biyu suka gabatar da hujjojinsu na bude shari'a.

    Derek Chauvin ya musanta tuhumar kisan kai da cin zarafi da ake yi masa.

    An sanya wa alkalan da ke jagorantar shari'ar bidiyon shaida da ke nuna lokacin da dan sandan ya danne wuyan bakar fatar har tsawon fiye da minti tara.

    Wani mai gabatar da kara ya ce ta karfi da yaji Mista Chauvin 'ya aika Floyd lahira.

    Sai dai lauyoyin da ke kare dan sandan sun ce kwayoyin da George Floyd ke amfani da su da kuma rashin lafiyar da yake fama da ita ne suka janyo ajalinsa.

    Ana sa ran za a ci gaba da zaman kotun a yau Talata.

  13. Mutum 45 ne suka mutu a turmutsutsun ganin gawar John Magufuli

    Tanzania

    'Yan sandan Tanzania sun tabbatar da mutuwar mutum 45 a turmutsutsun ganin gawar tsohon shugaban ƙasar John Magufuli.

    Ƙarin wasu 37 sun ji rauni a cunkoson jama'ar da ya afku a Dar es Salaam, babban birnin ƙasar.

    Sai dai 'yan sanda ba su bayyana sunayen waɗanda suka rasun ba.

    Tun farko mutum biyar aka ce sun mutu amma an matsa wa hukumomi su bayyana haƙiƙanin adadin fiye da mako ɗaya da faruwar lamarin bayan wani dangi sun bayyana mutuwar 'yan uwansu guda shida.

    Iyalan na cikin dubban mutanen da suka je wurin domin yin bankwana da tsohon shugaban.

  14. Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro kafin tafiya Landan

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro a fadarsa da ke Abuja.

    Taron na gudana ne jim kaɗan kafin shugaban ya tashi zuwa birnin Landan domin duba lafiyarsa.

    Wasu daga cikin waɗanda ke halartar taron sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaro Lucky Irabor, Hafsan Sojan Ƙasa Ibrahim Attahiru, Hafsan Sojan Ruwa Awwal Gambo, Hafsan Sojan Sama Isiaka Amao, Mai Bai wa Buhari Shawara kan Tsaro Babagana Munguno.

    Sauran su ne; Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari, Sufeto Janar na "yan Sanda Mohammed Adamu.

    Jami'an tsaro

    Ana sa ran Buhari zai koma Najeriya a mako na biyu na watan Afrilu daga tafiyar neman lafiyar.

    A 2017, ya shafe kwana 103 yana jinya a Landan, inda Yemi Osinbajo ya zama muƙaddashin shugaban ƙasa.

  15. An ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara

    'Yan sandan Najeriya

    Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta ce ta ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Maradun da ke jihar.

    A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar Mohammed Shehu ya fitar ranar Litinin, an samu nasarar ceto mutanen ne sakamakon haɗin gwiwar jami'an tsaro da kwamitin tsaro da zaman lafiya na jihar.

    'Yan bindiga sun afka wa ƙauyen Kaya na Maradun da sanyin safiyar Litinin sannan suka yi awon gaba da mutanen.

    Mutanen da suka haɗa da mata bakwai da maza uku, an yi garkuwa da su sannan aka kai su dajin Sububu, inda daga baya aka sako su sakamakon tattaunawar sulhu da gwamnatin jihar ta ƙaddamar.

    "Dukkan waɗanda aka sace 'yan sanda sun yi musu bayani kuma aka haɗa su da shugaban ƙaramar hukumar Maradun cikin ƙoshin lafiya, wanda shi kuma zai sada su da danginsu," a cewar sanarwar.

    Ta ƙara da cewa an ƙaddamar da bincike kan lamarin kuma za a bayyana sakmakonsa idan an kammala.

  16. Jirage sun fara wucewa a mashigar ruwa ta Suez

    Jirgin ruwa

    Jiragen dakon kaya sun fara ci gaba da wucewa ta mashigar ruwan Suez kwana ɗaya bayan an ƙetarar da katafaren jirgin ruwan nan na Ever Given.

    Jirage 37 da suka gaza wucewa saboda cunkoso, sun samu wucewa da tsakar dare yayin da wasu 70 za su wuce a yau Talata.

    Mahukuntan da ke kula da ruwan na fatan sama wa jirage 400 hanya waɗanda suke jira tsawon kwana uku da rabi.

    A gefe guda kuma, ƙwararru za su duba jirgin da aka tsallakar don tabbatar da lafiyarsa.

  17. Tinubu ya nemi gwamnatin Buhari ta fito da kuɗi a taimaki 'yan Najeriya

    Bola Tinubu

    Jagoran jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce wajibi ne 'yan majalisa da ɓangaren zartarwa su yi aiki tare wajen samar da kuɗi don rage talauci da rashin aikin yi a ƙasar.

    Tsohon gwamnan na Legas kuma tsohon sanata ya bayyana hakan ne a Jihar Kano yayin jawabinsa a wurin taron bikin cikarsa shekara 69 da haihuwa ranar Litinin.

    Ya ce dole ne shugaban ƙasa ya sauya salonsa na matse bakin aljihun gwamnati, ya mayar da hankali wajen sakin kuɗi da za su kai ga talakawa.

    A cewarsa: "Lokaci ya yi da za a saka shirin bayar da tallafi a gaba, lokacin matse bakin aljihu ya wuce. Babu wani sauran lokaci na matse tattalin arziki, lokaci ne na samar da damarmaki."

    Tinubu ya bayar da misali da kasafin kuɗi na tallafi da gwamnatin Amurka ta samar a kwanan nan, sannan ya soki halin rashin aikin yi da ake ciki a Najeriya.

    "Ƙididdigar rashin aikin yi ta kai kashi 33 cikin 100 amma kuna so mu ci gaba da azumi. Azumin da muke yi na nafila ne kuma mun daɗe muna yi. Ina fatan shugaban ƙasa da majalisa ba za su karkata ga matse bakin aljihu ba. Jihohi ne kaɗai ya kamata su matse bakin aljihu domin aiwatar da kasafin kuɗinsu.

    Har wa yau, Tinubu ya shawarci gwamnatin tarayya ta ɗauki mutum miliyan 50 aikin samar da tsaro.

  18. Yau Shugaba Buhari zai tafi Landan

    Muhammadu Buhari

    Nan gaba a yau ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kama hanyar zuwa Landan don duba lafiyarsa.

    Ana sa ran zai koma gida Najeriya a sati na biyu na watan Afrilu.

    Shugaban ya sha yin irin wannan tafiya zuwa Burtaniya don neman lafiya. A 2017, ya shafe fiye da wata uku yana jinya a can.

    A baya-bayan nan dai ba kasafai ake ganin shugaban mai shekara 78 a duniya ba, abin da ke haifar da damuwa a kan yanayin lafiyarsa.

  19. Har yanzu akwai cunkoson jiragen ruwa a mashigar ruwan Suez na Masar

    Jirgin ruwa

    Hukumomin kula da mashigin ruwan Suez a Masar sun ce suna fatan karasa bude hanya ga tarin jiragen ruwa da ke bin mashigin nan da kwana uku.

    Babbake hanyar da jirgin Ever Given ya yi kusan mako ɗaya ta haifar da cunkoson jiragen ruwa sama da 400.

    Shugaban hukumar kula da mashigin, Osama Rabie, ya ce ana sa ran jiragen ruwa sama da 100 za su yi jigila tsakanin Bahar Rum da Bahar Maliya a yau Talata.

    Wakiliyar BBC ta ce a yanzu haka ana duba lafiyar jirgin na Ever Given don gano ko ya samu wata matsala.

    Kashi 12 cikin 100 na kayan da ake amfani da su wajen yin kasuwanci a duniya na bi ta mashigin na Suez.

  20. Korona a Najeriya: Mutum 1 ya rasu, 48 sun kamu ranar Litinin

    Rigakafi

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 48 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Litinin. sannan mutum 1 ya mutu.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 13.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 7 a Kaduna, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    A jihar Nassarawa an samu mutum 7 yayin da aka samu 6 a jihar Kano. sai kuma jihar Kwara da aka samu mutum 5, da Akwa Ibom mai mutum 3 da Osun da aka samu mutum 3.

    Alkaluman hukumar sun nuna cewa mutum 28 sun warke daga cutar a jihar Ekii dake kudu maso yammacin ƙasar.

    Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 162,641 sannan an sallami 150,466 jumulla, baya ga mutum 2,049 da suka mutu kawo yanzu.