Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muke rufe wannan shafi na rahotanni kai-tsaye.

    Mu haɗu da ku gobe da safe domin kawo wasu sababbi daga sassan duniya.

  2. 'Yan sandan Birtaniya sun kama dan kasuwar Rasha kan halasta kudin haram

    Ƴan sanda a Birtaniya sun damƙe wani ɗan kasuwa ɗan ƙasar Rasha a gidansa da ke Landan.

    An kama shi ne bisa zarge-zargen aikata laifuka ciki har da halasta kudin haram.

    Zuwa yanzu ba a bayyana sunan mutumin ba mai shekara hamsin da takwas. Haka kuma akwai wasu mutum biyu da su ma aka damƙe su.

  3. Kongo ta ba da hutun zaman makoki na ƙasa kan kisan kiyashi

    Shugaban Congo ya sanar da hutun kwanaki uku a matsayin na zaman makoki kan kisan kiyashin da aka yi a gabashin ƙasar.An daɗe ba a samu irin wannan rikicin ba a yankin da lamarin ya faru amma Shugaba Feliz Tshisekedi ya bayyana cewa sama da mutum ɗari ne aka kashe a ƙauyen Kishi-she.

    Wakiliyar BBC ta ce gwamnatin ƙasar ta ɗora alhakin kisan kan ƴan tawayen M23, duk da cewa sun musanta zargin.

    An ta samun ƙarin rikice-rikice tun bayan da Jamhuriyyar Congo da Rwanda suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a makon da ya gabata.

    Congo da Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya duk sun zargi Rwanda da goyon bayan yan tawayen M23 duk da cewa Rwandan ta musanta hakan.

  4. Ba za mu yarda da ƙayyade farashin fetur ɗinmu ba - Rasha

    Peskov

    Rasha ta ce ba za ta yarda a ƙayyade farashin man da za ta dinga fitarwa ba a daidai lokacin da Tarayyar Turai ta ce kar man ya wuce dala 60 kan kowace ganga ɗaya.

    Mai magana da yawun Fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce a shirye Moscow take ta tunkari wannan yunƙurin kuma tana neman mafita a halin yanzu.

    Ofishin jakadancin Rasha da ke Washington ya kira wannan matakin da wanda ba halastacce ba inda ya ce zai iya kawo cikas ga yanayin yancin sayar da kayayyaki a kasuwa kan farashin da mutum ke so.

    Ana sa ran wannan matakin na ƙayyade farashin gangar mai zai soma aiki a mako mai zuwa wanda zai iya kawo cikas ga kuɗin shigar Rasha.

  5. Qatar 2022: Netherlands ta kori Amurka daga Kofin Duniya

    Netherlands ta doke Amurka

    Netherlands ta tsallake rijiya da baya zuwa zagayen semi fayinal a Gasar Kofin Duniya yayin wasan kwata fayinal tsakaninta da Amurka, inda ta cinye wasan da 3-1.

    Tawagar mai horarawa Louis van Gaal ta kai hari cikin nasara a minti na 10 da take wasa lokacin da Memphis Depay ya ci ƙwallon da Denzel Dumfries ya bugo masa.

    Netherlands ta sake jefa ƙwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, wadda Daley Blind ya ci.

    Amurka ta matsa wa Netherlands tun bayan da ta farke ɗaya a minti na 76 da ƙwallon da Haji Wright ya jefa a ragarta.

    Ba a tashi daga wasan ba sai da Dumfries ya zira ta uku a ragar Amurka.

    Sakamakon na nufin Amurka ta zama ƙasa ta farko da ta fita daga gasar a zagayen kwaf ɗaya.

    Argentina za ta fafata da Australiya a ɗaya wasan da za a yi a filin wasa na Al Rayyan da ke Qatar.

  6. Burkina Faso ta dakatar da rediyon RFI yaɗa shirye-shirye a ƙasar

    RFI

    Gwamnatin Burkina Faso ta dakatar da gidan rediyon Faransa na Radio France Internationale (RFI) daga yaɗa shirye-shirye a faɗin ƙasar.

    A cewar gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar, RFI ya yaɗa wani saƙon farfaganda na wani shugaban masu iƙirarin jihadi a ranar Asabar.

    Sanarwar da aka wallafa a shafukan zumunta na gwamnatin ƙasar ta ce "kafar yaɗa labaran[RFI] ta ba da gudummuwa wajen bai wa ƙungiyar 'yan ta'addan damar karya gwiwar 'yan Burkina Faso waɗanda ake ƙarfafa wa gwiwar kare ƙasarsu".

    Ta ƙara da cewa a jiya Juma'a RFI ya sake maimaita wasu bayanai na boge cewa Shugaban Riƙon Ƙwarya Kaftin Ibrahim Traoré ya tabbatar da cewa an yi yunƙurin ƙwace mulkinsa ne a yunƙurin juyin mulkin da aka yi.

    Gwamnatin ta ce ta nuna ɓacin ranta a watan da ya gabata game da yadda 'yan jaridar RFI ke kashe gwiwar 'yan ƙasa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadin.

    A watan Maris ne maƙwabciyar ƙasar, Mali ta dakatar da ayyukan RFI da gidan talabijin na France 24, waɗanda dukkansu mallakar Faransa ne, suna masu zargin su da yaɗa zarge-zargen cin zarafin da sojojin Mali ke yi.

  7. INEC za ta haɗa gwiwa da NCC wajen yaɗa sakamakon zaɓe kai-tsaye a 2023

    Na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a

    A shirinta na ci gaba da yaɗa sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a babban zaɓe na 2023, hukumar zaɓe ta INEC a Najeriya ta ce za ta gana da hukumar sadarwa ta ƙasar a ranar Talata.

    Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya faɗa wa editocin kafofin yaɗa labarai yayin wata ganawa a Legas cewa ganawar da za su yi za ta ƙunshi shugabannin kamfanonin sadarwa huɗu na Najeriya.

    Ya ce INEC na haɗa kai da NCC ne don gano kyakkyawar hanyar yaɗa sakamakon a kowane lungu da saƙo na ƙasar a kan loƙaci.

    NCC ce ke kula da dukkan harkokin sadarwa na Najeriya, wadda ke da ƙananan hukumomi a ƙarƙashinta.

    Wasu daga cikin jam'iyyun siyasa sun soki INEC game da yaɗa sakamakon ta intanet amma ta ce "babu gudu babu ja da baya".

  8. 'Yan Sanda sun daƙile hari kan ofishin INEC a Imo

    ...

    Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce dakarunta sun samu nasarar daƙile wani hari da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne tare da wata ƙungiya mai ƙawance da ita da ake kira Eastern Security Network, da aka fi sani da ESN suka kai kan ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar Orlu da ke jihar.

    Yan sanda sun ce 'yan bindigar sun tsaya daga bayan katangar ofishin zaɓen tare da jefa abubuwan fashewa zuwa cikin harabar ofishin.

    A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'uyan sandan jihar ya fitar ya ce cikin ƙwarewar aiki jami'an 'yan sanda suka mayar da martani, inda suka samu nasarar fatattakar 'yan bindigar bayan da da yawa daga cikinsu suka samu munanan raunuka daga harbin harsasai.

    Sanarwar ta ce 'yan sanda na gudanar da bincike domin gano tare da kama waɗanda ake zargi da kai harin.

  9. Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana damuwarta kan ƙaranci man fetur a Najeriya

    ,,

    Haɗakar ƙungiyoyin ƙwadago ta Najeriya ta bayyana damuwarta game da ƙarancin man fetur da ƙaruwar farashinsa a faɗin ƙasar.

    A wata sanarwar haɗin gwiwwa da ƙungiyoyin NLC da TUC suka fitar, sun ce ba su ga dalilin da zai sa a samu ƙarancin fan a fadin ƙasar ba, saboda a cewarsu gwamnati ce kaɗai ke da alhakin shigo da man cikin ƙasar.

    Dan haka a cewarsu ba su ga dalilin da zai sa wata hukuma ta gwamnati za ta ƙara kuɗin da take sayar wa 'yan kasuwa ba

    Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyoyin sun samu wata masaniya da ke nuna cewa da gayya aka ƙirƙiri matsalar domin a riƙa sayar da man sama da farashin da gwamnati ta amince da shi.

    ƙungiyoyin ƙwadagon sun umarci gwamnati da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar kafin abubuwa su lalace.

  10. Osinbajo zai tafi Vietnam domin ƙulla hulɗar kasuwanci

    Osinbajo

    Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, zai tafi zuwa ƙasar Vietnam ranar Asabar domin tattauna batun hulɗa kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

    A wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan kafofin yada labarai Laolu Akande ya fitar ya ce a yayin ziyarar mataimakin shugaban ƙasar zai gana da shugaban ƙasar Vietnam Nguyễn Xuân Phúc da mataimakin shugaban ƙasar Vo Thi Aah Xuan da firaministan ƙasar Pham Minh Chinh tare da wasu jami'an gwamnatin ƙasar da 'yan kasuwar kasar.

    Sanarwa ta ce ziyarar - ta kwana biyar da mista Osinbajo zai yi - na zuwa ne bayan da mataimakin firaministan Vietnam Vuong Hue ya ziyarci Najeriya a watan Oktoban 2019 domin duba hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

  11. Gwamnati ta yi asarar naira miliyan 113 saboda dakatar da jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya ta ce gwamantin tarayya ta yi asarar kuɗi kimanin naira miliyan 113 sakamakon dakatar da jirgin ƙasan Abuja zuwa ƙaduna na tsowan wata takwas.

    Babban daraktan hukumar Fidet Okhiria ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN.

    Ya ƙara da cewa wasu ma da yawa daga cikin ɗaiɗaikun 'yan ƙasar asarar ta shafe su sakamakon tsaida zirga-zirgar jirgin.

    “Akwai mutanen da ke sayar da kayayyaki a cikin jirgin, akwai masu sana'o'i daban-daban a tasoshin jiragen, kuma mutane suna sayen abubuwa a wajensu'', in ji shi.

  12. Za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Abuja - Kaduna ranar Litinin

    ..

    Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta ce za ta dawo da zirga-zirgai jirgin ƙasan Abuwa zuwa Kaduna daga ranar Litinin biyar ga watan Disamba.

    A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce jirgin farko zai bar tashar jiragen da ke Rigasa a Kaduna da misalin ƙarfe 8:00 na safe, yayin da jirgin farko da zai bar Abuja zai tashi daga tashar jirgin da ke Idu da ƙarfe 9:45 na safe.

    Hukumar ta kuma ce daga cikin sabbin matakan tsaro da ta ɓullo da su shi ne , a yanzu wajibi ne duk fasinjan da zai hau jirgin ya nuna katinsa na shaidar zama ɗan ƙasa da kuma tikitin shiga jirgi kafin a bar su su shiga jirgin.

    Idan za a iya tunawa dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin biranen biyu bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hari kan jirgin ƙasan tare da kama fasinjoji aƙalla 60 a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.

  13. Yadda mace za ta gane ruwa mai cutarwa da ke fita daga al'aurarta

    Cutar sanyi ta Candidiasis na daya daga cikin cututtukan da ke janyo kaikayi a al’aurar mata, musamman ma a tsakanin mata masu ciki.

    Sai dai rashin tsafta na daga cikin manyan abubuwan da masana a fannin kiwon lafiya suka ce yana janyo cutar sanyin.

    Wasu ƙarin dalilan da ke janyo wa mata samun cutar sanyin ta Candida, sun haɗa da ciwon suga da yin amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta fiye da kima da wasu magungunan hana daukar ciki da samun juna biyu.

    Haka zalika wasu daga cikin alamomin cutar su ne ƙaiƙayin gaba da ƙuraje da zafi lokacin fitsari da zafi lokacin saduwa da zafi a mara.

    Saurari cikakken shirin Lafiya Zinariya na wannan makon domin jin ƙarin bayani

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  14. Gwamnoni sun ƙaryata iƙirarin cewa su suka jefa Najeriya cikin talauci

    ..

    Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun ce sun yi mamakin yadda ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na ƙasar, Clem Agba ya zarge su da jefa Najeriya cikin talauci.

    A watan Nuwamba ne Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce mutum miliyan 130 ne a ƙasar ke fama da talauci, kusan kashi 63 cikin 100 na a'umar ƙasar.

    To sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ta bayyana kalaman ministan da cewa abu ne da bai kamata ba, kuma babu kanshin gaskiya a cikin kalaman ministan.

    Gwamnonin sun ce iƙirarin - da ministan ya yi cewa gwamnonin sun yi watsi da al'ummar karkara - ba shi da tushe balle makama.

    A cikin makon da ya gabata ne dai ƙaramin ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Clem Agba a wani taro da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ya ɗora alhakin katutun talaucin da ke damun ƙasar kan gwamnonin jihohi.

  15. Gane Mini Hanya

    A Najeriya ana ci gaba da bayyana ce-ce-ku-ce game da yadda wasu 'yan siyasa da wasu fitattun ma'aikan gwamnati ke karɓar albashi da alawus-alawus da kuɗin sallama mai tsoka, a yayin da na wasu kuma bai taka-kara-ya-karya ba.

    Inda Albashi da kuɗin sallama na shugaban ƙasa bai kai rabin na wani ma'aikaci a wata ma'aikata a ƙasar ba.

    Abdussalam Ibrahim Ahmed ya tattauna da Muhammad Bello Shehu, shugaban hukumar tattara kuɗaɗe na gwamnatin ƙasar da rarraba su ga gwamnatin tarayya, da na jihohi da ƙananan hukumomi

    Ga kuma ƙarin bayanin da ya yi.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  16. Qatar 2022: Yau za a shiga zagayen gaba a gasar Kofin Duniya

    .

    Bayan da aka kammala wasannin cikin rukuni a jiya, a yau kuma za a shiga matakin sili-ɗaya-ƙwale a gasar cin Kofin Duniya da ke gudana a ƙasar Qatar.

    Ƙasashe 16 ne suka samu nasarar tsallakawa wannan mataki bayan da kowacce ƙasa ta yi fafatawa uku-uku a cikin rukuni.

    Kawo yanzu dai ƙasashen Afirka biyu ne suka rage a cikin gasar da suka haɗar da Morocco wadda ta ja ragamar rukuni da shida, sai kuma Senegal da ta zo ta biyu a rukuni na ɗaya.

    A yau za a fara karawar matakin 'yan 16 da suka rage a gasar tsakanin Netherlands da Amurka sai kuma gumurzu tsakin Argentina da Australiya

  17. Yadda aka miƙa Aminu Adamu Muhammad hannun iyayensa

    .,

    A daren jiya Juma'a ne aka sako ɗalibin Jami'ar Tarayya ta Dutse, Aminu Adamu Muhammad daga kurkukun garin Suleja, wurin da wata babbar kotu ta aika da shi bisa tuhumar yin kalaman cin mutuncin matar shugaban Najeriya Aisha Buhari.

    Kama wannan dalibin dai ya ja hankulan 'yan Najeriya, har ta kai ga wasu na sukar matakin da hukumomi suka ɗauka, inda a ɗaya ɓangaren kuma wasu ke kallon halin da ya shiga a matsayin izina ga matasan ƙasar masu yawan wallafa sakonni irin wannan a shafukan sada zumunta.

    Abokin aikina Sani Aliyu na wurin da aka miƙa Aminu ga iyayensa, ga kuma rahoton da ya haɗa mana.

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton
  18. INEC ta sanar da ranakun karɓar katin zaɓe

    Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta sanar da ranakun da za ta rabar da katinan zaɓe a faɗin ƙasar.

    A wata sanarwa da hukumar ta wallafa shafinta na Tuwita ta ce ta saka ranar Litinin 12 ga watan Disamba zuwa Lahadi 22 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranakun da za ta rabar da katinan zaɓen a ofisoshinta da ke faɗin ƙananan hukumomin ƙasar 774.

    Tuni dai hukumar ta sanar da ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasar tare da na 'yan majalisun dokoki.

    Yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris ɗin 2023.

    View more on twitter
  19. An samu ƙaruwar yaɗuwar kalaman ƙiyayya a Twitter

    Twitter

    Masu rajin hana sanya kalaman ɓatanci da ƙiyayya a shafukan intanet sun ce an samu ƙaruwar irin waɗannan sakonni a shafin Tuwita tun bayan da, Elon Musk ya saye kamfanin.

    Wani rahoton Cibiyar Yaki da Ta'adar ta Intanet, Centre for Countering Digital Hate, ya gano cewa a yanzu ana samun akalla sakonni na cin mutuncin baƙaƙen fata aƙalla sau 4000 a duk rana, kusan ƙarin ninki huɗu tun bayan da kamfanin ya shiga hannun Mista Musk.

    Imran Ahmed shi ne shugaban cibiyar ya kuma ce, ''saboda haka ne muke buƙatar tsarin gaskiya da adalci a waɗannan shafuka domin mu tsayar da ra'ayi a kai.''

    Bayan sanar da wannan sakamako attajirin mai kamfanin Elon Musk, ya wallafa wani saƙo a Twitter da a ciki yake cewa ana samun raguwar ra'ayoyi na sakonnin yaɗa ƙiyayya.

  20. Maraba

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun tashi lafiya.

    Ku ci gaba da kasancewa tare da mu domin kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Haka kuma kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa.