Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai-tsaye karshen rahotannin kenan.

    Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kaimu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kotu a Masar ta yanke wa 'yar Ukraine hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan hodar-ibilis

    Court

    Wata kotu a Masar ta yanke wa wata 'yar Ukraine hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan kama ta da laifin safarar hodar-ibilis a jakarta a Filin Jirgi na Alƙahira.

    Liudmyla Balakina da ke zaune a Netherlands ta amsa cewa wani ɗan Masar ne ya ba ta kwangilar safarar hodar mai nauyin kilo huɗu zuwa cikin ƙasar.

    Za a ƙyale Ms Balakina ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

    A 2019 Masar ta tsaurara hukuncin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa na kisa.

  3. Girgizar ƙarƙashin teku ta afku a kusa da ƙasar Vanuatu

    Vanuatu

    Wata gagarumar girgizar ƙarƙashin teku ta afku a kusa da ƙasar Vanuatu da ke kan tsibiri a yankin Pacific.

    Girgizar mai ƙarfin maki bakwai da ɗigo biyu ta karaɗe tsawon kilomita arba'in yamma da tsibirin Espiritu Santo.

    An ba da gargaɗin afkuwar bala'in tsunami a Vanuatu, da New Caledonia da kuma Tsibirin Solomon, amma daga aka janye gargaɗin.

    Vanuatu na yankin da ake yi wa laƙabi da "zoben Wuta" na Tsibirin Pacific, inda ake yawan samun girgiza da aman wutar duwatsu.

  4. Biden na ziyara a iyakar ƙasar da Mexico karon farko tun hawansa mulki

    Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden na ziyartar iyakar ƙasar da Mexico a jihar Texas karon farko tun hawansa mulki.

    A birnin El Paso, shugaban zai tattauna game da matsalar 'yan ci-rani da masu neman mafaka.

    Wasu daga cikin jami'an tsaron iyakar sun soki Shugaba Biden kan sassauta dokoki masu tsauri da magabacinsa Donald Trump ya saka.

    Kazalika, yunƙurin Biden na bai wa 'yan ci-rani damar shiga Amurka a hukumance zai fuskanci tirjiya a Majalisar Wakilai, saboda yanzu 'yan jam'iyyar Republican ne ke jagorancinta.

    Amurka na son daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da 'yan magaru ke yi daga Mexico.

  5. 'Yan sandan Kano sun kama matashi da zargin kashe uwa da 'yarta

    Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe kishiyar babarsa da 'yarta mai shekara takwas.

    A wata sanarwa da kakakin 'yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a jiya Asabar a Fadama Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo bayan da mahaifin matashin ya dawo ya sami matarsa da 'yarsa cikin jina-jina.

    Sanarwar ta ƙara da cewa bayan da rundunar 'yan sandan jihar ta samu labarin abin da ya faru, nan take ta aika jami'anta zuwa wajen inda bayan an kai matar da kuma 'yarta Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne likita ya tabbatar da rasuwarsu.

    An dai kama wanda ake zargin ne mai suna Gaddafi a wani gida da ba a kammala ba a kokari da yake na tserewa ya bar jihar.

    A binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin kisan inda ya ce ya yi amfani da sukun-direba wajen daɓawa kishiyar babarsa a wuya da kuma kai sannan ta shake 'yarta da ɗankwali har sai da ta daina numfashi.

  6. Ukraine ta musanta iƙirarin Rasha na cewa ta kashe sojojinta guda 600

    Ukraine war

    Ukraine ta musanta ikirarin da Rasha ta yi na cewa ta kashe sojojinta guda 600 a wani hari, inda ta kira hakan da farfaganda.

    Moscow dai ta yi iƙirari ba tare da gabatar da hujjoji ba cewa 'hare-haren makami mai linzami' da ta kai a gabashin birnin Kramatorsk, ya janyo mutuwar sama da dakarun Ukraine 600.

    Ta ce hakan na a matsayin mayar da martani ne kan harin da Ukraine ta kai wani sansanin sojin Rasha tare da kashe gomman sojoji a ranar sabuwar shekara.

    Sai dai dakarun Ukraine sun ce hakan ba gaskiya bane.

  7. Gwamnatin Najeriya ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo bayan harin 'yan bindiga

    Train

    Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe tashar jirgin ƙasa ta Ekehen da ke jihar Edo, sa'o'i kaɗan bayan hari da 'yan bindiga suka kai tare da yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba.

    Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta

    Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba.

    To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan.

    Ya ce 'yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin.

    Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa, inda suka kwashe tsowon watanni a hannun 'yan bindigar.

    Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙasar dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin manyan biranen biyu na kusan sama da wata shida.

  8. 'Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta janye ƙarin kuɗin wutar lantarki'

    Electricity

    Kungiyar kare 'yancin harkokin zamantakewa da na tattalin arziki ta SERAP, ta buƙaci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar janye ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi ba bisa ka'ida ba a watan Disamban 2022.

    Kungiyar ta bukaci shugaban kasar da ya umarci ministan wutar lantarki, Goddy Jedy-Agba da shugaban hukumar kula da hasken wutar lantarki ta Najeriya (NERC), Farfesa James Momoh da su gaggauta janye karin kudin wutar lantarkin.

    A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya bukaci Buhari ya “tabbatar da binciken kashe kuɗaɗen jama’a a matsayin ‘zuba jari da ceto’ da gwamnatocin baya suka yi wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) tun 2005 da kuma gurfanar da wadanda suke da hannu gaban kuliya.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa biyo bayan amincewar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta bayar, an kara kudin wutar lantarki a fadin kamfanin rarraba wutar lantarki na kasar nan a watan Disambar 2022. Wasu kwastomomin da dama sun tabbatar da karin kudin.

    Ministan wutar lantarki da NERC duk sun ki tabbatarwa ko musanta ƙarin kudin.

  9. 'Shiga soja aiki ne na kare ƙasa ba aikin samun kuɗi ba'

    sojoji

    Babban hafsan sojin ƙasa na Najejriya Laftanar Janar Forouk Yahaya ya ce bai kamata a ɗauki aikin soji a matsayin sana'ar samun kuɗi ba kamar sauran sana'o'i.

    Janar Yahaya ya bayyana haka ne bayan da ya ziyarci sansanin tantance sabbin sojojin da rundunar sojin ƙasar za ta ɗauka aiki a cibiyar tantance lafiya da cancantar soji da ke dajin Falgore a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

    Yayin da yake bayyana matsayarsa, babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar ya ce saɓanin sauran sana'o'i, shi aikin soji amsa kira ne domin tsaron ƙasa, dan haka ake buƙatar 'yan ƙasar masu cikakkiyar lafiyar gaɓɓai da ƙwaƙwale tare da fikira.

    Ya ƙara da cewa shiga aikin soji ba sana'a ce ta samun kuɗi ba, a maimakon haka aiki ne na hidimta wa ƙasa, dan haka yake buƙatar sadaukarwa, da jajircewa da kuma juriya, domin kuwa ba aiki ne na gama-garin mutane ba.

    Babban hafsan sojin ƙasan ya shawarci matasan da ake tantancewar da su maida hankali domin kuwa waɗanda suka nuna ƙwazo ne kaɗai za su samu nasarar tsallake matakin tantancewar.

  10. Jamus ta kama ɗan ƙasar Iran kan zargin shirya harin ta'addanci a ƙasar

    harin

    'Yan sanda a Jamus sun kama wani ɗan ƙasar Iran bisa zargin yunƙurin shirya wani harin ta'addanci a ƙasar.

    Mutumin mai shekarar 31 ana zarginsa da amfani da sinadaran makami mai guba domin shirya kai harin kamar yadda sanarwar da 'yan sandan ta fitar ta nuna.

    'Yan sandan sun ce sun kai samame gidan mutumin wanda ke yankin Ruhr, inda suka ce sun samu sinadaran haɗa makamin mai guba.

    Ofishin babban mai gabatar da ƙara na ƙara ya sanar da kama wani daban, wanda ake zargi ɗan uwa ne ga mutumin, kuma ana ci gaba da tsare mutanen biyu.

    A 'yan shekarun baya-bayan nan ƙasar Jamus na yawan fuskantar hare-haren masu iƙirarin jihadi.

    Ko a shekarar 2016 ma wani hari da aka kai wata kasuwa a birnin Berlin ranar bikin Kirsimeti ya yi sanadin kashe mutum 12, tare da jikkata gommai.

  11. 'Yan sanda sun kashe masu safarar makamai biyu a Zamfara

    'yan sanda

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami'anta sun kashe wasu masu safarar makamai biyu a kan hanyar Gummi zuwa Anka.

    Bayan sun yi musayar wuta na kusan sa'o'i da masu safarar makaman, waɗanda ake zargin sun ɗauko makaman tun daga jihar Taraba domin kai su sansanin 'yan ta'adda a Zamfara.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Mohammed Shehu Anipr, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne bayan da jami'an nasu suka samu bayanan sirri game da mutanen waɗanda ke cikin ƙaramar mota ƙirar 'Toyota Corolla' ɗauke da muggan makamai domin kai su sansanin 'yan ta'adda a jihar.

    Bayan musayar wutar 'yan sandan sun kama mutum biyu waɗanda suka ji munanan raunuka yayin da wasu suka tsere da raunkan harbi a jikinsu.

    An kai mutanen biyu asibiti inda daga baya likita ya tabbatar da cewa sun mutu bayan an kwantar da su a asibitin.

    makamai

    Daga cikin abubuwan da 'yan sandan suka ƙwato sun haɗar da ƙaramar mota kirar Toyota Corolla, da harsasan manyan bindigogin harba gurneti uku, da abubuwan fashewa uku, da harsasan bindiga ƙirar AK47 151, da harsasan makamin harbo jirgin sama 200, da wasu layu da guraye.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya sake jadadda burin rundunar na fatattakar 'yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka daga jihar, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

  12. Senegal ta ayyana makokin kwana uku bayan mutum 40 sun mutu a hatsarin mota

    Mucky Sall

    Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ayyana hutun kwana uku a ƙasar domin yin makokin mutum 40 da suka mutu bayan wani mummunan hatsarin mota a ƙasar.

    Hatsarin wanda ya rutsa da manyan motocin ɗaukar fasinja biyu - waɗanda suka yi taho mu gama da asubahin ranar Lahadi - ya yi sanadin mutuwar mutum 40 tare da jikkata wasu gommai.

    Shugaba Mucky Sall ya ce gwamnatin ƙasar za ta yi zaman gaggawa ranar Litinin domin ɗaukar matakan kariya da suka dace, bayan hatsarin wanda ya kasance ɗaya daga cikin munanan hatsarin mota da ƙasar ta taɓa fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

    Haka kuma a wata mai kama da wannan aƙalla mutum 21 ne suka mutu a lokacin da wata motar bas da ke kan hanyarta ta zuwa birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta faɗi jim-kaɗan bayan da ta tsallaka kan iyakar Uganda da Kenya.

    Jami'an yan sanda su ce tsananin gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin.

    'Yan sandan Uganda sun ce an samu fiye da haɗura 100 a cikin kwanaki uku a ƙasar cikin sabuwar shekara, lamarin da a cewarsu ya yi sanadin mutuwar mutum 35.

  13. NDLEA ta kama ƙwayoyi masu yawa a jihohin Najeriya huɗu

    Kwaya

    Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya ta ce ta kama wasu ƙwayoyi masu yawa a jihohin ƙasar huɗu.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita, hukumar ta ce ta kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 3,975kgs da ƙwayar tramadol 58,200.

    A samamen da jami'an hukumar suka kai jihohin Kaduna da Kano da Imo da kuma jihar Legas, ta ce ta kama mutum 11 da take zargi da hannu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Hukumar ta ce mutanen na amfani da dabaru da dama wajen shigar da ƙwaya zuwa Najeriya tare da yunƙurin fitar da ita zuwa ƙasashen waje irin su Birtaniya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yaba wa jami'an hukumar a waɗannan jihohi bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen wannan kame.

    Haka kuma ya yi kira ga sauran jami'an hukumar a faɗin ƙasar da su tashi tseye domin kawar da harƙallar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    View more on twitter
  14. Hikayata: Labarin Jarabta

    A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alkalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo a bana, a yau za mu kawo muku labari mai taken 'Jarabta'.

    Wanda Maryam Ibrahim da ke Rijiyar shehu Sokoto ta rubuta, Umaima sani Abdulmumin kuma ta karanta

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  15. Mutum 19 sun mutu a wani hatsarin mota a China

    China

    Mutum 19 sun mutu, wasu sama 20 suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a lardin Jiangxi da ke gabashin China.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito cewa har yanzu ana kan bincike domin gano cikakken bayani kan musabbabin hatsarin.

    To sai dai hukumomin ƙasar sun gargaɗi direbobin ƙasar da su riƙa tuƙi cikin nutsuwa musamman a lokacin yanayi na hazo

  16. Amsoshin Takardunku

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  17. An kai hari tashar jirgin ƙasa tare da kama fasinjoji a Najeriya

    fasjinjoji

    'Yan bindiga sun kai hari tashar jirgin ƙasa da ke ƙaramar hukumar Igueben a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa.

    Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta

    Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba.

    To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan.

    Ya ce 'yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin.

    Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa, inda suka kwashe tsowon watanni a hannun 'yan bindigar.

    Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙasar dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin manyan biranen biyu na kusan sama da wata shida.

  18. Sojojin Ivory Coast sun koma gida bayan gwamnatin sojin Mali ta sake su

    sojoji

    Ivory Coast ta tarbi sojojinta da aka tsare tsawon wata shida a Mali, lamarin da ya haifar da takun-saƙa tsakanin ƙasashen biyu.

    Jami'an tsaron su 46, sun isa wani filin jirgin sama a Abidjan sanye da kakin soji suna murmushi riƙe da tutar ƙasar.

    Sojojin Mali da ke mulki a ƙasar ne suka yi musu afuwa ranar Juma'ar da ta gabata

    Dakarun dai sun samu tarba ne daga shugaban ƙasar Alassne Ouattara da wasu manyan jami'ai a ƙasar.

  19. China ta ɗage dokokin killace kai kan Korona

    China

    A karon farko cikin shekaru kusan uku, China ta ɗage dokokin killace kai saboda korona ga baƙin da suka isa ƙasar daga wasu kasashen.

    Matakin ya kawo ƙarshen tsare-tsaren gwamnatin China na yaƙi da annobar korona.

    Sai dai rahotonni na cewa har yanzu dokar da ta buƙaci matafiyi ya nuna shaidar ba ya ɗauke da cutar kafin isa ƙasar na nan daram.

    Sauyin na ba-zata da aka ya janyo ƙaruwar mutanen da suka kamu da cutar har wasu ƙasashen suka ƙaƙaba wa matafiya daga China takunkumi.

    China dai ta bayyana matakan da ƙasashen ke ɗauka a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

  20. Marabanku

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da Abdullahi Bello Diginza

    Ku biyo mu don samun labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Afirka da maƙwabtansu.

    Barkanmu da hutun ƙarshen mako.