Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a kowanne lokaci.

    A madadin sauran Abokan Aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai da safe

  2. Faransa za ta kwashe dakarunta daga Burkina Faso

    Faransa ta tabbatar da cewa za ta bi umurnin Burkina Fasso na janye sauran dakarunta daga ƙasar nan da wata guda.

    Sojojin Faransa kusan 400 ne ke ƙasar ƙarƙashin Shirin yaƙi da mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

    Gwamnatin sojin Burkina Fasson ta ce tana son ƙasar ta kare kanta.

    A cikin watani shida da suka gabata ne Faransa ta janye dakarunta daga Mali da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

    Ta kuma kawo ƙarshen shirinta na yaƙi da mayaƙa masu kaifin kishin islama da ake yi wa laƙabi da Barkhan

  3. Majalisar Dattawan Najeriya ta tafi hutun wata guda

    AHMAD LAWAN

    Majalisar dattawan Najeriya ta ɗage zamanta har zuwa wata guda domin bai wa 'yan majalisar damar yin yaƙin neman zaɓe a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    Shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba.

    Sanata Ahmad Lawan ya ce majalisar ta ɗage zamanta daga ranar Laraba domin bai wa 'yan majalisar damar yin yaƙin neman zaɓensu domin sake dawowa majalisar ko kuma taimaka wa jam'iyyunsu domin samun nasara.

    Ya ƙara da cewa “Muna addu'ar Allah ya bai wa waɗanda ke son sake dawowa majalisar dattawan nasara a zaɓen da ke tafe''.

    Haka kuma shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da jami'an tsaro da su tabbatar da cewa an gudanar da sahihi kuma amintaccen zaɓe a ƙasar ba tare da samun tashin hankali ba.

  4. Taliban za ta yi sassauci ga dokar hana mata aiki MDD

    Babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa ƙungiyar Taliban za ta ƙara yin sasauci ga dokar da ta hana mata aiki a ƙungiyoyin agajin ƙasar.

    Martin Griffits ya shaidawa BBC cewa ya samu bayanai masu ƙarfafa gwiwa daga ministocin Taliban

    Ya ce sun fada mini cewa za su fitar da sabbin ƙa'idoji nan ba da jimawa ba waɗanda nake fatan za su taimaka mana wajan sake mayar da mata a bakin aiki.

    Mista Griffit ya ce ayyukan jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan shi ne mafi girma da aka taɓa gudanarwa wanda ya shafi mutane miliyan 28.

    Ya kuma ce domin a iya kai ga kowa ana bukatar mata su shiga ciki.

  5. Dole mu tabbatar cewa muna noma abin da za mu ci har mu fitar waje - Buhari

    Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya umarci shugabannin ƙasashen Afirka da su mayar da hankali wajen ƙara bunƙasa harkokin noma a nahiyar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba Buhari na jawabin ne a taron harkokin noma da shugabannin kasashen Afirka ke halarta a birnin Dakar na ƙasar Senegal.

    Buhari ya yi kira ga takwarorinsa shugabannin ƙasashen Afirka da su rungumi sabbin tsare-tsaren noma domin tabbatar da samar da abincin da zai ciyar da nahiyar har a fitar da shi zuwa ƙasahen ƙetare.

    A yayin da duniya ke fuskantar hauhawar farashin kayan abinci sanadiyyar yaƙin Ukraine, musamman kan alkama da masara, shugaban na Najeriya ya zayyano wasu matakan da ya kamata shugabannin Afirka su ɗauka domin sauya wannan matsala.

    '‘Ciyar da Afirka wajibi ne. ‘‘Dole mu tabbatar da cewa muna ciyar da kanmu a yau da gobe da ma kuma nan gaba. Abin da za mu fara yi shi ne mu haɓaka harkokin noma a ƙasashenmu'', in ji Buhari

    ''Wannan na buƙatar samar wa manoma abubuwan da suke buƙata kamar ingataccen irin shuka da wadataccen takin zamani da sabbin dabarun noma''.

    ‘‘Idan muna son yin nasara dole mu tallafa wa manomanmu, babu shakka akwai buƙatar taimaka wa manoma, amma ya kamata mu yi haka cikin gaskiya, mu cire musu ɗabi'ar neman rance, a maimakon haka mu tallafa wa manoma''.

    ‘‘Ya kamata ƙasashen Afirka su ƙara kauɗi a ɓangaren noma a kasafin kuɗinsu, musamman zuba jari domin samar da abubuwan da ake buƙata kamar haɓaka bincike da samar da abubuwan more rayuwa musamman hanyoyi da noman rani da kuma makamashi'', in ji Buhari.

  6. Rundunar 'yan sandan Zamfara ta kwato makamai daga hannun ɓata-gari

    'yan sanda

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wasu mutum takwas da take zarginsu da alaƙa da 'yan fashin daji, tare da kwato makamai masu yawa.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandar jihar SP Mohammed Shehu ya fitar ya ce rundunar ta samu nasarar kwato bindigogi ƙirar gida 15 da harsasan bindigar AK-47 guda 146, da tabar wiwi, da kuma kuɗi da suka kai naira miliyan ɗaya.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar 'yan sandan jihar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda na jihar CP Kolo Yosuf na ci gaba da samun nasara wajen daƙile munanan laifuka a faɗin jihar.

    'yan sanda

    Rundunar ta ce tun lokacin da ta ƙaddamar da yaƙi da ayyukan 'yan fashin daji a jihar ta samu nasarar kama fiye da mutum 200 da take zargi da alaƙa da ayyukan 'yan fashin daji, tare da ƙwoto makamai da harsasan bindigogi ƙirar AK-47 da na manyan bindigogin RPG, da na GPMG da na harba rokoki, da sauran bindigogi.

    'yan sanda

    Sanarwar ta ce wannan yunƙuri ya taimaka wajen daidaituwar zaman lafiyar jihar wadda a baya ta sha fama da matsalolin tsaro.

    Haka kuma sanarwar ta zayyano wasu nasarori da ta ce ta samu a baya-bayan nan.

    Ciki har da batun kama wasu makamai daga a cikin buhunhuna tsakanin Tsafe zuwa dajin Munhaye, tare da kama mutane da ake zargi da safarar makaman

  7. Ana yi wa zaɓen 2023 zagon ƙasa – Tinubu

    Tinubu

    Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ƙirƙiri batun sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar da batun ƙarancin man fetur domin hana gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe.

    Mista Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar da aka gudanar a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    “Ba sa son zaɓen ya gudana. Suna buƙatar hana gudanar da shi. Shin za ku bar su?”, in ji Tinubu a lokacin da yake tambayar dubban magoya bayansa da suka halarci taron gangamin a filin wasa na MKO Abiola a birnin Abeokuta.

    Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi kira ga 'yan ƙasar za su yi watsi da batun ƙarancin mai, yana mai shawartarsu da su taka ƙafarsu domin jefa ƙuri'arsu a ranar zaɓen.

    Ya ƙara da cewa zaɓen ƙasar da ke tafe zai zama gagarumin sauyi ga ƙasar.

    “Sun fara zuwa da batun cewa ''babu mai''. Kada wannan ya dame ku, idan babu man fetur, za mu je da ƙafarmu domin jefa ƙuri'armu''.

    “Idan kuna so ku ƙara farashin man fetur, ku ɓoye man, ko ku sauya wa takardun kuɗi kala, amma mu za mu ci zaɓe'', in ji Tinubu.

  8. Yara 'yan makaranta takwas sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Ghana

    jiragen ruwa

    Wasu yara 'yan makaranta takwas sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwalensu a tafkin Volta da ke kudu maso gabashin Ghana.

    Yaran sun haɗar da maza biyar da mata uku, waɗanda shekarunsu suka kama daga biyar zuwa 12, sun taso daga ƙauyen Atikagome zuwa garin Wayokope inda makarantar tasu take.

    Hukumomin ƙasar sun ce yaran na daga cikin yara 'yan makaranta 20 da ke cikin kwale-kwalen.

    Hukumar kiyaye aukuwar bala'o'i ta ƙasar ta ce tuni aka tsamo gawarwakin yaran.

    Lamarin dai ya janyo kiraye-kiraye ga gwamnatin ƙasar da ta inganta harkokin ilimi musamman a yankuna karkara.

    A 'yan shekarun baya-bayan nan ana samun yawaitar hatsarin kwale-kwale a ƙasar, lamarin da ake yawan alaƙantawa da ɗaukar fasinjoji fiye da kima, da rashin ingancin kwale-kwalen da kuma samun guma-gumai a cikin ruwan.

    Ko a watan Afrilun shekarar da ta gabata ma mutum bakwai ne suka mutu a wani makamancin wannan hatsari.

  9. Majalisar wakilan Najeriya ta umarci NNPC ya kawo karshen ƙarancin man fetur a ƙasar

    Majalisa

    Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci kamfanin mai na ƙasar NNPC a matsayinsa na wanda ke da alhakin shigar da man fetur ƙasar da ya gaggauta magance matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta a gidajen mai na ƙasar.

    A zamanta na ranar Laraba majalisar wakilan ta buƙaci jami'an tsaro da su banƙado mutanen da ke da hannu wajen haddasa ƙarancin man fetur ɗin a faɗin ƙasar.

    Majalisar ta kuma ɗorawa kwamitocin majalisar da ke da alaƙa da batun alhakin gudanar da bincike game da batun, tare da kai rahoton binciken cikin kwana biyu.

    A 'yan kwanakin nan dai ana fuskantar ƙarancin man fetur a Najeriya, tun bayan da Shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC cewa sun samu umarnin ƙara kuɗin man fetur daga gwamnatin tarayya.

    To sai dai a wata sanarwa da ƙaramin ministan man fetur na ƙasar ya fitar kwana guda bayan sanarwar ta Bashir Danmallam, ya ce gwamnatin Nageriya ba ta yi ƙarin kuɗin man feter ɗin ba.

  10. Ɗaliban Indiya sun fusata bayan hana su kallon wani fim da BBC ta yi kan rayuwar Modi

    Dalibai

    Hankula sun tashi a ɗaya daga cikin manyan jami'o'in Indiya sakamakon haska wani film da BBC ta shirya kan rayuwar Firaministan ƙasar Narendra Modi da rawar da ta taka a tashin hankalin da ya faru a Gujarat a shekarar 2002.

    Ɗaliban na zargin mahukuntan jami'ar Jawaharlal Nehru da ɗauke wuta da gangan tare da katse internet domin dakatar da nuna film ɗin ranar Talata da yamma.

    Kawo yanzu dai mahukuntan jami'ar ba su ce komai ba game da zargin.

    Indiya dai ta ce fim ɗin na BBC ba shi da wata manufa ta gari, dan haka ''farfaganda'' ce kawai

    Dan haka cikin gaggawa ta buƙaci toshe fim ɗin a shafin You Tube da na Tuwita.

    Tun da farko mahukuntan jami'ar ta JNU sun buƙaci ƙungiyar ɗaliban jami'ar da kada su haska fim ɗin, saboda a cewarsu zai janyo ''ruɗani tare da shafar zaman lafiya a harabar jami'ar''.

    Duk da cewa ɗaukewar wutar ta dakatar da haska fim ɗin, shugabannin ɗaliban sun ƙirƙiri adireshin internet (QR codes) tare da raba wa mutane domin kallon fim ɗin a kwamfutoci da wayoyinsu.

    An dai jibje jami'an 'yan sanda a harabar jami'ar. Ma'aikacin BBC na sashen Hindi wanda ke jami'ar ya ce yayin da ɗaliban ke kallon fim din wasu ''gungun mutane'' sun yi ta jifansu da duwatsu. Daliban sun ce sun rubuta ƙorafi zuwa ga 'yan sanda.

  11. Ɗan takarar gwamnan jihar Abia na jam'iyyar PDP ya rasu

    Farfesa Uche Ikonne

    Ɗan takarar gwamnan jihar Abia ƙarƙashin jam'iyyar PDP, farfesa Uche Ikonne ya rasu.

    Ɗan mamacin, Dr Chikeze Uche-Ikonne ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa a yau Laraba.

    Mutuwar tasa dai na zuwa ne kimanin wata guda gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023.

    Bayanin da ɗan mamacin ya fitar na cewa "cikin matuƙar jimami, ina sanar da rasuwar mahaifina, farfesa Eleazar Uchenna Ikonne, wanda ya rasu yau, a babban asibitin ƙasa da ke Abuja."

  12. Yan hamayya na zanga-zanga a Afrika Ta Kudu

    Dubban magoya bayan ‘yan hammaya ne suka yi maci a tsakiyar birnin Johannesburg domin nuna rashin amincewa a kan tababbarewar daukewar wutar lantarki a sasan kasar.

    Masu zanga zangar waɗanda ke riƙe da kwalaye da aka rubuta ya isa na taruwa a hedikwatar jamiyyar ANC mai mulki.

    Kungiyar hammaya ta Democratic Alliance ta ɗora alhakin matsalar rashin wutar lantarkin akan jamiyyar ANC tana zarginta da cin hancin da rashawa.

    Kamfanin makamashi na ƙasar Watau Eskom ya taƙaita samar da wutar lantarki na saoi 10 a kowace rana, lamarin da ke kawo cikas ga tattalin arzikin kasar

  13. Kamaru ta mayar wa Najeriya 'yan gudun hijira 1,300

    bbc

    Gwamnan JIhar Borno Farfesa Babagana Zulum ya karɓi ƙarin gudun hijira 855 karo na biyu, waɗanda Kamaru dake makwaɓtaka ta maida musu.

    An miƙa wa Zulum waɗannan 'yan cirani da hukumomin Kamaru suka dawo da su, wanda gwamnan Arewa mai nisa Minjinyawa Bakari,ya jagoranci maƙawa a Marouwa a ranar Talata.

    Lokacin da yake yi musu bankwana tare da miƙa musu kyautar abinci da wasu kayan, Bakari ya sanar da cewa sun mayarwa da Najeriya 'yan gudun hijira 1,3000 cif-cif.

    A madadin Najeriya Zulum ya karbi waɗannan 'yan gudun hijira ya godewa shugaban Kamaru, tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka riƙe waɗannan mutane kimanin shekara 9 a hannunsu.

    Ka zalika ya yi wa Shugaba Paul Biya godiya na kyautukan da ya rabawa mutanen.

  14. An kashe 'yan Birtaniya a Ukraine yayin aikin agaji

    BBC

    Wasu 'yan Birtaniya Chris Parry da Andrew Bagshaw, waɗanda suka ɓace a gabashin Ukraine, amma iyalansu sun ce an kashe su.

    Mr Bagshaw ma shekara 47da Mr Parry da ke da shekara 28, an musu gani na ƙarshe a ranar 6 ga watan Janairu lokacin da suke tafiya Soledar.

    Iyalansu sun ce mutanen na ƙoƙarin ceto wata dattijuwa ne lokacin da aka kai wa motarsu hari.

    'Yan uwan Mista Parry sun ce mutanen sun mutu ne lokacin da suke yunƙurin ceto wasu mutanen.

    A farkon wannan watan ne sojin haya na Rasha suka ce an cintsi gawar ɗaya daga cikin mutanen.

  15. Zanga-zanga ta hana haska 'Pathan' a garuruwan Indore da Gwalior da Karnataka

    BBC

    An soke haska fim din Shah Rukh Khan da ake kira Patha a garuruwan Indore da Madhya Paradesh.

    Ya kamata a haska wannan fim a birnin Sapna Sangeet wanda mutane ke aka samu damar sayan tikiti ta intanet, sai dai lokacin da mutanen suka je kallon fim ɗin sai suka ci karo da masu zanga-zanga.

    Akwai 'yan sanda jibge a wajen ɗakin kallon amma ba za su iya dakatar da masu zanga-zangar ba.

    Bayan haka ne masu sinimar suka dakatar da haska fim ɗin da safiyar Laraba. Baya ga wannan an samu ɓullar wata zanga-zanga a kan fim ɗin a garin Gwalior.

    Shahrukh Khan ya yi wannan fim ɗin ne bayan shekara huɗu da ya yi nusau a masana'antar.

    An saki fim ɗin Pathan a ranar 25 ga watan Janairun a ɗakunan kallo.

    Mambobin Bajrang Dal masu kishin addinin Hindu ne suka yi zanga-zanga a kan Pathan a wajen sinimar da aka shirya haska shi a Bengaluru

    Sun rika ƙona hoton fim ɗin. Bayan nan, an ƙara wata zanga-zanga irin wannan a Kalburgi, a daren jiya kuma an yi a kofar gidan kallo na Belagavi da ke Karnakata.

  16. Guterres ya nemi Taliban ta kyale yara mata su ci gaba da zuwa makaranta

    BBC

    Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya nemi shugabannin Taliban da su bar yara mata su ci gaba da zuwa makarantu domin neman ilimi a fadin Afghanistan.

    Cikin wani sako da ya aike a jiya Talata, yayin bikin ranar Ilimi ta duniya, Sakataren MDD ya nemi yara su ci gaba da zuwa sakandire da jami'o'i domin ci gaban ƙasar.

    Ya ƙara da cewa, " bayar da damar neman ilimi wani ɓangare ne na 'yan cin ɗan adam, kuma wata dama ce ta haɓɓa girman al'umma da tattalin arziki da kuma samar wa daidaikun mutane aikin yi."

    MDD dai ba ta kallon gwamnatin Taliban a Afghanistan a matsayin halastacciya.

    Mista Guterres ya yi kira ga duniya ta gyara tsarin ilimi domin samar da al'ummar da kowa ke da dama iri guda, a kuma samar da yanayin tattalin arziki da zai yi daidai da yanayin da ake ciki a kowacce kasa domin ci gaban duk wani dalibi a duniya.

  17. Jamus za ta aika wa Ukraine tankunan yaƙi na zamani 14

    JA

    Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai bayyana gaban majalisa a Berlin yau, inda ake sa ran zai aminta da aike wa Ukraine tankunan yaki na zamani.

    Rahotanni sun ce zai ba da damar aikewa da tankunan yakin samfurin Leopard guda goma sha hudu zuwa Kyiv.

    Masana sun ce hakan ka iya bai wa Ukraine wata babbar damar fatattakar sojojin Rasha daga yankunanta.

    Kusan kashi 80 na tankunan zamani a Turai samfarun Leopard Jamus ce kera su, kuma ba bu kasar da za ta iya aikewa da su zuwa wani wuri ba tare da izinin Jamus din ba.

    Sai dai Shugaban Ukraine din Volodomyr Zelensky ya ce yana son a kawo karshen maganar fatar baki kan aike musu da tankunan yaki, su gani a kasa kawai.

  18. Mece ce na'aurar BVAS?

    BVAS

    A wata mai zuwa ne ƴan Najeriya za su je rumfunan zaɓe domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki.

    Wannan zaɓen da ke tafe zai bambanta da sauran na baya sakamakon za a yi amfani da na'urar Bimodal Voter Accreditation System, wanda wata na'ura ce da INEC ta fito da ita a 2021 daƙile maguɗin zaɓe.

    BVAS wata na'ura ce ƴar ƙarama kamar akwati da ke da sikirin wanda ya fi na'urar card reader ta tantance masu jefa ƙuri'a wadda ake amfani da ita a baya.

    Amfanin BVAS shi ne za a iya amfani da na'urar wurin tantance mutum ta ɓangare biyu, za a iya tantance mutum ta zanen yatsunsa ko kuma ta fuskarsa.

    Wannan matakin zai taimaka wurin dakatar da mutane waɗanda ba su da katin zaɓe daga jefa kuri'a

  19. Justin Bieber ya sayar da hakkin mallakar waƙoƙinsa kan dala miliyan 200

    BBC

    Justin Bieber ya sayar da wani bangare na hakkin mallakar waƙoƙinsa ga kamfanin waƙoƙi na Hipgnosis Songs Capital kan kudin dala miliyan 200.

    Yanzu kamfanin ne ke da hakkin mallakar wasu daga cikin waƙoƙin Justin na baya-bayan nan - ciki har da waƙar "Baby" da "Sorry".

    Wannan mataki na nufin kamfanin Hipgnosis zai rika karɓar kudaden sauraren duk wata waƙa da aka saurara a bainar jama'a ta mawakin.

    Kamfanin ke da hakkin wallafa wakokin Justin Bieber da suke faifansa mai dauke da waƙoƙi 290.

    Wannan ya haɗa da suka waƙoƙinsa da mawallafinsa ya saki gabanin ranar 31 ga watan Disambar 2021.

    Babban hakkin mallakar tsarin naɗar waƙoƙin mawaƙin shi ma na cikin wannan tsari.

    Kamfanin Hipgnosis bai bayyana sharudan da aka cimma ba a kwantaragin, amma wata majiya ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa darajar kwantaragin ta kai ta dala miliyan 200.

    Ana samun ƙaruwar mawakan da ke sayar da haƙƙin mallakarsu ga kamfanonin kiɗe-kiɗe - ciki har da Justin Timberlake da Shakira, waɗanda suma suka cimma yarjejeniyar kwantaragi da kamfanin Hipgnosis.

  20. Babu adadin 'yan Najeriya da suka ɓata a hukumance - Sadiya Farouk

    MOH

    Ministar Ma'aikatar jinkai da agajin gaggawa ta Najeriya Sadiya Umar-Farouk, ta ce babu wani takamaiman adadi mutanen da suka ɓata a Najeriya a hukumance, balle a dogara da shi a yi rijista.

    Ta bayyana haka ne a Abuja ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki wanda ma'aikatarta da hadin gwiwar Hukumar Red Cross suka shirta da kuma hukumar kare haƙƙin ɗan adam.

    Sadiya wadda babban sakataren ma'aikatar Dr Nasiru Sani Gwarzo ya wakilta ya ce, a halin da ake ciki yanzu Najeriya ba ta tsari a hukumance domin tunkarar matsalar mutanen da suke ɓata a ƙasar.

    Ta ce gwamnatin tarayya "ta damu kan yadda mutane ke wasa da taruwarsu saboda tafiye-tafiye".

    Tace tafiyar ciranin da 'yan Najeriya ke yi, wadda ke haɗawa har da ƙananan yara domin tsallaka iyakokin kasar, ta sahara da tekun maliya domin samun rayuwa mai kyau a kowacce shekara, tana taimakawa wajen ɓacewar mutane.

    Ta ƙara da cewa:"ƙididdigar da aka fitar da kwanan nan ta nuna cikin mutum 64,000 da suka ɓata a a nahiyar Afrika, 25,000 'yan Najeriya ne, kuma sama da 14,000 yara ne daga ciki."

    Shugaban ICRC a Najeriya Yann Bonzon, ya ce a kalla iyalai 13,000 a Najeriya na neman 'yan uwansu da suka ɓata.